BABI NA BIYU
by @mamyywriter
Da mamaki na kalle shi, tare da cewa.
“My Zaid… nan za mu shiga?”
Sai da buɗe seat belt ɗinsa yana kallona, ya ce.
“Ehmana. Ko kina tunanin zan kai Matata ko’ina ne?”
Kalmar “Matata” ɗin da ya faɗa ta sake sanyaya min zuciya, a tare muka fito daga motar.
Tun kafin mu shiga na lura yadda wasu mutane suke kallonmu. ni kuma sai na ƙara manne hijabina saboda kunya.
A hankali ya matso kusa da ni ya ce.
“Na faɗa miki kin yi kyau sosai, amma ba na son kowa yana kallonki.”
Baki na ɗan turo gaba ina cewa.
“To ai ni ban ce su kalle ni ba.”
Dariya ya yi sosai karon farko tun fitowarmu. Sosai ya yi min kyau na tsaya ina kallonsa.
Ganin ina kallonsa ne yasa ya ɗaga min gira. “Me kuma kika tsaya kina kallo?”
Kaina na girgiza da sauri, na ce.
“Ba komai.”
“Qarya.” Ya faɗa kai tsaye.
Muna shiga ciki wani ma’aikaci ya tarbe mu cikin girmamawa. Wurin ya yi kyau sosai da haske masu launika da ban da ban.
Kafin a kawo mana abinci ya zuba min ido kawai yana kallo na.
A hankali na ce. “Prof…”
“Hmm?”
Ya faɗa yana kashe min ido.
“Me yasa kake yawan kallona haka ne?”
Murmushi ya yi kaɗan kafin ya ce. “Saboda har yanzu ban gama yarda ke ɗin tawa ce ba.”
Numfashi na ja a hankali. Kaina na sunkuyar saboda yadda kalamansa suke shiga raina.
Sai ya miƙa hannu yana taɓa yatsuna a hankali ya ce. “Noor…”
Na ɗago ido na kalle shi.
“Na gode.”
Da mamaki na ce. “Saboda me?”
“Saboda irin son da kike min.”
Shiru ne ya ratsa mu gabaɗaya. Ban taɓa jin wani abu ya taɓa zuciyata ba irin haka, na ji kamar ni ɗaya ce a duniyar.
Kafin in yi magana wayarsa ta yi ringing.
Ya ɗan haɗe fuska yana duba screen ɗin. Na lura kamar bai son ɗagawa.
“Ka ɗaga mana.” Na faɗa a hankali.
Sai da ya sauke numfashi kafin ya ɗaga.
“Hello…”
Muryarsa ta canza kaɗan bayan ya ɗaga wayar. Na lura da yadda ya haɗe fuskarsa kamar wanda bai son a katse masa lokacin da yake tare da ni.
“Wa alaikum salam… Kamis?”
Shi ne abin da ya faɗa yana kallon fuskata.
Sunansa kawai da ya ambata yasa zuciyata ɗan bugawa.
Ban san dalili ba amma duk lokacin da aka ambaci Prof Kamis ina jin wani abu daban a raina, na tsoron, irin abin da ya yi min.
Shiru Prof Muhammad Zaid ya yi yana sauraron abin da ake faɗa masa. Daga ƙarshe cikin sanyin murya ya ce. “Yanzu? Kana ina?”
A hankali na ɗago ido ina kallon fuskarsa. Na lura yadda idanunsa suka ɗan canza.
“Okay… zan zo.” Ya faɗa daga ƙarshe kafin ya kashe wayar.
Shiru ne ya ratsa tsakaninmu.
A hankali na ce. “Lafiya?”
Sai da ya sauke numfashi kafin ya kalleni. “Wani emergency call ne a school.”
“Yanzu za ka tafi?” Na tambaya ba tare da na shirya hakan ba.
Kallon mamaki ya yi min kaɗan sannan murmushi ya bayyana a fuskarsa.
“Kin damu ne?”
Da sauri na kawar da kai na ce.
“A’a…”
Dariya ya yi a hankali, ya ce.
“Noor… idan kina son wani abu ki faɗa min kai tsaye.”
Kunya ce ta sake rufe ni gabaɗaya.
Kafin in yi magana waiter ya kawo mana abinci. Amma duk da hakan hankalina yana kan maganar wayar nan.
Can dai ya ɗan matso kusa da ni ya ce. “Ba zan daɗe ba. Zan kai ki gida sannan in wuce.”
Kai kawai na gyada masa.
Amma ban san dalilin da yasa zuciyata ta ɗan sauya ba.
Tun da muka fara cin abincin, Prof Muhammad Zaid yake ƙoƙarin saka ni dariya amma ni hankalina ya kasa kwanciya.
Sai can ya ajiye spoon ɗinsa yana kallona sosai, ya ce.
“Noor…”
Na ɗago ido a hankali.
“Kin yarda da ni ko?”
Tambayar, tasa ni ɗan rikice, na ce.
“Eh…”
“To ki daina tunani, zan dawo da wuri.” Ya faɗa cikin wata murya mai sanyaya zuciya.
Ban sake magana ba.
Bayan mun gama ne muka fito daga restaurant ɗin. Ya buɗe min motar na shiga. Shi ma ya shiga sannan muka fara tafiya.
Sai dai wannan karon ba kamar ɗazu ba.
Shiru ne ya mamaye motar.
Can ya miƙo hannunsa ya kama nawa a hankali ya ce.
“Noor…”
“Hmm?”
Na faɗa ina turo baki.
“Kin yi fushi ne?”
Kai na girgiza masa, ina cewa.
“A’a.”
“Qarya.” Ya faɗa kai tsaye.
Sai na ɗan turo baki gaba, na ce.
“To ai kai ne ka canza mood.”
Dariya ya yi sosai, yana cewa.
“Saboda call ɗin nan?”
Ban ce masa komai ba, na yi shiru ina kallon gefe.
Sai ya ɗan matso kusa da ni kaɗan yana cewa. “Ke kishi kike yi?”
Da sauri na janye hannuna ina kallonsa. “Ni kuma? Akan me?”
Wani irin murmushi ya yi wanda ya ƙarawa fuskarsa kyau, ya ce.
“Allah Noor… kina da bala’in kyau idan kina kishi.”
“Prof!”
Na faɗa ina ɓata fuska.
Ya ci gaba da dariya kafin ya ce.
“Kamis ne fa, ya kira ni ba wata mace ba.”
Haɗe fuska, na sake yi na ce.
“Ni ma ai ban ce wata mace ba.”
“Amma ai da farko kin yi tunani wata mace ce ko?"
Kaina na juya gefe, alamun na yi fushi.
A hankali ya kira sunana. “Noor…”
Na amsa da ƙyar, na ce.
“Hmm?”
“Ina sonki sosai."
Ban san lokacin da murmushi ya baiyana akan fuskata ba, na ji wani irin sanyi, zuciyata ta yi min daɗi, na ji duk duniya babu wacce ta kai ni, farinciki a lokacin.
Shi ma murmushi ya yi tare da cewa.
"Ba sai kin amsa min ba iya wannan murmushi ya wadatar, Noor."
Rufe fuskata na yi da hannayena, ina dariya.
Kafin ya sake magana wayarsa ta yi ringing.
Haɗe fuska ya yi yana dubawa.
Wayar tana cigaba da ringing a hannunsa.
Sai ya nuna min screen ɗin yana cewa.
“Kin gani? Kamis ne ai.”
Na ɗan kalli sunan sannan na kawar da idona, na ce.
“Ka ɗaga mana, ni ina ruwana ko ma budurwrka ce ta kiraka.” Na faɗa a hankali.
Murmushi ya yi yana amsa wayar.
“Hello Kamis...”
Ban ji abin da Prof Kamis yake faɗa ba, amma daga yanayin fuskar Prof Muhammad Zaid na gane maganar tana da muhimmanci.
“Yaushe?” Ya tambaya.
Shiru ya yi yana sauraro, sannan ya ce.
“Okay. Ina zuwa yanzu.”
Da ya kashe wayar ne na kalle shi.
“Me ya faru?”
Sai ya ɗan shafa goshinsa, ya ce.
“School ta turo ni Kano wani aikin gaggawa, da za a gabatar gobe da safe.”
Kai na gyada, ina cewa.
“To Allah ya sa alkhairi.”
Shiru ya yi yana kallona, sannan ya haɗe fuskarsa ya ce.
“Amma akwai matsala ɗaya.”
“Wace matsala?”
Na faɗa ina kallon fuskarsa.
Ɓata fuska ya sake yi tare da cewa.
"Ni gaskiya da ke zan tafi, ba na jin zan iya tafiyar kwana biyar ba tare da ke ba."
Ido na zaro na ce.
"Ni kuma? Gaskiya ni Abba ba zai yadda na bika ba, kuma ni ma ta yaya zan bi wani Namiji har wani gar.."
Kallon da yake min ne yasa na yi shiru ina kawar da kaina.
"Ni ne wani Namijin ko Noor?"
Shiru na yi, ban yi magana ba, sai yanzu na fahimci abin da na faɗa, ashe fa shi Mijina ne.
Har ya sake ni a gida ban sake magana ba, a hankali na fita daga motar ina kallon fuskarsa.
Ina fita ya ja motar da gudu, tsayawa na yi ina kallon yadda yake gudu, da alama ya ji haushi abin da na faɗa.
Jikina a sanyaya na shiga gida, sallama kawai na yi, na zauna kusa da Khadijah da take murmushi.
Kallon fuskata Aunty Mansura ta yi ta ce.
"Ashe Maryama fita kuka yi da Prof Muhammad Zaid?"
Raina a ɓace na ce.
"Eh ko da wane abu ne?"
Murmushi ta yi tana cewa.
"Babu komai amma ai da kin yi mana magana sai mu fita tare."
Kafin na yi magana Ummah ta karɓe zancen da cewa.
"To ke Uwar masu gida haka ake yi, ai da kin yi magana sai Mansura ta zo ku fita, gaskiya ki sake ka da haka ta sake faruwa."
Haushi ne ya kama ni, na tashi ina kallonsu na ce.
"Saboda mu biyu yake aure ko? Kin ga Aunty Mansura in son shi kike yi ki faɗa masa mana, ni bana son munafurci."
"So kuna na nawa, Uwar masu gida, tun da kika ce ba kya son shi, Mansura ta ce tana so, ko ba haka ba ne Maman Fati?"
Murmushi Mama ta yi tana cewa.
"Haka ne, Saratu."
Kallon fuskar Mama na yi, jin abin da ta ce, cikin jin haushi na ce.
"Sai na ga wanda zai sa shi ya sake ni, ai sai ya sake ni za ta aure shi ko?"
Murmushi Mama ta yi tana tashi daga wajen, kallon Ummah na yi domin na ji abin da za ta ce.
"Ai sakin ba zai wahala ba, Uwar masu gida, ke dai ki ce ba kya son shi, yanzu zai sake ki."
Hijabina da na cire na ɗauka ina cewa.
"Na faɗa ba na son shi, na ga ko da wanda ya isa ya sa shi ya sake n.."
Buge min baki Mama ta yi tana cewa.
"Wai ke ban hana ki rashin kunya ba, ita Saratun sa'arki ce."
Da gudu na bar wajen ina kuka sai da na buɗe ƙofar ɗakina, na ce.
"Kuma wallahi sai na faɗa ai na ga baƙin ciki ake yi min dan an ga na samu wanda yake sona, Allah ku fita harkata dan zan iya komai akansa, kun yi tunanin na yi sanyi ne, to wallahi ina nan yadda kuka san n..."
Da sauri na rufe ɗakin ganin Mama ta nufu ɗakin, ina ji tana buga ƙofar ɗakin, na yi shiru.
Kwanciya na yi ina jin haushi abin da ya faru tsakanina da shi, ina so na ba shi haƙuri amma bana so ya raina ni.
Haka na kwanta a ɗaki, ban fita sanin na yi laifin kuma na san ina fita sai Mama ta dake ni.
Sai tare na dare na buɗe ƙofar sanin Abba ya dawo,kuma babu wanda zai dake ni, a gabansa.
Ina buɗe Asiya ta shigo, cike da rashin mutunci ta ce min.
"Wai ki zo Abba yana kiranki."
Bata san duk rashin mutuncinta na fita ba, ina jinta na yi shiru ina cigaba da chat ɗinna.
Ina jinta ta fita tana ƙananun maganganun, ban taka mata ba, ashe zuwa ta yi ta ce wai na ce ba zan zo ba.
Sake dawowa ta yi tana cewa.
"Abba ya ce ki zo."
Tashi na yi ina cewa.
"Ke wai Uwarki ba ta koya miki yin sallama ba? Ka da ki sake shigo min ɗaki babu sallama."
"Wallahi ba Uwata ba.."
Ban san lokacin da tashi ba, kawai mari na ji ya wanke fuskarta da shi.
"Ni za ki zaga ko?"
Fita ta yi tana kuka, bayanta na bi, na san za ta iya yin ƙarya kuma Abba ya yadda.
Ina bayanta zuciyata na bugawa.
A tare muka isa parlour, tsayewa kusa da Abba ta yi tana kuka kamar wacce aka zalunta.
Idon Abba ya zuba min a kaina, ya ce.
“Uwata.”
"Na'am Abba."
Na faɗa ina yin ƙasa da kaina.
“Asiya ta ce kin mare ta?”
Shiru na yi ina ɗan sosa hannu.
Mama da Ummah kuwa sun zuba min ido suna kallona.
“Asiya.” Abba ya kira sunanta.
Da sauri ta share hawayeta, ta ce.
“Na'am Abba.”
"Me ya faru har ta mare ki?"
Hawaye ta sake gugewa ta ce.
"Abba zagina ta yi shi ne fa ta mare ni."
Kallon fuskata ya yi, yana cewa.
"Uwata."
Na san abin da yake nufi yasa na ce.
"Abba shiga min ɗaki ta yi babu sallama, kuma za ta yi min rashin kunya.."
"Au ke kina da bakin cewa wata ta yi miki rashin kunya, ba ɗazu kika gama yi wa su Ummah rashin kunya ba."
Hannunsa ya ɗagawa Aunty Mansura yasa ta yi shiru, Asiya ya kalla ya ce.
“Kin shiga ɗakin yayarki ba sallama ko Asiya?”
Sai a lokacin na ga fuskarta ta canza, ta yi shiru tana kasa magana.
Abba ne ya sake tambayarta.
“Ke ba tambayarki nake yi ba.”
A hankali ta ce.
“Eh Abba amma a yi haƙuri..”
“Dukanku kuna da laifi. Ita ba za ta mare ki ba, ke kuma ba za ki shiga ɗakinta haka ba.”
Abin da Abba ya faɗa ne yasa na ɗago kaina.
Ni ya juyo yana kallona, ya ce.
“Ki riƙa danne fushinki Uwata.”
Kaina na sunkuyar, na ce.
“Yi haƙuri Abba.”
Kai ya gyada, ya ce.
“Shi kenan.”