BABI NA ƊAYA
by @mamyywriter
****Washegari da safe…
Ina kitchen ina taimakawa Mama da aiki amma na kasa daina murmushi.
Aunty Mansura ce ta shigo tana kallona, ta ce.
“Lallai yarinyar nan wai ko breakfast ɗin ma soyayya ce za ta dafa shi?”
Da sauri na sunkuyar da kai, na ce.
“Mtswww aikin banza."
Dariya ta yi tana matsowa kusa da ni, ta ce.
“Ai na ga fitar Prof Muhammad Zaid jiya, yanzu ke ba ki yarda da abin da na faɗa miki ba ko.?"
Da sauri na ɗago idona ina kallonta, na ce.
“Kamar ya?"
Murmushi ta yi, tana cewa.
"Ke! Yarinya ce, har yanzu, wai in ma tambayeki me Prof Muhammad Zaid yake yi cikin ɗakinki?
Shiru na yi ina kallon fuskarta, can dai na yi murmushi na ce.
"Abin da Abba yake yi a ɗakinsa, shi da Ummah....."
Buge min baki ta yi tana cewa.
"Sai dai abin da yake shi da Mama, kuma wallahi za ki shigo hannuna.."
Rama buge min bakin da ta yi, na yi ina cewa.
"Ko ma da waye ai kin gane abin da nake nufi ko? Kuma wallahi in ba ki daina shiga harkata da shi, sai na faɗawa Abba...."
Wuyana ta shaƙe tana dukana, ni ma gamawa na fara kafin wani ya shigo a cikin mutanan gidan, mu daku sosai, Mama ce ta fara shigowa ta same mu muna yi.
Maganar da take yi mana ce tasa Ummah shigowa, ita da su Asiya, kama ni Khadijah ta yi ita kuma Ummah ta kama ta.
Muna fitowa waje ta zage ni, ni ma na rama, kafin na rufe baki ta buge min bakina, ni ma na sake ramawa, faɗa sosai muka fara
“Ke! Me yake faruwa ne haka da safe?”
Mama ta faɗa tana kallona.
Ni da Aunty Mansura duk muka yi shiru, amma idanunta a kaina suke cike da tsokana.
Ummah ce ta girgiza kai tana cewa. “Wallahi waɗannan idan suka fara rigima kamar yara ƙanana.”
“Ku tambayeta mana abin da take cewa.”
Aunty Mansura ta faɗa tana nuna ni.
Da sauri na ce. “Ni fa ita ce ta fara shiga harkata kuma wallahi sai na rama.”
Duka Mama ta kawo min na dugu, ɗaki, haushi Aunty Mansura nake ji sosai, sai da Abba ya fito yin breakfast sannan na fito.
Bayan mun gama breakfast ne na tashi zan shiga ɗakina, wayata ta yi vibration.
Da sauri na ɗauka, sako ne daga My Zaid, da murmushi akan fuskata na duba.
“Kin tashi lafiya My Noor?”
Wani murmushi ne ya subuce min.
Na rubuta. “Lafiya lau.”
Nan take ya sake turo min.
“Kin yi missing ɗina?”
Na girgiza kai ina murmushi kafin na rubuta. “A’a.”
Sai ya yi reply da:
“Karya kike.”
Dariya na yi kaɗan. Kafin in yi typing sai wani sabon saƙon ya sake shigowa.
“Ki shirya da wuri yau, zan zo.”
Gabana ne ya ɗan faɗi. Da sauri na rubuta. “Ina kuma?”
“Zuwa ɗaukar Matata.”
Na zaro idona sosai. Da sauri na duba kofar ɗakin saboda kunya kamar zai gan shi.
Sai kuma wani saƙon nasa ya shigo.
“Ina son mu fita.”
Numfashi na sauke a hankali. Ban san me yasa zuciyata ta fara bugawa haka ba.
Kafin na ba shi amsa, wayata ta sake vibrating.
“Ko kina tsoro ne?”
Na turo baki ina typing.
“Ni ba tsoro nake ba.”
“To shi kenan,ki jira ni ƙarfe huɗu.”
Sai kuma ya ƙara da:
“Kuma ki yi kyau… saboda yau bana son kowa ya kallonki sai ni.”
Na rufe fuskata ina mai farinciki.
"Aunty Maryama!”
Muryar Khadijah ce ta sa na ɗago kai.
Shigowa ɗakin ta yi tana kallona da ƙyau, ta ce.
“Wallahi akwai abu.”
Na haɗe fuska ina cewa. “Wani abu kuma?”
Sai da ta zauna kusa da ni tana ƙoƙarin ƙwace wayar hannuna. Da sauri na ja.
“Aha!” Ta faɗa tana dariya.
“Kenan da Prof ne.”
“Ba ruwanki."
Na faɗa ina ƙoƙarin ɓoye murmushina.
Ta yi dariya tana cewa. “To ki shirya. Yanzu na tabbatar yau za ki wani tsaya a gaban mirror fiye da kowa.”
Pillow na jefa mata. Ita kuwa da gudu ta fita tana dariya.
Karfe huɗu saura kaɗan na gama shiryawa.
Doguwar rigar peach na saka mai sauƙin aiki, tare da hijabi fari mai laushi na saka a saman rigar.
Na tsaya gaban mirror ina kallon kaina.
Sai kuma na tuna maganarsa:
“Ki yi kyau… saboda yau bana son kowa ya kallonki sai ni.”
Wani irin sanyi na ji a zuciyata.
Wayata ce ta yi ƙara.
“Ina waje.”
Na ga ya rubuta.
Lumshe ido na yi kafin na fita a hankali.
Kasa faɗawa Mama inda zan je na yi, na tsaya ina kallonta.
Shiru ta yi tana kallon fuskata, sannan ta ce.
"Lafiya na ga kin shirya ina za ki je da yamman nan?"
Shiru na yi ina kasa magana na yi ƙasa da kaina, haushi Mama ta ji ya sa ta ɗaga hannu za ta duke ni, na yi saurin cewa.
"Na ga shi ne yake jirana a waje."
Dariya Khadijah ta yi tana cewa.
"Taɓ amma Aunty Maryama sannu da aiki, yanzu dama kin san Yaya Muhammad Zaid ne yake jiranki shi ne ki ka tsaya.."
Harararta na yi ina cewa.
"Mama sai na dawo."
Ina fita na sameshi a cikin motar ya yi masifar yin kyau, kusan kala ɗaya muka sa kayan jikinmu.
Da sallama a bakina na shiga motar ina kallon fuskarsa na ce.
"Barka da zuwa My Zaid."
Shiru ya yi na wasu seconds yana kallona, sannan ya yi wani kyakkyawan murmushi ya ce.
"Amma Noor so kike ki kashe ni ko?"
Ido na zaro ina kallon fuskarsa na ce.
“Ni kuma? Me na yi?”
Kai ya girgiza a hankali yana ci gaba da kallona kamar wanda ya samu TV.
“Kin yi kyau sosai Noor I Love You?” Ya faɗa cikin wata ƙaramar murya mai cike da sanyi.
Kunya ce ta rufe ni gabaɗaya. Na kawar da kai ina murmushi kaɗan, na ce.
“Ka daina faɗan haka mana…”
Dariya ya yi a hankali kafin ya kunna motar.
Tun da muka shiga motar shiru ya ɗan ratsa mu, amma irin shiru nan mai daɗi.
Ni ina satar kallonsa. Shi kuma lokaci-lokaci idan idanunmu suka haɗu sai ya yi murmushi, ya ce. “Noor…”
Na amsa da, “Hmm?”
“Kin san wani abu?”
Ya faɗa yana kallon fuskata.
Kai na girgiza masa.
Ya ce.
“A duk lokacin da nake tare da ke… zuciyata tana samun nutsuwa.”
Wani irin bugun zuciyata na ji. Ban san me zan ce ba, sai kawai na yi murmushi ina wasa da gefen hijabina.
Bai sake magana ba sai da ya tsaya a wani wuri mai cike da flowers da haske masu kyau. Restaurant ne mai kyau da nutsuwa sosai.