LOKACI CHAPTER 10
by @fulani32
***
⏳🕛 LOKACI 🕛⏳
RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA.
Under Team Yota's Amazing Pen's.
SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️
FULANI ❣️
***
⏳🕛 LOKACI 🕛⏳
PAGE 🔟
"Dallah rufe mana baki, watakam kinga ƴarki ta rasa mashinshini shine zaki liƙawa babanmu ko toh wallahi ƙaryarki ta sha ƙarya". Wata ta katse Mahmah a fusace kamar zata kai mata duka.
"Ke ki kama kanki, duk haukan da zukuyi ya tsaya a iya kaina, amman Wallahi duk wanda ganganci ya saka shi, saka iyayena a ciki sai yayi danasani. Shi uban naku kuje ku tambaye shi idan nace ina sonsa, da bani da niyyar shiga gidanku, amman yanzu naji a raina dole na shiga, zan auri uban naku, nazo nayi takara da iyayen naku, kuma dole ne ku kirani da mama". Ta tari numfashin ta tana nuna su da yatsa.
"Wallahi kuwa kikai wannan gangancin da nima sai na auri ubanki" yarinyar ta bata amsa tana nuna Baffa da yayi ƙasa da kansa tun jin abin da ya kawo su gidan.
Wata ƴar bazawarar dariya Zahra tayi, ta nuna ta "wai da kema baki da auren kike neman ciwa wata mutunci akan bata da shi?".
"Haba yarinya koda me goma ai tafi biyar, kuma da ƙatuwar budurwa ai gwara ƙaramar bazawara". Itama ta bawa Zahran amsa kamar zata daketa.
Rigima ce ta kaure sosai, suke jifanta da mugayen kalamai. duk yanda take ƙokarin basu amsa, sunyi mata yawa, jikinta har rawa yake dan duk abin da ke faruwa da ita ba'a taɓa ci mata mutunci irin wannan ba.
"Ya ishe ku haka malamai, kuzo ku fice ku bar min gida" Mahmah ta katse su a tsawace.
Wata ce tayi kanta kamar mai shirin kai mata duka. Zahra bata yi wata wata ba ta ɗauke ta da mari, tana sakin wani irin huci.
A tare sukayi kanta zasu rufe ta da duka, sai dai wani irin ihu da akayi ya dakatar da su, gaba ɗaya gidan sai da ya amsa da ihun. Duk juyawa sukayi suna kallon me ihun. Salmah ce a tsaye jikinta na rawa sai kace mazari.
Tunda suka zo suka ga gidan a buɗe abin ya basu mamaki hakan yasa tayi saurin shigowa ta bar Inna da Maryam a wajen ta shigo, tana shigowa idonta yayi mata baƙin gani, taji wasu maganganun nasu hakan yasa ta fahimci su wane su.
"Kedai Salamatu anyi mara mutuncin yarinya, shine kika tawo kika barni da biyan kuɗin mota kamar kin bani ajiya"
Shiru tayi tana kallon mutanen gidan sai kuma ta ce "biki ake a gidan habibu ne?"
"Ba biki ake ba Inna ƴaƴan wanda za'a aura wa Aunty Zahra ne" Salmah ta bata amsa, tana cin ɗamara da mayafin jikinta.
"Kuje ku faɗawa shi uban naku ni Fatsima na ce jikata tafi ƙarfin sa" Inna tace tana riƙe ƙuƙu.
"Shikenan kin taimaketa wallahi, ke kuma karkiyi tunanin kin mari banza zamu haɗe koba yanzu ba, ku zo mu wuce" babu wanda yayi ƙoƙarin dakatar da su, har suka fice daga gidan. Maryam ce tabi bayan su ta rufe gidan ta dawo.
Tun kafin su gama ficewa daga gidan, Zahra ta yanke jiki ta faɗi a wajen. Rige rigen yin kanta sukayi suna kiran sunanta. Ita kuwa Mahmah kasa ɗaga ƙafarta tayi a wajen, sai ido da ta zuba mata daga inda take.
Ɗagota Salmah tayi, dake ba wani nauyi gare ta ba sai gashi ta zaunar da ita a jikin ta. "Zuciyata zata fashe Salmah, wani abu ya tokare min a ƙirjina, jina ke kamar numfashi zai ɗauke Salmah". Yanda tayi maganar kamar an shaƙeta. Wani irin marayan kuka Salmah ta saki na tausayin yayarta ta.
"Kiyi kuka big sister nauyin zai tafi" kanta ta girgiza mata alamun bazata iya ba.
"Hafsa da ke da Habibu wallahi duk abinda ya samu Fatsima sai nayi shari'a daku" yanda tayi maganar babu alamun wasa ne yasa suka san dagaske take ba wai wasa ba. Duk shiru suka yi, dan shi Baffa ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige, saboda kunyar Zahra da yake ji.
"Banda ma ku gantalallu ne, Allah ya baku yarinya kamar Fatsima, amman kuyi mishi butulci? Duk ƴaƴan ku akwai yarinya me tausayinta da jin ƙanku kamar tane, akanta aka fara jinkirin aure da zaku sakata a gaba. Badai auren Fatsima kuke son gani ba, ina mai baku tabbacin zaku gani, za kuma kuji kunya dan kaf ƴaƴan ku babu wanda zai samu miji irin nata, ku rubuta ku ajiye zaku ce na faɗa muku" duk shiru sukayi babu wanda yace mata komai. Faɗa take sosai ta inda ta shiga batanan take fita ba, sai da ta gaji dan kanta sannan tayi shiru. Duk ajiyar zuciya suka sauke dan babu wanda faɗan bai shafa ba.
"Hafsah!" Ta kira sunan Mahmah cikin kaushin murya.
"Na'am Inna" ta amsa a hankali dan tana shakkar uwar mijin nata, idan ta birkice.
"Zaki tuna wani lokaci da nake hanaki kuri da cika baki akan auren ƴaƴanki?" Ta tambayeta tana tsare ta da ido.
Shiru tayi ba dan ta rasa abin cewa ba, saidan tasan idan ta ce ɗin wata sabuwar rigimar zata ɓallowa kanta.
"Nasha faɗa miki, tun a wancan lokacin ba'a Allah haka, haka zaki zauna kina sakin maganganu kamar kece kike bawa ƴaƴanki mazajen aure suke yi, bakya jin kunyar kallon idon iyayen yara kice, ke yaranki suna candy kike kai su ɗakin miji, bayan shi Ubangiji ba'a yi mishi haka. Gashinan da ya tashi sai ya jarrabeki, yabarki da babbar ƴarki, tayi candyn amman babu miji, tazo tayi wata makarantar, har ta gama itama babu mijin, tazo ta fara aiki shima babu mijin. Kuma saboda rashin tsoron Allah, sai ki ɗora mata laifin akan itace taƙi aure, kije ki bin ciki kanki, ki nemi yafiyar ubangiji, hakan zai fi miki bawai ki ɗora mata laifi ba, wannan ɗin laifin kine ba nata ba".
Duk shiru sukayi domin duk mai hankali yasan maganar Inna akan gaskiya take.
"Kai kuma habibu" ta ce tana juyowa kan Baffa daya kasa haɗa ido da kowa.
"Nidai nasan ban sallama ka ba, da har zaka bari mace ta ringa juya tunaninka, ka biye mata kuna neman hallaka ƴarku da kanku, wallahi! wallahi!!! Daga yau na ƙara jin anyiwa Fatsima maganar aure, ko kuma ace za'a kawo mata miji sai na ɗaga maka hankali"
"Haba Inna kin saka min iyaye a gaba sai faɗa kike musu, ina ruwanki ne ma" Zahra tayi maganar cikin sanyin murya tana harararta.
Ƙanƙance idanuwanta tayi cike da bala'i ta ce "babu shakka Fatsima ni zaki kuncewa zani a kasuwa dan ina ƙoƙarin ƙwato miki ƴanci ko?"
"Na saka ki ne? Kuma sau nawa zance miki ba sunana Fatsima ba? Idan bazaki ce Fatima ko Zahra ba kiyi shiru da bakin ki, kiyi ta ɓatawa mutum suna haba" tana faɗar haka ta shige ɗaki dan tasan yanzu kuma zata fara wata rigimar, tunda dai ta ƙwaci Mahmah da Baffa a wajenta ai shikenan, ita daman sun saba.
Dariya su Salmah suka saka ganin yanda kuma ta dawo tace, babu ruwanta ko yanzu su Baffa su bada auren Fatsima bazata saka baki.
Da haka Baffa ya samu ya sulale ko gaisawa basuyi ba, ita kuma Mahmah taje ta haɗo mata kayan karin kumallo ta kai mata ɗakin Zahran.
Duk nan suka shige har su Salmah suka saka ta a gaba, yanda bazata samu damar yin wani dogon tunani ba.
Mahmah tunda ta shige ɗaki take kukan baƙin ciki, bana maganganun Inna ba, ko na abin da yaran suka zo har gida suka yi, sai baƙin cikin tasan auren ya rushe kenan har abada, bata san kuma yanzu yaushe wani mijin zai ƙara zuwar mata ba.
Baffa waje ya samu a ƙofar gidan shi, ya zubawa waje ɗaya ido, baya ko ƙiftawa, tabbas lokaci yayi da zai tsaya mata, wannan auren babu shi, koda kuwa mai zai faru, yanzu wannan cin mutuncin da aka zo aka yiwa musu har gida shine ya ja mata, da ace baiyiwa Malam Bala magana ba, babu ta yanda ƴaƴansa, za su zo har cikin gida suyi musu abinda sukayi. Wannan abin ba iya Zahra aka yiwa ba, har su da suke iyayenta, baƙin cikin sa ma shine silar yi mata abinda akayi mata, amman insha Allah lokaci yayi da komai zai zo ƙarshe. Zai gyara kuskuren sa, sannan kuma zaiyi ƙoƙarin dawo da kusancin su daya lalace in sha Allah.
Inna har azahar tana gidan, sosai take kwantar wa da Zahra hankali, duk da rabi faɗa suke yi. Salmah ma na tare da ita tana ta lallaɓata ranar ko wajen aiki bata je ba, tama ɗauki ɗan ƙaramin hutu, sai zuwa monday zata koma dan tana buƙatar nutsuwar zuciya.
Da Inna zata tafi Mahmah tazo mata rakiya, ta kira ta gefe tayi mata nasiha sosai, amman ko alamun shiga jikinta basuyi bare tayi aiki da su, hasalima mugun haushin Innar take ji.
Wajen ƙarfe goma Baffa ya dawo gidan, Salmah ya kira ya bata leda ta kaiwa Zahra, duk da bata san menene ba godiya tayi mishi ta wuce ta tafi.
Ɗaki ya shiga da sallama, amman Mahmah bata amsa masa ba. Zama yayi a kusa da ita "wanene ya taɓa min Hafsatuna" yace yana riƙe hannunta.
"Habib ina fatan dai ɗaurin auren nan yananan a goben ba'a janyesa ba" ta tambaye sa cikin wani irin yanayi. "Babu wannan auren Mahmah nama same sa, munyi magana, shiyasa kika ga na kai dare da yawa, an soke shi, muyi fatan Allah ya kawo mata nata zaɓin na alkhairi a duk inda yake nan kusa".
Zare hannunta tayi, ta fashe da kuka, kamar ƙaramar yarinya. Rarrashin ta yayi tayi, amman babu alamar zata yi shiru, ƙarshe dole ya haƙura ya ƙyaleta, ganin bata da niyyar kawo mishi abinci ne, ya buɗe ledar daya shigo da ita, yaci abinda ya siyo musu, bayan ya gama wanka yayi tare da shirin kwanciya ya bata baya.
Dare mahutar bawa, amman banda Zahra wani irin ƙunci take ci, ta rasa abinda yake mata daɗi gaba ɗaya, kamata yayi ace tayi farin ciki da fasa auren da akayi, amma ta rasa gane a wane yanayi take ciki gaba ɗaya, gajiya tayi da tunani ta tashi tayi alwala ta fara kaiwa Allah kukanta.
Wannan kenan...
★★★★
Ta jima a zaune a wajen daya barta, can ta tashi ta cire kayanta ta lallaɓa tayi wanka, kwanciya tayi dan tayi sallah tun a gida. "Masoyiya har kin kwanta? Tashi na samo miki kaza me zafi kici" ya ce yana ƙoƙarin ɗagota.
"Ka ƙyaleni Auwal, ka fita daga harkata, kar kayi tunanin dan nadawo zamane ya dawo dani, a'a in har kayi wannan tunanin wallahi kayi ganganci, inanan zanci gaba da kai ƙarar ka wajen Allah, da roƙonsa akan ya kawo min ƙarshen wannan ƙaddararren auren naka". Duk da yanda gabanta yake faɗuwa haka ta rufe ido tana faɗa masa abinda yake a ciki ranta.
"Kar ki wani damu masoyiya wannan ƙaddararren auren, yanzu ne ma kika fara zama a cikinsa" ya bata amsa yana shafa wuyanta.
Doke hannunsa tayi tana harararsa ta juya ta kwanta, shima kwanciya yayi a bayanta yana janyo ta jikinsa. "Auwal ka rabu dani dan Allah, ka kusa illatani yanzu kuma me kake buƙata?" Murmushi yayi na tura takaici a kunnenta ya ce "ke nake buƙata masoyiya, illatawa kuma tunda banyi ba adena maganarta"
Kukan takaici ne yake son ƙwace mata amman kuma tayi wa kanta alƙawarin bazata ƙara barin Auwal yaga hawayenta ba. Jin abin da yake mata ne yasa tasa ɗan ƙarfin da ya rage mata ta turesa. "Bakaji me na ce maka na bugu a ƙuguna taya kake tunanin zan iya yin wani abu"
"Zaki iya fa masoyiya, ai kin zama jaruma, hakan ba wani abu bane, ciwo kuma ai ba'a jikina yake ba, idan ba kya buƙata kizo kiyi min abinda zan samu nutsuwa, idan ba haka ba, kuma na turmushe ki, babu yanda zaki iya, iyakaci a zo daga gidanku a kaiki wajen gyara, daganan kuma dole a dawo min dake ina daga kwance, daga ƙarshe ma har da tukwuicin bada haƙuri zan samu".
Batasan kuka take ba sai da taji yana share mata hawayen nata.
"Auwal dan darajar manzan Allah ka sakeni"
Ya ce "bazan iya sakin ki ba Ummul khairi, babu saki a aurena dake, bar wannan maganar ma dai yanzu muyi magana akan abinda nake buƙata, ya kamata ma duk ki bar wannan tunanin ki fara tunanin fansar da zan ɗauka akanki, dan kinsan yayyanki basu daki banza ba"
Cikin muryar kuka ta ce "Allah ya fika".
Sanin zai iya illata ta bashi da asara, kuma maganar da yayi gaskiya ce, dan za'a dawo mishi da ita, dole tayi mishi abinda yake so tana kuka shi kuma yana jin daɗi.
Gaba ɗaya Auwal ya canza yanayin zaman su, ta ruwan sanyi yake gasata yan da yake so gaba ɗaya ta fige ta lalace, ta fita daga hayyacinta, dan a yanzu abun yafi damunta akan a da can baya, yanzu bata da wani buri da ya wuce saketa, shi kuma yace baisan zance ba.
Suna a cikin wannan yanayin ne ta fara wata iriyar rashin lafiya mai zafi, duk rashin imanin sa, hakan bai hana shi jin tausayinta ba, yana tausaya mata dan tana shan baƙar wahala, babu abinda take iya ci ya zauna a cikinta, ga rashin lafiya ga damuwa duk sai tabi ta fita daga hayyacinta gaba ɗaya.
Yau tun da ya shigo taga yana haɗa hanya, tasan ba'a hayyacinsa yake ba, dan haka ta kama kanta a waje ɗaya, ko motsin kirki ta kasa dan ma kar hankalinsa ya dawo kanta.
Tana kwance taji ya faɗo kanta, warin sigari da sholisho ne suka bugi hancinta, take wani irin amai ya ƙwace mata a jikinsa.
"Keee ni kike wa amai dan uban ki" yace cikin muryar maye yana shirin kai mata duka.
Ƙoƙarin ture shi take, dan ji take tamkar numfashinta zai ɗauke amman ta kasa, jin yana yin ƙasa da belt ɗin wandonsa, take hankalinta yayi mummunan tashi. "A'a Auwal bazan iya ba" shine abin da ta iya furta masa, numfashinta na ƙoƙarin ɗaukewa a ƙirjinta.
Bai bi ta kanta ba yayi abinda zuciyarsa take raya, zuwa lokacin ko numfashi bata iyayi. Yana tashi daga kanta, ya yanke jiki ya faɗi akanta, kansa ya bugu akan mararta, a take jini ya ɓalle mata daga ƙasanta........
YANZU NE ZAMU SHIGA CIKIN LABARIN *LOKACI* INA FATAN ZAKU KASANCE DA ALƘALAMIN ƳAR GIDAN BABA ACHADU🙌🏻
FULANI
***