BABI NA SHA BAKWAI
by @mamyywriter
************** Yau satin mu biyu da hudu, gobe Monday ake sa ran komawa Makaranta, wannan ce semester ta ƙarshe da zamu yi sosai muke shiri saboda gudun matsala.
Ina zaune a falo muna wasa da Zayyan yatsana ya riƙe yana dariya ni ma cike da farinciki nake murmushi.
A hankali Muhammad Zaid ya shigo yana cewa.
"Assalamu alaikum."
"Wa alaikumus salam."
Na amsa ina murmushi, zama ya yi kusa da ni yana kallon Zayyan ya ce.
"Noor."
"Na'am."
Na amsa ina tashi domin kawo masa ruwa.
"Na rasa yadda zan gode wa Allah."
Kallesa na yi da murmushi akan fuskata na ce.
"Saboda me?"
Yana shafa kan Zayyan ya ce.
"Saboda ya ba ni Mata irin ki... sannan ya ƙara ba ni wannan amanar."
Zayyan da yake kwance ya nuna yana dariya. sunkuyar da kaina na yi cikin kunya.
Daidai lokacin ne Zayyan ya fara kuka da sauri Muhammad Zaid ya ɗauke shi yana jijjigawa tare da cewa.
"To ranka ya daɗe, me ya sa ka fara kuka?"
Maimakon ya yi shiru sai ƙara fashewa ya yi da kuka, ido Muhammad Zaid ya zato dariya Ahmad Zayyan ya yi da ya shigo yanzu yana cewa.
"Professor ba ni ɗana tun farko bai saba da hannunka ba."
Muhammad Zaid ne ya harare shi yana miƙa masa Zayyan da yake kuka sosai.
Abun mamaki, Ahmad Zayyan yana karɓe shi sai yaron ya yi shiru.
Murmushi na yi ina cewa.
"Gaskiya My Zaid baka iya raino ba."
Girgiza kai Muhammad Zaid ya yi tare da cewa.
"Wai Noor Ke ma haka za ki ce?"
Ahmad Zayyan ne cikin dariya ya ce.
"Ka ga dai yarona ya zaɓi wanda yake so."
Murmushi ya yi suka ci abinci har lokacin yana hannnun Ahmad Zayyan.
***************
A ɓangaren gidanmu kuwa.
Ummah ce zaune suna magana da Mama yanzu Ummah ta yi hankali ba ta faɗa da Mama duk ta yi sanyin tun abin da ya faru.
Wayar ce ta yi ƙara alamar shigowar kira, tana dubawa ta ce.
"Maman Fati kin ga Mansura na kira".
Murmushi Mama ta yi tana cewa.
"Alhamdulillah! Addu'armu ta fara aiki ɗaga ki ji abin da za ta ce."
Ummah na ɗagawa ko ta ji Mansura tana kuka sosai.
Cikin tashin hankali ta ce.
"Mansura lafiya kike kuka? Wani abu ya faru ne?"
Shiru ta yi na ɗan lokaci sai ta saki wayar tana hawaye.
Mama ce ta taɓata tana cewa.
"Saratu lafiya? Me ya same Mansura?"
Ummah na hawaye ta ce.
"Wai Mijinta ne bashi da lafiya..."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Mama ta faɗa tana dafe ƙirji.
Ummah kuwa kuka take yi tana cewa.
"Ya Allah ka taimaki Mansura."
Abba da yake zaune a gefen falonsa ya ɗago kai a hankali.
Tun da ake ambatar sunan Mansura bai taɓa nuna wata damuwa ba, amma a wannan karon fuskarsa ta sauya.
Mama ce ta kalle shi, tana cewa.
"Ahmad..."
Amma Abba bai ce komai ba.
Wayar Ummah ya ɗauka daga ƙasa.
A hankali ya sa a kunne yana cewa.
"Mansura."
Da jin muryarsa Mansura ta fara kuka kamar ranta zai fita ta ce
"Abba..."
Tsawon watanni ba su yi magana da juna ba.
Mansura tana kuka tana cewa.
"Abba ku yafe min. Wallahi ban yi nufin cutar da ku ba."
Abba ya runtse idanunsa a dole ya buɗe bakinsa ya ce.
"Yanzu ba lokacin wannan magana ba ne Kin ce kina ina?"
Wani sabon kuka Mansura ta sake yi.
Ta faɗa masa sunan asibitin da take.
Da sauri Abba ya ce.
"Za mu zo."
Sai ya kashe wayar.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka shirya tun kafin su fita daga gida Khadijah ta kirani tana sanar da ni abin da yake faru.
Abba, Ummah, Mama da suka tafi.
A asibitin kuwa...
Tun daga nesa suka hangi Mansura.
Zaune take a ƙasa jikin bango.
Fuskarta ta rame sosai.
Idanunta sun kumbura saboda kuka.
Tana ganin Abba ta miƙe da sauri tana cewa.
"Abba!"
Da gudu ta nufe shi sai dai tana isa gabansa ta durƙusa ta kama ƙafafunsa tana kuka cikin kukan ta ce.
"Abba ku yafe min."
Mama da Ummah suka fashe da kuka ganin yanda Mansura ta dawo a yan watannin nan kowa ya ganta sai ta bashi tausayi.
A hankali Abba ya kalli Mansura.
A karon farko tun bayan faruwar komai ya ga yadda ta rame da yadda damuwa ta sauya mata kamanni.
A hankali ya ce.
"Ki tashi."
Kai ta girgiza tana cewa.
"Ba zan tashi ba har sai kun yafe min."
Hawaye ne suka cika idanun Abba sai dai ya danne su ya kamo hannunta ya ce.
"Kina jina? Na ce ki tashi."
A hankali ta miƙe.
Nan take ta rungume Ummah tana kuka.
Ummah ma kuka take yi tana cewa.
"Mansura me ya sa kika yi mana haka?"
"Ummah ku yafe min."
Daga nan suka shiga ganin Mijinta.
Wani saurayi ne mai kamala amma jikinsa duk bandeji yana kwance cikin mawuyacin hali.
Likita ne ya zo wajen su.
Ya ce.
"Muna ci gaba da ƙoƙari. Amma ku ci gaba da addu'a."
Abba ne ya yi shiru yana kallon saurayin.
Sai abubuwan da suka a faru duk suka fara dawo masa.
Da guduwar Mansura.
Da ciwon da ya kwantar da shi.
Da hawayen Ummah.
Da tashin hankalin da Maryama ta shiga har ta haihu lokacin haihuwar bai yi girgiza kansa yana sake ajiyar zuciya.
A hankali ya juya ya kalli Mansura tana tsaye sai kuka take yi.
Wani tausayinta ne ya kama shi, ya zauna a asibitin.
Har dare suna tare kuma har lokacin babu wani mutum daga ɓangaren Mijin Mansura.
Likitoci ne suka fito fuskokinsu cike da damuwa Mansura ta yi saurin miƙewa tare da cewa.
"Doctor lafiya?"
Likitan ne ya kallesa ya a ce.
"Yanayinsa ya sauya ku cigaba da addu'a"
Fashewa da kuka Mansura ta yi baki na rawa ta ce
"Don Allah ku ceci Mijina."
Likitan ne da tausayin Mansura ya kama shi ya ce.
"Za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu."
Cikin ɗakin ya koma Mansura ta durƙusa a ƙasa tana kuka sosai.
Abba yana tsaya yana kallonta can kuma ya taka zuwa gabanta yana ɗora hannunsa a kanta.
Wani abu da bai yi mata ba tun watanni bayan, da sauri ta ɗago tana kallonsa.
Abba ya ce.
"Ki yi addu'a."
Hawaye suka gangaro mata ta ce.
"Abba..."
A hankali ya ce.
"Allah Mai jin ƙan bayinsa ne."
Nan take ta fashe da kuka ta rungume shi.
Sai ƙarfe goma na dare su Abba suka koma gida, washegari ni ma na zo na duba shi.
Zuwana ne Aunty Mansura ta faɗa mana abin da ya faru, ashe Mijinta baya dawowa gida sai cikin dare, shi ne mutanan unguwar suke zuke zargin cewa shi ɓarawo ne suka yi masa duka.
Ni ce na tambayeta yan uwansa, a nan take bamu labari wai babu wanda ta sani a cikinsu Abba yana jin mu bai ce komai ba.
My Zaid ne ya shiga lamarin har bincike ya saka aka yi masa, duk wani kuɗin magani na asibitin shi ya ɗauki nauyi.
Binciken da My Zaid yasa aka yi akan Mijin nata babu daɗi faɗa ta tabbatar zigin da mutunan unguwar ke yi daidai ne.
Sosai My Zaid ya yi wa Aunty Mansura faɗa sannan ya nemi shawarar Abba akan a raba auren, amma Abba ya nuna bai san zancen ba, har Papa sai da ya saka baki amma Abba ya kafe.
Dole sai haƙura aka yi, Aunty Mansura ta yi kuka sosai tana so a raba auren babu wani abu da ta ƙaru da shi sai baƙin ciki amma Abba ya kafe.
Cikin sati biyu Mijin nata ya ji sauƙi My Zaid ya bashi kuɗi masu yawa ya yi sana'a har kuɗin hayar da ya kama sai da My Zaid ya bi.
Ummah ma ɗan kuɗin da take tarawa duk ta bawa Aunty Mansura ta riƙe a hannunta, Mama sai da ta bata wani abu har gidan da take sai da muka je.
**************
Saboda jinyar Mijin Aunty Mansura ban koma Makaranta ba sai yau.
A hankali na fito daga ɗakin yana ɗauke da Zayyan a hannuna, a zaune na samu Muhammad Zaid yana amfani da wayarsa.
Zama na yi ina cewa.
"My Zaid ya baka shirya ba ne?"
Zayyan ya karɓa yana ɗan murmushi ya ce.
"Mu je na sauke ki ni yau ba Makaranta zan shiga ba."
Harararsa na yi ina turo baki na tashi ko magana ban sake yi ba na fita.
Da Sauban na tsaya muke magana har ya zo ya wuce, a hankali na bi bayansa lokacin har ya rufe motar.
A cinyarsa ya zaunar da Zayyan yana tuƙi murmushi na yi ina cewa.
"Gaskiya My Zaid wannan ganganci ne kawo Zayyan ɗin na riƙe."
Ban min magana ba har muka hau titi wasa yake yi wa Zayyan haushi ya kamani har muka isa Makaranta ban sake yi masa magana ba.
Yana tsayar da motar ya fita yana bari min Zayyan ɗin ɗaukar Zayyan na yi ina gyara jakata sannan na tsaya bawa Zayyan nono.
Lokacin da na fito na samu da yawan yan Department ɗinmu a waje, da kallon duk suka bi wasu na nuna ni.
Zayyan na ji an taɓa ta bayana na juya domin ganin waye Samiha ce take dariya ta ce.
"Professor ɗan Prof yau Abbanka ya rufe ƙofa."
Murmushi na yi ina bata shi na ce.
"Wai Prof Ahmad Zayyan ɗin ne ya koma rashin mutunci wannan semester ko dan ya ga zamu rabu ne?"
Wata Fatima Hassan ce ta yi saurin cewa.
"Wane Prof Ahmad Zayyan to Muhammad Zaid ne wancan sati ma haka ya yi mutum uku kawai ya yi wa lecture."
Baki na saki ina so jin abin da take faɗa min gaskiya ko a'a kenan My Zaid ne ya rufe min ƙofa mu zo tare ya barar ni a mota har ya shiga class ya rufe.
Samiha ce ta yi murmushi tana kallon fuskata ta ce.
"Ai wancan satin mun yi tunanin ke ce kika ɓata masa rai ya zo ya huce akanmu ashe ba haka ba ne gashi yau har ke ɗin ya rufewa ƙofar."
A hankali na neƙa domin na tabbatar shi ne da gaske bayan ya ce min yau ba zai shiga Makaranta ba.
Ido na zaro ganin shi ɗin ne yake lecture mamaki ne sosai ya kama ni, kamar ya san ina kallonsa ya ɗago kansa fuskarsa a hade ya zo bakin ƙofar da muke tsaye ya ce.
"Ku matsa gefe kun tare mana isa."
Ni ce ta farko a matsawa, gefe guda na samu ina zama abin duniya ya yi min yawa kamar a mafarki nake ji wai ni My Zaid ya rufe wa ƙofa.
Ina jin ɗaliban suna magana wai ya rufewa matarsa ƙofa, wasu ɗaliban sai nuna ni suke yi.
Samiha ce ta zauna kusa da ni Zayyan yana ganina ya fara kuka dariya ta yi tana cewa.
"Kai professor ni ma fa Uwarka ce."
Murmushi dole na yi ina karɓansa na ce.
"Ki faɗa masa dai wannan da kike ganin ba sa da daɗin zama."
Hafsat ce ta zo tana ganina ta yi tsalle tana ihu, tsorata Zayyan ya yi tare da fashewa da kuka.
Dariya na yi ina bata shi na ce.
"Kin ga ai kin tsorata yaronki sai ki rararsheshi."
Karɓasa ta yi tana jijigashi tana tsokata wai faɗa muka yi da My Zaid har ya rufe ƙofa kafin na shiga, ko kallonta ban yi ba na zauna ni kaɗe na san irin haushin da nake ji a zuciyata.
Sosai Zayyan yake kuka karɓasa na yi amma ba yi shiru ba, raina ne ya fara ɓaci.
Samiha ce ta ce.
"Maryama ki ba shi nono mana."
Zama na yi ina cewa.
"Nono kuma yanzu fa na bashi a mota kawai dai rigima ce dama ya sab..."
Prof Ahmad Zayyan da na ga tsaye akanmu ne yasa maganar tawa tsayawa, hannunsa ya miƙa min alamar na bashi Zayyan.
Miƙa masa na yi ina komawa na zauna, yana karɓasa ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya, shafa kansa yake a hankali yana murmushi.
Ɗagowa ya yi tare da cewa.
"Lafiya kuke tsaye a waje?"
Na san da ni yake yasa na kawai da kaina gefe na ce.
"Makara muka yi shi ne ya rufe ƙofa."
Mamaki ne ya bayyana akan fuskarsa ya ce.
"Ba tare kuka zo ba?"
Baki na turo na ce.
"Tare muka zo a mota ya barni ya shiga hall ɗin."
Murmushi gefen baki ya yi yana cewa.
"Allah ya rufa asiri."
Tafiya ya yi da Zayyan ɗin a hanunsa.
Zaman hira muka zauna har ya gama lecturesa ya fito, tun fitowarsa yake kallona.
Ban kula shi ba, har ya shiga motarsa ya nufi office ɗinsa, Hafsat ce ta dafa kafaɗata tana cewa.
"Ga fa Prof ce ya fito."
Samiha na kalla na ce.
"Samiha ina za ki samu min Zayyan na bashi nono ya fara damuna?"
Dariya Samiha ta yi tana cewa.
"Ɗazu fa na ce ki bashi kika ce ya sha ni wallahi ban san inda zan samu Prof Ahmad Zayyan ba, ni kuma ba zan je office ɗin ni ɗaya ba."
Class yan Department ɗinmu suka koma, mu ma shiga muka yi, har aka gama lecture Prof Ahmad Zayyan bai kawo min Zayyan ba.
Ga lokacin biyu da rabi, masallaci muka je sai bayan mun yi sallah ne na fara jin yunwa.
Allah ya rufa min asiri da kuɗi a jakata. Abincin na siya mana muka ci, muna dawowa class Prof Ahmad Zayyan ya shiga da Zayyan da yake kuka.
Karɓansa na yi ina cewa.
"Yau dai ka nuna wa Abbanka halinka."
Murmushi Prof Ahmad Zayyan ɗin ya ɗan yi tana shafa kan Zayyan ya ce.
"Yunwa yake ji tun ɗazu Muhammad Zaid yake kiran wayarki bakya ɗagawa."
Hanyar fita na nufa Prof Ahmad Zayyan kuma ya fara lecturesa sosai Zayyan ya sha sannan muka dawo.
Ko zama ban yi ba ya fara kuka tsaki na yi kafin na ce wani abu Prof Ahmad Zayyan ya karɓe shi.
Dole sai da shi a hannunsa ya yi lecture Muhammad Zaid ne ya shigo murmushi ya yi ganin Zayyan a hannun Ahmad Zayyan ya ce.
"Hey Zayyan."
Dariya yaron ya yi yana kallon fuskar Muhammad Zaid hannu ya miƙa zan karɓe shi ya juyar da kai dariya duk wanda ke Ajin ya yi.
Murmushi Muhammad Zaid ya ce.
"Good ni zaka yi wa haka ko?"
Ahmad Zayyan ya kalla ya ce.
"Ni fa gida zan tafi, zaka taho da Zayyan ɗin ko?"
Kallon inda nake Ahmad Zayyan ya yi tare da cewa.
"Okay Allah ya tsare hanya."
Fita ya yi ban sake magana ba, tun shigowarsa na daina gane komai har Prof Ahmad Zayyan ya gama kowa ya fito ina mamakin abin da ya faruwa ban gama mamaki sai da na da alamar ya tafi gida kamar yadda ya ce.
Ina tsaye Prof Ahmad Zayyan ya aiko kirana, a gaban motarsa na same shi ina wasa da Zayyan da yake dariya.
"Maryama shiga na sauke ki a gida Muhammad Zaid ya tafi."
Idanuwana ne suka ciko da kwalla na kawai da kaina gefe na ce.
"A'a Yaya Zayyan kawai ka tafi zan taho."
Buɗe motar ya yi yana shiga ya ce.
"Shiga mu tafi bana son musu."
Goge fuskata na yi ina shiga cikin motar tun da muka fara tafi nake hawaye.
Zayyan ya miƙo min, har muka isa gida ina hawaye. Ahmad Zayyan yana sauke ni ya juya.
Kafin na shiga cikin gidan na goge fuskata sai da na zauna a falon Ammyy muka yi hira da Siyama zuciyata ta yi sanyi, sannan na shiga ɓangarenmu.
Bedroom na shiga a kwance na same shi, kayan jikina na cire zan shiga toilet ya ce.
"Noor kin dawo? Ina Zayyan ɗin?"
Ban iya cewa komai na shigewata toilet wanka na yi, har na fito yana kwance shiryawa na yi sannan na shiga kitchen domin yin abincin dare.
Ina aikin na ji shi akan a tsaye yana cewa.
"Noor wai me yake faruwa ne? Tun da kika shigo nake yi miki magana kike yi min shiru."
Tsayawa na yi ina kallon fuskarsa na rasa abin da zan ce masa kawai na cigaba da aikina.
Ya jima a tsaye a bakin ƙofar kitchen ɗin yana kallona.
Ni kuma na ƙi ɗago ido na kalle shi.
A hankali ya ƙaraso kusa da ni tare da rungumeni ya ce
"Noor... me na yi miki?"
Ban amsa ba na cigaba da jujjuya abincin da ke kan wuta.
A hankali ya sake cewa.
"Tun daga Makaranta kika daina yi min magana ban san laifin da na yi muku ba?"
Wutar girki na kashe sannan na juya a hankali.
Na kalle shi idanuwana cike da ƙwalla na ce
"Da gaske ba ka san abin da ka yi ba?"
Kai ya girgiza yana cewa.
"A'a Noor."
Murmushi na yi mai ciwo ina janye jikina daga nasa na ce.
"To bari in tuna maka."
Na ɗan yi shiru kafin na ce.
"Da safe ka ce min ba za ka shiga Makaranta ba sai da muka je ka bari ni a mota ka shiga class."
Murmushi ya yi yana rungume hannayensa a hankali ya dafe goshinsa.
Cikin sanyin murya ya ce.
"Astaghfirullah..."
Matsowa ya yi kusa da ni tare da kwantar da kansa a kafaɗata ya ce
"Noor ba laifina ba ne fa."
Kallon mamaki na ke masa gira ya ɗaga min ya ce.
"Duk laifinki ne ai kin san zan shiga class yau amma kika zauna a ɗaki bayan kin fito ma kika tsaya magana da Sauban na ji haushi sosai."
Abincin na ɗauko ina fitowa daga kitchen ɗin bayana ya biyo zama na yi ina turo baki.
"Noor I'm sorry ba zan sake ba."
Kallonsa na yi na ga ya kama kunnuwansa alamar na yi haƙuri shiru na yi ina cika cikina da abinci.
Ranar dai haka na kwana ina fushi, tun yana ba ni haƙuri har ya rabu da ni, dama kun san ina da taurin kai sosai.