RANTSATTSEN RABO

LOKACI CHAPTER 21

by @fulani32

Follow this link to join my WhatsApp group: ***

🕛⏳LOKACI🕛⏳

RABI'ATU FULANI 

YOTA

Under Team Yota's Amazing Pen's 

SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️ 

    ***

        PAGE2️⃣1️⃣

Wata da ke a kusa da ita ce ta yi saurin riƙeta, ta ce.

"Subhanallahi Sister Zahra baki da lafiya ne?"

Cikin ƙarfin hali ta ce mata "a'a lafiyata ƙalau" zame hannunta tayi ta nufi inda zata fara haɗa kayan aikinta, cikin rashin kuzari ta ke aikin, dan gaba ɗaya jikinta ya yi weak.

★★★

Zaune yake a cikin jirgi, yana jingine da jikin kujera, sanye da suit Black, hannunsa ɗauke da agogo sai yatsun sa da azurfa guda biyu, gashin kansa a gyare ya ke tsaff sosai sajen fuskarsa da gemunsa, suka fito da zallar kwarjininsa da kamala, wasu takardu ya zubawa ido yana nazarinsu, lokaci_lokaci yana duba saƙonnin da suke shigowa wayarsa, jin ana sanar da saukar jirgi ya rufe computer, ya tattara kayansa, sai ya jingina da kujera yana jiran saukar jirgin, ba'a wani jima ba jirgin ya sauka, cikin nutsuwa ya fito ya samu drivern sa na jiransa.

Kai tsaye Zay'd Signature Restaurant suka nufa dan hankalinsa gaba ɗaya yana can, 11 a can tayi masa, motar na tsayawa ya fito cike da nutsuwa ya nufi ƙofar yana duba agogon hannunsa, kai tsaye V.i.p ya nufa inda office ɗinsa yake a saman bene, office ɗin neat yake kamar yana nan kullum, zama ya yi ya lumshe idonsa.

Zuwa can ya ɗauki wayar office ɗinsa ya yi kira. "Ka sameni a office yanzu" yana faɗa ya yanke kiran, ba'a ɗauki dogon lokaci ba akayi knocking, izinin shiga ya bayar, cike da girmamawa manager ya gaishesa, wajen zama ya nuna masa, bayan ya zauna ya maida hankalinsa kansa.

"Ina fatan komai ya kammala?" Ya jefa masa tambayar har lokacin yana kallonsa.

"Eh in sha Allah nasan zuwa yanzu ta gama, dan tana da saurin aiki" kanshi kawai ya gyaɗa masa, daga nan sukayi magana akan abin da ya shafi wajen, sannan ya sallame sa.

Yana fita daga office ɗin kitchen ya nufa dan tabbatar da komai ya kammala kamar yanda ya bawa me gidan nasa tabbaci, sai dai da zuwansa ya samu saɓanin haka.

Cikin fargaba ya ce "Zahra ya naga haka? Ko rabin aikin bakiyi ba, kuma da an dawo daga masallaci zasu zo su ɗauka, duka baifi nan da 1hour" 

"Zanyi ƙoƙarin kammalawa kafin lokacin in sha Allah" ta basa amsa tana datse bakinta, dan sosai take jin ciwon nata yana ƙaruwa ga wata iriyar kasala da ta rufe, sannan ga fargabar da take jinta a ciki wadda ita kanta batasan kota menene ba, hakan sai ya haɗu ya ƙara mata rashin kuzari da karsashi.

"Nasan yanzu masallaci oga zaije, dan Allah kafin mu dawo komai ya zama ya ready" 

"In sha Allah" ta basa amsa tana maida hankalinta kan aikin, juyawa ya yi ya fita, ita kuma ta ci gaba da aikin, daga lokacin da ta fara aikin zuwa yanzu ya ci ace ta gama, koda bata gama ba kaɗan ne ƙarashen, amman ta rasa kuzarinta, sosai ciwon ya ke takura mata, tana daɗewa batayi ciwon mara ba, amman duk sanda ya tasar mata bazaka taɓa cewa zata rayu ba.

★★★

Suna dawowa daga masallaci ya dakata bai hau sama ba.

"Aje a fito min da kayan" ya ce ya na zama akan kujera.

Manager ne ya nufi kitchen ɗin, yana fatan ace ta gama aikin, sai dai fatansa bai tabbata ba, dan ko a bayan tafiyarsa ba wani abin kirki ta ƙara akan wanda ya barta tana yi ba, shi dai ya rasa yau me ya ke faruwa da ita dan yasan ba haka take ba, dole ya dawo ya ce masa da saura ba'a kammala ba.

Agogon hannunsa ya kalla ba tare da yace komai ba, ya miƙe ya nufi sama, zama ya yi yana ta faman duba agogo, a ƙalla sai da ya ƙara musu cikakkiyar awa ɗaya, aka koma shi ma bata gama ba.

"Menene matsalar ne?" Ya tambayi manager yana tsare sa da idanuwansa masu kaifi.

"Sir wadda aikin yake hannunta ne ba ta kammala ba, ina tunanin.."

"Wadda aikin ya ke hannunta? Wacece haka?" Ya katse sa idonsa yana canza launi.

"Sabuwar ma'aikaciyar mu" ya ba sa yana janye kallonsa daga kan ogan.

Shiru Zay'd ya yi, da farko ya yi tunanin matsala ce ta kayan aiki, ko kuma daga ma'aikatan, amman ashe ba haka bane, saboda mutum ɗaya ne, me ya sa take son dole sai ta rusa masa kasuwanci ne. "Daman bata san aikinta ba kuke ta zuzuta har muka dawo da ita nan?" Ya jefa masa tambayar kamar shine Zahran.

"Sir tana ƙoƙarin aiki sosai, kawai dai yau.." kallon da ya ke masa ne ya hanasa ƙarasa abin da yayi niyyar faɗa.

"Wannan wane irin sakaci ne haka?" Ya faɗa cikin ɓacin rai yana miƙewa tsaye daga kan kujerarsa. "Mutane sun zaɓi restaurant ɗina a cikin wurare da dama da suke da su, sun ba mu wannnan daman ne saboda sun amince da mu da ƙwarewarmu, amman a ƙarshe me za mu nuna musu rashin iya aiki?" Shiru yayi yana ƙoƙarin danne fushin da ya fara taso ma sa.

"Yanzu an ɗauki ragamar aikin gaba ɗaya an bata, amman ƙarshe tayi min shirme, batasan menene aikinta ba gaba ɗaya, bata cancanci zama a cikin restaurant ɗina ba"

Sunkuyar da kai manager ya yi, gaskiya ne, shi ma ya san muhimmancin aikin, kuma daman yasan jinkirin kammala shi ba ƙaramin abu ba ne, amman shi yanzu abin da yafi ɗaga masa hankali yanayin CEO ɗin, ya san Zay'd, ya kuma san yanda yake ɗaukar aikinsa da muhimmanci, baya wasa da duk wani abu da zai iya kawowa restaurant ɗinsa matsala, gashi babbar matsalar idan har ransa ya ɓaci baya buƙatar jin komai daga bakin wanda yayi masa laifin, duk da shi ɗin managernsa ne, sai ya ji ya kasa ce masa komai kamar shine yayi masa laifin.

"Kasan adadin manyan mutanen da zasu halarci wannan taron da suke?" Zay'd ya tambayesa yana mayar da kallonsa garesa.

Sai da ya haɗiye yawu sannan ya ce "na sani sir"

"Idan har ka sani, me ya sa ka bari hakan ya faru, ina saka idonka akan aikin? Meyasa baka tsaya akan komai ba kamar yanda aka saba, ka sakar mata ragamar gaba ɗaya? Toh ma ina sauran ma'aikatan?"

"I'm sorry sir, zanje yanzu a kammala aikin, ka ƙara mana ko 1 hour ne"

Agogon hannunsa ya kalla "mun ƙara 1 hour akan lokacin da akai za'a kai musu kayan su, zaku kunyata ni a wajen mutanen da suka yarda dani" ya faɗa cikin wani irin yanayi.

Shi dai manager ƙara sunkuyar da kansa yayi, saboda ganin yanda ɓacin rai ya bayyana ƙarara akan fuskar ogan, shiru yayi masa badan bashi da abin cewa ba, sai dan ya ga a duk sanda yayi magana kamar yana ƙara harzuƙa shi ne, amman ko ba komai ya so a ce ya kareta, babu yanda zai yi shiyasa ya yi shiru.

"Ya sunan yarinyar?" Ya jefa wa manager tambayar yana ɗaukar wayar office ɗin.

"Zahra" ya basa amsa yana kallonsa ta ƙasan ido.

Kai tsaye kitchen ɗin ya kira, yana jin an ɗaga cikin kakkausar murya ya ce "Zahra ta zo office ɗina yanzu!" Bai jira amsar wanda ya ɗaga ba ya katse wayar ya juyawa office ɗin baya..

★★★

A kiɗime wadda ta ɗaga kiran ta ce "innallilahi sister Zahra" 

Idanuwanta da suka yi wata kala saboda ciwo ta ɗago ta watsa mata. "Me ya faru?" 

"CEO ne ya kira ya ce kije office ɗinsa, nasan kuma akan aikin nan ne" ta faɗa tana bin ta da kallon tausayi. Kusan gaba ɗaya sai da suka maimaita kalmar CEO.

"Allah sarki wallahi ina tsoron Allah ina tsoron case ya haɗani da oga akan aiki, gaskiya na tausaya miki, daman tun da aka fara maganar order nan, da kuma yanda aka ce zai zo da kansa, nasan ba ƙaramin abu bane, amma gaskiya banyi tunanin zai kira ki kai tsaye ba, na zata faɗan akan manager zai ƙare" cewar wata tana kallon Zahra.

Wata kuma ta girgiza kanta "Ni dai shawara ɗaya zan baki, kawai ki basa haƙuri ki faɗa masa baki da lafiya, yana da tausayi sosai matsalar kawai baya wasa akan aiki, mussamman idan ya shafi manyan mutane" caa suka mata aka kowa da abin da yake furtawa.

Ita dai tana zaune, hannunta dafe da mararta da take mata wani irin ciwo, sosai take ƙoƙori wajen shanye ciwon, duk da yanda maganganun nasu suke shiga cikin kunnenta ba su ne a gabanta, ciwon da ya ke ƙaruwa shine damuwarta. Kallon kayan aikin da bata ƙarasa ba ta yi, haka kawai taji wani irin yanayi na damuwa ya ratsa zuciyarta, saboda bata taɓa fuskantar irin matsalar nan akan aikinta ba sai yanzu, bata da yanda zatayi ne shiyasa, ta so kammala aikin, amma yanayin jikinta ya ƙi bata haɗin kai, dole kuma tabi sa a yanda yake so.

"Zahra kina jin abin da muke ce wa?" Ɗaya daga cikin su ta tambayeta tana taɓa hannunta.

A hankali ta ɗago idonta daya kaɗa yayi ja ta ce "Na ji" 

"Toh yanzu ya za ki yi da kiran da yake miki?"

Bata son magana su kuma sunƙi ganewa, maganar ma gani take ƙara mata ciwo ta ke " ya zanyi kuwa, zanje naji me zai ce min" cikin sanyin murya ta yi maganar, sannan ta miƙe a hankali tana cize baki.

Duk kallon juna sukayi, ganin kamar bata damu ba, su duk suna jiye mata tsoro, amman ita da alama ko a jikinta, sosai suka ci gaba da zuzuta mata abin amman ta kasa ƙara ce musu komai, ƙarshe kawai ɗan murmushi ta yi musu, sannan ta fita ta nufi hanyar office ɗin. Da kallon tausayi suka bita, tare da yi mata addu'ar Allah yasa su wanye ta lafiya, suna jin tsoronsa kodan yanayinsa da kuma kwarjinin da Allah ya yi masa, amman sun ga ita babu ruwanta, duk da dai da yawa daga cikinsu suna ganin dan batasan sa ba ne, ko kuma dan basu taɓa haɗuwa ba.

Tana tafiya tana hutawa, sosai ciwon yake ƙara cinta, duk yanda take so tayi sauri, abu ya gagara, so take ta yi sauri gudun ƙara laifi, amman ta kasa, da ta ɗaga ƙafarta da niyyar yin sauri, sai ciwon ya ƙara tsananta, da ƙyar ta iya hawa benen ta ƙarasa bakin office ɗin, wani irin birki ta ci ta dafe saitin zuciyarta da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ta ɗorasa akan cikinta, idonta ta runtse ta fara karanta duk addu'ar da ta zo bakinta, sai da ta samu nutsuwa sannan tayi knocking.

Manager ne ya bata izinin shiga, dan shi kam ko nuna alamun yaji ana masa knocking bai yi ba.

A hankali ta tura ƙofar office ɗin ta shiga, kanta a ƙasa, so take ta buɗe bakinta ta gaishesu, amman ta kasa buɗewa, sai ma kakkarwa da lips ɗinta suka fara, wanda ta alaƙanta hakan da ciwon da mararta yake.

Manager yana tsaye fuskarsa cike da rashin jin daɗi, kallo ɗaya yayi mata ya fahimci tana cikin ciwo, shi kuma ogan ya bata baya bare ya fahimci halin da take ciki.

Zay'd ya na tsaye, hannuwansa a bayansa, ransa a mugun ɓace yake, mussamman saboda wayar da ya amsa kafin ta shigo office ɗin, wanda itace ta ƙara tunzura shi, tun da ta shigo bai juyo ya kalleta ba, tafi 10minute a tsaye, cikin dakakkiyar muryarsa ya fara magana, cike da ɓacin rai.

"Kin san irin aikin da aka baki kuwa? Kin san muhimmancin orɗern nan a wajena?" Ɗan dukan teburin gabansa yayi, saboda ya fara rasa control ɗinsa, ganin ana kiran wayarsa, idonsa akan wayar ya ci gaba da magana. "Manyan mutane ne suka zaɓi restaurant ɗin nan, bansan ta ya zan iya basu uzuri ba, kin kunyata ni da ni da restaurant ɗina, dan abu ne damu taɓa fuskata ba, an ɗora miki nauyi kin gaza, tun yaushe ya kamata ace kin gama aikin, amman gashi har lokacin da ya kamata ace kin kammala aikin ya wuce baki gama ba!"

Tana jin duk abin da ya ke cewa amma ta kasa ɗago kanta, ciwon da take ji shi hanata mayar da hankali akan abin da yake faɗa gaba ɗaya, da kuma wani abu da take ji na daban. Tana jin yanda ya ci gaba da faɗa da faɗar muhimmanci aikin, amman ta kasa taɓuka komai.

Manager ya rasa abin yi daga ya kalli Zay'd sai kuma ya kalli Zahra da kanta ya ke ƙasa, ba ka gane yanayin da take ciki, sai dai shi da yake kallonta, yana ganin yanda bakinta yake ta motsi, haka kawai ya ji wani irin tausayinta ya na ratsa shi, tsoro ya ke ogan ya ci gaba da magana, saboda akwai inda baya son ya je a faɗan nasa, dan haka ya yi ƙoƙarin dakatar da shi.

"Sir.."

"Kayi min shiru" Zay'd ya katse shi ba tare da ba shi damar ƙarasa maganarsa ba.

Shiru yayi ya haɗiye yawu, sannan da dabara ya ɗan matsa kusa da Zahra, addu'a ya ke tayi a zuciyarsa abin ya tsaya iya haka, kallonta ya ke tayi yana mata alamar ta ɗago kanta ta basa haƙuri, amman taƙi ya.

Tana tsaye a waje ɗaya, tana ta faman wasa da zoben hannunta, hannunta yana ta rawa duk da tana ta ƙoƙarin hana tasirin hakan bayyana a fili, amman Allah kaɗai yasan a irin halin da zuciyarta take ci, sosai muryarsa take ratsa ta, ji take kamar tasan muryar a wajen wani, wani irin sauti ne da take ta ƙoƙarin hana kanta amincewa da shi, sosai sautin muryar tasa ta sauya mata bugun zuciya, ita kanta tasan a lokacin bugun da zuciyarta take ba'a bisa ƙa'ida take yin ta ba.

Saurin kawar da duk abin da take ji ta yi tare da kawar da tunanin da yake kutso mata. "A'a ba zai yiwu ba, ba shi ba ne, wataƙila saboda yawan tunaninsa da nake yi ne, shiyasa nake jin muryar wani tana min kama da tasa" ta faɗa a cikin zuciyarta. Sosai take ƙoƙarin kawar da tunanin, kawai kuma ta ƙara jin muryar Zay'd ɗin ta ƙara ratsa cikin kunnenta.

"Kin ji abin da nace miki?" Ya tambaye ta cikin fushi.

Haɗiye yawu tayi, jin yanda zuciyarta ta ƙara bugawa da ƙarfi, wannan muryar.... Me ya sa take jin muryar nan, me ya sa duk lokacin da ya yi magana, sai taji kamar wani abu yana motsa wa a cikin zuciyarta, sosai take ƙoƙarin danne wannan tunanin amman ta kasa, a hankali wani ɓangare na zuciyarta, ya fara gazgata mata cewar muryar ce, ji tayi tsayuwar tana neman gagarar ta, haka kawai taji lallai tana son kallon fuskarsa dan tabbatar da muryar tasa ce, ko kuma kawai tunaninta ne yake bata hakan.

A ɓangare ɗaya kuma zuciyarta tana jin tsoron abin da za ta gani, domin idan har dagaske shi ne wanda take tunani, toh me hakan yake nufi? Ƙara matsa zoben hannunta tayi da ƙarfi, tare da ƙoƙarin dawo da nutsuwarta jikinta.

Shirun da ta yi masa yafi komai ƙara fusata shi, abin da bai sani ba, bama fahimtar abin da yake cewa take bare tayi ƙoƙarin kare kanta.

Manager sosai yake kallonta, har ya gaji da yi mata alamar ta basa haƙuri.

"ko kin ɗauka saboda ke ce kike aikin nan, kina da damar yin duk abin da kika ga dame ne?"

Da ƙarfi ta runtse idanuwanta, mararta ta murɗa fiye da yanda take murɗa mata, ba ciwon bane damuwarta, wannan muryar ta mutumin da ke gabanta ne, ƙarshe ta kasa sarrafa kanta da zuciyarta, ta kasa jurewa, ta ka sa gazgata zuciyarta akan cewa hasashe ne take kawai.

A hankali ta fara ɗago kanta, kamar mai jin tsoron abin da za ta gani.

A lokacin ne ya juyo a fusace dan ganin da me take taƙama da har zai ta mata magana ta kasa ce masa uffan, wacece ita???

Saukar idanunsa akan fuskarta yayi daidai da ɗagowar fuskarta, a lokaci ɗaya idanuwansu yayi wani irin sarƙewa a cikin na juna......

FULANI
***