LOKACI CHAPTER 22
by @fulani32
Follow this link to join my WhatsApp group: ***
🕛⏳ LOKACI 🕛 ⏳
RABI'ATU FULANI
YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA
Under Team Yota's Amazing Pen's.
SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️
FULANI ❣️
***
PAGE2️⃣2️⃣
Wani irin shiru ne mai matuƙar nauyi ya biyo bayan haɗuwar idanunsu, sosai shirun ya mamaye office ɗin gaba ɗaya, baka jin komai sai ƙarar Ac, inda mutum kuma zai nutsu tsaff zaiji yanda zuciyoyi guda biyu suke bugawa, tare da fitar numfashinsu.
Cak Zahra ta tsaya kamar an dasata, idanuwanta akan fuskarsa, zuciyarta na bugawa da wani irin gudu kamar zata faso ƙirjinta ta fito, wani irin abu mai nauyi ne ya tokare mata a maƙogaro, tana jin yanda ta kasa haɗiyar miyau, bare ta iya buɗe bakinta da niyyar magana, ta ka sa kowane irin ƙwaƙwƙwaran motsi.
Ƙoƙarin kawar da idanunta tayi daga nasa, amman ta kasa kamar ya saka magnet ya riƙeta, fuskarsa, ita ce fuskar da ta ɗauki shekaru ashirin tana ƙoƙarin mantawa da ita, shekaru ashirin ba kwana ashirin ba, ko sati ashirin ko kuma wata ashirin, a'a shekara ashirin.
Shekaru ashirin da suka isa su sauya yanayinsa, sai dai duk yanda zai canza ba zai taɓa canzawa a cikin idanunta ba, yau gashi a gabanta, a zahiri, ba'a mafarki ba, ba kuma a tunani ba, ba'a cikin tunanin da take ba, idan ta keɓe kanta.
*"Muhammad Sani Muhammad"*
Sunansa ya maimaita kansa a cikin zuciyarta, a take wata ƙofa da take ƙoƙarin binne wa ta buɗe kanta, wata ƙofa da ke ɗauke da wasu abubuwa masu matuƙar sirri da suke binne a cikin zuciyarta.
Bakinta ne ya fara rawa, ƙanƙame jikinta tayi jin wani irin sanyi yana ratsa har ɓargonta, duk da office ɗin ba wani sanyi ne da shi ba, wani irin kakkarwa hannunta suke yi, duk da a ɗazu tayi ƙoƙarin ƙin barin hakan ya bayyana, amman yanzu a bayyane suke rawar, da ƙyar take fusgo numfashinta a cikin ƙirjinta.
"Muhammad, dagaske shine a tsaye a gabanta, mutumin da ta cire rai da sake ganinsa, amman yau bayan shekara ashirin ta gansa a gabanta, me ya sa yau? Me ya sa a nan? Me ya sa a irin wannan yanayin?" Ta tambayi kanta, amman bata samu amsar tambaya ko guda ɗaya ba.
A kallon da tayi masa ta kula da yanda ya sauya, fuskarsa ta nuna alamun girma, da tsantsar kamala, kwarjinin da ta sansa da shi ya ƙaru fiye da baya, kyaun nan da yake ruɗar ƴan matan ajinsu ya zarta fiye da baya, ya sauya sosai da sosai, amman duk da wannan sauyin bai hana ta ganesa ba, shine dai Muhammad, Muhammad ɗin da ta daɗe tana ƙoƙarin mantawa, mutumin da ta daɗe da yin imanin *LOKACI* ya riga da ya raba su har abada, amman sai ga shi yau, *LOKACI* ya haɗa su a waje ɗaya, a *LOKACIN* da bata taɓa tsammani ba.
Hawayen da ta ke ta ƙoƙarin danne wa ne suka fara ƙoƙarin zubo mata, da sauri ta lumshe idonta, dan ba zata taɓa son zubar da su a gabansa ba, duk da tasan daman a gabansa itaɗin me rauni ce, amman bai kamata ta bari rauninta ya bayyana a gabansa ba a yanzu.
Ba faɗan da ya yi mata ba ne a gabanta, ba kuma maganganunsa ba, abin da ya fi komai firgita ta da ɗaga mata hankali shi ne, ganin fuskarsa bayan tsawon shekaru ashirin, da kuma sanin cewa mutumin da ta daɗe da cire sa a babin rayuwarta, yau gashi a tsaye a gabanta yana kallonta, kamar dai shekarun baya daya ke yawan tsareta da idanunsa..
Zay'd kam, tun haɗuwar idanunsa da nata, komai ya tsaya masa cak, fushin da ya ɗakko tun kafin ta shigo office ɗin ya fara dusashewa, a take wata iriyar damuwa da fargaba suka maye gurbin fushin, ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta.
Kallon da take masa da yanda leɓenta yake rawa, da yanda idanunta suka cika taf da hawaye ba tare da sun zubo ba, wani irin kallo take masa, wani abu yake gani a cikin idanuwanta da ya kasa fahimta, saboda zurfin kallon da take masa, da wani irin ƙarfi zuciyarsa take bugawa, yana jin yanda wani abu ya faɗa masa a ƙirji, wanda tun daga ranar da ta bar rayuwarsa abun ya ke maƙale a ƙirjinsa, duk yanda yayi yaƙi akan abun ya faɗa ya gaza, amman ya faɗa masa a yanzun.
So yake ya tambayeta shin itace? So yake ya kira sunanta, tambayoyi ne masu matuƙar yawa da ya ke son mata amman ya kasa, harshensa yayi masa nauyi, bare ya iya furta mata, lokacin da ya buɗe bakinsa da niyyar kiran sunanta, sai yaji wani tsohon suna ya taso masa tun daga can ƙasan zuciyarsa, sunan da bai taɓa kiran wata halitta da shi ba, sunan da ya kasance mallakinta ita kaɗai.
Manager kallon su ya ke, idan ya kalli Zahra sai ya mayar da kallonsa kan Zay'd, yana mamakin dalilin da ya sa Zay'd ya yi shiru kwatsam, ga kuma Zahra da ta tsare sa da ido tana masa wani irin kallo, gaba ɗaya ya rasa tunanin da ya kamata ya kama.
Duk da halin da take ciki na tsananin firgici, ta na jin yanda wani suna yake ta kai komo a cikin zuciyarta, sunan da ta saba kiransa a da, sunan da ke ɗauke da tunanin da ta yi shekaru ashirin tana ƙoƙarin nisanta kanta da shi.
Idanunsu ne suka ƙara haɗuwa a cikin na juna, kallon tsakiyar ido suke wa junansu, tamkar kowannesu yana jiran ɗayansu ya furta abin da ke a cikin zuciyarsa, ba tare da sun shirya ba suka furta sunayen da suke kiran junansu a lokaci ɗaya.
"*Besty!!!*"
*"Best friend!!!"*
A lokaci ɗaya sunayen ya fito daga bakinsu, kamar dai wancan lokacin, lokacin da suke cike da ƙuruciya, lokacin da suke kiran sunayen cike da wani abu da su kansu basu san da shi ba, sai dai basu taɓa tunanin zasu yi nisa da juna ba, basu taɓa hasashen samun wannan tazarar ba.
Zay'd ƙara zuba mata ido yayi, zuciyarsa na bugawa da wani irin ƙarfi fiye da ka'ida, ji ya yi wani abu ya tokare masa a ƙirji.
"Besty" ya furta sunan a saman leɓensa, dagaske dai ita ce a tsaye a gabansa, Falmata ɗinsa, yarinyar da ya shafe tsayin shekaru yana nemanta, yarinyar da a kanta baya kallon kowa ce mace, yarinyar da ta daɗe da mallakesa, ta zama wani sashi na musamman a cikin rayuwarsa. Kasa sarrafa kansa ya yi ya nufi inda take, sai dai kafin ya ƙarasa ya tsaya cak, saboda yanda ya ga fuskarta ta ƙara canzawa.
A kallo ɗaya yake fahimtar a yanayin da take ciki, tun a wancan lokacin shiyasa yanzu ma bai sha wahalar ganewa ba, fushi me tsanani yake gani akan fuskarta, ga kuma hawayen daya ɓalle mata kamar da bakin kwarya, kuka take jikinta har yana rawa, kallo ɗaya yayi wa kukan nata yasan daga can ƙasan zuciyarta yake fitowa, kamar ta daɗe tana riƙe da shi, yau kuma ya saki kansa ba tare da ta shirya ba, kanta take girgiza wa da yake sara mata kamar zai cire.
"Ina ba zai yiwu ba" ta yi maganar cikin raunin murya, shi kansa badan kallonta yake ba, da ba zai gane me ta ce ba.
A hankali ya buɗe bakinsa gabansa yana faɗuwa.
"Falmata.."
Jin sunan da ya kirata da shi sai taji kamar ya ƙara mata wani abu mai nauyi a cikin zuciyarta, kasa ci gaba da jurar tsayuwa tayi, juyawa tayi cikin sauri ta nufi ƙofar office ɗin. "Falmata" Zay'd ya kirata da ƙarfi, kamar ba ta ji shi ba, ta buɗe ƙofar ta fita a guje tana kuka. Ƙofar da ta fita ya bi da kallo, ya ka sa yarda da abin da ya faru a cikin ƴan mintuna kaɗan, cikin ƙanƙanin lokaci komai yana neman ƙwace masa, saurin fita daga office ɗin ya yi ya bi bayanta.
"Besty dan Allah ki tsaya!" Kafin ya ƙara so har ta sauka daga kan benen, rasa ina ya kamata tayi, ta yi, hakan yasa kawai ta nufi hanyar waje, so take kawai ta bar wajen, so take ta yi nesa da shi ko zata samu nutsuwarta ta dawo jikinta, kuka take sosai tana jefa ƙafarta ba tare da ta san ina take jefawa ba, lokaci_lokaci tana saka bayan hannunta tana goge hawayen da ya ƙi tsaya mata.
"Zahratah"
Ta ji muryarsa a bayanta, ta san muryar, ta kuma san mai kiranta da wannan sunan mussamman idan yana son wani abu a wajenta, sauri ta ƙarawa tafiyarta ba tare da ta waiwaya ba.
"Besty! Best friend ne fa" ya faɗa cikin wani irin yanayi, dan ya fara tsorata da abin da take masa, ganin tana niyyar fita daga cikin restaurant ɗin gaba ɗaya sai ya dakata, daga inda yake ya ci gaba da kallonta, ya rasa gane dalilin da yasa take gudunsa, yayi tunanin tsayawa za tayi ta nuna masa farin cikin ganinsa, saurin koma wa yayi, hannunsa ya saka a aljihu cikin sa'a ya ji mukullin mota a ciki, da sauri ya shiga motar ya take mata baya.
Tana fita taga napep zai wuce, cikin gaggawa ta tare sa, ba tace masa komai ba ta shige ciki yana tsayawa, " dan Allah ja mubar wajen nan yanzu" tayi maganar cikin muryar kuka.
Da mamaki me napep ɗin ya kalleta ta mudubi, yana mamakin yanda take kukan, saboda numfashinta kamar zai ɗauke. "Ina zan kai ki Hajiya?"
"Gida" ta basa amsa tana ƙara fashewa da kuka.
Kasa ja ya yi ya juyo yana kallonta, "to a ina gidan yake Hajiya?"
Faɗa masa tayi, sannan ta sunkuyar da kanta, rufe fuskarta tayi da tafin hannunta, tana sauke ajiyar zuciya irin ta wanda yaci kuka ya ƙoshi, jin napep ɗin ya fara tafiya ne yasa ta ɗago kanta, kamar ance ta kalli mudubi, taga ya fito daga cikin restaurant ɗin a mota, yana bin bayansu, ji tayi zuciyarta ta sake bugawa da ƙarfi, ɗauke kanta tayi lumshe idonta tayi, babu shiri ta buɗe saboda yanda taga fuskarsa ta haska a cikin idanuwanta,koya ta motsa sai ta tuna da yanda ya kira sunanta.
Ta daɗe tana tunanin ya zama tarihi a rayuwarta, amma yau da ta gansa, ta fahimci duk tsayin lokacin da zaka ɗauka abu ya wuce, ganinsa kaɗai zai iya dawo maka da duk abin da kake tunanin ka manta, jingina tayi da jikin kujerar napep ɗin, tana kuka a hankali, ji tayi mararta ta murɗa da ƙarfi, hannunta ta ɗora a kai, ta ƙanƙame jikinta, saboda azabar da ta ji tana ratsata.
"Ya rabb" maganar ta fito a hankali daga cikin bakinta, hawaye ne ya sake zubo mata, sai a lokacin ta tuna da wayarta, gabanta ne ya faɗi, dan babu wani abu nata da ta ɗakko a wajen aikin a haka ta fito, kamar ance ta lalubi aljihun rigarta sai ta jiyota, ajiyar zuciya ta sauke, ta saka hannunta ta ɗakko, babu security a wayarta, wajen kira ta shiga, amman bata gani sosai, saboda hawayen daya ƙi barin idonta, ɗayan hannunta ta saka ta goge hawayen, ɗayan hannun kuma ta lalubi number Salmah.
Wayar na ta ringing bata ɗaga ba, ƙara kiranta tayi, sai a lokacin ta ɗaga.
"Hello Big Sister"
Buɗe bakinta tayi zata yi mata magana, amman ta kasa saboda kukan daya tokare mata a maƙogwaro ya hanata magana. Cikin tashin hankali Salmah ta ce "Aunty Zahra me ya faru?"
"Autah" ta kira sunanta kuka ya ƙwace mata.
"Na'am Big Sister, me ya faru? Kina lafiya? Kina ina?" Ta jera mata tambayoyin tana tashi tsaye.
"Ki.. ki fito ki sameni, dan Allah"
Tsakar gida ta fito "kina ina? Me ya faru naji muryarki haka?"
Ƙoƙarin yi mata bayani ta yi, amman kuka ya ci ƙarfin ta, dole ta yi shiru. Gaba ɗaya Salmah ta ruɗe har ta fara kuka, Mahmah da take zaune kallonta kawai take ba tare da tace mata komai ba, amman sosai take jin fargaba, kar dai wani abu ne ya samu Zahran.
"Ki fito waje ina hanya" tana faɗar haka ta katse wayar.
Hanyar waje Salmah ta nufa, Mahmah ta riƙota dan kamar bata cikin hayyacinta. "Ina zaki a haka Salmah ki saka hijabi" sai a lokacin ta tuna babu hijabi a jikinta, Mahmah ce ta saka mata hijabi sannan ta barta ta fita ƙofar gida jiranta.
Zahra hannunta ta saka a aljihu da tunanin ko zata samu kuɗi, sai dai babu ko sisi, jakarta tana can, unifoam ne kawai a jikinta, ko hijabi babu a jikinta, a lokacin da ta fito daga office ɗin abin da take tunani kawai ta bar wajen, kafin ta rasa sauran ƙarfin da take da shi na tsayawa a gabansa.
Ganin sun kusa gidansu ne ya sa ta kalli me napep ɗin, ta yi ƙoƙarin yi masa magana "yayana, dan Allah ka yi haƙuri, yanzu idan mun ƙarasa za'a baka kuɗin"
Kallonta yayi ta mudubi "bakomai, Hajiya"
Gyaɗa kanta tayi a hankali, amman bata iya ce masa komai ba, duba wayarta tayi, jin tana ringing, ganin Salmah ce sai ta ƙyaleta.
Zay'd tuƙin yake cikin wani irin yanayi, da bai saba da shi ba, hannunsa yana kan sitiyarin, amman gaba ɗaya hankalinsa yana a kan besty, ya kasa daina tunanin yanda ta kalle shi, da yanda ta furta sunan da ta saba kiransa, hoton kukan da ta fashe da shi ya kasa barin idanunsa, yanda ta juya ta bar office ɗin ba tare da ta saurari ko kalma ɗaya daga bakinsa ba, yafi komai ɗaga masa hankali.
Me ya faru da ita a cikin waɗan nan shekarun? Me ya sa ta gudu daga garesa kamar wadda ta ga wani abin tsoro ko kuma wanda zai cutar da ita, anya tana tuna baya? Ko kuma akwai wani abu da baisaniba, tambayoyi ne masu yawa suke giftawa a tunaninsa, amman ba shi da amsar ko guda ɗaya.
Ya daɗe yana kallon kansa a matsayin Mutumin da ya iya sarrafa kansa da zuciyarsa, mutumin da baya taɓa barin wani abu ya girgiza sa, ba abu bane mai sauƙi yake saka sa kasa sarrafa kansa, amman yau ganin Zahra kaɗai ya sa ya kasa sarrafa kansa, ƙara taka ƙafarsa ya yi a kan birki, saurin sauya hanya yayi yana ƙoƙarin ganin ko zai iya ƙarasawa inda take kafin ta ɓace masa, ba ya son ya sake rasa ta, ba zai iya jura ba a karo na biyu.
A can gabansa ya hango napep ɗin da take ciki, yana tafiya a hankali saboda cunkoson ababen hawa, ba tare da ɓata lokaci ba, ya ci gaba da bin su a baya, idanunsa a kan hanyar da suke bi.
Sosai take ƙoƙarin jure murɗawar da mararta take yi, amman ta kasa, addu'a take tayi a ranta, duk addu'ar da ta zo bakinta yinta take, da ciwon ya lafa tana tuna fuskar Zay'd sai marar ta kuma murɗa mata, napep ɗin yana tsayawa ta fara ƙoƙarin fitowa.
Salmah da take ta zagaye kamar tayi wa sarki ƙarya, da sauri ta matsa wajen napep ɗin, tana fitowa ba ta jira jin abin da Salmah zata ce ba, ta wuce ta nufi hanyar gida, tana share hawayenta da bayan hannunta, amman hawayen sun ƙi tsayawa.
"Aunty Zhara" Salmah ta kirata tana bin bayanta, "wai lafiya? me ya faru? Me ya sa kike kuka?" Ba ta amsa mata ko tambaya ɗaya ba ta ci gaba da tafiya, zuciyarta cike da tashin hankali.
"Ki tsaya mana big sister" Salmah tayi maganar ta na shan gabanta.
A lokacin ne wata mota ta tsaya a kusa da su, ba tare da ya yi parking daidai ba, ya buɗe ya fito, ko rufe motar baiyi ba ya matsa kusa da Zahra, fuskarsa ɗauke da damuwa da tashin hankali.
"Besty!" Ya kira sunanta a hankali.
Ɗaga ƙafarta tayi da niyyar barin wajen amman ta kasa, Salmah kuma juyawa ta yi tana kallonsa, a take ta tuna a inda ta taɓa ganinsa.
Ƙarasowa gabanta ya yi ya tsaya.
"Dan Allah ki tsaya ki saurareni Besty" ya yi maganar tashin hankali bayyane a cikin muryarsa.
Salmah ta na tsaye a gefe, tana kallonsu duka biyun cike da mamaki, ta kalli Zahra da take kuka har tana shiɗewa, sannan ta kalli Zay'd wanda ya kasa ɗauke idanunsa daga kan Aunty Zhara, buɗe bakinta tayi kamar zata yi magana, amman ta kasa cewa komai, a fili take ganin wani abu a fuskarsu su biyun, sunan da taji ya kira Aunty Zahra da shi kamar ta san shi a bakinta..
Matsawa ya yi kusa da ita, ita kuma ta ja da baya tana girgiza masa kanta, har lokacin hawaye bai dakata da zuba ba, akan fuskarta, kamar wadda aka zabura ta juya a guje ta shiga gida, Mahmah tana tsaye kamar mai jiran tsammani, ba tayi wata_wata ba, ta faɗa jikinta ta ƙanƙameta, tare da fashewa da wani matsanancin kuka....
FULANI
***