YAR GIDAN YARBAWA

Page1

by @zahrawriter12

YAR GIDAN YARABAWA

Kuka take kashirban harda su shan majina da goge kafafu a kasan tsakar gidan.

Fitowar da babanta yayi da tsumagiya a hannu yasa ta mikewa da gudu ta fita waje tana kara sautin kukanta.

Kokarin bin bayanta yake yi mamanta ta rikoshi tana cewa rabu da ita malam idan ka bita zagaye zagaye kawai zata sakaka dan ba iya kamata za kayi ba", to yanzu bilkisu kina nufin kyaleta zanyi?

Ey mana idan baka rabu da ita ba ai kai zata wahalar kadai san halin yarka sarai", maman ta fada tana ci gaba da tattara musu ragowar kayan da basu tattara ba.

Kwafa yayi kawai tare da komawa dakin dan cigaba da abinda yake yi,

Ita ko zahra tana fita ta Wada makotansu tana ci gaba da ihun kukanta,matar gidan me suna asabe ce ta tare ta tana cewa lafiya? Me akayi miki zahra ? Ko har yanzu kukan komawa gidan YARABAWAn kike?

Da sauri ta daga kai tare da cewa wlh ummansu larai bazan koma gidan yarbawa ba sai dai na koma gidan kaka",ta kare maganar da ci gaba da murza idanunta ko ta samu hawayen su cigaba da zuba,to ke zahra kiyi hakuri mana tunda dai iyayenki sun dage sai kun koma",

Harara ta ballawa me maganar wadda take kawa a gareta wato larai", sannan ta ce", bazan koma din ba ke ki koma mana ai dai kinsan yadda na tsani yarbawa bare kuma ace zama zai hada mu",ummansu larai ta ce", to ai dole kuwa kiyi hakuri tunda Kinga nan kuka samu kuma me gidannan ya baku notice iya yadda zai iya tunda shima bukatar gidansa yake", shiru zahra ta yi tana ci gaba da kunci a fuska da zuci.

Bata koma gidan ba sai daf da magriba shima sai da innarsu larai ta tasata gaba dan rakata sanann ta yadda amma da cewa ta yi babu inda zata babanta dukanta zaiyi.

Da sallama suka shiga gidan ,zahra sai boyewa take bayan innarsu larai saboda Abbanta da ta gani zaune a tsakar gidan yana alwalar magriba,amsa sallamar yayi daidai lokacin mama ta fito daga banɗaki tana cewa a'a lale da innar larai", ko kallon zahra dake makale da ita bata yi ba,zama su kayi a kan tabarmar dake shimfide a tsakar gidan suna gaisawa,abban zahra wajen ka nazo", cewar innar larai", mikewa yayi daga kujerar sakamakon kammala alwalar da yayi,yana cewa innar larai ki kyaleni inndai akan maganar zahra ne dan ba saurarenki zanyi ba", yana gama fada ya fice yana cewa za a tada sallah",

Shima bai kallo inda zahra take ba yayi ficewarsa,mama ce taja numfashi sannan ta ce", innar larai wlh zahra bata jin magana ta raina mutane idan ba haka ba ya za ayi kice ba za mu tashi mu koma inda muka samu ba,in banda kuruciya tafa san cewa yawan gidan haya muke yi", innar larai ta ce", to ai kuruciyar kenan amma dan Allah kuyi hakuri kar a dake ta ko bawa abban zahran hakuri", harara mama ta wullawa zahra tana cewa hakuri da zahra ai ya zama dole Allah dai yasa wannan shashashancin naki ya tsaya a kuruciya", Amin shine addu'armu garesu kawai cewar innar larai.

Bari na tashi na wuce ana ta kiran sallah mu dai sai dai muyi muku addu'a sai munzo ganin gida", to an gode innar larai Allah ya kara zumunci mama ta fada tana saka hijabi sallarta, Amin Amin .

To zahra sai mun biyoku ganin gida tunda fitar asuba zakuyi", zahra bata ce komai ba saboda har ga Allah bata so a dinga tuna mata gobe iyanzu tana cikin yarbawa tsulum tsulum,ita dai innar larai bata tsaya sauraron jin tabakinta ba ta fice daga gidan.

Sum_sum ta wuce banɗaki ta ɗauro alwala tazo tada sallah,tana idarwa ta ta dauko tuwonta tana ci tana harararsa kamarshi yayi mata laifin.

Da asubar fari ana idar da Sallah Abban zahra ya dauko musu me mota har kofar gida ya kwashesu sai unguwar yarbawa dake cikin garin bayelsa ,sun baro unguwar hausawa wadda ke cike da ƴaƴan hausawa da Fulani mazauna garin bayelsa ɗin.

Kafin su fito sai da zahra tasa Abbanta ya daketa saboda kukan da tasa ita ba zata bisu ba.

Har suka je gidan tana kuka kasa kasa saboda zare mata idon da Abbanta yayi akan idan ta kuma yin kuka sai ya zaneta.

Duk da cewa asuba ce gari bai gama wayewa ba,amma hakan bai hana YARABAWAN dake gidan fitowa dan fara hada kayan sanaar su ba,tsayawa su kayi suna kallon su zahra wadda kafin ta shigo gidan sai da ta kuma tada wani darun,ba komai ne yasa suke kallonsu ba sai dan ganinsu kyawawa sananan kuma hausawa duk da cewa sun saba zama cikin hausawan wadannan daban suke saboda kyawunsu me sanyi da tsayawa a rai, wannan abunne ya kuma harzuka zuciyar zahra take ta faman kumburi da hare harere ji take kamar ta kai musu duka,tana zaune har suka gama shirya musu ragowar kayansu da suka zo dasu mama ta share wajen tsaf,sai ga waje ya dau kyau kunsan dai duk munin waje ya samu tsafta kyau yake yi,to bare kuma gidan bashi da wani mugun muni katon gida ne me dauke da dakuna goma sai ban daki kwara biyu na wanka dana ba haya,kowa a nan yake bukatarshi girki kuwa a kofar daki ko cikin daki ake yinsa,tsakar gidan simintine fetal kuma ɗakunan babu laifi suna da dan girma kuma ciki da falone, sai dai babu tsafta ko guda kun dai san yarbawa babu ruwansu da tsaftar waje sai ta jiki,dan haka ban daki da tsakar gida zuwa zauren gidan sai hakurin zama ga me tsafta da tsentseni irinsu zahra.

Har yau da suke cika kwana biyu da tarewa a gidan zahra bata saki ranta ba,dan hatta da wanka taki yi dan kawai kar ta shiga banɗaki abincinma dan mama ta ritsata ne shi yasa ta ci,duk da cewa kuwa basu su kayi ba kuma ba daga hannunsu ya fito ba.

Haka nan zahra ta tsangwami kanta har da su cuta wanda hakan ya tayarwa da iyayenta hankali,kakarta da tazo haka ta yi ta fada ta ce ", sai ta tafi da ita dakyar abban zahra ya bata hakuri dan shi sam baya son zaman zahra a gurin mahaifiyartasa saboda tsananin kaunar da take yi mata wanda duk wannan tabara da sangartar a wajenta ta samosu,sakamakon zaman da ta yi a wajenta shi yasa yayi dabarar karbota to gashi yanzu tana son kara karbar ta,dan haka ya bata hakuri tare da kafa mata hujjarsa nason zahran tayi karatu,dole ta hakura ta tafi ba dan ranta yaso ba.

Kwanan zahra uku sannan ta samu lafiya,alokacin tuni Abbanta ya karbo mata transfer daga makarantarsu ta unguwar hausawa,dan haka tana jin sauki ya Kaita mkrtr gwamnatin dake kusa dasu wadda take cike da ƴaƴan yarbawa dan hatta da malaman hausawan basu da yawa duk sai yarbawa.

Cikin kankanin lokaci YARABAWAn da suke gida daya da su zahra suka fahimci irin tsana da kyamar da tayi musu,duk da cewa kuwa su din musulmaine amma hakan baisa zahra ta rangwanta musu ba.

Take sunanta ya tashi daga zahra ya koma yar gidan yarbawa,sai dai da yawan abokanta basa iya gaya mata sunan a gabanta saboda tsoran masifa irin tata,amma manya basa shayin fada a gabanta su kam bata iyawa dasu, ba wai dan tana storo ba sai dan kawai tasan idan tayi musu rashin kunya zata daku wajen Abbanta da mamanta,sai dai tayi ta gunguni tana harere_harare zuciyarta fal takaici.

Da haka suka kwashe wata daya a gidan yarbawa,tuni mama ta kama sana'a irin wadda ta saba yi a tsohuwar unguwarsu ta bagoburi,kamar danginsu magi gishiri kanwa barkono da dai sauransu,zahra kuwa da yamma idan ta dawo daga makarantar islamiya aya da su goruba da kantu take kasawa a kofar gidansu,yarbawa idan zasu sayi kayan zahra saidai su tura yaran Hausawa na makotansu su siyo musu dan zahra bata saida musu da kaya,zahra manyan kasa gashi dai ita za ayiwa ciniki amma ko akwalar rigarta.

Su kuma kamar wanda aka asirce dole sai sun sayi kayan zahra,suna son zahra duk da kyamar da take nuna musu da hantara kunsan beyerabe da son abu me kyau shi yasa suke son zahra saboda tana da kyau gashi tana da shiga rai duk da cewa ita din matsiwaciya ce mafadaciya ta bugawa a jarida.

A kullum sai an raba fada da ita,zahra fada ko ba nata bane siyansa take yi gata da shegiyar tsokana,mama tun tana dukanta har ta gaji sai fada kamar zata ari baki haka Abbanta,so biyu tana guduwa gidan kaka Abbanta yana daukota.

Idan uwa tazo wucewa da danta ta bari zahra ta Ganshi to ta tabbata sai ta saka shi kuka daga karshe kuma tayi masa kyauta ba wai dan cin hanci ko kashe bakin uwar ba,a'a wannan halintane kyauta gareta kamar me shi yasa kawayenta maza da mata basa iya yin dogon fushi da ita.wannan kenan.

ABRAHAB BAKARE MUHAMMED(ABM COMPANY) wani shahararren kamfanine a nan cikin anguwar yarbawa wanda ya kusan cinye rabin anguwar,a cewar mutanen anguwar me kamfanin matashine yazo yayi kamfanin a cikin anguwarne saboda taimako da rage masu shaye_shaye da masu zaman banza harma da masu kwace,ya debi matasa masu jini a jika da yara masu tasowa da yanmata har da tsofaffi aiki dan kawai ya inganta rayuwarsu,basu taba ganinsa ba amma kullum sallah sai anyi masa addu'a,bakin mutane cike yake da yabon wannan matashin zakin me wuyar gani,akwai tarin kamfanunuwansa a cikin garin bayelsa da gidajen mai da plazer Wanda ba boyyyayu bane saboda tambarin BAKARE 'S FAMILY dake jikin ko wane ma aikata,amma duka babu wanda yake zama a ciki hasalima ance baya kasar gaba daya.

Gaba dayan yaran anguwar a duk ranar da babu makaranta to dif zaka ga anguwar tayi saboda sun tafi kamfanin gyaran anduga na ABM wato bakare's company,to hakan da Abban zahra ya gani yasa itama zahra ya ce ta dinga binsu bayan yaje ya tambayo manager an saka sunanta cikin list din ƙananan ma aikata,hakan yasa ta fara zuwa itama tare da kawayenta hausawa.

Suna tafe kan hanyarsu ta zuwa kamfanin zahra ta dubi kawarta nadiya ta ce", nadiya wai shi me kamfanin nan wane Yarene Dan naji sunansa wani iri kamar yarbanci_yarbanci kamar Kuma larabci_larabci?

Nima ban sani ba kuma duk wanda zaki tambaya ce miki zaiyi bai sani ba saboda bai sani ba din", cewar Nadiya Sharif.

To Allah yasa dai ba beyerabe bane", zahra ta fada tana gyatsina kyakkyawar fuskarta da ke cike da kuruciya tamkar taga Kashi....

Diiiiiiiii........

Yar gidanyarabawa nasa salon nadabanne kar ku sake a Baku labari....

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: YAR GIDAN YARBAWA