AMRAH (Force Marriage)

Chapter 4: A Lingering Fear

by @hauwajaywrites

Gobe za su fara exams, don haka suka shirya duk wani abu da za su buƙata. Tun da safe suke girki, sai wajen ƙarfe 11 suka kammala, Amrah ta wuce ɗakinta domin ta shirya, ita kuma Mufydarh ta wuce guest room ita ma domin ta shirya


Sai wajen ƙarfe 12 duk suka fito Mufydarh ta ce, “Wow mai ciki, kin yi kyau”


Amrah ta ce, “Kyaji da gulma! Kin san fa ba za mu daɗe ba, muna zuwa za mu fito. Kin san yau ba mu da enough time”


Duk suka shiga mota, Mufydarh ce take driving har suka isa gidan su Sultan


Suna shiga, suka haɗu da cousin sister ɗinsa Khadijah, a compound ɗin gidan, karar buɗe gate ɗin ya sa ta juya. Ganin Amrah da Mufydarh ya sa ta sake goron ruwan da take riƙe da shi ta yi ihu ta zo ta rungume Amrah, sannan ta rungumi Mufydarh


Ta karɓi basket ɗin da ke hannun Amrah ta ba wasu maids suka kai ciki, sannan ta riƙe hannun Amrah ta ce, “Kin ga Sister Mufydarh, ki masawa sweet aunt dina ta riƙa takawa a hankali”


Ta ƙarasa maganar tana karɓar jakar Amrah


Mufydarh ta yi dariya ta ce, “Wannan kuma ku kuka sani” Ta yi gaba ta bar su Amrah


Ammin Sultan ce kaɗai a parlour. Maids suka shigo da basket ɗin, ta ce, “Amrah ce ta zo?”


Suka ce, “Eh”


Ba su ma gama rufe baki ba sai ga su Amrah sun shigo. Ammi ta karɓe su hannu bibbiyu “Toh Amrah, har da wahala? Ke da ba ki da lafiya”


Ta faɗi hakan tana buɗe warmers ɗin. Hadaddiyar sinasir ce da miyar margi special, sai tamarind juice da snacks


Ammi tana son girkinta, hakan ya sa ta ji daɗi sosai, ta yi mata godiya


Ba su daɗe a gidan Ammi ba suka wuce ASD Mall domin siyayya. Sun yi siyayya sosai, sun tsaya ne sun sayi kayan babies da yawa, set ɗin kayan wanka, abin ɗaukar babies da sauran abubuwan da za su buƙata. Bayan sun biya suka wuce mota


Mufydarh ta ce, “Ni kam, na ga ba ki tsaya kin sayi komai na kanki ba, at least, ki samu abin fita kunya idan banda shegen mijinki ma by now da kin gama komai”


Amrah ta kalleta bata san cewa wannan ma kudin da Abbah ya bata bane, ta ce “Hmm, Mufydarh kenan”


Ta yi saurin juyowa ta kalleta

“Ko dai kin gama komai ne don ki yi mana surprise? But why har da ni?”


Amrah ta ce, “Mufydarh, I’m not really sure I’ll make it to that time, shi ya sa na maida hankalina kan baby. Ita na san za ta amfana da kayan”


Mufydarh ta ce, “Ban gane wannan maganar yaren da kike yi ba”


Ta ce, “Ki daina damuwa. In na haihu lafiya, komai ba zai gagara ba, in sha Allah”


Mufydarh ta ce, “Kin ji, idan har wannan tunanin naki za ki riƙa yi, toh please ki daina faɗa min, kin ji?”


Amrah ta ce, “Ai ni Musulma ce, dole ne in saka mutuwa a raina, balle haihuwa wadda take ƙaramin mutuwa”


Sai yamma sosai suka ƙarasa gida. Duk sun gaji, kowacce ta wuce ɗakinta. Bayan sun shirya, jin lokacin sallah ya yi ya sa suka yi sallar Magrib


Amrah ta fara fitowa. Da ta ga har lokacin Mufydarh ba ta fito ba, sai ta wuce kitchen ta ɗan shirya musu wani abu. Ta fito ta yi arranging ɗin abincin a dining area, amma har lokacin Amrah ba ta ga Mufydarh ba


Ta wuce ɗakinta ta buɗe ƙofa tana sallama. A bakin ƙofar ta gan ta tana waya. Mufydarh ta yi mata sign cewa ta jira ta a parlour. Amrah ta juya ta rufe ƙofar, hakan ya sa Mufydarh ta ending call ɗin ta biyo ta


Tare suka yi dinner, suka sake yin revision, sannan kowacce ta wuce ta kwanta


Washe gari tun da safe suka bar gidan. Dukansu sun yi exams ɗin, and it went well, Alhamdulillah


Tun daga nesa Mufydarh ta hango Amrah tana zaune a kan cool-down, kamar ba ta cikin walwala, ta yi sauri ta ƙarasa wajenta


“What’s wrong, bestie? Is it your health?”


Amrah ta ce, “Eh, bana jin daɗin jikina ne”


Ta ce, “Subhanallah! Toh, tashi mu wuce asibiti”


Amrah ta ce, “No, zan kira Mami, mu wuce gida kawai”


Suna isa gida, Amrah ta gagara hawa sama saboda stairs ɗin, sai kawai ta zauna a parlour. Mufydarh ta shiga kitchen ta fara sarrafa abinci. Spaghetti kawai ta daura saboda ta san yana dahuwa da wuri


Da ya dahu ta zuba musu a plate ta kai musu cikin parlour, tana cewa, “Amrah, I think you might be hungry”


Amrah ta ce, “Toh, hala”


Suna fara cin abincin sai suka ji sallamar Ayrah tana cewa, “Aunty Amrah, I’m here!”


Dariya Amrah ta yi ta ce, “Please, Mufydarh, open the door for her”


Mufydarh ta buɗe mata ƙofa. Ayrah ba ta ma gaida Mufydarh ba, ta wuce wajen Amrah da gudu tana dariya


Amrah ta ce, “Welcome back, my baby”


Sai a lokacin Ayrah ta gaida Mufydarh. Tare suka ci abinci, Ayrah tana ta ba Amrah labarai


Sai can yamma Ayrah ta ce za ta koma. Amrah ta riƙe hannunta suka tafi gidan Mami. A lokacin Mami ta dawo daga aiki tana hutawa. Su Amrah suka shiga suka gaisa sosai, sannan Amrah ta faɗa mata cewa ba ta jin daɗin jikinta, ta kuma gaya mata abin da yake damunta


Mami ta ce, “Kada ki damu, Amrah. This isn’t something to worry about”


Ba su daɗe sosai ba, sai Amrah ta koma gida


Washe gari da safe, suna shirin fita, sai suka ga driver ɗin Sultan yana wanke mota. Su Amrah da Mufydarh suka kalli juna


Amrah ta ce, “Na shiga uku, Mufydarh! Ko dai Ya Sultan ya dawo ne?”


Mufydarh ta ce, “Oh, kin ji ki! Wallahi, haushi kike ba ni idan kina nuna irin tsoron da kike masa”


Ta ɗauke kai ta wuce wajen motarsu ta shiga. Amrah ma ta ƙarasa ta shiga suka wuce


Bayan su Amrah sun gama exams, ta fito ta ƙarasa department ɗin Mufydarh tana jiran fitowarta. Sai can ta fito, kuma da ta ga Amrah sai ta fara murmushi


Amrah ta ce, “Mufydarh, I think it would be better if you stayed in the hostel, if you don’t mind, since Sultan is coming back today”


Mufydarh ta ce, “Okay”


Sai ta juya za ta tafi, Amrah ta yi saurin riƙe veil ɗinta


“Mufydarh, are you upset? Kin san halin Sultan, kuma ba na son ku haɗu, tunda a idonsa ke mai laifi ce”


Ta ce, “It’s okay, dear. I understand”


A nan suka yi sallama suka rabu