AN UNYIELDING HEART
*ZAYD ARMAAN*
*CHAPTER 105*
*AN UNYIELDING HEART*
*JIDDAAH BARKUM*
—————
Ta ɗaga gira, tana kallon Bintu da wani irin expression na wulaƙanci, “Because honestly, I wouldn’t be surprised, someone has to take care of her, right?” Ta yi wata ƙaramar dariya, sannan ta ƙara da wata murya mai cike da izza, “But seriously, Bintu sunanki koh?, what exactly are you doing here? Of all the places you could visit, you chose this house?” Ta sake kallon gate ɗin, kamar ma gidan kansa bai cancanci kasancewarta a cikinsa ba, “Unbelievable,” a hankali ta gyara zamanta a kujerar motar, ta ɗora hannunta a kan steering wheel, sannan ta kalli Bintu da wani irin kallo na raini, “Tell me something, do you people now come here to beg for attention, or is there some other reason I’m not aware of?” A wannan lokacin ne Raihana ta bayyana a wajen, ta fito da sauri, fuskarta ɗauke da murmushi saboda farincikin waɗanda suka zo mata ziyara, amma da ta ga Seeyama a cikin motarta tsaye a wajen murmushin ya ɗan dusashe, Seeyama kuwa ba ta damu da kallon Raihana ba, idanunta suna kan Bintu ne kawai, tana jiran amsar da za ta ba ta, Bintu ta ɗan ɗaga gira, sannan ta kalli Seeyama daga cikin nutsuwa, “Seeyama, nasan kinsanni ba zaki musa haka ba amma kin tana ganin nazo bara wani wajen ne?” Seeyama ta yi wata ƙaramar dariya, “Nasanki fa kikace? Please, don’t flatter yourself,” ta ɗan karkatar da kanta, sannan ta ƙara da raini, “I asked you a simple question, answer it,” ta nuna gate ɗin da yatsanta, “What are you doing here?” Bintu ta yi murmushi sosai har haƙoranta suka bayyana, as though Seeyama’s attitude was nothing more than an amusing joke to her, sannan ta juya ta kalli Raihana dake gefenta, wacce ta tsaya cak kawai tana kallon ikon Allah, apparently still trying to process what was happening, a hankali Bintu ta ƙarasa wajenta, ta dafa kafadarta da hannu ɗaya cikin yanayin maida martani, kafin ta juyo ta fuskanci Seeyama, ta buɗe baki a hankali, with an unusually innocent expression on her face, wanda ko kaɗan bai yi kama da na Bintu da aka sani ba, “Kin ga wannan?” ta tambaya, tana nuna Raihana, tana dan karkatar da kanta, “Na san kin santa, ita ce uwargida a nan, ko?” Ta ɗan dakata, tana kallon Seeyama kai tsaye cikin idanu, “Toh, wajenta na zo, kanwata ce, she’s my little sister, are we clear?” Seeyama ta kalli Bintu da wani shegen kallo, as if she couldn’t believe the nonsense she had just heard, sannan ta maida kallonta ga Raihana, kafin ta fashe da wata irin dariya ta raini, “Ke, kina da hankali kuwa? Are you even in your right senses?” ta tambaya, tana kallon Bintu kamar wacce ta gama rasa hankalinta, “Kin san me kike cewa kuwa?” Bintu ta yi dariya, this time without even trying to hide her amusement, “A cikinmu dai za a gane wanda ke hauka,” ta faɗa cikin nutsuwa, tana ɗan karkatar da kanta, “Because what I just said is very simple, Seeyama, just like ABCs,” ta ɗaga kafaɗarta kaɗan, as if the whole argument meant absolutely nothing to her, daga haka ta juya wajen Raihana, ta sake kallonta da murmushi, sannan ta kalli Maryam ma, wadda har yanzu take tsaye cikin mamaki, ta kasa ko motsi, “Mu je,” Bintu ta faɗa a sauƙaƙe, Raihana kam, ta fara tafiya ba tare da ta ce komai ba, she was still too surprised to find the right words, musamman ganin yadda Bintu ta tsaya ta yi magana irin wnn da Seeyama without the slightest hesitation, Maryam ma ta biyo su, har yanzu tana kallon Bintu da mamaki, as if she had just discovered an entirely different side of her, amma kafin Bintu ta juya ta bi su, sai ta sake kallon Seeyama, ta yi mata wani ƙaramin wink da ido ɗaya, a fuskarta akwai murmushin da ke nuna cewa she knew exactly how much her words had annoyed her, daga nan ta juya ta ci gaba da tafiyarta, as though nothing unusual had happened, Seeyama kuwa tana zaune a cikin motarta, tana kallonsu har suka shige part ɗin Raihana, fuskarta ta sauya gaba ɗaya, murmushin rainin da ke tattare da ita tun farko ya ɓace, “Unbelievable!” ta furta cikin mamaki, tana matse steering wheel ɗin da hannunta, ta sake kallon ƙofar da suka shiga, her jaw tightening as Bintu’s words replayed in her head, she’s my little sister, “Kanwarta?” ta maimaita a hankali, tana dariya cikin disbelief, “We’ll see about that,” daga ƙarshe ta juya cikin fushi, ta kalli gateman, wanda tuni ya wangale gate ɗin domin ta fita, da alama shi ma ya fahimci cewa idan ya yi jinkiri, zai iya zama wanda za ta sauke wa haushinta, aikuwa, Seeyama ta figi motar da mugun gudu, har sai da tayi kamar zata taka shi gateman ya ja da baya da sauri, the car sped out of the compound like she was racing against time, as though staying there for another second would make her lose her mind, gateman ya bi motar da kallo, sannan ya girgiza kai a hankali, “Allah ya kyauta,” ya furta a ƙarƙashin numfashinsa, a can kuwa, suna shiga part ɗin Raihana, Maryam ta juya ta kalli Bintu, fuskarta a haɗe, clearly, ba ta ji daɗin yadda Bintu ta tunkari Seeyama ba, “Dama abin da ya sa kika ce mu zo kenan? Kin san kina da hidden agenda! Meyasa za ki yi haka? Kin san wacece ita kuwa, har za ki zo nan ki mata haka?” Ta ɗan dakata, tana kallon Bintu cikin damuwa, “Idan Baffa ya ji fa? What if ta gaya wa mijinta, shi kuma ya kai ƙararki wajen Baffa? Kin san ba kanki ke kaɗai abin zai tsaya ba, dukanmu abin zai shafa!” Bintu ta tabe baki, ba tare da ta nuna wata damuwa da maganganun Maryam ba, ta zauna a kan sofa ɗaya, idanunta suka fara yawo a cikin ɗakin, tana kallon kayan alfarma da ke ciki yadda aka tsara komai cikin tsari, sannan ta mayar da hankalinta ga Maryam, fuskarta ɗauke da halin ko-in-kula, “Ta ina zai sani? Sai dai idan ke ce za ki gaya masa,” ta ɗan gyara zamanta a kan sofa, sannan ta ƙara da wata murya mai nuna cewa batun ya gama ƙarewa a wajenta, “Kuma kin san me ta yi min kuwa?, ba ki sani ba, so, please, ki bar maganar nan, babu ruwanki,” Maryam ta buɗe baki kamar za ta sake magana, amma ganin yadda Bintu ta nuna ba ta son ci gaba da tattaunawar ya sa ta yi shiru, Raihana kuwa, tun lokacin da suka shigo, take kallonsu kawai, she was still processing everything that had happened at the gate, musamman yadda Bintu ta kira ta kanwarta a gaban Seeyama ba tare da ko ɗan shakku ba, daga ƙarshe, Maryam da Raihana suka zauna suma, a hankali aka ajiye maganar Seeyama gefe, aka fara hira, Bintu kuwa, da farko tana ta wani shegen shan kamshi, sai kuma daga baya ta saki jikinta ta fara saka baki a hirar, Raihana ta ɗan kallesu, sannan ta tuna da cewa ba ta ma ci abinci ba, “Ni fa ko breakfast ban yi ba, ku zo mu shiga kitchen mu samu abinci,” Maryam ta miƙe nan take, “Toh, mu je, I’m actually getting hungry too,” su uku suka shiga kitchen, da suka shiga, Maryam ta kalli tuwon jiya dake nan kan kitchen island din, ta ɗan buɗe warmer ɗin tana duba abin da ke ciki, “Ai kawai mu dumama wannan tuwon mu ci, yana da ɗan yawa ma, idan ya so, anjima kafin mu tafi sai mu taimaka miki ki dafa wa mijinki abincin dare,” Raihana ta ɗan dakata tana kallon Maryam, Maryam kuwa ta juyo ta kalleta, fuskarta ɗauke da murmushin da ke nuna cewa tana shirin yi mata tambayar da ta daɗe tana son yi, “Amma, wait a minute… ko ba a ɗakinki yake ba?” Raihana ta zuba mata harara, a fili tambayar ba ta yi mata daɗi ba, “Ban sani ba, ki jira ya zo, sai ki tambaye shi!” Maryam ta fashe da dariya, “Ke, rayy! Wai kishi daga tambaya sai ki fara faɗamin baƙar magana? What did I even say?” Raihana ta yi mata banza, ta juya tana ƙoƙarin yanayinta, “Please, Maryam, just leave me alone,” Maryam ta sake dariya, tana kallonta da wasa, “Ai kuwa na ga alamun akwai abin da kike ɓoyewa, you can’t even answer a simple question without getting defensive,” Raihana ta ɗan girgiza kai, “Wallahi, Maryam, ki daina, ba ni da lokacin shirmenki,” amma a zuciyarta, ta san Maryam ta taɓo wani wuri da ba ta son a taɓa, gaskiya ita sam ta manta cewa daga nan gaba, rabon kwana zai fara, tun bayan zuwanta gidan, hankalinta ya fi karkata ga abubuwan da suke faruwa tsakaninsu, har ba ta tsaya tunanin yadda tsarin zaman aurensu zai kasance ba, da ta ga Maryam na shirin sake buɗe baki, sai ta yi saurin sauya maganar, “Anyway, ku gaya min, ya gida? Umma fa?” Maryam ta fahimci cewa Raihana ba ta son a ci gaba da maganar Zayd, don haka ta karɓi sabon topic ɗin ba tare da ta matsa mata ba, suka ci gaba da hirarsu suna dumama abincin, bayan sun gama haɗa abincin, suka koma falo, suka zauna suna ci, ana yin hira lokaci-lokaci, Bintu kuwa ta sake sakin jikinta gaba ɗaya, tana shiga hirar da dariya, har sai da Raihana ta fara jin daɗin kasancewarsu a gidan, for the first time that day, hankalinta ya ɗan kwanta, aƙalla tana da mutane a kusa da ita da za ta iya zama da su ba tare da tunanin duk wani abin da ke damunta ba, kuma yayin da suke ci suna hira, Bintu ta ci gaba da harkarta kamar dai abin da ya faru a gate ɗin ba wani abu ne mai muhimmanci a wajenta ba, amma Maryam kuwa, duk da tana dariya tare da su, har yanzu tana tunanin abin da zai iya biyo bayan yadda Bintu ta ma Seeyama a gabansu, Seeyama tana fita daga gidan, kai tsaye ta ƙarasa wajen aikin Safina, ta tsaya a gate safinan ta fito, ta ɗauke ta a mota, sannan ta ja motar suka bar wajen, fuskarta a haɗe, hannayenta a kan steering wheel, tana driving cikin wani irin yanayi da ke nuna cewa tana da abubuwa da yawa a ranta, bayan sun ɗan yi nisa, Safina ta juya ta kalleta, tana nazarin fuskarta, “Hey, girl, you sound moody, what happened? Is everything alright?” Ta ɗan dakata, sannan ta yi wata ƙaramar dariya, “Wait a minute… ko ke da sarkin naki ne?” Seeyama ta ja wani shegen tsaki, tana ɗan girgiza kai, “Please, share shi, ni yanzu ba ta shi nake ba, I have bigger problems to deal with,” Safina ta ɗan ɗaga gira, “Oh really? So, what happened this time?” Seeyama ta ƙara matse steering wheel ɗin, sannan ta juya ta kalleta na ɗan lokaci kafin ta mayar da idanunta kan hanya, “Kin iya tuna wata shegiyar yarinya da ta zo ta buɗe ɗakina ranar aurena?” Safina ta ɗan zaro ido kamar tana ƙoƙarin tunawa, amma kafin ta ce komai, sai ta fashe da dariya, “Wannan mai shishiggin zaki ce min, of course,” Seeyama ta amsa da sauri, kamar ita ma ta daɗe tana jiran ta samu wanda za ta yi wa maganar, “Uhm! What about her?” Safina ta juya ta kalleta da wani irin kallo mai ɗauke da tambaya, “Me ya faru da ita kuma?” Seeyama ta yi ƙaramar kwafa, fuskarta ta ƙara haɗewa, “Ashe wai ita ce yayar shegiyar matar Zayd!” Safina ta buɗe baki da mamaki, tana kallon Seeyama kamar ba ta yarda da abin da ta ji ba, “You can’t be serious!” “Wallahi kuwa!” Seeyama ta faɗa da sauri, tana jin haushin tunawa da abin da ya faru a gate ɗin, “Just imagine! Na fita daga gida na zo na tarar da ita a gate, kuma ba wai kawai ta zo ba, har tana da ƙarfin halin cewa ita yayarta ce!” Safina ta ja dogon numfashi, tana girgiza kai a hankali, “Lallai ma, what a coincidence!” Seeyama ba ta ce komai ba, ta ci gaba da driving, amma fuskarta ta nuna cewa har yanzu tana jin haushin abin da ya faru, Safina ta ɗan kalleta daga gefe, tana mamakin yadda Seeyama ta ɗauki lamarin da muhimmanci haka, amma abin da ya fi ba ta mamaki shi ne yadda Seeyama take da tabbacin cewa komai zai tafi yadda take so, duk da irin matsalolin da take iqirarin tana shiga, bayan ɗan lokaci, Safina ta sake magana, “So, what have you decided? Kina ganin mu koma wajen bokan nan? Maybe there’s another way he can help us,” Seeyama ta yi shiru na wasu daƙiƙu, idanunta a kan hanya, ta yi kamar tana nazarin maganar, amma a zahiri tana tunanin abin da za ta iya yi ba tare da ta sadaukar da abin da take ƙoƙarin karewa ba, a ƙarshe ta girgiza kai, “No, gaskiya I can’t sacrifice my pride because of this,” ta ɗan dakata, sannan ta ƙara da wata murya mai cike da taurin kai, “Ina gab da cimma burina, I can’t let one stupid decision ruin everything I’ve been preparing for all these years,” Safina ta kalleta a hankali, tana sauraron ta ba tare da ta katse ta ba, Seeyama ta ci gaba da magana, tana matse leɓenta, “Kar na je saboda rashin haƙuri ya sa na rasa abin da na shafe shekara da shekaru ina tanadawa saboda mutum ɗaya, no way,” ta yi ƙaramar kwafa, sannan ta gyara zamanta, “Mu dai nemi wata mafitar kawai, there has to be another way,” Safina ta yi shiru, tana kallon Seeyama wadda hankalinta ke kan driving ɗinta, a ranta kuwa, tana mamakin yadda Seeyama take ji da wannan budurcin nata, da kuma irin taurin kai da take da shi idan ta sa abu a gaba, ta san Seeyama mai kafiya ce tun can, but she honestly hadn’t expected her to take things this far, Safina ta sauke numfashi a hankali, ta juya ta kalli hanya, tana tunanin irin shawarar da za ta ba ta, Allah kaɗai ya san abin da Seeyama take sakawa a ranta a wannan lokacin.