RANTSATTSEN RABO

LOKACI CHAPTER 23

by @fulani32

Follow the 💫✨ RABI'ATU FULANI CHRONICLES ✨💫 channel on WhatsApp: ***

⏳ 🕛LOKACI 🕛⏳

RABI'ATU FULANI 

YOTA

Under Team Yota's Amazing Pen's.

SADAUKARWA GARE KI KARYMAT BASHEER ❣️ 

FULANI ❣️ 
***

       PAGE 2️⃣ 3️⃣

Ƙanƙame Mahmah ta yi sosai a jikinta, kuka take mata kamar ƙaramar yarinya, jin ta a jikin Mahmah sai ta ji wani irin rauni ya mamaye ta, abu ne da bazata iya tuna lokacin da hakan ya faru a tsakaninsu ba, ƙara shigewa jikinta take kamar zata koma ciki.

Cak Mahmah ta tsaya, dan ta rasa abin da ya kamata ta yi, bayan Zahra ta zubawa ido ba tare data taɓa ta ba, ta na jin yanda hawayenta yake jiƙa mata gaban riga, kukan da take mata ita kanta ba zata ce komai ba, saboda abu ne da bata taɓa gani tayi mata shi ba, a hankali ta ɗaga hannunta, ta ɗora a bayanta, bata cikin nutsuwarta ita kanta Mahmahn, saboda tana cikin ruɗani da mamaki, sannan ga wani abu da take ji yana taso mata kamar tausayin Zahran, ƙoƙarin dannewa take amman ta kasa.

"Me ya faru Zahra?" Muryarta ta fito da ɗan tsauri, kamar yanda ta saba mata magana.

Ba ta ce mata komai ba, sai ƙara ƙanƙameta da ta yi, tare da ƙara ƙarfin kukanta. Mahmah ƙoƙarin janye jikinta ta fara, amman Zahra ta hanata damar hakan, ɗan ture ta tayi da ƙarfi, tare da ƙoƙarin ganin fuskarta.

"Ke, ina miki magana, na ce me ya faru?" Ta yi mata maganar a hasale, idan ta ce kukan nata baya taɓa ta tayi ƙarya, saboda bata saba ganin Zahra a irin wannan yanayin ba, ko da zata yi kuka sai da tayi kanta a ƙasa, amman yau da take a jikinta, haka kawai ta ji zuciyarta na buga da ƙarfi, shekaru sun ja, kamar yanda dangantakar su ta canza, dan basu da kusancin da ya kamata ace ta kasance na uwa da ɗiyarta.

Ita kam Zahra tunda ta ji ta a jikin Mahmah sai taji wata iriyar soyayyarta ta taso mata, ga wani irin rauni da ya rufeta, dan haka da ta tureta sai tayi ƙasa da kanta, tana share hawayenta da hannunta.

"Ki yi min magana Zahra, me ya faru? Ko baki da lafiya?" Tayi maganar muryarta a ƙasa, tana ƙoƙarin kawar da fargabar data rufeta.

Da wani irin sauri Salmah ta juya zata bi bayan Aunty Zahra, duk da bata san abin da ya faru ba, halin da ta ga Aunty Zahran ya matuƙar ɗaga mata hankali, dan abu ne da bata taɓa gani a tare da ita ba, koda kuwa me Mahmah zata mata, dan haka ita ma sai ta ji duk hankalinta ya ta shi, hanyar gidan ta nufa, tana gaf da shiga ta dakata jin anyi mata magana.

"Please tsaya" 

Muryar Zay'd ta katseta daga shiga gidan, cak ta tsaya, sai kuma ta juyo a hankali, idanunta ta ɗora a kansa, a zuciyarta kuma tana jinjina baiwar kyan da Allah ya basa.

Yana tsaye a bayanta, fuskarsa cike da damuwa, idanunsa akan Salmah, yana ganin kamar ta da yayarta a bayyane.

Ƙoƙarin juyawa ta ke ya ƙara dakatar da ita.

"Ki saurareni please" 

Kallonsa tayi, sai kuma ta kalli cikin gidan, dan Allah ya sani hankalinta gaba ɗaya yana cikin gidan.

"Kayi haƙuri dan Allah hankalina yana kan Aunty Zhara, bansan a wane hali take ciki ba, ina son zuwa na duba ta"

"Nasani" ya amsa mata a hankali dan ga tashin hankalin nan a bayyane a fuskarta, bayan damuwar da yake gani. "Ina son ki taimaka min, nasan ke ƙanwarta ce, amman kafin nan ina son ki san wanene ni a wajenta.."

Wannan karon da mamaki Salmah ta kallesa.

Shiru ya yi, ya rasa ta ina zai fara ma, gaba ɗaya shima a ruɗe ya ke.

"Sunana Muhammad Sani Muhammad"

A take Salmah ta fara hasashen wani abu. "Muhammad?" Ta ambaci sunansa da sigar tambaya, ƙara kallon fuskarsa ta yi, tare da fara ƙoƙarin haɗa sunan da labarin da aunty Zahra ta taɓa bata, Muhammad Sani Muhammad, Best friend ɗin Aunty Zahra, shine kenan wanda ta taɓa bata labarin sa.

"Kai ne..?" Sai kuma ta kasa ƙarasawa dan bata san me zata ce masa ba.

Ya fara gajiya da magana, amman yanda Salmah tayi maganar dole ya tanka mata "Ni ne wa?" 

"Kai ne Muhammad ɗin da ta taɓa bani labarinsa, Best friend ɗin ta, yawwa na tuna classmate ɗinta ko?" Ta ƙarasa maganar da tambaya, fuskarta kuma da murmushi, wanda ita kanta bata san dalilin yi ba.

Jin yanda Salmah tayi magana, da kuma yanda ta faɗi sunansa, hakan sai ya tabbatar masa da Zahra bata manta da shi ba, a take yanayin fuskarsa ya canza.

"Eh" ya amsa mata a takaice.

Kallon gidansu tayi kamar zata ga Aunty Zahran a tsaye, sai kuma ta mayar da kallonta kansa, sai yanzu ta fahimci abin da ya gigita Aunty Zahra, amman ita ta zata ai duk sanda suka haɗu, kwanan farin ciki zata yi amman sai ta ga saɓanin haka, ita dai ko ba komai tayi farin ciki da bayyanar sa a daidai wannan lokacin.

Cikin sanyin murya ta ce "toh amman Yah Muhammad me ya faru?"

Kansa ya girgiza mata alamun bai sani ba, sai kuma ya kalli gidan kamar zai ganta.

"Ya sunan ki?" Ya tambayeta ba tare da ya kalleta ba.

"Ummu Salmah, amman Salmah ake cemin ko kuma Autah"

Kan shi ya gyaɗa mata, zai magana ta katse sa.

"Lah kai ne yayan Teemah princess da Ya khaleel ko?" 

Ɗan kallon mamaki ya bita da shi sai kuma ya gyaɗa mata kai.

Cikin wani irin farin ciki da ya gaza ɓoyuwa a fuskarta ta ce "Ranar mun gaisa fa a Dara restaurant, ka tuna?" Yanda tayi maganar sosai yarintarta ta fito a fuskarta.

Duk da halin da yake ciki baisan yayi murmushi ba, dan sai ta koma masa kamar princess ɗinsa.

"Kar ka damu Yah Zay'd, ni da Princess muna team ɗin ka, yanzu ka bani number ka, ga ta Big Sister" tayi maganar tare da fara karanta masa number, bayan ta gama basa, ya karɓi wayar Salmah ya kira number sa, sannan yayi saving.

"Amman yah Zay'd me ya sa ka tafi ka barta?" Ta tambayesa ganin yana niyyar juyawa.

Dakatawa ya yi, ya rasa abin da zai ce mata, wannan maganar da yayarta zai yi ta, amman Salmah ta shiga ranshi sosai, ba zai so ya yi mata shiru ba, kar ta ji babu daɗi, juyowa yayi yana kallonta.

Diriricewa ta yi ganin yanda ya zuba mata idonsa "ka yi haƙuri" ta ce a hankali, ta juya.

"Na neme ta Autah, ban same ta ba, yau da na ganta kuma.." shiru ya yi ya cize bakinsa, sai kuma ya ci gaba "ta ganni ta fara kuka, ba ta bari munyi wata magana ba, ta tawo, ban samu damar magana da ita ba, sannan...." Kasa ci gaba da magana ya yi.

Sauke kanta ƙasa ta yi, ganin yanda fuskarsa tayi ja, sai dai tasan wacece Aunty Zahra, dan haka a hankali ta ce "ka bata lokaci Yah Zay'd"

"Lokaci?" Zay'd ya maimaita yana kallonta, "ba zan iya ba"

Rasa abin da za ta ce masa ta yi, duk shiru suka yi can ta numfasa ta ce "ban san abin da ya haɗa ku ba, amman a yanda naga big sister, ba na jin zata yi magana da kai a yanzu, shiyasa na ce daman ka bata lokaci"

Shiru ya yi, bayan wani lokaci ya gyaɗa mata kansa, "zan kira ki, ki faɗa min halin da take ciki, itama zan kira ta, je ki gida"

Kallonsa ta yi sannan ta juya ta shige gidan.

Yana tsaye yana kallonta, har ta ɓacewa ganinsa, a hankali ya juya ya nufi motarsa, kasa kunna motar ya yi, hannunsa ya ɗora akan sitiyari, idonsa akan gidan, tsoron tafiya ya ke gani yake kamar idan ya tafi ba zai dawo ya same ta ba..

★★★

Kamar wadda aka ja, Zahra ta ƙara komawa jikin Mahmah, kasa ƙara tureta tayi, a hankali ta fara tunanin wani lokaci can baya, indai shagwaɓa ce da son jiki kaf cikin yaranta babu wanda ya kai Zahra, hannunta yana rawa ta ɗora a bayanta ta fara bubbugawa a hankali alamun rarrashi, sai kuma ta fara ƙoƙarin ganin fuskarta, amman Zahra ta ɓoye fuskar a ƙirjinta.

"Ki dai na wannan kukan kar kiyi ciwon kai, ki faɗa min me ya faru kin ji" ta yi maganar a hankali kamar ba muryar Mahmah ba. Ƙara ƙanƙameta Zahra ta yi tana sauke ajiyar zuciya, ji tayi ba zata iya barin jikin Mahmahn ba, mussamman yanda take mata magana a hankali da kuma bubbuga bayanta da take.

A haka Salmah ta shigo ta same su, turus ta tsaya mamaki rubuce akan fuskarta, kasa yarda tayi har sai da ta shafa idonta, ta dai ga dagaske Zahra ce rungume a jikin Mahmah, a hankali ta matsa kusa da su.

"Big sister! Mahmah!!" Sai tayi shiru ta ci gaba da kallonsu.

Haka kawai sai taji wani irin tausayinsu ya kamata, daga yanda Aunty Zahra ta ƙanƙame Mahmah tana wannan kukan, zaka san tayi kewar jin ɗumin mahaifiyarta, ba iya kukan abin da yake damunta take ba, hannunta ta ɗora a bayanta, ɗayan hannun kuma ta riƙe na Mahmah da ke bayan Zahra.

Kallonta Mahmah ta yi, sai kuma ta mayar da kallon kan Zahra.

"Me aka mata Salmah, na tambayeta bata ce min komai ba" 

Jin yanda Mahmah ta yi maganar Salmah bata san sanda ta rungumeta ba, ita ma tana fashewa da kuka.

Jikin Mahmah ne ya fara rawa, ganin yanda suka rungumeta suna kuka kamar ance musu ta faɗi ta mutu, "Mah.. mahh..." Salmah ta kira sunanta a rarrabe tana ƙara fashewa da kuka. Ji tayi idonta na neman cika da hawaye, amman ta dake. "Bana son shirme Salmah meye zaku saka ni a gaba kuna kuka, ko mutuwa a kayi ne?" Tayi maganar muryarta na rawa, dan sosai take jin wata iriyar zazzafar soyayyar yaran na taso mata, mussamman Zahra.

"Salmah me aka mata?" Ta tambayeta tana ƙoƙarin raba su da jikinta.

Shiru Salmah ta yi, dan ko hauka take ba zata faɗawa Mahmah komai ba, tayi hankali, anyi ɗaya da ita ba za'ayi na biyu ba. "Ban sani ba Mahmah" ta ce tana sakinta.

"Toh kukan uban me kike min?" Ta tambayeta a hasale.

"Na farin ciki ne Mahmah, ganin Aunty Zahra a jikinki, abu ne da ban taɓa gani ba Mahmah, dan Allah Mahmah ki rungumi ƴar ki" ta haɗe hannayenta alamun roƙo.

Da sauri Mahmah ta zare Zahra daga jikinta, tare da juya musu baya, da dabara ta goge hawayen da ya zubo mata, ba tare da ta bari sun gani ba.

Bayanta Zahra ta zubawa ido, tana jin kamar ta koma, ta ƙara rungumeta, idanunta sosai sukayi ja, fuskarta kuma ta kumbura, saboda kuka "Mahhhmahh na!!!" Ta kira sunanta cikin raunin murya tare da jan sunan, a hankali Mahmah ga juyo tana shanye duk abin da take ji.

"Me?"

Buɗe bakinta tayi zata yi mata, ji tayi mararta ta murɗa mata da ƙarfi "aaah!" Ta ce tana yarfe hannunta, sai kuma ta durƙushe, hannunta akan mararta, a tsorace Salmah ta ce "big sister menene?"

"Marata" ta ce tare da runtse idonta.

"Mahmah marata zata fashe" ta ce tana miƙa mata hannunta. Kamar wadda aka ja haka ta matsa ta riƙe hannun Zahran "tun yaushe take miki ciwo?" Lumshe idonta tayi, tare da yarfe hannunta guda ɗaya. Salmah Mahmah ta kalla "zo ki riƙe ta mu kai ta ɗakinta" da sauri Salmah ta matso, hannunta ta riƙe guda ɗaya, suka ɗagata, ɗakinta suka kaita, a kan gadonta suka kwantar da ita, gam Zahra ta riƙe hannun Mahmah taƙi saki, zama ta yi a gefen gadon tana kallonta.

"Salmah je ki ɗakina akwai maganin ciwon mara ki ɗakko min" gyaɗa kanta tayi, sai ta juya ta fice da sauri, bayan fitar Salmah gyara mata filo tayi. "Sannu" ta ce cikin muryarta ta ko yaushe.

Kasa amsawa ta yi, janye kanta tayi daga kan filon ta mayar kan cinyar Mahmah, bata hanata ba, sai fuskarta da ta zubawa ido, sosai yanayin da Zahran take ciki ya taɓa wani ɓangare na zuciyarta, sai dai bata san ta yanda zata nuna mata hakan ba, saboda ta manta rabon da su, samu kusanci irin haka da ita, mussamman a waɗannan shekarun da rashin jituwarsu yayi mugun tsanani, tunani ne kala_kala suke kutso mata, doguwar ajiyar zuciya ta sauke.

"Allah ya baki lafiya" ta faɗa a hankali. Salmah ce ta shigo da maganin har da ruwa, ɗagota tayi ta bata ta sha, ta koma ta kwanta, ruwan wanka ta saka Salmah ta haɗa mata, da kanta ta kaita toilet ɗin, daga nan ta fice dan jinta take kamar akan ƙaya.

Bayan ta fito, Salmah ta ɗakko mata kayan da zata saka, bayan ta shirya koma wa tayi ta kwanta, sosai bakin Salmah yake ƙaiƙayi hakan ya sa ta matsa kusa da ita tare da riƙe hannunta.

"Big sister" kallonta tayi, shiru tayi ta rasa abin da zata ce mata, ga dai shi maganar cinta take kamar me.

"A ina kika haɗu da best friend ɗinki, gaskiya kyakykyawa ne, har na fara.." kallon da ta ga tana mata ne yasa ta haɗiye sauran maganar, sosai fuskarta ta canza, cikin shakkarta Salmah ta ce "Big Sister" ta kira sunanta a hankali.

Juya mata baya tayi "kiyi min shiru Autah" ta ce muryarta na sarƙewa. "Amman big sister naga Best friend ɗinki ne, na zata farin ciki zaki yi" 

"Salmah!!, kar ki kuma kira min sunan wani anan wajen" tayi maganar a tsawace duk da muryarta bata fita sosai.

Matsawa kusa da ita tayi "kiyi haƙuri ba zan kuma ba" a hankali ta janye hannunta da ga na Salmah. "Je ki Autah bar ni ni kaɗai please" toh ta ce ta fita tana waiwayenta. Filon gefenta ta janyo ta rungume, mutumin da take tunanin ba zata ƙara ganinsa ba, kwatsam sai ya bayyana a gabanta a lokacin da ba ta shiryawa hakan ba, babban tashin hankalinta, ba tasan ta ina ma zata fara fuskantar saba.......

FULANI 
***