MATAR AURE CE

BABI NA TARA

by @mamyywriter

********** A ɓangarena kuwa.

Tun bayan shiga ɗakin da aka yi da ni, aka yi min allurai, sannan suka saka min ruwa, na ji ɗan sauƙi ina kwance shiru ina tunanin abin da yake damuna.

Shigowa wata babbar likita ta yi tana yi wa sauran bayani game da zubar da cikin jikina, na yi shiru ina sauraronsu, sai bayan ta gama na ɗago kaina na ce.

"Sister ni ce mai cikin da kike magana za'a zubar?"

Murmushi ta yi tana tsayawa kusa da ni ta ce.

"Eh cikin ne ya lalace dole sai an zubar da shi, na yi mamaki ma da bai fita da kansa ba ƙaramin bai fi wata ɗaya ba.."

Gyara kwanciyata na yi ina cewa.

"Ni ina son kayana a haka, ba sai kun zubar min ba."

Kallon juna suka, babbar likitan ta yi murmushi tana cewa.

"Ku yi aikinku ba ta cikin nutsuwarta, allurar ce take juyata."

Ganin sun taho kaina ne yasa na yi saurin cewa.

"Wallahi ina cikin hankalina babu mai zubar min da ciki ina gan.."

Ihu na yi jin marata ta ɗaure, sosai nake kuka ina ƙoƙarin tashi daga gadon amma na kasa juyani kawai na ji ake kowa biyu-biyu nake ganinsa.

Babbar likitan ce ta ce.

"Ke kira mana Maman yarinyar nan, kamar tana da matsala a ƙwaƙwalwa."

Ina jinta sama sama babu bakin magana sai ihu da nake yi, maganar Mama da Ammyy na ji a kaina likitan ta faɗa musu na ce babu me zubar min da cikina.

A hankali Mama ta ce.

"Likita ku rabu da ita ba ta da hankali ne ku yi aikinku."

Murmushi likitan ta yi tana cewa.

"Ni dama na gama kafin ruwan nan ya ƙare cikin nan zan fita na yi mata allura a ciki, ba na so ne a samu matsala shi ne na ce ki zo."

Zama Mama ta yi a kujerar gaba gadon da nake ta ce.

"Babu komai likita na gode sosai, kin san yarinta, da hauka irin ta yara in ba haka fa a ce cikin ya lalace amma ki ce kina so."

Fashe na yi da kuka ina cewa.

"Wallahi ni ina son cikina, Allah sai an biyani duk wanda ya zubar min da shi, dan ba kusan irin wahalar da na sha ba ne kafin na samu cikin."

Dariya likitan ta yi tana cewa.

"To gaskiya Hajiya ku biyata cikinta, ku baku san wahalar da ta sha ba."

Ammyy ce ta yi dariya tana cewa.

"Sannu Maryama ki yi haƙuri."

Murmushi Mama ta yi tana cewa.

"Hajiya kin ji fa lokacin da suka yi abun su ai babu wanda ya sani."

Hannayen Mama na kama ina cewa.

"Mama! Mama! Kin ji marata dama haka ake ciwon marar?"

Tausayi na ba ta, ta san halina ba ni da ɗauriya a ciwo ko zazzaɓi nake sai kowa ya sani ga bakina baya shiru.

Hawaye ta goge min tana cewa.

"Haƙuri ake yi Uwata na san ya kusa fita Allah ya baki lafiya."

Shiru na yi har likitar ta dawo ta ce su Mama su fita, ni dai ban san lokacin da cikin ya fita ba a kwance dai na gan ni da ruwa a jikina sai Muhammad Zaid zaune kusa da ni.

Shi ya taimaka min na tashi zaune, kallon mutane da suke ɗakin nake ɗaya bayan ɗaya, Ahmad Zayyan ne da A'isha a kujerar sai Aunty Mansura a bakin ƙofa.

"Noor."

Kallon fuskarsa na yi ina hawaye.

Babu kunya ya rungume ni yana cewa.

"Sorry Noor ya jikin ya yi sauƙi ko? Yanzu me kike so? Na yi miki wanka, sai ki ci abinci ko?"

Kwanciya na yi a jikinsa na ce.

"Wai ciki ne da kuma suka zubar min, bayan na ce ina son kayana."

"Sorry Noor dole a cire cikin ba shi da kyau, mun yi magana da babban likitan ya ce wai cikin ma ba a mahaifa yake ba."

"Ki yi haƙuri Allah zai ba mu wani."

Shiru na yi da kukan na ce.

"To yanzu yaushe na san zan samu wani ni gaskiya da an bar min cikina."

Murmushi Muhammad Zaid ya yi yana girgiza kansa ba tare da ya yi magana.

A'isha ce ta dariya ta ce.

"Za ki sami wani a inda kika samo wacan ɗin."

Ahmad Zayyan ne ya yi min sannu da jikin sannan ya ɗagawa Muhammad Zaid gira suka fita da A'isha.

Aunty Mansura ya kalla fuska babu walwala ya ce.

"Gat out."

Fita ta yi tana hawaye, suna fita ya sake rungume ni sosai yana faɗa min kalmomin masu daɗi, dole na yi shiru da kukan shi ne ya taimaka min na yi wanka ya shirya ni.

Kafin na kwanta sai da ya ba ni tea na sha ya gyara gadon sannan ya kwantar da ni. Abba ne da Papa suka shigo, shiru na yi ina rufe fuskata kamar me bacci.

"Uwata ya jikin?"

Muryar Abba da na ji ce yasa na fashe da kuka.

Papa ne ya ce.

"Sannu Maryama ko har yanzu jikin ne?'

Shi ma ban yi masa magana, sai kuka da nake.

"Allah ya baki lafiya amma Muhammad Zaid daga nan ku wuce gidanku, na gode haka."

Sosai kansa ya yi tare da cewa.

"Abba ai da an yi haƙuri ta ji sauƙi sai..."

"Sai me? Ai zaman gidana ya ƙare, saura kaɗan zuciyata ta buga a'a wallahi na gode Alhaji ga su nan."

Dariya Papa ya yi tare da cewa.

"A'a Ahmad ta zauna har ta ji sauƙi sai mu sa ranar tarewar ko?"

Da sauri Abba ya ce.

"Wace tarewa kuma Alhaji ai sun tare, Allah dai ya rufe asiri, Uwata Allah ya ba da zaman lafiya zan sa Khadijah ta kawo miki kayanki daga nan ku tafi gidanku."

Kuka nake sosai na kasa magana yanzu kowa ya san irin abin da muka yi, sosai kunya ta kama ni har su Abba suka fita ban yi magana ba.

Rungume ni Prof Muhammad Zaid ya yi da farinciki ya ce.

"Gaskiya na yi farinciki sosai, Noor kin ji abin da Abba ya ce wayyoo! Allah na."

Kallonsa na yi da idanuwana da suka yi ja saboda kuka, na ce.

"Ka yi farinciki ko? Ni kuma ka ja min abun kunya wai don Allah kai baka jin kunyar abun da yake faruwa ba?"

"Ni ban jin kunya ba daɗi ma na ji."

Haushi ya ba ni na yi masa shiru, har dare ban sake yi masa magana ba, Khadijah ce ta kwana da ni, da safe kuma ta tafi Makaranta tun ƙarfe shida na safe ya zo ban ko kalle shi.

Shi ma da yake ba ya son maganar ban sake yi min magana, daga tambaya ya jiki da ya yi, amma duk da haka komai shi yake min, ya yi min wanka ya ba ni abinci.

Zuwan Ahmad Zayyan ne ma na saki jiki muka yi magana da A'isha, goma na yi Ahmad Zayyan ya ce su tafi Makaranta, ya ce.

"A'a zan zauna ne da Noor."

Kallon fuskarsa na yi ina turo baki na ce.

"Ni dai wallahi ka tafi, tun ɗazu sai kallona kake yi ni na gaji ka tafi kawai."

Murmushi gefen baki ya yi tare da cewa.

"Ai ba ke kika zaunar da ni ba ko?"

Hararar sa na yi ina cewa.

"Eh amma ai ni kake kallo duk ka hana su Mama zama tun da ka zo ka zauna kai ko kunya ba ka j...."

Idona na rufe jin bakinsa cikin nawa, buɗe ƙofar Ahmad Zayyan na ji, hawaye kawai nake yi.

Yana cire bakinsa na juya masa baya, cikin ciki na ji yana cewa.

"Duk ranar da kika sake cewa ni bana jin kunya wallahi sai na baki mamaki, sai na dawo."

Bai jira na yi magana ba ya fita, sai bayan wani lokaci A'isha ta shigo tana dariya ta ce.

"Lailai za'a koya min irin wannan soyayyar wai dama haka koka iya soyayya"?

"Sauran kaɗan Yaya Zayyan ya faɗi gaskiya a koya min kafin wata rana ku haukata min Miji."

Tana surutunta har na yi bacci sai zuwa Ammyy da Sauban ne na farka, da Ammyy muka zauna har ƙarfe biyu sannan ta tafi.

***********

A Makarantar kuwa sai bayan ya fito daga class ne, Ahmad Zayyan ya shigo office ɗinsa.

Murmushi ya yi tare da cewa.

"Muhammad Zaid."

"Na'am."

"Amma kai dai baka da mutunci yanzu a gabana ka rungume Matarka bayan haka ma har da kiss ko?"

"Ba Matata ba ce? Na ga kai ma, kana da taka matar ko?

Dariya ya yi tare da cewa.

"A'a wallahi ni nafika kunya, kuma Allah gaskiya Maryama take faɗa maka kana jin kunya dai."

Dariya ya yi yana cewa.

"Abba fa ya ce mu wuce gidanmu da Noor, ya ce kayanta ma zan sa akai mata."

Dariya Ahmad Zayyan ya yi sosai yana dukan kafaɗarsa ya ce.

"Gaskiya Abba ya yi abin da ya kamata, ya san kafin ƙarshen wata za ku sake wani cikin, ni wallahi ya burge ni sosai."

"Ni ma na ji daɗi sosai yanzu sai na fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali."

"Allah ya shiryeka."

"Amin."

********Ƙarfe biyu Khadijah ta gaba lecture amma dai gulma sai da ta je Department ɗinmu ta samu Samiha da Hafsat.

Ita da Siyama ne da murmushi akan fuskata ta ce.

"Aunty Hafsat, albashir?"

Dariya Hafsat ta yi tana cewa.

"Yanzu nake cewa zan tambaye ko lafiya Maryama ba ta shigo ba, kuma na kira da wayarta ba ta shiga."

Siyama ce ta yi saurin cewa.

"To ai labari muka kawo muku, Aunty Maryama dai tana asibiti ta yi miscarriage."

"What Ke! Dama Maryama ɗin ciki ne da ita?"

Kallon Samiha Khadijah ta yi tana cewa.

"Ciki ne da ita, amma babu wanda ya sani har ita da shi, sai jiya, yanzu haka ma tana asibiti."

Dariya Hafsat ta yi tana cewa.

"Taɓ amma Maryama munafuka ce, Samiha zo mu je yau sai ta bamu labari a ina aka yi cikin."

"Haka ne Khadijah zo mu tafi ai kun gaba ko?"

"Eh Aunty Samiha."