Chapter 7-8
by @momislam11
ƘULLIN ƘAUNA
(Erotic Love Romance and funny
💋💋💋💋💋💋
Mom Islam
Page 7-8
Ɗingis-ɗingis take taka ƙafafunta tana tafiya a harabar gidan kamar wata sarauniya, kasancewar compound ɗin yanada tsayi da girma yasa ta ɗanyi tafiya kafin ta kawo bakin get, dan bata so ta shiga mota Jay ya fahimci ta fice ne kokuma driver's su tona mata asiri, tana isa bakin get mai gadi ya tashi tsaye, cikin tsiwa da rashin kunya take kallonsa, tace “malam ka buɗe min ƙofa“ mai gadi yace “ai me gidana yace kar a bari kije ko ina“ Ayra ta wani zabgawa mai gadi harara, tare da buɗe hand bag ɗinta ta ɗauko gilashi no respect tasa baƙi mai faɗi wanda ya kusa mamaye kumatunta, cikin tsiwa ta sake cewa “wannan gilashin rashin mutunci ne, idan kanason kanka da arziƙi kuma kar insa a koreka ka buɗemin get in fita, me gidanka ɗin banz....“ taji an damƙo gashin kanta dake ɗaure da ribom a cikin mayafi, sam ta kasa juyowa sai ma tsala ihu da tayi tana cewa “momy.....dady....“ ya buge mata baki, sannan ya riƙe gashinta ya dinga janta har suka shigo parlour fuska babu walwala, jikinta har wani rawa yake tsabar tsoro, Jay ya yiwa kansa mazauni akan sofa one sitter kana ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, idanunsa suna cikin farin gilashi, sumar kansa tana a ɗaure ya zuba har gadon bayansa sai sheƙi yake, cikin Izza yace “me kike cewa?“ ta kalleshi ta sunkuyar da kanta bakinta yana karkarwa, “Nace me kike cewa...!!!?“ Jay ya Watso mata tambayar cikin daka tsawa, “bab....ba...babu...babu komai“ Ayra tayi maganar cikin sarƙewar murya, Jay yace “kiyi Kneel down, ki rufe idanunki ki ɗaga hannayenki sama“ Jay yayi maganar yana danna wayarsa, Ayra ta fara hawaye, tare da ajiye handbag ɗinta, sannan ta cire gilashin dake manne a idanunta ta ajiye a gefe, tayi inda yace tana kuka“ system ɗin dake ajiye a gefensa ya buɗe, ya fara magana dasu Hajiya da yake basa Nigeria sun tafi aikin hajji, fuskar Momy na ɗauke da murmishi take kallon Jay tace “yarona sai ƙara kyau kakeyi ina ƙanwarka ina fatan tana cikin ƙoshin lafiya?“ Jay yace “eh Momy ɗazu muka dawo daga siyan su ice cream dasu chocolate tare da ita“ Momy tayi murmishi tace “masha Allah ashe dai Ayra zata daina rikishi...?" Wani uban ihu Ayra ta darara wanda yasa maganar da Jay zeyi ta maƙale masa a maƙoshi, ya fara kallonta cikin hassala katse maganar da sukeyi, dan Momy tana ta ce masa lafiya me ya samu Ayra be kulata ba, tana ganin ya juyo gareta ta miƙe zata gudu, ya riƙeta gam tare da zare belt ɗin dake ɗaure a ƙugunsa ya fara lafta mata tana ihu, ta shige jikinsa tana ta cukuikuyeshi shiko zunguro masa Dick ɗinsa da takeyi yasa shi sakinta da sauri ta faɗi ƙasa, “wayo Allahna ashe kace zan ɗauki ciki, Mugu kawai Allah ze saka min“ ta sake rugawa da gudu yanzu kam Allah ya taimaketa dan ta isa bedroom ɗinta be bita ba, tana shiga tayiwa ƙofar key, cikin takaici ya wuce ɗakinsa, hannunsa na riƙe da waya da system, sai da ya ajiye su system ɗin akan table kana ya nema wa kansa gurin zama, yana zama ya miƙe riƙe da ɗuwawu yana ihu, shafo ɗuwawun da zeyi sai jini, yasa hannu ya laluba gurin yaga allura ne, ya isa gaban mirror yana cigaba da kallon Allurar da ya ciro wacce ta sokeshi a ɗuwawu, da mamaki ya kalli fuskarsa a cikin mirror ya ware idanu, bakinsa yasha janbaki sannan kuma ga zanen baƙi, “kenan haka yaje har gurin get mutane suna kallonsa, tabbas babu me yi masa wannan aikin face Ayra“ ya faɗa a cikin zuciyarsa yana riƙe da ɗuwawu idanunsa suna shirin fitar da hawaye, dan allurar ta shiga sosai...!
Mom Islam