RANTSATTSEN RABO

LOKACI CHAPTER 19

by @fulani32

Follow this link to join my WhatsApp group: ***


LOKACI 

RABI'ATU KABIR ACHADU FULANI 

YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA 

Under Team Yota's Amazing Pen's.

  SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️ 

FULANI ❣️ 
***


       PAGE1️⃣9️⃣

Da kallo Teemah tabi sa har ya shige part ɗinsa, ta iya mota duk da ba wani ja take ba, idan ba suna tare da Yah Khaleel ba, amman haka kawai bata ja, shiga ta yi ta kashe motar, sannan ta ɗauki abin da hannunta zai iya ɗauka, ta shiga part ɗin Ammie, suna zaune dukansu, ita kaɗai ce kawai babu da Zay'd.

"Yah Khaleel zo mu ɗebo kaya a motar Yah Zay'd ba zan iya ba ni kaɗai" ta yi maganar tana tura masa baki, dan bata manta ba sunyi faɗa. 

Ganin idon Abhie da Ammie ne ya sa shi bin ta, ba tare da gardama ba, shiga cikin motar ya yi, dan ya fito da kayan da ta ce, sai da yana shiga ta rufe murfin da ƙarfi, sannan ta yi locking ɗinta ta waje.

"Princess!"

Ya kira sunanta da ƙarfi yana zare mata ido.

Harararsa ta yi "me ye?" 

"Zo ki buɗe motar nan kafin ranki ya ɓaci" 

Dariya ta ƙyalƙyale masa da ita, sai kuma ta noƙe masa kafaɗa, sauran kayan ta ɗauka, tayi gaba tana rera waƙa.
 
Ganin dagaske zata tafi sai ya fara rarrashinta, amman ta yi biris da shi ta wuce.

"Ammie gashi" ta ce bayan ta ajiye kayan a gabanta, sai kuma ta matsa kusa da Abhie ta gaishesa.

"Ina kika baro Khaleel ɗin?" Abhie ya tambayeta.

"Yana can ya tsaya wajen Yah Zay'd" ta basa amsa tana ƙifƙifta ido. Kallo ɗaya Ammie ta yi mata tasan bata da gaskiya, amman ba ta nuna mata ba.

"Ina kuka je da Babban mutum?" Ammie ta ce bayan ta buɗe abubuwan da ta shigo da su.

"Wani restaurant ne ba na sa ba amman, Ammie har ƙawa na yi a can" ta bata amsa fuskarta da murmushi.

Kallon mamaki suka bita da shi, jin wai restaurant amman ba na sa ba.

"Sai mai ya faru a can?" Inji Abhie.

Mayar da kallonta ta yi kansa. "Bansaniba Abhie, fita na yi waje na yi hoto, anan na yi ƙawa Salmah, daga nan kuma na koma aka kawo masa order, bayanan muka tawo gida ransa a ɓace, sai ya shiga part ɗin sa shikenan" 

"Ok" kawai ya ce mata. Ta shi ta yi ta shiga kitchen, ta ɗebo flet, cake ɗin ta yanka musu, sannan ta haɗa da doughnut da sauran abubuwan, ta na ajiye musu ta fita da wayar Khaleel a hannunta, ya na ganinta ya harareta.

"Mu yi ciniki ga wayarka na buɗe ka" 

Baiyi musu ba ya karɓa yana jin idan ya kamata sai ya daketa a ransa, kuɗi ya saka mata, ta na jin alert ta buɗe masa, kafin ya fito ta yi part ɗin Ammie a guje, ta na shiga ta zauna kusa da Abhie ta na maida numfashi.

Ko da ya shigo bai nuna mata komai ba, zama yayi shima ya yanki cake ɗin, suna ci suna hira, tare da santin daɗin abubuwan, bayan sun gama su kayi wa iyayen sallama kowa ya nufi makwanci.

"Nasan waye shi haka kawai ba za shi restaurant na wasu ba, bayan shima a nasa suna yin kayan nan"
Ammie ce ta kalli Abhie da ya yi maganar kamar ba daga bakinsa ta fito ba, ganin bama ita yake kallo ba.

Anan ta faɗa masa maganar da su kayi rannan da shi. Shiru ya yi alamun tunani, daganan ya ɗauki wayarsa ya kira wani.

"Assalamu alaikum Abhie Barka da dare"

Amsa masa sallamar ya yi.

"Me yake faruwa a restaurant ɗin abokinka Sameer?"

Shiru ya yi yana tunanin me zai ce masa, sai dai tun da har ya tambaya da kansa, dole yayi masa bayani amman ba duka ba, sallama sukayi ya tashi ya bar Ammie a zaune a wajen, dan kar ma tayi masa wata maganar.

Wani irin farin ciki ne ya ratsa ta, ganin Allah ya fara amsa addu'arta, daman burinta Abhie ya sakko, kuma daga dukkan alamu yana gab, tunda gashi kwana biyu yana shiga abin da ya shafi Zay'd ɗin, ta shi tayi ta bi bayansa, cike da jin daɗi.

"Hello dude" Sameer ya ce bayan Zay'd ya ɗaga kiran da ya masa.

"Bana son damuwa Meye kuma Sameer ba yanzu muka gama magana ba?" 

Murmushi ya yi "afuwan kiran ne ya kama, yanzu Abhie ya yi min waya" 

"Abhie" ya maimaita cike da mamaki.

"Eh" na. Ya faɗa masa yanda suka yi.

Shiru ya yi dan ya rasa abin da zai ce, saboda mamaki.

"Zan shigo Abuja gobe da yamma, ranar monday muna da meeting" yana faɗar haka ya datse kiran.

★★★★

A hankali kwanaki suka fara wucewa, wasu masu daɗi wasu akasin su, a kuma cikin kwanakin ne gidan Alhaji ya fara komawa yadda yake a da.

Sosai Khairiyya ta yi ƙoƙari wajen barin komai ya wuce kamar bai faru ba, babban abin da ya ke mata daɗi, bai wuce ganin babu wanda yake ce mata ta yi abu, sai abin da ta ga ya dace tayi, sosai hakan kuma ya taimaka mata, dan yanzu kanta take ginawa, ba abin da wani ya gina mata ba, a yanzu ramin da ta haƙa da kanta take shiga ba wanda wani ya haƙa mata ba.

Ranar asabar da safe, tana zaune a parlown Ummu tana kallon, takardar da Aunty Maryam ta kawo mata, tun jiya amman bata duba ba sai yanzu, a hankali ta fara tuna tattaunawar ta su.

"Khairiyya takanas saboda ke yau na zo gidan nan, karɓi ki duba"

Kallonta ta yi da mamaki jin, wai saboda ita ta zo, sai kuma ta karɓi takardar ta juya ba tare da ta buɗe ba, ta ajiye ta ce.

"Ta mece ce?"

"Foam ne na koyon sana'a, wata ƙawata ce ta gaya min, ana koyar da abubuwa daban-daban, har da girke_girke na zamani, duk wasu nau'ikan abinci suna koyarwa, kinga idan kin koya ba sai ki dinga yi ba, ki na saka order daga gida, itama sana'a ce me kyau dan ana samu"

Takardar ta ɗakko tana kallo, duk da bata buɗe ba.

"Girke_girke Aunty Maryam?"

"Eh"

Shiru ta yi ba ta ce komai ba, tana tuna wani lokaci da suna makaranta, burinta ta zama ƙwararriya a ɓangaren girke_girke, ƙawarta Zahra kuma a ɓangaren Snacks, har ce wa suke za su buɗe restaurant na su na kansu, Zahra ta kula da ɓangaren Snacks ita kuma abinci, shiyasa suka zaɓi ɓangaren catering, amman a ƙarshe tana ji ta gani haka mafarkinta ya rushe.

"Kin taɓa faɗamin kina son girki sosai, dukanmu mu ma mun san wannan burinki ne, badan Auwal ya hanaki ci gaba da karatu ba da yanzu kin zama chief na sani" Maryam ta katse mata tunanin da take.

Kallon takardar ta ƙara yi.

"Yaushe da yaushe ake zuwa?" Ta tambayeta tana jin wani abu na motsa wa a cikin zuciyarta.

"Ki duba zaki gani, duka wata uku dai zaku yi, a baku certificate"

Shiru ta yi na ɗan lokaci.

"Shikenan zan duba, nagode sosai Babbar yaya"

Murmushi tayi mata suka ci gaba da tattaunawa.

Ajiyar zuciya ta sauke, bayan ta duba foam ɗin, a sati sau huɗu, za su dinga yi, haka kawai taji tana son ganin Zahra dan sun daɗe basu haɗu ba.

Cike foam ɗin ta yi, sannan ta tashi ta shiga wanka, cikin dogon hijabi ta shirya har ƙasa, ta ce wa Ummu zata gidan ƙawarta, bata hanata ba ta ce ta dawo lafiya.

Tana fita daga gidan ta shaƙi iska ta fesar, rabonta da waje, tun ranar da suka dawo daga asibiti, jinta take kamar ba ita ba, da ƙafa ta fito daga layinsu, napep ta tare ya kaita, dake babu nisa, cikin ƴan mintuna ta sauka, ƙarasawa tayi gidan, sannan tayi knocking, ba ta jima a tsaye ba aka buɗe mata.

"Lah Aunty Khairiyya" Salmah ta kira sunanta da shaƙaƙƙiyar murya, kamar ta mai mura.

"Autah kece kika girma haka?" Ta ce tana riƙe haɓa, ganin yanda Salmah ta cika mata ido.

Murmushi kawai tayi ba tace komai ba, ta bata hanya ta shigo, ɗakin Mahmah ta fara zuwa ta gaisheta sannan ta shiga ɗakin Zahra.

Tana kwance idonta a lumshe, kamar mai bacci sai dai ba baccin ta ke ba, tunani ne fal a cikin zuciyarta.

"Bestyn Best friend!" Ta kirata da sunan da ya sakata buɗe idonta babu shiri.

"Khairiyya?" Ta kira sunanta tana ta shi zaune cike da mamaki.

"Na'am Zahra" ta amsa mata da murmushi.

"Ɓatan kai kika yi? Ko kuma tunawa kika yi da ni?" Ta jera mata tambayar har lokacin da mamaki a fuskarta, dan rabonta da ita wajen shekara uku kenan, tun bikinta.

"Ke dai Zahra kin manta da mutane, shiyasa na ce, bari na zo na ga ko kinanan a raye"

Dariya Zahra ta yi "ga ni nan da raina, zauna kin kwaso rana"

Zama tayi a kusa da ita, Salmah ce ta shigo da flet a hannunta, ta sako ruwa da lemo, sai kuma wani na abinci daban. Bayan ta fita hirar yaushe gamo suka fara, sosai suke raha, dan sun tuna wasu abubuwan da suka faru a baya can lokacin ƙuruciya, da kuma rayuwar makaranta, har suka gangaro kan auren Khairiyya, inda daga nan ne Khairiyya ta yi shiru. 

Zahra da ta kula da yanda lokaci ɗaya yanayin ta ya sauya ta ce.

"Khairiyya, lafiya naga kin yi shiru?"

Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta ɗago ta kalleta, cikin sanyin murya ta ce.

"Aurena ya mutu Zahra!"

Zaro ido ta yi cike da tashin hankali.

"Me kika ce? Da shi Auwal ɗin? Innallilahi wa'inna ilaihir'raji'un" idonta har ya tara hawaye.

Gyaɗa mata kai ta yi a hankali, itama tana jin yanda idonta ya cika da ƙwalla.

"Aurena ya mutu da Auwal, a lokacin da kike faɗa min na nutsu akan Auwal banji ba, burina kawai nayi auren, na shiga damuwa da tashin hankali Zahra, har ɓarin ciki nayi wanda shi yafi komai tsaya min a cikin zuciyata" 

Anan ta ci gaba da bata labarin duk abin da ta fuskanta, ita kuka Zahra kuka an rasa wanda zai rarrashi wani a cikinsu.

Hannunta Zahrah ta riƙe, ta kasa furta mata komai sai kukan da take, sosai taji tausayin Khairiyya, dan ita kaɗai tasan yanda take son Auwal, duk mazan da ta aura soyayyar Auwal daban take a cikin zuciyarta, amman ya saka mata da haka, idan har anyi haka auren soyayya, toh ina ga auren da babu soyayya.

"Allah ya maye miki shi da mafi Alkhairi, Allah ya baki ikon cinye wannan jarabawar" 

Cikin kuka itama tayi mata bayanin abin da take fuskanta da matsin lamba. Kukan nasu ne ya dawo sabo, lokacin da Zahra ta kai ƙarshe, daman can su biyu take tattaunawa da su, dan haka yanzu da tasamu Khairiyya sai ta buɗe mata dukkanin wata damuwarta.

"Zhara" ta kira sunanta cike da nutsuwa, tana haɗiye kukan ta.

"Ina son ki fahimci wani abu, ki daina ɗaga hankalinki a kan maganar aure. Ki saurari abin da zan faɗa miki"

Shiru tayi itama tana kallonta.

"Kin san ni, kuma kin san nayi aure har sau uku kenan haka ne?"

Gyaɗa mata kai Zahra tayi.

"Na yi auren farko, kishiya ta hana ni zama. Na yi na biyu, matsalar abinci, har sai an kai min daga gidan mu. Na zo na yi na uku, shi kuma ga shaye-shaye, ga duka, ga cin mutunci. Zahra faɗamin mene ne amfanin irin wannan auren?"

Ɗan dakatawa ta yi, sannan ta ci gaba da magana cikin nutsuwa.

"Wallahi Zahra kullum cikin danasanin yin aure nake a rayuwata, dan ban ga amfaninsa ba, ba wai ina ce miki aure ba shi da amfani bane a'a, amman auren da babu zaman lafiya da kwanciyar hankali, auren da kullum kike rayuwa cikin tsoro da tashin hankali, kullum cikin kuka da baƙin ciki, faɗa min menene amfanin wannan auren Zahra?"

Sunkuyar da kanta ta yi ta rasa amsar da zata bata. Ƙara riƙe hannunta Khairiyya ta yi.

"Saboda haka, ina son ki daina ɗaga hankalinki a kan maganar aure, ki tsaya kiyi addu'a, ki roƙi Allah ya zaɓa miki abin da yake alkhairi a rayuwarki, ki roƙi shi ya zaɓa miki wanda ya dace da ke, wanda zai so ki, ya tausaya miki, ya girmama ki, ya mutunta ki, ya kuma sauke duk wani haƙƙinki, ki tuna ke macece kina da daraja, ba inda aka ce dole sai kinyi aure dan kawai mutane suna tambayar ki yaushe zaki aure, kuma ba dole bane kiyi zaman aure cikin ƙunci da baƙin ciki dan kawai kina gudun a kira ki da bazawara"

Murmushi ta yi, duk da damuwar da ke kan fuskarta.

"Ni dai a ganina Zahra, gwara ki ci gaba da zama, a gidanku, cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, da dai ki auri mutumin da bai dace ba, dan kawai an matsa miki da maganar aure, duk runtsi ba za'a kira ki da bazawara ba, kuma babu wanda zaiyi zaman irga miki aure"

Shiru ɗakin ya ɗauka.

Sosai maganganun Khairiyya suka ratsa zuciyarta, dan duk wata magana da tayi mata ta bata misali akanta, sai taji a ranta kamar tana jin tsoron yin auren ma, tunda dai shi namiji halinsa ba'a goshi ake liƙa masa ba, bare ka zaɓi wanda ya dace.

Sosai suka ƙarawa bawa kansu shawarwari, kafin tayi mata sallama, rakata tayi sai da ta shiga napep sannan ta dawo.

Zama tayi ta buga tagumi da hannu bibbiyu, tabbas nauyin da zuciyarta tayi mata na ajiye abubuwa ya ragu, amman kuma a halin yanzu ta shiga wani sabon zullimin akan auren kansa, sai dai ta ji a ranta zata dage ta ci gaba da addu'a, dan ita kaɗaice kawai mafita.

"Allah yasa mu dace" ta furta a bayyane.

Jin wayarta na ringing ne yasa ta duba me kiran.

"Manager" 

Haka kawai da ganin kiran ta ji gabanta ya yanke ya faɗi ba tare data san dalili ba......

FULANI
***