ZAYD ARMAAN

A MOMENT WITHOUT PRIDE

by @jiddaahbarkum



*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER 103*

*A MOMENT WITHOUT PRIDE*

*JIDDAAH BARKUM*

————-

Raihana ta ɗan buɗe fuskarta kaɗan, ta leƙo da idanunta ta cikin hijab din, kafin ta ce cikin wata murya mai ɗauke da ɗan haushi, “Ehh, na cinye. Ka koma inda ka je ka ci mana!” Zayd ya zuba mata ido, kamar ba zai ce komai ba, ya ci gaba da kallonta na wasu daƙiƙu, kafin ya ce calmly, “Tashi ki dafa min tea,” Raihana da sauri ta miƙe zaune, sai kuma kamar zaman bai ishe ta ba, ta miƙe tsaye tana ɗauke kai gefe, “Au! Ashe kasan dama ni ce mai haƙƙin ba ka abinci a yau? Amma shi ne ka tafi can ba ka ko faɗa min ba! Ai dai nasan ka san hukuncin mai ɗaukar kwana wata yana kai wa wata!” Zayd ya ɗan buɗe idanunsa, yana kallonta da uban mamaki, what does she mean? Wanne kwanan ya ɗauka ya kai ina? Ya tsaya yana nazarinta, kamar yana ƙoƙarin fahimtar inda maganar tata ta dosa, Raihana kuwa ta ɗauke kai, kamar ba ita ce ta yi maganar ba, kuma honestly, ba wai ta yi niyyar faɗin maganar a fili ba ne, ita ma jinta kawai ta yi tana escaping daga bakinta, Zayd ya ɗan matso kusa da ita, da sauri Raihana ta yi ƙoƙarin matsawa baya, amma kafin ta yi nisa, sai ya janyo ta cikin zafin nama, ya dawo da ita gabansa, ta sauke kanta ƙasa nan take, ta ƙi yarda ta kalle shi, Zayd ya zuba wa fuskarta da take kallon ƙasa idanu, kafin ya tambaye ta cikin sanyin murya, “Are you sure na kai mata kwananki?” Raihana ta murguda baki, gabanta na faɗuwa, ta yi shiru na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin tattara kalamanta, kafin ta fara magana a hankali, “Ai dai tun da nazo gidan nan, haka kake yi, jiya ma da muka zo, ai ko zama ba ka yi ba, can ka tafi, yau ma da safe ka je ka karɓo min wani jagwalgwallen dankali, yanzu ma ga shi, ai daga can kake, to, me ya sa za ka zo kuma kana tambayata abinci?” Ta ƙarasa maganar tana ɗan ɗaga kai, amma da ta haɗu da idanunsa, sai ta sake mayar da kanta ƙasa da mugun sauri, Zayd ya yi shiru, sai kuma a hankali ya ɗan ɗaga gira, kamar yanzu ne yake haɗa abubuwan da take faɗa, “Jagwalgwallen dankali?” ya maimaita cikin wata murya mai ɗauke da mamaki, Raihana ta haɗe rai, “Eh mana! Ai ka san abinda nake nufi,” Zayd ya ɗan karkatar da kansa, yana kallonta, “So, let me get this straight, kina kishi ne saboda na je part ɗin Seeyama?” Raihana ta buɗe baki da sauri, “Ni?!” Ta nuna kanta da yatsa, tana kallonsa da mamaki, “Waye ya ce maka ina kishi? Kishin me? Kawai dan mutum ya fadi gaskiyar shi, sai ka ɗauka kishi yake yi!” Zayd ya ɗan matsowa kusa da ita, da sauri ta sake mayar da kanta gefe, “Then why are you explaining where I went?” Raihana ta yi shiru, sai ta turo baki, tana ƙoƙarin ganin ko za ta iya samun wata amsa da za ta rufe maganar, “Saboda… saboda ka zo kana neman abinci ne! Ni kuma na gaya maka cewa ka je inda ka fito ka ci a can,” Zayd ya zuba mata ido, a wannan karon, ya ɗan sunkuyar da kansa kaɗan, kamar yana son ya tabbatar da abin da kunnuwansa suka ji, ya ɗan ɗaga gira, sai kuma ya sake tambayarta cikin nutsuwa, “Is that why you were watching me through the window?” Raihana ta ɗago kai da sauri, “You saw me?!” Da kalaman suka fita daga bakinta, sai ta gane kuskurenta, Zayd ya tsaya yana kallonta, Raihana kuwa ta buɗe baki, amma babu wata kalma da ta fito, ta sake buɗe baki, sai kuma ta rufe, kafin ta juya kanta gefe, ya Allah! Me ya sa bakina yake cin amanata ne haka?! Zayd ya ɗan taune leɓensa, yana kallonta da wannan nutsuwar tasa, hmm… ya ce kawai yana sake zuba mata idanunsa, waɗanda suka sa Raihana jin kamar duniya aka tara a kanta suke kallonta, ganin ba zai sake ta ba, kuma ba shi da niyyar daina kallonta, sai ta turo baki tana sake ɗauke kanta, “Toh, cikani! Na je na ɗauko maka abincin,” a hankali ya tambaya, cikin sanyin muryarsa, “Wanne abincin?” Ya ɗan karkatar da kansa, “Abincin da ya wuni a cikin warmers ɗin za ki ba ni?” A hankali ta ɗago kanta, suka haɗa idanu, sai ta kasa janyewa, shi ma kallonta yake, kamar yana ganin wata duniya ce daban a cikin idanunta, for a moment, babu wanda ya ce komai, shiru ne kawai ya mamaye tsakaninsu, yayin da idanunsu suka ƙi rabuwa da juna, sun kusa good two minutes a haka, kafin Raihana ta janye idanunta da sauri, tana jin yadda zuciyarta ke barazanar fasa kirjinta, a hankali ta buɗe baki, muryarta na dan rawa, “Ba shi ne ba… wani ne daban,” Zayd bai sake cewa komai ba, ya cika ta, yana ba ta hanya da alamar ta je ta kawo masa abincin, ganin abin da yake nufi ne ya sa ta sake kallonsa da pleading eyes, tana dan matsawa baya dan ta samar da tazara a tsakaninsu, “Don Allah toh… ka ɗauko, ni tsoron fita nake, yana nan a kitchen, please,” ya tsaya kawai yana kallonta, ba tare da ya ce komai ba, Raihana ta ɗan ƙara turo baki, tana kallonsa da shagwaɓa, “Please mana….” Zayd ya ci gaba da kallonta na wasu daƙiƙu, fuskarsa babu alamun abin da yake tunani, sai kuma a nutse ya juya, ya nufi hanyar fita daga ɗakin, har ya buɗe ƙofar ya fita, ba tare da ya ce mata komai ba, Raihana ta tsaya cak tana kallon ƙofar, da ƙofar ta fara rufewa, sai ta dafe kirjinta, “Na shiga ukuuuu!” ta faɗa a hankali, tana lumshe idanunta, what was that?! Ta girgiza kanta da sauri, kamar tana son korar tunanin da ya fara mamaye ta, sai kuma ta juya da sauri, ta koma inda take kafin shigowarsa, ta kwanta ta ja hijab ɗinta ta rufe kanta.

Zayd kai tsaye ya nufi kitchen ɗin, da ya shiga, ya tarar da warmers ɗin nan a jere a kan kitchen island ɗin, ya ɗan tsaya yana kallonsu a hankali, kafin ya ƙarasa kusa da su, ya buɗe warmer na farko, kamshin miyar ya tashi nan take, wani irin azababben ƙamshi da ya sa ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, kamar yana jin daɗin ƙamshin kafin ya sake buɗe su, a hankali ya buɗe na biyun, lafiyayyen tuwon da Raihana ta tuƙa ne, ya yi kyau sosai a cikin ledar da ta saka shi, Zayd ya tsaya yana kallon abincin na wasu daƙiƙu, fuskarsa babu alamun wani abu, amma a ransa yana mamakin irin yadda ƙamshin abincin ya jawo hankalinsa, normally, idan dare ya yi haka, ba ya iya cin heavy food, yawanci abin sha ko wani abu mai sauƙi kawai yake buƙata kafin ya kwanta, amma a wannan daren, for some reason, ya ji yana son cin abincin, ya ɗan karkatar da kansa, yana kallon tuwon da miyar, “Hmm…” ya furta a hankali, kafin ya juya ya ɗauko plate da spoon, ya ƙarasa wajen sink, ya wanke su sosai, sannan ya dawo, ya ɗauko tuwon, ya cire guda ɗaya ya zuba a plate, sannan ya zuba miyar a gefe, ya gama shirya komai, ya ɗauki plate ɗin, har ya juya zai fita daga kitchen ɗin, sai kuma ya tsaya, kamar ya tuna wani abu, ya juya ya nufi fridge ɗin domin ya ɗauko ruwa, amma a lokacin da ya buɗe fridge ɗin, idanunsa suka sauka kan glass jug ɗin coconut drink ɗin da Raihana ta yi, ya ɗan tsaya yana kallon jug ɗin, for a second, ya kasa kawar da idanunsa daga gare shi, sai ya tuna yadda ya ga ta shirya abincin a cikin warmers, yadda ta gyara kitchen ɗin, da yadda komai ya kasance cikin tsari, ya miƙa hannu ya ɗauki jug ɗin, ya ɗauko cup, ya zuba coconut drink ɗin a ciki, sannan ya haɗa su da abincin ya fito, bayan kusan minti arba’in, Zayd ya gama cin abincinsa, ya ajiye spoon ɗin a kan plate, ya jingina da bayansa, sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali, he had actually enjoyed the meal, abin da ya fi ba shi mamaki ma shi ne, ya cinye abincin da yawa fiye da yadda ya saba yi da dare, ya ɗan kalli plate ɗin da ya rage a gabansa, sannan ya ɗauki cup ɗin coconut drink ɗin ya shanye sauran, bayan ya gama, ya ajiye cup ɗin, amma maimakon ya miƙe nan take, sai ya yi shiru yana kallon wuri ɗaya, sai tunanin Raihana ya faɗo masa, ko ta ci abinci kuwa? Ya ɗan haɗe gira, ya girgiza kansa kaɗan, this girl and her drama, ya yi niyyar barinta amma bayan wasu daƙiƙu sai ya miƙe tsaye, ba tare da ɓata lokaci ba, ya koma kitchen ɗin ya ɗauko duka warmers ɗin da suka rage, a hannunsa, sannan ya nufi bedroom ɗinsa, da ya shiga, ya ajiye su a kan centre table ɗin da ke tsakiyar ɗakin, daga nan ya juyo da kallonsa zuwa kan sofa, ya zuba mata ido, yana jiran ko za ta motsa, ko kuma ta sake kawo wata dramarta, amma ga dukkan alamu, ta yi nisa a bacci, ya tsaya yana kallonta, a wannan karon, baccin gaske ne ya ɗauke ta, hijab ɗinta har yanzu ya rufe jikinta, sai dai ɗan motsin numfashinta yana nuna cewa tana barci sosai, hannunta ɗaya na manne da gefen hijabin, yayin da ɗayan yake ƙarƙashin kumatunta, Zayd ya tsaya a inda yake, yana kallonta na wasu daƙiƙu, fiye da minti biyar ya yi tsaye a haka, fuskarsa ba ta nuna wani abu na musamman ba, amma idanunsa suna kan ta, kamar yana nazarin yadda ta yi bacci, sai ya juyo ya kalli gadonsa, sannan ya sake kallon Raihana, a hankali ya nufi gadon, ya ɗauko duvet ɗin da ke kansa, ya dawo wajenta, ya sunkuya ya rufa mata da kyau, garin akwai ɗan sanyi, sannan sanyin AC ɗin ya ƙara sa ɗakin yin sanyi, ga dukkan alamu tana jin sanyi, musamman yadda ta kudundune jikinta a kan sofa, ya gyara duvet ɗin a hankali, ya tabbatar ya rufe mata jikinta sosai, a lokacin da ta ji dumin duvet ɗin, Raihana ta ɗan motsa, ta sake lafewa a ciki, sannan ta sauke ajiyar zuciya a hankali, Zayd ya tsaya yana kallonta na ɗan lokaci, sai ya miƙe ya koma kan gadonsa, ya zauna a gefen gadon na wasu daƙiƙu, idanunsa a kan wani wuri guda, kamar yana tunanin wani abu da shi kansa bai san mene ne ba, daga nan ya miƙe ya nufi wardrobe ɗinsa, ya buɗe ya ɗauko wani duvet din tare da wata armless shirt, ya koma ya kashe hasken ɗakin, ya bar hasken da ya rage daga compound yana ratsa gefen curtains ɗin yana haska ɗan ɓangaren ɗakin, daga nan ya koma wajen gadon, ya cire jallabiyarsa ya ajiye ta a kan rag ɗin da ke gefe, ya saka rigar da ya dauko, ya hau gadon, ya kwanta rigingine, yayi pillow da hannayensa, the room was finally quiet, Zayd ya lumshe idanunsa, yana tunanin ko zai iya samun barci cikin sauƙi kamar yadda ya saba yi a duk dararen da ya kwanta, amma sai ya ji wani irin yanayi da ya kasa fahimtar dalilinsa, ya buɗe idanunsa a hankali, ya ɗan juya kansa zuwa inda sofa ɗin take, Raihana tana nan a kwance, ba ta motsa ba, ya sake lumshe idanunsa, after a few minutes, ya buɗe su kuma, wannan karon kuwa, sai ya ɗan ɗage gira, yana mamakin kansa, ya sauke numfashi a hankali, ya juya ya kwanta da gefensa, yana mai ƙoƙarin kawar da duk wani tunanin da ya cika masa kwakwalwa, amma kamar yadda ya saba kasancewa mai son fahimtar komai, sai tunaninsa ya koma kan maganganun da ta yi masa a baya, ya tuna yadda ta ɗago kai da sauri lokacin da ya tambaye ta ko tana kallonsa ta window, a hankali, wani ɗan murmushi ya so bayyana a fuskarsa, jealous? He wasn’t sure, amma tabbas, yadda ta yi ta ƙoƙarin musanta komai ya fi komai ba shi mamaki, bai taɓa tunanin Raihana za ta damu da inda yake zuwa ko wanda yake tare da shi ba, a tunaninsa, kawai tana ganin sa ne a matsayin mutumin da kawai ta samu kanta a gidan aurensa, kuma ba ta da wani zaɓi face ta zauna, to, me ya sa ta damu da abin da ya yi? Me ya sa ta shirya masa abinci? Me ya sa ta ajiye shi a cikin warmers har komai ya yi tsari? Ya buɗe idanunsa sosai, yana kallon ceiling ɗin ɗakin, perhaps she was just being considerate, ko kuma tana ƙoƙarin cika haƙƙinta na mata, he didn’t know, and for someone like Zayd, not knowing something had always been irritating, ya ɗan juya ya kalli sofa ɗin a karo na ƙarshe kafin ya rufe idanunsa.

Tsakar dare ya riga ya yi nisa, shirun da ke cikin ɗakin kuwa babu abin da ke karya shi sai sautin AC da kuma numfashin mutanen da ke kwance, Zayd yana barci rigingine, hannunsa ɗaya a kan cikinsa, ɗayan kuma a gefe, babu alamar wani abu da ke damunsa, kamar yadda ya saba kasancewa a duk dararen da ya kwanta, sai kwatsam ya ji wata murya a hankali, “Maciji… maciji… maciji…” da farko, ya dauka a mafarki ne, ya ɗan motsa a kan gadon, amma bai bude ido ba, amma sai muryar ta sake tashi, “Maciji…” a wannan karon, Zayd ya buɗe idanunsa a hankali, ya ɗan ɗaga kansa, yana ƙoƙarin gano inda muryar take fitowa, sai kuma wata irin ƙara ta tashi a cikin ɗakin, har Zayd ya miƙe zaune cak, ya juya kansa zuwa inda take kwance, amma kafin ya fahimci abin da ke faruwa, sai ya ga tana kiciniyar faɗowa daga kan sofa, jikinta na rawa, hannayenta suna ta kai-komo kamar tana ƙoƙarin tserewa daga wani abu, idanunta a rufe suke sosai, “Maciji! Maciji! Ka cire shi! Ka cire shi!” Ta yi ta ƙoƙarin matsawa gefe, kamar tana son tsallake kujerar, amma saboda yadda take ta motsawa ba tare da sanin inda take ba, sai ta kusa faɗowa, da sauri Zayd ya miƙa hannunsa ya riƙe ta a tsayen da suke, “Raihana!” Amma kamar ba ta ji shi ba, ta fara ture shi da dukkan ƙarfinta, tana karkada kanta, “A’a! A’a! Ka cire shi! Zai cije ni! Zai cije ni!” Zayd ya daure ta da hannayensa, yana ƙoƙarin hana ta faɗowa daga sofa din, amma ina! Ta ci gaba da ƙoƙarin kwacewa, jikinta na rawa kamar tana ganin ainihin abin da take tsoro a gabanta, “Maciji! Maciji! Don Allah ka bar ni! Ka bar ni!” A hankali ya gane cewa ba farkawa ta yi ba, mafarki take yi, “Hey, look at me,” ya faɗa cikin wata murya mai zurfin nutsuwa, amma ita ba ta buɗe idanunta ba, sai kawai ta ƙara ƙoƙarin kwacewa, “Ba zan bar shi ya cije ni ba! A’a! A’a!” Ta yi wani irin motsi, har ta kusa sulalewa daga hannunsa, Zayd ya matse riƙonsa kaɗan, yana tabbatar da cewa ba za ta faɗi ba, amma duk da haka, ba ta daina ba, sai ya ɗan sauke numfashi, sannan ya fara karanta addu’o’i a hankali, yana tofa musu a hankali kamar yadda ya dace, yana maimaita su cikin wata murya mai taushi wadda ba kasafai yake amfani da ita ba, a hankali, sautin muryar Raihana ya fara raguwa, daga ihu, sai ta koma gunaguni, hannayenta suka daina turjewa da ƙarfi, amma har yanzu tana manne da shi, kamar tana tsoron cewa idan ta sake shi, abin da take gani a mafarkin zai dawo ya same ta, Zayd bai daina addu’ar ba, ya ci gaba da karantawa a hankali, hannunsa ɗaya yana riƙe da ita, ɗayan kuma yana shafaa bayanta, yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali, a hankali, Raihana ta fara yin shiru, numfashinta ya fara daidaituwa, ta sake yin wani ɗan motsi, sannan ta matso kusa da shi da kanta, kamar tana neman mafaka daga wani abu da ba ta son sake gani, Zayd ya ɗan tsaya na wasu daƙiƙu, sai ya rungume ta sosai, ya ɗora haɓarsa a kan kanta, idanunsa a lumshe, yana ci gaba da addu’o’in har sai da ya tabbatar ta daina firgita, a ƙarshe, Raihana ta yi shiru, ta yi luff a jikinsa, ta sauke ajiyar zuciya a hankali, kamar wanda ya yi gudu mai nisa ya samu wurin hutawa, Zayd ya buɗe idanunsa a hankali, ya ɗan sauke kansa, yana kallon ta, har yanzu idanunta a rufe suke, babu alamar ta farka, ya cigaba da kallonta, sannan ya ɗan motsa hannunsa a bayanta, still asleep, ya sauke numfashi, yana mamakin yadda ta koma barci cikin sauƙi bayan irin firgicin da ta shiga, a hankali ya gyara riƙonsa, sannan ya fara tafiya da ita zuwa kan gadon, still tana rungume a jikinshi, ya kwantar da ita a hankali, yana ƙoƙarin kada ya tashe ta, da ya tabbatar ta samu wuri mai kyau, sai ya fara ɗago jikinsa, yana shirin komawa gefensa, amma ya tsaya cak, ya ji hannun Raihana ya matse bayansa, da farko, ya yi tunanin wataƙila tana neman gyara kwanciyarta ne, sai ya sake ƙoƙarin tashi, a wannan karon kuwa, sai ta ƙara manne masa sosai, hannayenta biyu suka zagaye shi, kamar ba za ta yarda ya bar ta ba, Zayd ya tsaya cak, ya ɗan sunkuyar da kansa, yana kallon hannayenta da suka manne a bayansa, sai ya ɗaga idanunsa zuwa fuskarta, har yanzu tana barci, sai dai ta ɗan motsa kanta, ta matso da fuskarta kusa da kirjinsa, tana ƙara manne masa kamar ƙaramin yaro da ya samu wanda yake ba shi kariya daga abin da yake tsoro, Zayd ya yi shiru, ya yi ƙoƙarin cire hannayenta a hankali, amma duk lokacin da ya ɗan motsa, sai ta ƙara matse shi, a ƙarshe, ya tsaya, ya ɗan kalli duhun ɗakin, sannan ya sake kallon ta, “What am I supposed to do with you?” Ya furta a hankali, kusan kamar magana yake yi wa kansa, amma babu amsar da ya samu, bayan wasu daƙiƙu, sai ya sauke ajiyar zuciya, da alama ba zai iya tashi ya bar ta a haka ba, a hankali ya koma ya kwanta, ya gyara kansa a kan pillow, sannan ya ɗaga hannunsa ya jawo ta zuwa jikinsa, ya ɗora kanta a kan kirjinsa, ya rungume ta a hankali, sannan ya janyo duvet ɗin ya rufe su duka, Raihana ta yi wani ɗan motsi, kamar tana jin daɗin sabon matsayin da ta samu, ta gyara kwanciyarta, ta ɗan matse rigarsa a hannunta, sannan ta sauke ajiyar zuciya mai zurfi, Zayd ya tsaya ba tare da ya motsa ba, ya ji yadda numfashinta yake sauka a kirjinsa a hankali, ya ji yadda ta lafe gaba ɗaya, ba tare da wani alamar tsoro ba, sai ya ɗan sunkuyar da kansa, yana kallon kanta da ke kwance a kirjinsa, a wannan lokacin, babu wata magana a fuskarsa, babu kuma wannan yanayin sanyin da ya saba amfani da shi wajen ɓoye duk abin da yake ji, sai wani irin yanayi da shi kansa bai san yadda zai bayyana shi ba, domin a duk tsawon rayuwarsa, bai taɓa tunanin zai kwana da wata mace a rungume da shi saboda ita ce take buƙatar nutsuwa ba, amma ga shi yanzu, Raihana tana barci cikin kwanciyar hankali a kirjinsa, kamar ita ce ta fi kowa cancantar wannan wurin, Zayd ya ɗan lumshe idanunsa, ya so ya ce wa kansa cewa saboda mafarkin da ta yi ne kawai ya bar ta a haka, cewa idan ta farka, zai mayar da ita gefensa, cewa wannan ba wani abu ba ne da ya kamata ya yi tunani a kai, amma duk da ƙoƙarinsa, sai ya kasa hana hannunsa da ke bayanta ɗan matsawa, yana ƙara tabbatar da cewa ta samu perfect position, sannan tana cikin kwanciyar hankali, ya sake sauke numfashi, me ya sa yake jin wani irin abu a zuciyarsa? Me ya sa ganin ta cikin wannan halin ya sa ya ji wani abu da bai saba ji ba? Ya buɗe idanunsa a hankali, ya kalli fuskar da ta ɓuya a kirjinsa, ta rungumeshi gam gam da hannayenta kamar zai gudu, sai ya lumshe idanunsa shima, ya na dora ya sake rungumeta a hankali.

Da asuba, Zayd ya rigata tashi, ya shiga bathroom ya yi wanka, ya ɗauro alwala, sannan ya saka jallabiyarsa domin tafiya masallaci, ya ƙarasa bakin gadon, ya ɗan bubbuga gefen da take a hankali, Raihana ta fara motsawa kaɗan, kafin ta buɗe idanunta a hankali, “Assalah,” kawai ya faɗa mata, sannan ya juya ya fita, ya nufi part ɗin Seeyama kamar yadda ya saba, saida ya tabbatar ta tashi, sannan ya wuce masallaci, Raihana ta ɗan bi shi da kallo, tana ƙoƙarin buɗe idanunta sosai, da ƙyar dai ta samu ta tashi, ta zauna a kan gadon na ɗan lokaci, tana jin yadda barcin yake ƙoƙarin sake ɗaukarta, kafin ta sauko ta nufi toilet, ta yi alwala, tana ta mamakin yadda ta dawo ta kwanta a kan gadon, how did I get back here? Ta daɗe tana ƙoƙarin tunawa da abin da ya faru, amma duk yadda ta yi, ba ta iya tuna komai ba, ta girgiza kanta a hankali, ta ajiye tunanin a gefe, sannan ta fito, ta shimfiɗa darduma, ta yi sallah, bayan ta idar, sai ta ɗauki Qur’aninsa ta zauna tana ɗan karatu, ta yi karatun na ɗan lokaci, kafin ta ajiye Qur’anin a gefe, ta sake kwanciya a wurin da ta yi sallar, a hankali ta lumshe idanunta, kafin ta ankara, barci ya sake ɗaukarta.

A Malali kuwa… Bintu ta je wajen Maryam bayan sun idar da sallah, ta zauna kusa da ita, sannan ta dubeta cikin ɗan shagwaɓa, “Maryam, ko za mu je gidan Raihana? Yau na gaji da zaman gida, kwana biyu ban fita ko ina ba,” ta ɗan gyara zama, sannan ta ƙara da cewa, “Ki gwada tambayar mana Baffa, don Allah,” Maryam ta bita da kallo, kamar ba ta fahimci abin da take nufi ba, sai kuma ta ɗan ɗaga gira, “Toh, ki tambaye shi da kanki mana,” Bintu ta ɗan langwabe kai, “Kin san ni fa, Baffa ba wai sakar min fuska yake ba, idan ke kika tambaye shi, zai fi yiwuwa ya bar mu, don Allah ki tambaye shi, ya shigo daga masallaci fa,” Maryam ta yi shiru na ɗan lokaci, kafin ta amsa kawai da, “Toh,” aikuwa, da ta faɗa masa, ba dogon jayayya ya yi ba, ya ce su je, amma su tabbatar kafin la’asar sun dawo gida, haka nan da gari ya waye, suka fara shiri.

Zayd kuwa, sai wajen 8 ya shigo daga masallaci, sai da ya koma part ɗin Seeyama domin ya ga ko ta yi sallah, ai kuwa, a parlour ma ya tarar da ita, ta gaishe shi sama-sama, sannan ta ɗan gyara zamanta kafin ta ce, “Ina so in je asibiti anjima, har yanzu ban jin daɗi,” Zayd ya yi shiru yana kallonta, kamar yana jiran ta yi masa cikakken bayani, bayan wasu daƙiƙu, sai ya ce, “If kin shirya, tell me, sai na kai ki,” da sauri ta katse shi, tana ɗauke kanta gefe, “Ai da Mommy za mu je, ba asibiti ba ne, wajen mai magani ne, kwanaki da na yi ciwon kai irin wannan, can muka je,” ta ɗan dakata, sannan ta ƙara da cewa, “Yanzu dai anjima idan na shirya zan fito, na ɗauke ta sai mu je,” Zayd kamar zai yi magana, amma sai ya yi shiru kawai, ya gyada kai, “May Allah grant you shifaa,” “Amin,” ta amsa a ƙasa-ƙasa, tana harararsa ta ƙasan ido, tana jin wani irin haushi da ita kanta ba ta san yadda za ta bayyana shi ba, a hankali Zayd ya fice daga ɗakin, da ya fita, Seeyama ta ja wani uban tsaki, tana zabgawa bayanshi harara.