AMRAH (Force Marriage)

Chapter 5: Corpse

by @hauwajaywrites

Ta kwana, ta wuni, amma ba ta ji motsin Sultan ba. Gashi babu Mufidarh, gidan ya yi mata shiru, kuma ba ta jin daɗin zama ita kaɗai. Dan ma Ayrah ta zo mata dazu, ta ɗan rage mata kaɗaici, shi ya sa yanzu da ta koma karatu ita kaɗai, sai ta ji gidan ya sake yin mata shiru


Allah ya so, paper ɗaya ne ya rage mata. Sai yanzu ta ƙara tabbatar da cewa Mufidarh is her bond


Kafin ta wuce school, ta tambayi gateman ko Sultan ya dawo. Ya ce mata a’a, kawai an wanke motarsa ne, sai wata ta zo ta ɗauki motar ta fita da ita. Godiya ta yi masa, sannan ta tafi, zuciyarta ta samu wani irin relief


Tana fitowa daga exams ɗin, ta ga classmates ɗinta suna ta ɗaukar hotuna, suna murnar sun gama final exams ɗinsu. Zainab da Hafsa suna cewa ta zo ita ma a ɗauki hoto da ita. Karasawa gun ta yi, amma ta ce ba za ta shiga hoton dukansu ba na mixed gender, sai dai ta ɗauki hoto da Hafsa, sannan ta yi da wasu matan ajinsu kafin ta wuce department ɗinsu Mufydarh


Ai kuwa da ƙyar Amrah ta cire ta daga gun, domin Mufidarh kamar kam ba’a cewa komai, A ganinta result ne kawai zai hana ta zama graduate


Sai da suka ƙarasa wajen motar Amrah ta ce, “Toh Malama, ai sai ki nemi hijab ko veil ki saka ko?”


Mufidarh ta yi dariya ta ce, “Come on, ki ƙyaleni, kin san yadda nake ji idan na tuna cewa na kusa shiga camp? Oh my God!”


Tare suka koma gidansu domin su sanar da iyayensu cewa sun kammala exams, sannan suka wuce gidan Amrah


Washegari, Amrah na lissafin cewa saura kwana biyar a yi mata CS. Hakan na nufin daga lokacin za ta daina fita, amma at least, kafin ta daina fita, ya kamata ta haɗu da Farouq. Ko da zai wulaƙanta ta ne, ya kamata su haɗu ta nemi yafiyarsa::


Amrah na zaune a ɗakinta a bakin dressing mirror, tana updating wasiƙarta a cikin diary, sai Mufidarh ta kwankwasa ƙofa


“Yes Mufidarh, come in” Amrah ta hamsa


Mufidarh ta shigo, Amrah ta ɗago kai tana kallonta cikin murmushi “Wani abu ne?”


Mufidarh ta nuna diary ɗin da take rubutawa “Ke har yanzu kina nan kina fama da waɗannan rubuce-rubucen naki?”


“Yauwa Mufidarh, duk lokacin da na mutu, please ki ɗauko wannan diary ɗin, ki san yadda za ki yi da wasiyyar da ke cikinta, shi kenan, abin da nake buƙata from you”


Mufidarh ta ja dogon tsaki “Please, ki ƙyaleni haka” Ta juya ta fita, Amrah kuma ta ajiye diary ɗin, ta ɗauki hijab ɗinta ta sauka ƙasa


“Mufidarh ten minutes, ina zuwa”


Mufidarh ta ɗago kai “Ina za ki?”


“Ke dai na ce miki ina zuwa”


Ba ta jira ta ji abin da Mufidarh za ta sake faɗa ba ta fita da sauri, ba ta tsaya ko’ina ba sai office ɗin Umar Farouq


Ta yi sallama da secretary ɗinsa, ta sanar da ita cewa tana son ganin Umar, da ƙyar ta samu damar shiga office ɗin nasa


Farouq ya ɗago kai yana kallonta “Lafiya, Malama?”


“Please Farouq, ka ba ni minti biyar”


Shirun da ta ji ya yi ya sa ta gane cewa ya ba ta damar yin magana “Please Farouq, ka yafe min ka daina kallon abin a upside down”


Ta faɗa masa duk halin da take ciki. Hawaye sosai suke zuba daga idanunta, shi kuma yana kallonta, kamar yana ƙoƙarin gano gaskiyar abin da take faɗa


“Za ka iya zuwa wajen gateman ɗina, ya nuna maka CCTV footage ɗin. Maybe ka yarda da ni, sannan ka daina kallona a matsayin wadda ta zalunce ka” Ba ta jira abin da zai ce ba, ta juya ta fita abinta


Bayan kwana biyu, Umar Farouq na zaune a kan kujera, ya dafe kansa da hannayensa, duk abin da Amrah ta faɗa masa yana ta dawowa a cikin ƙwaƙwalwarsa


Kwanaki biyu kenan da ya kasa samun nutsuwa, gashi ba ya cikin walwala, zuciyarsa kuma tana son sanin ko gaskiya ne ko ƙarya, hakan ya sa dole ya yanke shawarar zuwa ya tabbatar da gaskiyar abin da ta faɗa masa


Amma idan har gaskiya ne, dole ya ɗauki mataki a kai. Dole Amrah ta bar gidan, domin ba zai iya jurewa yana kallonta tana cikin wahala ba


Suna zaune suna hira, Mufidarh ta ce, “Oh, wato dai nan da kwana biyu kin zama mama fa”


Amrah ta girgiza kai “Wallahi, zuciyata tana tsinkewa idan na tuna”


Suna cikin hirar sai suka ji ƙarar an buɗe ƙofar da ƙarfi, dukansu suka juya suna kallon ƙofar


Sultan suka gani a tsaye, fuskarsa cike da wani irin yanayi da ba su saba gani ba


A hankali Amrah ta juya ta kalli Mufidarh “Mufidarh, run!”


Ta miƙe kenan za ta gudu, shi kuma ya ƙaraso cikin ɗakin “Ban ce ki gaya musu su raba auren ba?”


Kafin Amrah ta iya cewa komai, ya ɗauke ta da mari


Mufidarh, wadda ta kusa isa bakin ƙofa, ta tsaya cak jin marin da ya sauka a fuskar Amrah ta ce


“How heartless are you?” Hawaye na bin kuncin Amrah, amma a wannan karon, ba ta ji tsoronsa kamar da ba


Ba ta san lokacin da Sultan ya ƙaraso gabanta ba. Kawai sai ta ji mari ya sauka a fuskarta ita ma


Ta dafe wajen, sannan ta ɗago kai ta kalle shi eyes to eyes “I’m Mufidarh not Amrah. I definitely won’t take this from you!”


Ga mamakinsa, kafin ya fahimci abin da ke faruwa, Mufidarh ta wanke shi da mari guda biyu, da dukkan ƙarfin da take da shi 


Daga haka ta juya ta gudu, tana mai alƙawarin cewa Amrah ba za ta sake kwana a gidan ba, no matter what. Shi ya sa ba za ta yi gangancin zuwa gidansu ba; gidan Anty Badiyya za ta je, domin ta san ba ta ɗaukar nonsense


Sultan ya tsaya a wajen sama da minti biyu, yana mamakin ƙarfin halin Mufidarh. A ransa ya yi alƙawarin cewa sai ya koya mata hankali a wannan ranar


Ganin haka ya sa Amrah ta miƙe da niyyar guduwa, don kada Sultan ya sauke haushinsa a kanta, kawai ya bi ta


Da ta kai bakin stairs, sai ya jawo ta da ƙarfi zuwa baya, ta faɗi ƙasa, bayanta ya bige da wani abu mai ƙarfi


Wani irin azababbèn ihu ta saki, da hannunta ta kama bayanta, zafin da ta ji ya sa ta kasa motsawa yadda ya kamata


Sultan ya tsallake ta ya wuce sama, ya ɗauki wani abu sannan ya sauko. Har yanzu Amrah tana ta kuka tana neman taimako, amma bai kula da ita ba, ya fita daga gidan gaba ɗaya.


Amrah kuwa ta fara bleeding, har ta ji kamar za ta tsuma


Da yardar Allah, sai ga Ayrah ta shigo. Ganin halin da Amrah take ciki ya sa ta fita da gudu, tana kuka, domin ta je ta kira Mami


Mami ba ta ɓata lokaci ba ta shiga gidan, amma ganin halin da Amrah take ciki ya tsorata ta matuƙa. Salati kawai take yi, domin ba ta san abin da za ta fara yi ba


Ba za ta iya kula da ita a gida ba, don haka ta kira driver ɗinta. Suka ɗauki Amrah suka nufi asibiti


Hankalin Mami ya tashi sosai. Gashi dama Amrah ba za ta iya haihuwa da kanta ba, ga kuma wannan matsalar da ta faru. Hakan ya sa Mami ta kira gidansu Amrah, ta sanar da su cewa dole su zo…


Farouq ya iso gidan, ya yi parking ɗinsa a ɗan nesa da gate ɗin, sannan ya ƙarasa da ƙafa


Ya yi sallama da mai gadin, ya kuma fara yi masa wasu tambayoyi cikin dabara. A nan ne ya ji cewa Sultan ba ya gidan Amrah ita kuma tana asibiti


Ya bi mai gadin zuwa ɗakin da ke gefen nasa, inda aka ajiye na’urar kallon CCTV footage. Da ya kunna ta, sai ya fara kallon abin da ya faru


He was totally shocked


Ya ci gaba da kallon footage ɗin, har zuwa lokacin da ya ga an fitar da Amrah cikin gaggawa, jikinta na zubar da jini


Ya kasa daurewa. Hawaye suka fara zuba daga idanunsa


Yana cikin wannan yanayin sai ya ji an buɗe gate, aka shigo gidan, amma ya kasa motsawa, tunani ya faɗo masa watakila Sultan ne ya dawo


Ya buɗe ƙofar ɗakin a fusace, yana jin kamar zai iya kashe Sultan da hannunsa


Amma Mufidarh da Anty Badiyya ya gani suna fitowa daga cikin babban gidan


Mufidarh kamar za ta zare. Kuka kawai take yi, har fuskarta ta sauya.


Farouq ya ƙarasa wajenta “Mufidarh, which hospital did they take her to?”


Sai a lokacin ta lura da shi “Oh, they’re at the hospital, please Farouq, take us there”


“I have no idea which hospital they took her to, ki gwada kiran gida maybe ba zasu rasa sani ba, but come pls abu zan nuna muku”


Da jin yadda ya yi maganar, kowa ya san cewa yana ƙoƙarin danne wani irin yanayi da yake ciki…


After sun fara kallo, Mufida ta rantse cewa sai ta kashe Sultan, ta fita gate da gudu 


Da ƙyar Anty Badiyya ta iya controlling ɗinta. Daga nan ta kira Mummy, ta tambaye ta asibitin da aka kai Amrah


Farouq ya shiga mota, ya ja su suka wuce asibitin


Everyone was there, da gudu Mufidarh ta ƙarasa wajensu. Kuka kawai take yi, ta kasa furta komai


Farouq ma ya ƙarasa wajen su, ya tsaya yana son jin halin da Amrah take ciki, amma kowa a wajen ya kasa magana, addu’a kawai suke yi, suna roƙon Allah Ya taimake ta ya sa abun yazo da sauki


Can sai ga Ammi ta iso ita ma, amma ganin halin da Mufidarh take ciki ya girgiza ta matuƙa


Amrah ta sha wahala, iya wahala, da ƙyar likitocin suka ciro baby girl ɗin


Sai a lokacin dukansu suka fara kallon juna, zuciyoyinsu cike da fargaba


Mami ta share hawayen da suka zubo daga idanunta, sannan ta fita ta ƙofar baya, gudun kada ta haɗu da family ɗin


Wani doctor ya ɗauki farin zanin da ke jikin Amrah, ya rufe fuskarta da shi, sannan ya fita daga ɗakin


Dukansu suka nufi wajensa, suna tambayarsa yadda Amrah take


A hankali ya girgiza kai “I’m sorry to say this, but there’s nothing more we can do. May Allah grant her Jannatul Firdaus”


A take, Mufidarh ta faɗi ƙasa, ta suma


kuna discouraging dina gaskiya, babu like comment🤦‍♀️ ko dan following acc din ma baku yi

and you guys haka kuke so na kawo dukka chapters din nan?🙄