Chapter 33
*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
NACINA YA JAWO MINI...
033
Suna isowa wurin kamar ance Sa'eeda ta kalli gefan Sauban,karaf! Kamar magnet haka idanunsu ya sarƙafe,lokaci guda gaban Sa'eeda ya bada Dummmmm! Cikin rawar murya Sa'eeda tace
"Mai idona yake ganemin kamar Sauban"
Mijinta ƙadai yaji mai ta ce saboda bada ƙarfi tayi maganar ba,da sauri Sadam ya kalleta alamun tambaya kashe masa ido tayi da cewa
"Zaka ji komai da zarar mun koma gidan da yardar Allah"
"Ok"
Duk wannan tattaunawar da sukeyi babu wanda a cikin ma'aikanta yaji mai suka cewa illa nuna Sauban da Sa'eeda tayi wanda koshi kansa Sauban ɗin bai san mai ta ce ba,Sauban kuwa tuni ya jiƙe da gumi tsabar ruɗu saboda abin yazo masa a bazata,taya hakan ta faru? How? When? Sauban da sauran ma'aikatan suka gaishe dasu cike da girmamawa shi Sauban Mai gidansa kadai ya gaisar tare dayi masa Allah ya sanya alkhairi,ganin Sauban bai gaida Sa'eeda ba yasa Sadam ya ce masa cikin cool deep voice ɗinsa
"Idanunka basu ga Madam bane,kowa ya gaisheta amma kai baka gaisheta ba"
Ras! Ƙirjin Sauban ya bada a zuciyarsa yana cewa 'What! in gaishe da Sa'eeda wacca nayi soyayya da ita a baya,a gaskiya girmana ya faɗi idan na gaidat....' Katse mishi tunani Sadam yayi da cewa
"Manager naji kayi shiru what's going on in your brain"
Firgigit kamar wanda aka tsikara Sauban ya dawo cikin hayyacinsa tare da gaisheta duk da zuciyarsa ta ƙyamaci yin hakan amma ya zaiyi tunda matar mai gidansa ce,cikin girmamawan dole ya ce
"Sannu da zuwa Madam,fatan kunzo lafiya"
Wani irin ɗauke kai Sa'eeda tayi kamar bata ji gaisuwan da Sauban yayi mata ba,kuma sarai taji sa amsar ne bayi niyyar basa ba,Mukhtar ne yace ma Sauban
"Manager, Madam bata ji mai kace ba"
Wani tuƙuƙin baƙin ciki ne ya tasoma Sauban tare da zuwa masa daidai wurin *tantani-maƙwallatonsa* ya tsaya cak! Wallahi ko rantsuwa yayi ba zaiyi kaffara ba Sa'eeda taji mai ya ce,kawai dai wulaƙanci take so tayi masa shiyasa taƙi amsa gaisuwarsa,cike da takaici haɗi da ɓacin rai Sauban ya sake gaidata da cewa
"Sannu da zuwa Madam, fatan kun zo lafiya"
"Lafiya"
Ciki-ciki tayi maganar wanda ƙalilan ne a cikin ma'aikatan suka ji mai ta ce,Mukhtar ne ya ce ma Sauban su kaisu ko'ina na kamfanin saboda Madam Sa'eeda ta gani,babu musu ya musu jagora sauran ma'aikatan suka biyo bayan su Sadam suna take musu baya.Haka Sauban yaje dasu ko'ina na kamfanin tare dayi musu bayanin ɓangarorin kamfanin, bayan ya kammala bayani ne sai suka ɗunguma zuwa babban hall na kamfanin wanda ake meeting a cikinsa,daman tuni an gyara ko'ina,har kayan ciye-ciye an kawo saboda wata ƙwarya-ƙwaryar walima za'ayi duk da basu san maƙasudin taron ba,har Mukhtar bai san me Uban gidan nasa zai faɗa a meeting ɗin ba,bayan kowa ya samu wuri ya zauna,Sadam da Sa'eeda suna a high table,Manager Sauban da sauran manyan ma'aikatan kamfanin suna a side tables,sauran ma'aikata da wasu securities haɗi da cleaners suna a kujeru.Mukhtar ne ya miƙe tare da cewa
"Assalamu Alaikum ƴan Uwa na wannan Kamfanin mai akbarkha"
Amsa masa sallamar sukayi sai ya cigaba da cewa
"Ina muku fatan alkhairi sannan Mai gidanmu,Sadaukin Uba,mai sharai kukanmu,CEO Alhaji Sadam Dauda Ghali Mai Nasara zai yi magana yanzu,don haka kowa ya kasa kunnansa dakyau wurin sauraron wani alkhairi yazo mana dashi"
Mic ɗin ya miƙa ma Sadam cike da ladabi haɗi da ƙanƙan da kai,amsa yayi sannan ya miƙe zuwa inda aka tanardar doyin magana,cike da izza ya taka zuwa wurin,cikin cool deep voice ɗinsa ya fara magana da cewa
"Assalamu Alaikum"
Amsa masa sukayi sannan ya cigaba da cewa
"Bazan ɗau lokaci ina magana ba,saidai zan je kai tsaye akan maƙasudin taruwanmu a nan,haƙiƙa inajin daɗin yadda kuke tafiyar da Kamfanin nan mai albarkha,so yau nake ƙara muku wani albishir da Sabuwar *CEO* ɗinku wacca zata cigaba da jan ragamar wannan Kamfanin mai albarkha,My Darling Star Sa'eeda Sulaiman,na tabbata zaku ji daɗin kasancewarta a matsayin *CEO* na wannan Kamfani,sannan kar kuga ita mace ce kuma tanada rauni ku kawo mata raini,idan na samu ɗaya a cikinku yana handama da babakere a wannan Kamfanin to ya tabbata lokacin barinsa wannan Kamfanin yayi,domin duk tsare-tsaran da nayi a baya dasu za'a cigaba da bi sannan zan dinga bibiyar komai na wannan Kamfanin,Fatan zakuyi maraba da Princess ɗina Sa'eeda,My Darling Star zo ki gabatar da kanki"
Murmushi ta sakar masa mai sanyaya zuciya,shima ya mayar mata da martanin murmushi,ma'aikata dai suna ganin ikon Allah,soyayya a bayyane babu ko sakayawa,Sauban tunda yaji Sa'eeda ce yanzu mai kamfanin ya kuma rasa natsuwarsa,ƙirjinsa sai dukan uku-uku yake,ga wani irin gumi na tsattsago masa a duk ilahirin jikinsa,komai ganinsa yake a bibbiyu,ga kansa na wani irin sara masa,koda Sa'eeda tazo zata gabatar da kanta miƙewa yayi tare da barin hall ɗin gaba ɗaya saboda zuciyar bazata iya ɗaukar wannan tashin hankalin ba,assistant manager ne ya biyosa yana tambayar ko lafiya, girgiza masa kai kawai yake domin bakin yayi nauyin da bazai iya furta komai ba a yan,zuciyarsa na ƙara masa zafi kamar *garwashin wuta* ,gashi yanzu daya ga Sa'eeda sai ya sake fama mikinsa,domin wata iriyar zazzafar soyayyar Sa'eeda ta taso masa wanda ma tafi na da,assistant manager ya shiga ruɗu ganinsa a haka,sai ƙara tambayarsa yake ko baida lafiya ne ya kaisa asibiti,a nan ba girgiza masa kai yayi da a'a,sai kawai ya masa alamar ya koma ciki,babu yadda assistant manager ya iya haka ya koma cikin hall ɗin.Wurin parking ɗin motoci ya je tare da shiga motarsa,zama yayi yana ɗora kansa a sitiyarin motar,abin duniya duk ya ishesa,komai ya tsaya masa cak! Ƙwaƙwalwarsa ta daina basa haɗin kai,ya rasa ina zai je yaji daɗi hankalinsa ya kwanta,idan ya je gida wani sabon tashin hankali ne domin ganin Maryam kawai zai ƙara saka shi wata sabowar damuwa domin ita ce silar rushewar farin cikinsa,da yanzu ya auri Sa'eeda mai hankali da natsuwa yanzu kuma tayi mishi nisa,fita yayi daga duniyarmu zuwa duniyar tunani tare da nemoma kansa mafita,yana a wannan yanayin sai can zuciyarsa ta ambata masa *Captain Fu'ad* tabbas! Wurinsa kaɗai ne zai je ya samu kwanciyar hankali da natsuwa,inda tun farko yabi shawararsa da bai samu kansa cikin tashin hankali da damuwa ba,jikinsa na rawa haka ya ciro wayarsa daga aljihunsa,scrolling contacts ɗinsa yayi har ya samo numban Captain Fu'ad kasancewar sun kwana biyu rabon da suyi waya,dailing numban yayi tare da karata a kunnansa,ringing ɗaya-biyu a na ukun yayi picking tare da sallama yana cewa
"Wata sabon gani angon Maryam da Khairat"
Bai bi takan zolayarsa ba ya ce
"Kana Kaduna ne"
"Eh jiya na dawo Lafiya naji muryarka sai a hankula"
Sauban saida yaja wani dogon numfashi tare da furzarwa sannan ya ce
"Ina fa lafiya Fu'ad komai na duniyar nan juyamin yake,a bibbiyu nake kallon komai,gani ni nan zuwa yanzu"
"Subhanallahi Sauban meke faruwa ne"
"Fu'ad komai ma ya faru,komai ya faru Fu'ad na shiga uku na lalace,everything is turning upside down,yanzu zan zo"
"A'a bara nazo na ɗaukeka yanzu,tunda baka cikin yanayin tuƙi"
"No karka damu zanzo yanzu in shaa Allah"
Katse kiran yayi tare da murza key ɗin motar,da sauri ya finciki motar kamar ita tayi masa laifin, mai gadi da sauri ya buɗe masa gate ganin yadda ya danno motar da gudu,Allah yasa mai gadin yayi saurin buɗe gate da ina tunanin ta saman gate ɗin zaibi.(O'ohhh su Sauban hankali ya tashi😂😂😂)
Gudu yake sosai a saman titi,mutane sai kallon motar suke ganin yadda mai motar yake sharar gudu kamar don shi kaɗai akayi titin,nan da nan ya iso layinsu Captain Fu'ad kasancewar shima yayi aure bayan Sauban ya auri Maryam har ma matarsa ta haihu,ta haifi ɗiya mace mai suna Faɗima amma ana kiranta da Zahra.Tun kafin Sauban yazo gidan Fa'ud yake danna horn a jejjere,wasu masu gadin gidajen layin sai faman buɗe gates suke a tunaninsu ko gidansu ne,a haka ya isa gidan Fu'ad yana danna horn,da sauri mai gadinsa ya buɗe masa gate,ai kamar jira Sauban yake,da gudu ya danno motar cikin gidan har zuwa parking load ko kashe motar baiyi ba ya sauka tare da sassarfa zuwa falon gidan,koda yazo cikin falon ya tarar da Fu'ad a tsaye yana kai-kawo,zubewa yayi a saman kujerar falon kamar wani mara lafiya,da sauri Fu'ad yazo wurinsa tare da cewa
"Sauban what's going on,meke faruwa ne don Allah,na kasa natsuwa tunda ka kirani"
Bai amsa masa tambayarsa ba,saidai ya fara nuna bakinsa da hannu,yana cewa cikin muryarsa wacca bata fita sosai
"Rrruwa Fu'ad, ruwa zzzan shaaa"
Ai da sauri Fu'ad yazo ɗauko masa ruwa a fridge masu sanyi har gora biyu,jikinsa na rawa ya amsa tare da buɗe marfin,kwankwaɗa ya fara yi ji kake Ƙwat! Ƙwat! Ƙwat! Saida ya shanye ruwan gorunan nan guda biyu tare da sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya.Fu'ad dai na kallonsa bai ce dashi komai ba yana jira natsuwarsa ta dawo masa kafin ya ƙara tambayarsa,Saida yakai kusan mintuna biyar a haka bai ce komai ba kansa na jingi ne a bisa kujera.Ganin hankalinsa ya dawo masa Captain Fu'ad ya ƙara tambayarsa da cewa
"Meke faruwa ne Sauban"
Shiru yayi bai bashi amsa ba saima sauke ajiyar zuciya da yake akai-akai sai can ya fara magana cikin kasalalliyar muryarsa da cewa
"Fu'ad komai ma ya faru,idan nace komai to komai nake nufi"
"Sauban ka fito fili kamin bayani ta yadda zan fahimceka,you are talking to me in a passive way how did you expect me to understand you and your problems Sauban"
Hannunsa yasa tare da yamutsa dumar kansa,da wani irin ƙarfi ya buga hannunsa a saman kujerar tare da cewa
"Ya Salam,na shiga uku ni Sauban wai kasan wace ce *CEO* ɗinmu ya aure"
Da sauri Fu'ad ya girgiza masa kai,cigaba da magana Sauban yayi da cewa
"My Ex girlfriend ya aura *SA'EEDA* "
Da sauri Captain Fu'ad ya mike tare da cewa
"What!!!! Sa'eedan da na sani budurwarka ya aura,how comes that happen,Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un! Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un! Tabbas! dole ka shiga ruɗu hadi da tashin hankali Sauban"
"Hmmmm Fu'ad kenan don ya aureta bashi ne tashin hankalina ba ko kuma matsalata ba,kasan mece ce babbar matsalar a yanzu? "
Girgiza masa kai Fu'ad yayi da cewa
"A'a Sauban"
Saida Sauban ya ɗan nisa sannan ya ce
"A yau ɗin nan *CEO* ɗina ya mallakama Sa'eeda Kamfanin da nake aiki a ciki *Halak malak* a gaban kowa"
" Meneeeeeee??????? You mean the whole of that your big and famous company belongs to her now!!! "
"Sosai ma kuwa,hmmm wai kasan a gaban kowa yake nuna mata *tsantsan soyayyar* da yake mata kuws,suna sakarma junansu murmushi kowa yana gani ba tare da jin kunyar kowa ba"
Shiru Fu'ad yayi yana tunani hadi da nazari,sai can ya kalli Sauban tare da cewa
"Kayya Sauban,kaga irin wannan ranar na gujan maka a baya,amma ka kasa fahimtana ,naso kayi haƙuri ka auri Sa'eeda saboda duk inda mace take to tabbas Sa'eeda takai amma sai kayi watsi hadi da fatali da shawarata,to yanzu fa! wa gari ya waya? Kai! Sauban,sakayyarta ce ta tabbata akanka gaida Maryam, ka manta rashin zaman lafiyarku tare da matsalolin da kuka samu kaida Maryam a zaman auranku har zuws yanzu,hmmm wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba *Alhakin* Sa'eeda ne ya kama ku tare dayi muku talala ta yadda bazaku taɓa kwancewa ba,ƙarin daɗi sai ya ƙara ɗaukakata a samanku musamman ba kai Sauban domin babu abinda yafi tashin hankali haɗi da ruɗu ace *Budurwarka wacca ka yaudara a baya,ta zamo mai gidanka kuma mai faɗa aji a kamfanin da kake aiki* mai yafi wannan ƙasƙanci tare da tozarci,a gaskiya bazan ɓoye maka ba alhakin Sa'eeda ne ke ɗawainiya dakai har da Maryam,domin kun cutar da Sa'eeda,kun yaudareta,kun saka cikin matsananciyar damuwa,kun ci amanarta kai da Maryam, to taya Allah zai barku Sauban!,kasani Allah baya bacci sannan baya yafe hakƙin wani akan na wani,har ila yau baya barin addu'ar wanda aka cutar ta tafi a banza,babu shamaki ga adduar wanda aka zalunta,Allah yayi ikonsa a kanku kaida Maryam"
Shiru Sauban da yayi yana sauraron Fu'ad, ko motsin kirki ya gagari yinsa,domin sai yanzu ya ƙara tabbatar da alhakin Sa'eeda ne ke bibiyarsu hadi da ɗawainiya dasu shida Maryam,shiyasa tunda sukayi aure sun kasa samun zan lafiya kullum ciki rigima suke,ashe-ashe sun dade da *barin gini tun ranar zane* tabbas! Sunyi kuskure,kuskuran ma mai girman gaske gashi Allah ya saka mata akansu tun kan a ɗauki shekaru masu yawa.Sauke ajiyar zuciya Sauban yayi sannan ya ce
"Fu'ad tabbas! Munyi kuskure ni da Maryam domin sai yanzu na ƙara tabbatar da alhakin Sa'eeda ne ke bibiyarmu tun sanda mukayi aure,har yau ɗin nan da Ubangiji ya ƙara ikonsa a kaina,tabbas! munyi kuskure,Allah mun tuba ka yafe mana"
"Sauban mafitarku a yanzu ɗaya ce idan kuna son rabauta sannan ku samu kwanciyar hankali"
"Mece ce mafitar Fu'ad"
"Dole kaida Maryam ku je ku roƙi gafarar Sa'eeda, domin idan bata yafe muku wallahi wallahi wallahi haka zaku dawwama Allah yana ikonsa akanku,amma idan kuka nemi yafiyarta to na tabbata *Allahu Gafurun Rahim ne* zai yafe muku in har ta yafe muku,sannan kuga canji a rayuwarku"
"Hmmmm hakane Fu'ad in shaa Allah hakan za muyi nida Maryam har gidanta zamu je da yardar Allah"
"Kaga yanzu sai ya zamo maka ishara,idan kaga wani zaiyi kurkure irin makamancin naka zakayi saurin nosar dashi akan illar hakan"
"Tabbas! Kuwa Fu'ad ai ni yanzu malami ne babba a wannan ɓangaren"
"Allah kasa mu dace"
"Ameen ya Rahman, bara na wuce gida na ɗauki Maryam zuwa gidansu yanzu"
Dariya Fu'ad yayi da cewa
"Sauban! Sauban! Sauban! Miye na gaggawa,what are you eating while na baka is falling down,ka bari zuwa gobe ku tafi la'alla yau idan kun je bazaku samesu ba tunda a Kamfani ka barsu"
"Eh kuma fa hakane,wallahi bazaka gane bane Fu'ad duk na ƙagara naga na sauke wannan nauyin ko zan samu natsuwa a zuciyata"
"Yawwa,Allah ya ɗoraka akanta,yasa ta yafe muku,Allah ya shiga lamarinku baki ɗaya"
"Ameen Ameen ya Jabbar"
Sun ɗanyi hira sannan ya ɗauki motarsa ya nufi gidan domin a yadda yake bazai iya komawa wani kamfani ba,a haka ya iso gidan.Direct ya wuce ɗakin Maryam domin tattaunar wannan batun,a lokacin Maryam na zaune ta saka plate agaba tana cin kallalabar da Khairat ta soya mata,don yanzu ba komai take iya ci ba,ga cikin nata mai shegen kwaɗayi ne da yawan sakata amai duk tabi ta rame.Da sallama ya shigo ɗakin,ɗagowa tayi tare da amsa masa sallamar sannan ta cigaba da cin kallalaɓarta,wuri ya samu kusa da ita ya zauna sannan ya ce
"Maryam ajiye plate ɗin nan a gefe,magana ce nazo da ita muhimmiya wacca tashemu baki ɗaya"
Jin ya ce maganar mai muhimmanci ce kuma tashafesu baki ɗaya ya sakata ajiye plate ɗin a gefe tare da maida hankalinta kacokar! Gunsa tana cewa
"Ina jinka Sauban"
Saida ya ɗan nisa sannan ya fara magana
"Maryam munyi kuskure babba a rayuwarmu,kuskuran shi ne ya hanamu zaman lafiya da natsuwa a gidan nan,shi ya hanamu samun damar fahimtar junarmu har yanzu"
Shiru Maryam tayi tana nazarin wani kuskure ne haka babba da ya hana duk wa'innan abubuwan da ya lissafa,can ta ce
"Wani kurkure ne haka Sauban da ya hanamu duk wa'innan abubuwan daka lissafa"
Dafe kansa yayi domin har yanzu sara masa yake,kallonta ya ɗanyi na ƴan wasu sakwanni kafin ya ce
"Maryam munci amanar Sa'eeda! Mun mata zambo cikin aminci! Mun karya mata zuciya a lokacin da ta yarda damu! Mun wofantar da yarda da amintuwar da tayi damu! Maryam alhakinta ne yake bibiyar rayuwarmu tun bayan auranmu,ya hana mu duk abubuwan da na lissafa miki a baya,kinsan duk wa'innan abubuwan basu ne matsalarmu a yanxu ba! "
Tun lokacin da ya fara magana idanunta na kallon bakinsa ko ƙiftawa batayi,ƙwaƙwalwarta na ƙara faɗaɗa mata maganarsa tare da taimaka mata wurin yin analysis ɗin maganar, a zuciyarta take cewa 'Ashe bani kaɗai nake wannan tunanin ba harda kai,domin kafin muyi aure muna soyayyar mu mai tsafta amma daga auran mu shikenan soyayyar mu ta koma ƙiyayya,kamar kowa na kallon hanjin ɗan uwansa,bama zama wuri ɗaya ba tare da yin faɗa ba...' Katse mata tunani yayi da cewa
"Kinyi shiru ko jikin ne"
Firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lula tana cewa
"Nima tunanin nan nake kwana nake tashi dashi,yanzu wani matsala ne haka wanda yafi wa'incan"
"Na tuna da maganar Sa'eeda da kacemin a lokacin da nazo ɗaukarki daga school kina amarya ta ce min "In shaa Allah sai Ubangiji ya ɗaukakata sama damu sannan zamu zo da kafafunmu muna roƙonta yafiyar abinda muka aikata mata* hmmm Maryam could imagine Mai gidana *Alhaji Sadam Dauda Ghali Mai Nasara* Sa'eeda ta aura"
"What!!! Mai gidanka Sa'eeda ta aura!!! How will that on earth happen!!! When? How? Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!! Ni Maryam na shiga uku!!! Sauban!!! Sauban!!! Yanzu Sa'eeda mai gidanka ta aura!!! "
"Hmmm duk wannan ba shi ne matsalar ba kuma hakan mai dameni ba"
"Sauban kana nufin wannan ba shi ne matsalar ba? To mece ce matsalar!!! Yau manga takanmu ni Maryamu"
Saida yaɗan nisa sannan ya ce
"A yau Mai gidana kuma mijinta ya mallaka mata Kamfanin da nake aiki,daga yanzu Sa'eeda zata zama *CEO* din kamfaninmu"
Dafe ƙirji Maryam tayi tare da waro idanunta waje tana cewa
"Ya mallaka mata Kamfanin da kake aiki!!! Shikenan ni Maryam maganarta ta tabbata akanmu,bakin da tayi mana a baya ya kamamu!!! Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!! Yanzu ta ɗaukaka sama damu!!! Allah! Allah! Allah! Mun tuba ka yafe mana! Wayyo Allah! Tabbas! Zama bai gammu ba dole muje mu roƙi gafararta koma samu sassauci a zukatanmu"
"Hakan za'ayi zuwa gobe in shaa Allah, saidai bansan ina suke da zama ba"
"Ummm bara na tambayi aminiyarta Iman saita bamu address ɗin gidanta"
"Fine,Allah ya kaimu"
Mikewa yayi sannan yabar ɗakin zuwa ɗakin Khairat.
Washe gari da ƙarfe 11:20am na safe suka nufi gidan Sa'eeda a Miloniyan City ta address ɗin da Iman ta turoma Maryam bayan tasha tambayoyi kafin ta bata don tabbatar da ba cutar da Sa'eedar zasuyi ba.Har gidan suka iso da taimakon address ɗin,fitowa sukayi tare da bin ilahirin gidan da kallo saboda tsarin gidan baiyi kama da gidajen da ake ginawa a Nigeria ba,idan kaga gidan zakayi tunanin a Dubai gidan yake saboda haɗuwarsa,ƙwanƙwasa ƙofar gate din sukayi tare da jiran a buɗe musu,mai gadin ne ya buɗe ƙofar yana kallonsu sama da ƙasa tare da tambayar meke tafe dasu.Maryam ce tace
"Wurin Sa'eeda mukazo"
Daka mata tsawa mai gadin yayi da cewa
"Gyara kalamanki yarinya!!! *Ruwa ba sa'ar kwando bane!!!* Hajiya Sa'eeda zaki ce ba Sa'eeda ba"
Haƙiƙa taji tsawar nan har cikin kwanyar kanta,shiru kawai tayi bata iya bashi amsa ba,Sauban ne ya ce
"Ayi mana afuwa wurin Hajiya Sa'eeda mukazo ka ce mata Sauban ne da Maryam matarsa"
Bai bashi amsa ba ya rufo ƙofar tare da tafiya zuwa ƙofar falon,danna alarm yayi sannan ya jira,kasancewar dukkaninsu suna falon bayan sun kammala break fast suna wasanninsu na ma'aurata sukaji ƙarar alarm ɗin,tsaki Sadam yayi irin za'a katse musu jin daɗinsu,miƙewa yayi zuwa ƙofar tare da buɗewa,cikin ɓacin rai ya ce
"Lafiya"
Cike da girmamawa mai gadin ya ce
"Ranka shi daɗe wasu ɓaki Hajiya Sa'eeda tayi a waje,sunce ince mata Sauban ne da Maryam matarsa"
Ras! Ƙirjin Sa'eeda ya bada,mai ya kawosu gidanta kuma,hijab ta sako tare da zuwa wurin da Sadam ya tsaya tana cewa
"Kace Sauban da Maryam? "
"Eh Ranki shi daɗe haka suka cemin"
Kallon Sadam tayi wanda shima itan yake kallo,duk da bayan dawowarsu daga Kamfani jiya ta sanar masa alakarsu da Sauban tare cin amanar da ƙawarta Maryam tayi mata ta hanyar auran saurayinta Sauban duk babu abinda ta ɓoye masa,komai ta sanar masa,ce ma mai gadin yayi
"Kace musu su shigo,sannan idan sun shigo ka kaisu ɗakin baƙi,zamu samesu a can"
Amsa masa yayi da
"To Ranka shi daɗe"
Komawa yayi tare da buɗe musu suka shigo cikin gidan,da kallo suke bin ko'ina na gidan,tabbas! Naira tayi kuka wurin gina wannan katafaren gidan mai kyau da tsari kamar a ƙasar waje,har masaukin baƙi ya kaisu,kasancewar Sa'eeda taje da buɗe ƙofar shiyasa da suka buɗe sai ƙofar ta buɗe,lokacin Sadam da Sa'eeda suna zaune a two seater suna manne da juna(wanga toyayya haka),runtse idonsa Sauban yayi da ƙarfi ganinsu a haka amma su ko a jikinsu,haka Maryam ma saida gabanta ya faɗi ganin Sadam,domin kuwa ya mata bala'in kwarjini da kyau,har zuciyarta ta fara harsaso mata wani abu a game dashi.(kingani-kingani kwalelanki Haj. Mairoro😂😂😂)
Zama sukayi bisa three seater,a gabansu kuma tray din kayan marmari ne da ruwa,da fara'arta Sa'eeda ta ce
"Sannunku da zuwa manyan baƙina,fatan kunzo lafiya"
Cikin sanyin murya suka amsa mata da cewa
"Yawwa"
Sannan suka gaishesu,Sa'eeda ce ta ce
"Bismillah ga ruwa da dan kayan marmari wallahi bansan da zuwanku ba da na shirya muku girki,I'm sorry for that"
"Haba wannan ma ya isa,muna godiya sosai" cewar Maryam
Daƙin shiru yayi na ɗan wani lokaci kowa na karanta wasikar zaki a zuciyarsa, sai can Sauban yayi gyaran murya tare da fara magana
"Munzo neman yafiya a wurinki Sa'eeda,kanmu a ƙasa muna neman gafarki akan abubuwan da muka miki a baya,don Allah tare da son da kikewa fiyayyan halitta wato annabinmu kuma manzonmu Muhammad (S.A.W) ki taimaka ki yafe mana,tabbas! Allah yayi ikonsa akanmu tun kan aje ko'ina,munga isharori kala-kala kuma mabanbanta duk akan cin amanar da muka miki"
Shiru ɗakin ya sake yi,can Maryam ta ɗora daga inda Sauban ya tsaya
"Don girman Allah Sa'eeda ki yafe mana ko zamu samu sassauci a cikin zuciyoyinmu,wallahi munyi nadamar abubuwan da muka miki a baya"
Idanun Sa'eeda na kallon ƙasa,hawaye na gangarowa bisa kunchinta tuno da abubuwan da suka faru baya tayi,sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya tayi sannan ta ce
"Na yafe muku Allah ya yafe mana baki ɗaya"
"Alhamdulillah mun gode sosai Sa'eeda Allah ya kara muku so da ƙaunar juna tare da dawwarma da farin ciki a rayuwarku, ya kara daukakaku,mun gode sosai" cewar Sauban
"Mun gode sosai Sa'eeda" cewar Maryam
Murmushi Sa'eeda tayi sannan ta ce
"Babu damuwa,ana tare"
Sadam ne yayi gyara murya wanda tun sanda suka fara magana bai ce ko *kanzil* ba sai yanzu yake da niyyar saka baki
"To Alhamdulillah tunda an yafe ma juna,Allah ya yafe mana baki ɗaya,tunda yanzu kamfanin da kake aiki a matsayin manager na mallaka ma My darling Star Sa'eeda so wani tunani ne yazomin yanzu,babu dadi ace kana aiki a ƙarƙashin Ex girl friend dinka,it sounds somehow koni bazan iya aiki a ƙarƙashin budurwata ba misali balle Ex girlfriend ɗina,idan kana so zan iya baka wani aikin a sabon Kamfanin da zanyi lauching ɗinsa next month a nan garin Kaduna,amma fa idan kana da ra'ayi,kaje kayi shawara idan ka amince zaka iya sanar ma P.A ɗina saimu mu baka muƙaminka na Manager a kamfanin"
"Sosai ma kuwa ai yallabai babu wata shawarar da zanyi hakan yayi ɗari bisa ɗari,ina godiya sosai Allah ya ƙara ɗaukaka tare da nisan kwana"
"No karka damu"
Haka suka cigaba da hirarsu sannan sukayi sallama,Maryam ta amsa numban Sa'eeda saboda su dinga gaisawa.Har gate Sadam da Sa'eeda suka rakasu tare da musu abin arziƙi,suna godiya haka suka taga motarsu.Dawowa Sadam da Sa'eeda sukayi cikin falon tare da cigaba da wasansu.
*TUNATARWA*
*Hattara gareku ƴan uwana maza da mata masu cin amana tare da yuudarar masoyanku,hmmm kunga dai yadda Sauban da Maryam suka kasance saboda yaudara hadi da cin amanar Sa'eeda da sukayi.Shin wai in tambayeku meye ribar yaudara hadi da cin amanar masoyin da ya yarda dakai ɗari bisa ɗari,mai yasa wasu a cikin mu suke jin daɗi idan suka da wasu sun shiga cikin halin damuwa saboda su,ko sun manta ne Ubangiji baya yafe hakƙin wani akan na wani ne,ko sun manta adduar wanda aka zalunci bata faduwa ƙasa banza,ko sun manta Allah yana sakayya akan wanda aka zalunta tata-izan da gaggawa,wannan hawayen da yake zubarwa ko kuma take zubarwa saboda ku wallahi! Wallahi! Wallahi! Bazasu zubu a banza ba Ubangiji zaiyi ikonsa akan duk wanda ya zaluncesu ko ba daɗe ko ba jima.Ƴan uwana maza da mata mu guji karye zukatan masoyan da suka yarda damu.Allah kasa mu dace*
@@@@@@@@@@@@
A ɓangarensu Umma Kande lamari yaƙi daɗi domin yanzu gabanta tsutsa yake fitarwa haɗi da ruwa mai yauƙi ga ɗoyin gaske,ko tafiyan kirki bata iyawa,sai an kwantar sai an tayar,har yanzu bakinta bai mutu ba,tana nan tana zuba kamar ruwan famfo,su Maman Jummalo suna ƙoƙari akanta sosai.
Alhamdulillah an dace a aikin da akama Nusaiba a Abuja wanda Umman Sa'eeda tayi jagoranci komai,tun daga biyan kuɗin aikin,magunguna da dai sauransu,babu laifi aiki yayi kyau sosai don yanzu ta daina yoyon kashi,har sun dawo gida ta cigaba da shan magungun nan da aka ɗorata a kai,har jikinta ya fara cikowa.
Su Iklima Allah ya kawo musu mazaje masu wadata ita da Jummalo,yanzu ma haka har an saka ranar auransu nan da wata huɗu masu zuwa,Uncle Hassan ya bama Abban Sa'eeda jari mai tsoka sosai wanda zai dinga kasuwanci dasu,sirikinsa Sadam ya siya shakuna uku ya haɗe mishi su tare da ƙara mishi wani jarin ya ƙara,kuka ne kaɗai Abban Sa'eeda baiyi ba saboda farin cikin da yake ciki,yayi godiya yafi ƙarfin cikin kwanda ga wa'innan bayin Allah,kasuwancin saida atamfofi,shaddoji,laisussuka,da dai sauransu ya fara,babu laifi kasuwancin nasa na tafiyi a yadda ya kamata,ƙofofin alkhairai sai ƙara buɗe masa suke ta ko'ina,har ƴan uwansa na ƙauye yakan tura musu kuɗi wanda zasu tallafi rayuwasu dana ƴaƴansu.
Umman Sa'eeda ne tayi wani tunani haɗi da neman yardar mijinta akai,bayan sun kammala break fast suna zaune a falo suna kallon TV sai Umman Sa'eeda tayi gyaran murya tare da cewa
"Abban Sa'eeda ina so muyi wata magana mai muhimmancin gaske yanzu"
Waiwayowa yayi tare da cewa
"To,ina jinki sahibata"
Ɗan murmushi tayi sannan ta ce
"Wata shawara ce nazo da ita kuma ina fatan zata karɓu a wurinka,ganin Umma Kande a irin wannan hali,gashi su Iklima sun kusa aure,ita ma Nusaiba muna mata fata samun miji a nan kusa tayi auran ita ma,shi ne nace mai zai hana ka auri Maman Jummalo domin idan yaran sukayi aure gidan watsewa zaiyi,ya zama babu kowa don kasan Maman Jummalo da wuya ta cigaba da zama gidan,kaga idan ka aureta zata cigaba da kula da Umma Kande sannan yaranka zasu samu madogara tunda ni ba'a gidan nake ba yanzu,kuma yaran sun ɗauki Maman Jummalo a matsayin mamansu,kaga a nan dadi zasuji idan ka auri Maman Jummalo"
Shiru yayi yana kallonta ko ƙifta idanunsa baya yi,sai can ya sauke goron ajiyar zuciya sannan ya ce
"Kenan...............
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***