ZAYD ARMAAN

A NIGHT OF DECEPTION

by @jiddaahbarkum



*ZAYD ARMAAN*

*CHAPTER 108*
 
A  NIGHT OF DECEPTION

*JIDDAAH BARKUM*

———-

A hankali Zayd ya tura ƙofar bedroom ɗin Seeyama, ya shiga cikin nutsuwa, idanunsa suka fara yawon tantance ɗakin, da farko dai, bai ga Seeyama ba, sai dai komai yana cikin ɗan gyara, idan banda gadon da yake a ɗan hargitse, wataƙila saboda ta fi zama a kansa, tunda ba ta da wani wajen zama da ta fi so kamar nan, ya ɗan zuba wa gadon ido, sannan ya sauke numfashi a hankali, ya juya da niyyar fita kenan, sai ga Seeyama ta shigo, tana tura ƙofar da bayanta kafin ta rufe, “Babeee!” Ta faɗa cikin wata murya mai taushi, tana ƙarasowa kusa da shi, Zayd ya tsaya cak, ya tsaya yana kallonta, fuskarsa babu wata alama ta musamman, ita kuwa, kamar ba ta lura da yanayin fuskarsa ba, sai ta nufi ledojin da ke hannunsa, ta miƙa hannayenta ta karɓe su, tana ɗan risinawa, “Sannu da zuwa, babe,” Zayd ya ɗan jinjina kai, “Yauwa,” Seeyama ta ɗago kanta ta kalle shi, murmushi dauke a fuskarta, a hankali yace, “Ya jikin naki? I called you, but you weren’t answering my calls,” Seeyama ta zuba mata ido na ɗan lokaci kafin ya amsa tana kokarin hada amsar da zata bashi, sai ta ɗan langwaɓe kai, ta sauke idanunta kan ledojin da ke hannunta, kamar wadda ta tuna wani abu mai muhimmanci, “Da sauƙi, babe, tun da muka je wajen, na ɗan samu sauƙi, ka san kuma can hanyar ɗin babu network sosai, kira yana shigowa, sai ya katse,” ta ɗan yi shiru, sannan ta ɗago idanunta ta kalle shi, “Shi ya sa ma, bayan na iso gida, na fara hidimar tarbar ka, ban so ka dawo ka ga gidan a hargitse, so I decided to put everything in order first, shi ne na manta ban sake kiranka ba,” Zayd bai ce komai ba, ya ci gaba da kallonta, fuskarsa a sanyaye, Seeyama kuwa, da ta ga bai ce komai ba, sai ta ƙara da wata murya mai taushi, “Gashi ma yanzu, abin da nake so shi ne in kira Mommy, in gaya mata ta bar maganar kawo Rabi, I don’t need a maid anymore, zan koyi komai da kaina,” ta ɗan yi murmushi, tana ƙoƙarin karanta yanayin fuskarsa, “Babe, I want to be a total submissive wife to my husband, I want to learn how to take care of you and your home myself, I know I haven’t been doing things right, but I’m ready to change,” ta ƙarasa maganar tana murmushi, kamar wadda ta gama gabatar da wani babban alƙawari, Zayd ya ɗan ɗaga gira, har yanzu idanunsa suna kanta, amma bai nuna ko ya gamsu da maganarta ba, ko kuwa yana da wani tunani dabam, Seeyama ta ƙara matsowa kusa da shi, “Babeee…” Ta kira shi a hankali, tana ɗan turo baki saboda yadda yake kallonta ba tare da ya ce komai ba, “Why are you so quiet?” Zayd ya sauke idanunsa kan ledojin da ta riƙe, sannan ya dawo da su kan fuskarta, sai ya jinjina kai a hankali, “Okay,” kalmar guda ɗaya ce ya furta, ba tare da ya ƙara komai ba, Seeyama ta tsaya tana kallonsa, murmushin da ke fuskarta yana ƙoƙarin kasancewa duk da cewa amsar tasa ba ita ce take tsammani ba, ta yi tunanin zai yaba mata, wataƙila ya ce yana jin daɗin yadda take ƙoƙarin canzawa, ko kuma ya nuna mata cewa ya lura da ƙoƙarinta, but Zayd was giving her nothing, babu yabo, babu tambaya, babu ko wata alama da za ta nuna cewa kalamanta sun taɓa shi, ta ɗan haɗiye yawu, “Baby, ka ji abin da na ce kuwa?” Zayd ya ɗan karkatar da kansa, “Na ji,” “Then?” Ya kalleta na ɗan lokaci kafin ya amsa cikin sanyayyar muryarsa, “Seeyama, if you want to learn how to take care of your home, then learn, you don’t need to announce it to me,” ta ɗan yi shiru, Zayd ya ci gaba, har yanzu cikin nutsuwa, “Let your actions speak for you,” murmushin da ke fuskarta ya ɗan tsaya cak, sai dai ba ta bari ya ɓace gaba ɗaya ba, ta sake murmushi, tana mai jinjina kai kamar ta fahimci abin da yake nufi, “Of course, baby, you’re right, I understand,” ta matsa gefe, ta ajiye ledojin a kan stool, sannan ta dawo kusa da shi, “Ka zauna mana, you’ve had a long day, let me get you something to eat or drink,” Zayd ya kalleta, sannan ya ɗan sauke idanunsa kan ledojin da ta ajiye, “Na ci abinci a wajen Ummie,” “Oh, okay,” ta amsa da sauri, sannan ta yi ƙoƙarin ɓoye ɗan rashin jin daɗin da ta ji, “To, ko ruwa? Zan kawo maka ruwa,” “Ba sai kin wahalar da kanki ba,” “It’s not a problem, baby, I want to do it,” ta faɗa da sauri, kamar tana tsoron ya ƙi yarda da ita, Zayd ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya juya ya zauna a kan sofa, Seeyama ta ɗan yi murmushi ganin ya zauna, a zuciyarta, ta ɗauki hakan a matsayin wata ƙaramar nasara, at least, ya zauna, ba kamar yadda yake yi a baya ba, ta juya ta kwashe ledojin snn ta yi sauri ta nufi kitchen domin kawo masa wani abun, tana tafiya cike da wani sabon tunani, a ganinta, idan ta nuna masa cewa za ta iya zama matar da yake so, wataƙila zai fara kallonta da wani sabon ido, ba za ta sake zama matar da take korafi a kan komai ba, za ta yi haƙuri, ta yi murmushi, ta kula da shi, ta kuma nuna masa cewa babu wadda za ta iya zama cikakkiyar matarsa kamar ita, but what Seeyama didn’t understand was that Zayd wasn’t a man who could be won over by sweet words alone, he watched actions, and right now, he was waiting to see whether her sudden change was real or just another attempt to get what she wanted.

Seeyama ta ajiye ledojin da ta karɓa daga hannun Zayd, akan kitchen island din sannan ta juya ta kalli bakin kofar na ɗan lokaci, da ta tabbatar ba mostin komai, sai ta sauke muryarta, tana magana a hankali kamar tana yi wa kanta magana, “Wato can gidan munafukar uwarka ka je ka ci abinci?” Ta yi wani irin tsaki a hankali, ta kaɗa kai cike da ɓacin rai, “Hmm! Wallahi, idan tsohuwar kirki ce, ai da ta ce ka bar abincin can, ka zo gidanka matarka ta ba ka, amma a’a! Sai ta bar ka ka ci a can,” ta ɗan tsaya, ta lumshe idanunta, sannan ta sake magana cikin wata murya mai ɗauke da takaici, “Toh, duk baƙin cikin da take yi, sai ka ci wani abu a wajena tonight, I won’t let her have the last laugh,” a hankali ta ɗaga robar fura da nonon da Zayd ya kawo mata, ta riƙe ta tana kallonta, kafin wani murmushi ya bayyana a fuskarta, “And I think this will do the magic,” ta faɗa tana ɗan jujjuya robar a hannunta, murmushin da ke fuskarta yana ƙara faɗaɗa, sai ta ɗan juya kai, tana leƙen bayanta don tabbatar da cewa babu wanda ya shigo, ta duba ƙofar, ta sake dubawa, amma ba ta ga kowa ba, nan take ta sa hannu cikin rigarta, ta zaro wata ƙaramar leda da ta ɓoye, sannan ta buɗe ta da sauri, idanunta suka sauka kan abin da ke ciki, sai ta ɗan murmusa, wani irin murmushi mai ɗauke da sirri, ta juya ta fara dube dube cikin kitchen din, sai idanunta suka sauka kan wani ƙaramin turmi da ake amfani da shi wajen daka seasoning ko spicy, sabon turmin ne, har yanzu ba a yi amfani da shi ba, bayan ɗan lokaci, ta kammala shirinta, sannan ta koma kan fura da nonon, ta shirya komai a hankali, tana ƙoƙarin tabbatar da cewa babu wani abin da zai sa a yi mata tambaya, daga nan ta ɗauko kofi mai kyau, ta zuba fura da nono a ciki, ta kuma shirya wani kofin daban, ta tsaya tana kallon kofunan biyu, ya murmushi a fuskarta, “Perfect,” ta furta a hankali, ta ɗauki kofunan, ta gyara zamansu da kyau akan tray, sannan ta nufi ɗakin da Zayd yake, a duk lokacin da ta yi tunanin yadda komai zai kasance idan shirinta ya yi nasara, murmushin da ke fuskarta sai ya ƙara bayyana.

Seeyama ta dawo a nutse, being very careful kamar ba ita ba, ganin Zayd ya bar dakinta taşa definitely yana cikin ɗakinsa sai kawai ba ta tsaya ɓata lokaci ba, ta wuce kai tsaye zuwa inda yake, ai kuwa, yana nan shingide a kan doguwar kujera, yana kallon wayarsa cikin nutsuwa, ta jawo stool ta ajiye kofunan fura da nono a kai, sannan ta koma kitchen da sauri, inda ta fara kiciniyar wanke fruits ɗin da ya saya, haka dai ta yi ta faman hidima, dan ba ma wai sun wanku bane yanda ya kamata, sai ta kwaso fruits ɗin a plate, ba ta ma tsaya ta yanka waɗanda ake yankawa ba; kawai ta watsar da su a ciki, ta gyara plate ɗin yadda zai yi kyau, sannan ta ɗauko komai ta dawo, bayan ta gama arranging ɗin komai, sai ta ɗaga kai ta kalli Zayd, wani murmushi mai ɗauke da kwaɗayin ganin sakamakon shirinta a fuskarta, “Babe, ga fura nan sai fruits, na san dare ne, and you probably won’t want anything heavy, so ka daure ka sha kaɗan,” Zayd ya ɗan kalleta a ƙasan ido, honestly, ya riga ya ƙoshi tun da ya ci abinci a gidan Ummie, amma bai son ya yi wani abu da zai sa ta ji kamar yana wulaƙanta ƙoƙarinta, musamman da yake yau ta nuna wani sabon hali na son kula da shi, saboda haka, sai ya ɗan gyara daga kishingidar da yake, ya zauna da kyau, sannan ya miƙa hannu zai ɗauki ɗaya daga cikin kofunan, Seeyama ta ɗan turo baki, “Babe, ba ni ina wajen ba? Ka ce na miki maka mana sai ka wahalar da kanka?” Ba ta jira ya amsa ba, ta yi saurin ɗaukar ɗaya daga cikin kofunan biyun ta miƙa masa da murmushi, Zayd ya ɗago idanunsa ya kalleta na ɗan lokaci, sannan ya karɓa, “Thank you,” ya faɗa a sanyaye, kafin ya koma ya jingina da sofa ɗin, yana riƙe da kofin a hannunsa, Seeyama kuwa ta zauna kusa da shi, tana ƙoƙarin ɓoye irin farin cikin da ke son bayyana a fuskarta, ta ɗauki kofinta, ta kai bakinta ta sha kaɗan, sannan ta sauke shi, Zayd ya ɗaga kofin nasa a hankali, ya kai bakinsa, sannan ya fara sipping ɗin fura da nonon a hankali, Seeyama ta zuba masa ido, tana kallon yadda yake sha, zuciyarta na bugawa da sauri saboda wani irin tsammani da take ƙoƙarin dannewa, a zahiri, murmushi kawai take yi, amma a zuciyarta… “Allah ya sa komai ya tafi yadda na tsara,” sanyin furar da gardin nonon ya kwashi Zayd, sai da ya sha fiye da rabin cup ɗin kafin a hankali ya ajiye shi a kan stool ɗin, ya lumshe idanunsa, ya koma ya jingina da sofa ɗin, hannunsa ɗaya ya sauka a kan cikinsa yana shafawa a hankali, kamar wanda ya ji daɗin abin da ya sha, Seeyama kuwa, ji take kamar ta tashi ta taka rawa saboda farin ciki, but of course, babu damar yin hakan a gabansa, sai dai duk da ƙoƙarinta na ɓoye abin da ke zuciyarta, the happiness on her face was noticeable, duk wani motsi da Zayd yake yi, tana kallonsa ta gefen ido, tana jiran wani abu ya faru, sai ta ɗauki kofinta, ta kankance murya cikin wani irin shagwaɓa, “Babe na yanka fruit ɗin?” Zayd ya ɗan buɗe idanunsa a hankali, ya juyo ya kalleta, bai ce komai ba, kawai ya yi mata nod, alamar a’a sannan ya sake lumshe idanunsa, kamar wanda yake jin daɗin hutunsa, “Okay,” ta amsa a hankali, tana ƙoƙarin danne murmushin da ke son subuce mata, ta ajiye cup ɗin hannunta, sannan ta miƙe ta fara tattare abubuwan wajen, ta kwashe plate ɗin fruits ɗin da sauran abubuwa, ta nufi ƙofa da sauri-sauri, tana ƙoƙarin kada farin cikin da ke cikinta ya bayyana fiye da yadda ya kamata, da ta fita daga ɗakin Zayd, sai ta ƙara sauri har ta isa kitchen, ta ajiye abubuwan a kan kitchen island, sannan ta juya ta jingina da shi, ta ɗora hannayenta a kan ƙirjinta, finally! Ta saki wani shegen murmushin mugunta, tana jin kamar an cire mata wani babban nauyi daga zuciyarta, “Finally!” ta maimaita a ƙasan murya, tana girgiza kai, “Yau duk taurin kanka, duk wannan uban steeze ɗin da pride ɗin nan naka… zai sauko!” Ta ɗan yi dariya, tana kallon kofin da ta bari a kitchen, “And I promise you, Zayd Armaan, you will beg me for everything, when I say everything I mean Everything!” Ta gyara tsayuwarta, wani sabon ƙarfin gwiwa ya bayyana a fuskarta, “It’s now my turn,” wata ƙaramar dariya ta kufce mata, cike da mugunta da gamsuwa da abin da take ganin ta cimma, amma a ɗaya ɓangaren gidan… Zayd yana nan a kan sofa, babu wani motsi na gaggawa a tare da shi, fuskarsa a nutse take, idanunsa a rufe, numfashinsa a hankali, da sauri ta fito daga kitchen, amma maimakon ta koma ɗakin Zayd, sai ta nufi nata ɗakin direct.

Tana shiga, ba ta ɓata lokaci da tunanin yin wanka ba, kawai ta fara cire kayan jikinta, ta nufi gaban wata drawer da ta shirya turarukanta a ciki, perfumes ne iya ganinka! Daga khumra, kullaccam, har zuwa turaruka masu tsada iri-iri, ta fara buɗe kowanne ɗaya bayan ɗaya, tana shafawa a jikinta, tun daga wuyanta zuwa ƙafafunta, she wanted to smell irresistible tonight, bayan ta tabbatar ta yi wa kanta cikakken wankan turare, sai ta juya ta ɗauko wata ƙaramar kwalba, ta ɗaga ta sama, tana kallonta da wani irin murmushi da ya bayyana a fuskarta, wannan kuwa, ta daɗe da tanadarta tun asali, ta ajiye ta ne domin darenta na farko da Zayd, but somehow, tonight felt like the perfect opportunity to finally use it, a hankali, cikin kulawa, ta buɗe kwalbar, ta shafa turaren a wuyanta, a ƙasan kirjinta, bayan kunnuwanta, har zuwa ƙasan mararta, ta yi komai da nutsuwa, as though she was preparing for a very special occasion, bayan ta gama, sai ta juya ta kalli kanta a mudubi, she tilted her head slightly, inspecting her reflection, a satisfied smile spread across her face, “Perfect,” ta furta a hankali, daga nan sai ta nufi wardrobe ɗinta da sauri, ta fara yawo da idanunta a kan kayan da ke ciki, tana neman abin da zai dace da shirin da take yi, nan kuwa idanunta suka sauka kan wata haɗaddiyar burgundy luxury net nightgown, ta ɗauko ta, ta ɗaga sama tana kallonta na ɗan lokaci, “This is it,” ba ta tsaya ɓata wani lokaci ba, ta saka nightgown ɗin, tana gyara shi a jikinta, sannan ta sake komawa gaban drawer ɗin turarukanta, ta sake buɗewa ta ƙara yi wa kanta wankan turare, ta yi wa kanta kallon ƙarshe a mudubi, tana tabbatar da cewa komai ya kasance exactly the way she wanted, sai da ta gamsu da yadda ta kasance, sannan ta juya ta ɗauki wayarta, 21:10, ta kalli lokacin a screen ɗin wayarta, sannan ta ɗan gyara gashinta, ta ja numfashi a hankali, a wannan karon, babu shakka ko fargaba a fuskarta, confidence ɗinta ya dawo, kuma a tunaninta, wannan daren zai bambanta da sauran darare, a hankali ta nufi ƙofar fita, ta buɗe ta, sannan ta fita daga ɗakinta.

Seeyama ta nufi ɗakin Zayd da wani irin taku na musamman, tana karairaya a hankali, tana ƙoƙarin jawo hankalinsa tun kafin ta ƙarasa inda yake, da ta shiga, sai ta tarar yana nan a kan sofa, jikinsa a jingine, idanunsa a rufe, ta ɗan tsaya tana kallonsa, wani murmushi ya subuce mata, ta gyara tsayuwarta, sannan ta ƙarasa cikin ɗakin da nutsuwa, her every step carefully calculated, Zayd kuwa, a hankali ya buɗe idanunsa, sai dai idanunta suka haɗu da nasa, ta lura da wani canji a yanayin idanunsa, kamar launinsu ya fara sauyawa a hankali, ta ɗan tsaya na daƙiƙa, amma ganin yadda yake kallonta ya sa ta sake samun ƙarfin gwiwa, da sauri ta zauna a kan sofa kusa da shi, sosai har babu wani tazara mai yawa a tsakaninsu, ta kama hannunsa a hankali, ta ɗan matsa jikinta kusa da nasa, “Babe, you look sleepy,” ta faɗa cikin wata murya mai laushi, tana kallonsa da wani irin murmushi da ta yi niyyar amfani da shi wajen jan hankalinsa, Zayd bai amsa nan take ba, ya zuba mata lumsassun idanunsa, yana kallonta sosai, fuskarsa babu wani sauyi da za ta iya karantawa, Seeyama kuwa, ganin cewa hankalinsa ya karkata gare ta, sai ta ɗauka shirinta yana fara yin tasiri, a hankali ta ɗora kanta a kan kafaɗarsa, ta zagaye hannayenta a kugunsa, tana shigewa jikinshi, “Babe…” ta sake kira cikin wata shegiyar murya, tana ɗan ɗaga kanta ta kalle shi, “Let’s sleep, dare ya yi,” ta ƙare maganar da wani murmushi, tana tsammanin zai mayar mata da martanin da ta daɗe tana jira, amma Zayd? Ya ci gaba da kallonta a hankali, ba ta san abin da ke cikin tunaninsa ba, ba ta san ko yana nazarin sabon halin da take nunawa ne, ko kuma akwai wani abu dabam da ya riga ya fara zargi, abin da ta sani kawai shi ne, a wannan daren, tana son ta ga wani sabon Zayd Armaan, sai dai ita ma ba ta san wane irin amsa za ta samu daga mutumin da ko a lokacin da ya yi shiru, har yanzu yake da ikon sa mutum ya kasa gane abin da ke ransa ba.

Ganin Yayi Shiru sai ta zame hannunta ɗaya daga kugunsa ta fara yawo dashi a jikinsa. Ta fara zamar da shi a a hankali daga gefen kugunsa, tana bin layin jikinsa ta ciki da wani irin salo na seducing mai cike da dabara. Yatsunta sun bi ta saman rigarsa ta Sauke zip din jallabiyarsa a hankali tana kallon fuskarshi ko zai hanata amma ta ji shiru hakan ya sa ta cigaba, tana shafa lafiyayyen fatarsa cikin salon da ta San zata rikita masa tunani da duk wata nutsuwa . A hankali ta dinga tura hannunta sama, tana ratsa tsakiyar kirjinsa, tana zagaye yatsunta a saman faffadan ƙirjinsa  har tayi landing hannun kan nipple dinshi ta shiga murza shi at the same time tana ci gaba da kai masa numfashi mai zafi a wuya.
"Babe..." ta raɗa da wata murya mai cike da shauƙi da marari, tana ɗago fuskarta kaɗan domin ta gauraya numfashinta da nasa.
Zayd, wanda tun ɗazu idanunsa ke lumshe Sabida sakon da ke yawo a jikinsa ga kuma wani fitinannen kamshi da ya ke kokarin rudarsa yana lura da ita, ya ji yadda sakonta suka fara shiga cikin jikinsa. Duk da cewa fuskarsa ta kasance a natsu, amma wani ɗan yanayi na daban ya ziyarci jikinsa ba tare da ya shirya hakan ba. Yayin da hannunta ya ci gaba da shawagi a kan kirjinsa yana ƙara kusantar da shi gare ta, bata daina murza nipple dinshi ba hakan nan bata daina sakin numfashi a kunnenshi ba sai ga wani irin nishi mai nauyi da aka fi sani da moan ya kubucee a fil ba tare da ya ankara ba, wani irin sanyi ne ya ratsa shi wanda ya kasa ɓoye shi a lokacin.
Seeyama ta lura da hakan, wani murmushin nasara ya bayyana a fuskarta . Ta ƙara matse jikinta da nasa, Tana ganin shirin nata ya fara cin nasara.

 ta ɗan matsa kusa da shi, tana kallon fuskarsa lokaci-lokaci don ganin irin reaction ɗin da zai yi, Zayd haryanzu idanunsa a lumshe suke, bai ce komai ba, bai kuma motsa daga inda yake ba, ya yi still, kamar wanda ya yanke shawarar barin ta ta yi abin da take so, yana lura da duk wani motsi nata cikin nutsuwa, Seeyama kuwa, idanunta sun tsaya a kan kyakkyawar fuskarsa, the more she looked at him, the more her feelings seemed to overwhelm her, tana son wannan mutumin fiye da yadda take son ta amince, kuma duk da irin girman kai da ta saba nunawa akan shi ne kadai zuciyarta je betraying dinta bata iya muna masa girman kan, amma wannan son nata ya gauraya da wani irin kishi mai zafi, a hankali ta tuna da Raihana, ta tuna da kasancewar Zayd a gefenta, da yadda yake zuwa wajenta, da yadda komai ya canza tun bayan zuwan waccan yarinyar rayuwarsa, sai ga tunanin ihun da ta taɓa ji ya dawo mata a rai, fuskarta ta ɗan sauya, murmushin da ke kan leɓunanta ya zama wani abu daban, ta ƙara kallon Zayd, amma a zuciyarta, ba shi kaɗai take tunani ba, Raihana… Ta furta sunan a zuciyarta, idanunta suka ɗan ƙanƙance, ke ma za ki dandana irin abin da na ji, sak! Ko ma fiye da nawa, ta ji wani irin zafi ya ratsa ƙirjinta, kishi da ƙiyayya suka sake gaurayewa a zuciyarta, kin zo kina tunanin za ki karɓe min komai? No, ba zan taɓa barin hakan ya faru ba, ta sake ɗago kai ta kalli Zayd, ta mayar da murmushinta, tana ƙoƙarin ɓoye tunanin da ke tafasa a zuciyarta, a wajen mutane, tana iya zama matar da take son mijinta, amma a cikin zuciyarta, akwai wani shiri da take ganin zai tabbatar mata cewa ita ce za ta yi nasara a ƙarshe, kuma a wannan daren, Seeyama ta yi imanin cewa ta fara ɗaukar matakin farko.