THE BATTLE OF HEARTS
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER 102*
*THE BATTLE OF HEARTS*
*JIDDAAH BARKUM*
———-
Zayd ya sallame sallarsa, ya zauna a kan prayer mat ɗin na kusan minti goma, yana ta yin addu’o’insa cikin nutsuwa, bayan ya gama, ya miƙe, ya naɗe prayer mat ɗin, sannan kai tsaye ya ƙarasa kan gadonsa ya zauna, ya miƙa hannu ya ɗauko wayarsa, ya fara dubawa cikin nutsuwa, kamar wanda babu wata damuwa a ransa, Raihana kuwa, tun daga kan sofa din da take binsa da kallo ta gefen ido, duk motsin da ya yi, tana lura da shi, amma tana ƙoƙarin kada ya fahimci hakan, bayan wasu mintuna, Zayd ya miƙe daga inda yake zaune, ya sa wayarsa a aljihu, sannan ya nufi ƙofa ba tare da ya ce mata uffan ba, ganin haka, Raihana ta miƙe zumbur daga kan sofa, idanunta suka bi bayansa, tana kallonsa har ya kai bakin ƙofa, da ta ga da gaske fita zai yi, sai ta buɗe baki cikin sauri, “Ina za ka je toh?” Zayd ya ɗan waigo, ya jefa mata wani calm, unreadable look kafin ya amsa cikin sanyin murya, “Inda kika aikeni,” ya juya zai ci gaba da tafiya, amma Raihana ta turo baki, ta ɗan tattare fuska, “Ai dai ka na sane ni bazan iya zama ni kaɗai a ɗakin nan ba! Ni duk inda za ka je, sai na bika,” Zayd ya tsaya cak, a hankali ya juyo gaba ɗaya, ya jingina da ƙofar yana kallonta, fuskar nan tasa a hadenta, sai dai kallon da yake mata kamar yana ƙoƙarin fahimtar abinda take nufi kuma, Raihana kuwa, da ta haɗu da idanunsa, sai ta ɗan sadda kanta, amma ba ta janye maganarta ba, ta ma ƙara turo baki, tana jiran ya ce wani abu, Zayd bai ce komai ba, ya ci gaba da kallonta na wasu daƙiƙu, sannan ya juya ya fita, kafin Raihana ta ankara da abin da ke faruwa, sai ta ji ƙofar ta rufe, ya sa key daga waje, da sauri, tana ƙarasa bakin ƙofar, ta kama handle ɗin ƙofar, ta murɗa, ƙofar ba ta buɗe ba, ta sake murɗawa, wannan karon da ƙarfi, zuciyarta ta buga da sauri, ta lumshe idanunta na ɗan lokaci, sannan ta buɗe su a firgice, “Wayyo Allah na!” Ta sake gwada buɗe ƙofar, amma hakan ya ci tura, Raihana ta tsaya cak, tana kallon ƙofar kamar ba ta yarda da abin da ya faru ba, da gaske ya kulle ta a ciki? Ita kaɗai zai fita ya bar ta? Ta waiwaya ta kalli ɗakin, sannan ta koma kan ƙofar, “Ka buɗe min ƙofar dan Allah,” ta tsaya tana sauraron ko za ta ji motsinsa a waje, amma babu komai, sai ta haɗe hannayenta a ƙirji, zuciyarta na bugawa, ta sake kallon ƙofar, idanunta cike da dan tsoro, sai ta juya da sauri ta nufi window ɗin ɗakin, kamar wadda ta tuna da wani abu, da ta isa, ta kama curtains ɗin ta yaye su gefe guda, tana leƙen compound ɗin gidan, gidan ya yi shiru saboda dare ya riga ya yi nisa, fitilun compound ɗin suna haskaka wajen, amma babu motsin komai, iska mai laushi ce kawai take kaɗa ganyen bishiyoyin da ke gefen hanyar shiga, yayin da ƙananan tsuntsaye ke fitar da sautinsu lokaci-lokaci, suna ƙara karya shirun daren.
Raihana ta tsaya tana kallon wajen, hannunta har yanzu a kan labulen, ta yi niyyar sakin curtains ɗin ta koma, amma wani motsi da ta hango a gefe ya sa ta tsaya cak, Zayd ne, yana tafiya a nutsensa, hannunsa ɗaya a aljihu, bai nuna alamun gaggawa ba, kamar mutumin da yake da dukkan lokacinsa a duniya, kai tsaye ya nufi hanyar da za ta kai shi part ɗin Seeyama, Raihana ta buɗe idanunta sosai, ta matsa kusa da window ɗin, tana ƙoƙarin tabbatar da abin da take gani, but there was no mistake, shi ne, yake tafiya zuwa part ɗin ɗayan matarsa a wannan lokacin na dare, zuciyarta ta fara bugawa da sauri, ta kasa sakin labulen, wani irin feeling ne ya sauko mata daga inda ita kanta ba ta san shi ba, wani abu mai nauyi ya tokare mata ƙirji, har ta ji numfashinta ya ɗan tsaya na ɗan lokaci, ta haɗiye yawu da ƙyar, me zai je yi a part ɗin Seeyama da wannan lokacin? Tambayar ta faɗo mata a rai ba tare da ta shirya ba, nan take ta sake haɗiye yawu, idanunta suna bin Zayd har ya ƙarasa ƙofar part ɗin Seeyama, ya tsaya na ɗan lokaci, ya buɗe ƙofar, sannan ya shige ciki, Raihana ta ji kamar wani abu ya faɗo a cikinta, ta lumshe idanunta a hankali, amma da ta sake buɗe su, Zayd ya riga ya ɓace daga ganinta, har yanzu tana tsaye a wajen, hannunta bai saki labulen ba, ƙafafunta kuwa sun kasa motsawa daga inda take tsaye, kamar an dasa ta a wajen, she couldn’t even explain what she was feeling, abin da kawai ta sani shi ne, tun lokacin da ta ga Zayd yana nufar part ɗin Seeyama, zuciyarta ta sauya mata yanayi, wani irin rashin jin daɗi ya mamaye ta, wanda ta kasa ba wa suna, ta haɗiye yawu a karo na uku, sannan ta sauke labulen a hankali, amma ko bayan labulen ya rufe mata compound ɗin, har yanzu hoton Zayd yana tafiya zuwa part ɗin Seeyama yana nan a idanunta, ta tsaya tana kallon labulen da fuska mai ɗauke da tambayoyi, me ya sa tafiyarsa can ta dame ta haka? Raihana ta juya daga wajen window ɗin a hankali, ta koma kan sofa, ta zauna na ɗan lokaci tana kallon gabanta, kafin ta kwanta, ta kudundune jikinta cikin hijab ɗin ta, ta yi shiru, amma duk da ta rufe idanunta, barci ya ƙi zuwa, wani irin feeling ne take ji a ranta, wanda ita kanta ba ta fahimci asalinsa ba, ta juya ta koma ɗayan gefen, ta qara dukunkunewa a cikin hijab din, sannan ta lumshe idanunta da ƙarfi, why should I even care where he goes? Ta tambayi kanta a zuciyarta, sai dai abin takaicin shi ne, duk ƙoƙarin da take yi na ganin ta daina tunanin Zayd, sai tunaninsa ya ƙara mamaye mata zuciya.
Zayd kuwa, kai tsaye part ɗin Seeyama ya wuce, tun lokacin da Raihana ta yi ihun ganin maciji, Seeyama ta ji ta sarai, sai dai ba wannan ne ya fi ɗaukar hankalinta ba, abin da tunaninta ya ba ta shi ne, watakila ita da Zayd sun shiga wani sabon babi na rayuwarsu ne, a new chapter unfold, wannan tunanin ne ya dugunzuma hankalinta tun farko, ta rasa nutsuwa, ta sha kukanta, har sai da ta gode wa Allah ta ɗan samu sauƙi, amma daga ƙarshe, ta kasa haƙuri, ta ɗauko wayarta ta kira Safina, da aka ɗaga wayar, Seeyama ta fashe da kuka, “Safinaaaa! Kina ganin dai na zama hoto a gidan nan?!” ta faɗa cikin kuka, muryarta cike da ɓacin rai, “Ni fa duk yadda na tsara abubuwa, ba haka suke tafiya ba! Everything is going completely wrong!” Safina ta yi shiru tana sauraron ta, “Mommy ta gama min nata, babu abin da ta manta da shi, babu abin da ba ta faɗa min ba, amma duk da haka, a gaban kowa ta nuna tana maraba da wannan matsiyaciyar! Kamar ita ce wadda aka daɗe ana jira a gidan nan!” Ta share hawayenta da bayan hannu, amma hakan bai hana su sake zubowa ba, “Daga ƙarshe, ta maida laifin a kaina! Ni ce nake da matsala, ni ce ban iya zama da mutane ba, now tell me, Safina, how am I supposed to deal with all this?” Ta ja dogon numfashi, amma zuciyarta ta ƙara zafi da zarar ta tuna da Raihana, “Shi kuma yanzu yana can! Who knows what is going on between them? Maybe he has already gotten used to her, ya gama saninta, shegiya matsiyaciya, bakiji wani uban ihu da tayi ba, kamar wacce ya hade kuma duk dan na ji ne kuma naji din, yanzu tunda ya kusanceta, ai na shiga uku!” Ta yi tsaki, ta goge hawayenta, sannan ta ci gaba da magana cikin wani irin fushi, “Ba a ma fara komai ba kenan, jiya ne fa ta tare, amma ni har na fara jin kamar an gama da ni! Yanzu fa muka fara zama tare, amma duk da haka, look at where I am now!” Ta yi shiru na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin daidaita numfashinta, sai dai kamar wadda ta tuna wani abu, sai ta sake magana cikin zafin rai, “I swear, Safina, I will make that girl’s life miserable, no matter how long it takes!” Ta faɗi hakan cikin ƙarfin hali, amma nan take hawayenta suka sake kwaranya, “Wallahi sai na yi maganinta, sai na wulakanta ta, na tagayyara rayuwarta, I don’t care what it takes, ba zan zauna ina kallonta tana kwace min duk abin da na yi shekaru ina buri a kai ba!”
Safina ta yi shiru, tana sauraron Seeyama har ta gama maganarta, sai ta sauke numfashi mai nauyi kafin ta yi magana, “Ai Seeyama, ke ce da kafiya da taurin kai, mutumin nan ba sonki yake ba, kin sani, but tell me, even if you keep forcing things, do you think he will suddenly start loving you?” Seeyama ta yi shiru, amma Safina ba ta tsaya ba, “So ko kin kai masa pride ɗinki, he still won’t appreciate it, toh ba gwara ki bayar a inda zaa miki maganinsa ba, kuma dan yi sau daya takkk, a ina zai gane, kina ta wahalar da kanki a kan mutumin da bai ma fahimci irin abin da kike yi domin ki samu soyayyarsa ba,” ta ɗan dakata, “Toh wlh tun wuri kafin ta ita ta fitar dake, gwara ki yi tunani a kan hanyar da za ta taimaka miki ki cimma burinki ba? Kuma ai ba sai kin maimaita abin da kika riga kika gwada ba, sometimes, one carefully planned move is enough to change everything,” Seeyama ta yi shiru, ta jingina da jikin gadonta, tana kallon wani wuri babu komai a idanunta, maganganun Safina suna shiga kunnenta, amma kamar tana buƙatar lokaci kafin ta fahimci abin da take nufi, Safina ta ci gaba da magana cikin sanyin murya, “Wallahi, da ni ce ke, kuma da kin bi shawarata tun farko, da tuni mun wuce wannan stage ɗin, amma ke kin tsaya kina kuka a kan abin da kike tunanin ya gagare ki, alhali kina da zaɓuɓɓuka da za ki iya nazari a kansu, kuma maganin damuwarki na hannunki,” Seeyama ba ta amsa ba, shirun nata ya sa Safina gyara zamanta, kamar wadda ta lura abokiyarta ta fara tunani da gaske, “Seeyama, listen to me carefully, Zayd zai dawo hannunki, kuma ma idan kina son ya jiki kamar budurwane, ai akwai hanyoyin da ake dabaru, ba zai gane ba, beside mutumin ma da zai dawo karkashin ikonki, sai abinda kika ce, yaushe zai tsaya ma yana ja dake, akan baki kawo budurcinki ba, amma idan har kina son ya dinga kallonki da wani irin kallo na musamman, sai kin tashi da wuri ki nemi mafita, there are ways to handle this situation without making him suspicious,” Seeyama ta ɗan ɗaga kanta, tana sauraron ta sosai yanzu, Safina ta ƙara da cewa, “Kuma mutumin da kike son ya zama mai sauraronki, wanda zai dinga la’akari da abin da kike so, ba zai zama haka cikin dare ɗaya ba, kina buƙatar ki nemi mafita, ko a mutu ko ai raii,” ta yi ɗan murmushi, kamar wadda ta tuna wani abu, “Amma dai batun da kika gaya min a baya, har yanzu kina buƙatar ki yi tunani a kansa, idan kina son wani abu ya canza, dole ne ki fahimci cewa wasu abubuwa suna buƙatar lokaci da tsari, ki tsara komai da kike buqata, mu koma garin nn, mu bawa mutumin nn hakuri, zai hakura, za kuma ki samu cikar burinki,” Seeyama ta yi shiru na tsawon lokaci, a hankali ta sauke wayar daga kunnenta, tana kallon screen ɗin kamar tana nazarin duk abin da Safina ta faɗa mata, was Safina right? Ta tuna yadda Zayd ya yi mata magana, yadda ya hana ta yin abin da take so, da kuma yadda ya nuna wa kowa cewa ba zai bari ta sarrafa rayuwarsa ba, zuciyarta ta ƙara nauyi, Safina ta sake magana daga ɗayan ɓangaren wayar, “Seeyama, ki yi tunani a kan maganata, da safe zan sake kiranki, na ji abin da kika yanke, ni yanzu ina hanya ne, zan ƙarasa gida,” “Hmm,” Seeyama ta amsa a taƙaice, har yanzu tana cikin tunani, “Toh, sai da safe,” Safina ta faɗa, sannan ta katse wayar, Seeyama ta sauke wayar daga hannunta ta ajiye ta gefe, sai dai maimakon ta samu nutsuwa, maganganun Safina sun buɗe mata ƙofar wasu sabbin tunane-tunane, ta kwanta a hankali, ta ɗora hannu a goshinta, idanunta suna kallon ceiling ɗin ɗakin, a wannan karon, ba kuka take yi ba, tana tunani, tana nazari, kuma duk da ba ta yanke shawara ba tukuna, abu ɗaya ya fara bayyana a ranta, ba za ta zauna kawai tana kallon Raihana tana samun abin da ita ta daɗe tana buri a kai ba.
Zayd ya buɗe ƙofar ɗakin nata, ya shigo ciki a hankali, Seeyama kuwa, wacce idanunta suka kumbura sosai saboda kuka, ta ɗago kai ta zuba masa idanu, a take, wani uban kishi ya fara nukurkusarta, haɗe da wani irin bala’in sonshi da ba ta taɓa jin irinsa ba a rayuwarta, ta kasa kawar da idanunta daga kansa, tana kallonsa kamar wadda ta daɗe ba ta gan shi ba, shikenan, ya fara sanin Raihana a matsayin diya mace kafin ita, wannan tunanin ya faɗo mata a rai, ya ƙara hura wutar kishin da ke cin zuciyarta, ta kalli yadda yake glowing, ta kalli kyakkyawar fuskarsa da ta yi sharrr, da irin nutsuwar da ke tattare da shi, komai nasa ya yi kyau a idanunta, amma a wannan lokacin, kyawun nasa ya zama wani irin azaba a gare ta, was he this happy because of Raihana? Tambayar ta faɗo mata a rai, amma ba ta da amsar da za ta kwantar mata da hankali, ba ta san hawaye sun fara wanke mata fuska ba sai da ta ji muryar Zayd, “Are you alright?” Da sauri ta dawo hayyacinta, ta sa hannu ta goge hawayen da ke fuskarta, tana ƙoƙarin tattara kanta kamar babu abin da ya faru, Zayd ya ƙara shigowa, ya ƙarasa wajen dressing mirror ɗinta, ya jingina da shi, sannan ya naɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallonta, Seeyama kuwa ta ƙi kallonsa, wani bala’in haushinsa take ji a wannan lokacin, har ta kasa jure kallon fuskarsa, da tana iya cire duk tunanin Raihana daga ranta, da ta ji sauƙi, but how could she, when the very man she wanted was standing right in front of her, looking as calm as ever? Zayd ya ɗan karkatar da kansa, yana nazarin yanayinta, a hankali ya sake cewa, “Meya faru?” Ba tare da ta kalleshi ba, ta amsa a taƙaice, “Ba komai, just headache,” Zayd ya zuba mata ido na wasu daƙiƙu, kamar bai yarda da amsar da ta ba shi ba, ya lura da kumburin idanunta da kuma yadda ta ke ƙoƙarin ɓoye fuskarta daga gare shi, amma bai matsa mata ba, a hankali ya sake tambaya, “Kin ci abinci?” Seeyama ta jinjina kanta kaɗan, sannan ta amsa, “Ehh,” “Magani fa? Kin sha?” “Ehh,” amsoshinta sun kasance a taƙaice, ba tare da ta nuna wata sha’awa ta ci gaba da tattaunawar ba, Zayd ya yi shiru, ya ci gaba da kallonta, hannayensa har yanzu a naɗe a ƙirjinsa, Seeyama kuwa ta ɗauko pillow ɗinta ta gyara, tana ƙoƙarin kauce wa kallonsa, bayan wani ɗan lokaci, Zayd ya sake tambaya, “Kin yi sallar Isha?” Seeyama ta gyara pillow ɗin, ta ja duvet ɗin sama tana shirin kwanciya, “Ban yi ba, zan yi idan na ɗan ji sauƙi,” bayan ta faɗi haka, ta lumshe idanunta, ta juya masa baya, da alama tattaunawar ta ƙare a wajenta, Zayd ya tsaya yana kallon bayanta, fuskarsa babu wani sauyi da za a iya ganewa, bai ce komai ba, bai kuma matsa mata da wata tambaya ba, Seeyama kuwa, tana kwance ne da idanunta a rufe, amma zuciyarta cike take da tunanin da ta kasa sarrafawa, ta san Zayd yana tsaye a bayanta, ta san yana iya kallonta, amma ta ƙi juyowa, domin idan ta sake kallon fuskarsa, tana tsoron kada hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa su sake zubo mata, bayan wasu mintuna, Zayd ya juya a hankali, ya nufi wajen switch ɗin, ya kashe fitilar ɗakin Seeyama, daga nan ya fice, ya ja ƙofar ya rufe, Seeyama kuwa, tana jin motsin ƙafafunsa yana nisa, sai ta fashe da kuka, da sauri ta ɗora hannunta a kan bakinta, tana ƙoƙarin danne sautin kukanta don kada ya kuɓuce mata ya fita waje, hawayen suka ci gaba da zuba mata, jikinta yana rawa saboda tsananin damuwar da ta kasa sarrafawa, tabbas, Zayd ba ita yake so ba, a wannan karon, ta yarda da hakan a ranta, ya zo ya same ta a cikin wannan halin, ya ga yadda idanunta suka kumbura saboda kuka, ya ga yadda ta ke ƙoƙarin ɓoye masa damuwarta, amma duk da haka ya kasa tsayawa ya rarrashe ta, he had simply walked away, as if her pain meant nothing to him, wannan tunanin ya ƙara rikita mata kwakwalwa, ta juya ta rungume pillow ɗinta sosai, tana kuka a hankali, “Zayd…” ta furta sunansa cikin raɗa, muryarta na rawa, “Why don’t you love me?” Amma babu wanda zai amsa mata tambayar, ta share hawayenta da bayan hannu, ta ja dogon numfashi, sannan ta lumshe idanunta, a cikin wannan halin nata na baƙin ciki, wani sabon ƙuduri ya fara ƙarfafa a zuciyarta, duk inda mafita take, sai ta nemi ta, no matter what it takes, ko da kuwa tsadarta ya kai nisan dake tsakanin sama da kasa.
Zayd ya fito daga part ɗin Seeyama, ya rufe ƙofar entrance ɗin da key, sannan ya nufi wajen maigadi, da ya isa, ya sanar da shi cewa da safe ya nemo wanda zai cire macijin yazo, tunda suna iya jiran macizai indai akwai a gida, gateman ɗin, ya amsa cikin girmamawa, daga nan ya juya ya nufi part ɗin Raihana, sai a lokacin ne ya tuna cewa tun bayan kunun da Suhaila ta ba shi, bai sake cin wani abinci ba, yunwa ta fara damunsa sosai, amma saboda abubuwan da suka faru da daddare, bai ma kula da hakan ba, kai tsaye ya buɗe ƙofar ɗakinsa ya shiga, abin da ya fara gani shi ne Raihana a kwance a kan sofa, ta kudundune jikinta, har kanta a cikin hijab ɗinta, Zayd ya tsaya cak a bakin ƙofar, yana kallonta, what is she doing now? Ya rufe ƙofar a bayansa, ya shiga cikin ɗakin a hankali, Raihana kuwa, tun tana jin motsin ƙafafunsa, ta san shi ne, da ta ji an buɗe ƙofar, kunnuwanta suka gane sautin takunsa, amma ba ta motsa ba, ta ci gaba da kwanciya, jikinta a nade, kamar wadda barci ya ɗauke ta tun tuni, Zayd ya ƙarasa kusa da sofa ɗin, ya tsaya yana kallonta cikin nutsuwa, “Ke, tashi and get me something to eat,” babu amsa, ya ɗan karkatar da kansa, yana kallonta da wani irin kallo, “Can you hear me?” Har yanzu shiru, Zayd ya san tana farke, he could clearly see the slight movement of her legs beneath the hijab, duk da yadda ta yi ƙoƙarin ɓoye kanta, ya ɗan ja numfashi, sannan ya fara takawa a hankali, yana niyyar janye hijabin da ta rufe kanta da shi, amma kafin hannunsa ya kai gare shi, sai ya ga ta riƙe hijabin gammm! Zayd ya tsaya, ya kalli hannunta da ta damƙe hijabin, sannan ya ɗaga idanunsa zuwa inda fuskarta take a ɓoye, a hankali ya haɗe rai, ya ɗan ja baya, ya ɗan girgiza kansa, sannan ya sake magana, a wannan karon, muryarsa ta fito firmly, amma har yanzu cikin nutsuwa, “Tashi, kina ji ina miki magana? Ko kin cinye abincin ne bayan na fita?”