YAR GIDAN YARBAWA

Pg4

by @zahrawriter12

..........Da gudu Zahra ta karasa fita daga gidan tana ci gaba da ƙyalƙyalawa lola dariyar mugunta.har ta fita ta kuma leƙowa tare da yiwa lola gwalo tana cewa yau dole naci kuɗin bati 'yan anguwa kuma suci banza dan ina saida rabi zan ƙarasa rabin da kyauta' sai dai yau zuciyar ki ta buga saboda anyi alheri marowatan banza marowatan wofi",

Ihu lola ta kuma sawa gashi ta kasa mikewa dan bin Zahra, saboda yadda take jin tsamin kafarta wanda take kyautata zaton gocewar kashi Zahra ta jawo mata,ga kuma idanunta da suke rufe ta kasa budesu dan sosai Zahra tayi mata barbaɗen yaji a cikinsu,su kuma su bola kowa ya yi takansa yana fama da atishawar yaji.

Tana cikin wannan halin ƙaƙanikayin mijinta Adebayo ya shigo,shi ya dagata ya Kaita daki yana tambayarta abinda ya faru? Take ta sanar mishi da abinda Zahra ta yi mata,ihu ya saka cikin irin hargaginsu yana cewa walle bazai bar cegiyar yarinyar nan ba yan sanda zai dauko,lola najin haka ta rungume Adebayo tana cewa thank you Ade shi yasa nake da ɗa sonka",daga haka ya fice fakam fakam zuciyarshi cike da son zahra da kwadayinta,yana ganin wannan kamar wata dama ya samu ta samun kan Zahra.

Kai tsaye wajen sana'ar lola ya nufa dan haɗuwa da Zahra,ya tabbatar da zarar yayi mata barazana da 'yansanda zata bashi haɗin kai,ji yake a rashi inama ace Zahra beyerabiya ce da bashi da wata fargaba gurin samun biyan buƙatarshi.

Zahra kuwa tuni ciniki ya miƙa,Zahra me farinjinin mutane kan kace me kosai ya kare fanke na gab da karewa,idan bahaushe ko wani yare daban yazo siya zata bashi kyauta,amma bayerabe har da alakoron tsada,a haka suka kare tas,tana cikin tattara kuɗadenta Adebayo ya ƙaraso tun daga nesa ta hangoshi fuskarnnan sai shuni take kamar ta arnan daji,dauke idanunta tayi daga kallonsa dan ita har ga Allah kyankyaminshi take ji,tana jin lokacin da ya ƙaraso ya tsaya a kanta yana faman huci kamar zai cinyeta ɗanye sai faman muzurai yake yi,kallon sama da ƙasa ta yi masa kafin ta banzatar dashi da ci gaba da abinda take yi.

Ke" Zahra kina kallona kina dauke kai saboda kinsan abinda kika mana ko? To wallahi baki ci bulus ba yau a cell Zaki kwana yanzu daga nan sai polictation. zaki san wa kika tabo yau me karyar iskanci kawai", dalla malami rufe mana baki kazo sai wani tofeni da miyan bakinka me wari kake.nabi yansanda da gudu idan ban kwana cell a yau ba kai baka cika beyeraben da yazo duniya kafin aure ba nonsee kawai", ta kara maganar da watsa mishi kallon banza tamkar manyam idanunta zasu fado ƙasa.

Mamakine ya kamashi saboda bai taba zaton rashin tsoron Zahra ya kai haka ba,da yayi tunanin yana yi mata maganar yansanda zata rikice da kuka ta fara rokonsa da yayi hakuri a yayinda shi kuma zaiyi amfani da wannan damar ya samu abinda yake so,firgigit ya dawo daga mamakin da ya tafi sakamakon tsakin Zahra a kunnenshi lokacin da tazo giftashi.

Binta yayi da kallon mamaki wanda ke cakuɗe da zallar ƙwadayi,dan idan ka kalli maƙoshinsa zaka kula da yadda yake hadiyar miyau kamar tsohon maye.

Zahra kuwa tuni ta manta dashi ta wuce gida tana yan wake wakenta na nishadin da har yanzu baiyi galabar cire mata baƙincikin abinda ABM yayi mata ba.

A kan hanyar ne tayi siye siyenta da kuɗin ta bada mafi yawa sadaka,dan karma taje gida mama tace sai tabaiwa Lola kuɗin,tab abinda ma ba zai taba yiwuwa ba,haka kawai kare da shan bugu kura da lashewa,ta fada a fili har da ɗan murguɗa ƙaramin bakinta tare da Farfara fararen idanunta masu kamar an ɗiga mai.

Da rangaɗeɗiyar salllamarta ta shiga gida duk da cewa wani bangaren rayuwarta cike yake da tsoron hukuncin da mama da Abba zasu yi mata,ta baya ta rago kenan lokacin da zata yi lefinta bata tunawa da kowa sai bayan komai ya kammala zata fara tsoron hukunci wanda hakan bashi ke nuna cewa gobe bazata ƙara.

Ile kuwa da hararar mama ta fara cin karo,sai kuma lola dake bakin ƙofarta tana kaiwa da kawowa burinta kawai Adebayo ya dawo mata da kudinta yace" mata zahra na cell,sai kuma kawai taji zazzaƙar Muryar zahra na kwarara sallama wanda ta amsheta a kahon zuciyarta,(sufa yarbawa ba a cin kudinsu shi yasa lola kejin duniyarta na juya mata😆)

Da gudu ta nufi Zahra idanunta har yanzu basu dawo daidai daga yajin da Zahra ta antaya musu ba,Zahra ina kudina? Ta fada kirjinta na bugun amsar da Zahran zata bata,kafin Zahra tayi magana saiga Adebayo tafe da macen yansanda yana cewa gashinan yaro bayaji ku bugeshi ya fito da kudi kawai",wani kallon ko a jikina Zahra tayi musu kafin ta ɗauke kanta zuwa kan mama da har yanzu take zuba mata harara ta kuma ƙi cewa komai.

'yarsandar ce ta ce" da Zahra ina kuɗinsu yake ki basu kuɗinsu mu rabu dake a gida,idan kuma babu kudi mu tafi dake ki kwana cell", duban me maganar Zahra ta yi kafin ta yi wata ƙwafa ta ce", a kira duka mutanen gidannan su fadi idan lola ta bani kudinta hukunci dole ba zai yiwu ba sai da shaida in dai adalci za ayi", ta faɗa tana maida kallonta kan sauran mutanen gidan da su kayi cirko cirko suna kallon ikon Allah zuciyarsu fal tsoron Zahra,daya Yar sandar ta ce", ai dama muna bukatar sheda amma dole sai mun tafi dake in yaso sai su biyomu suyi shaidar abinda suka sani," to muje Zahra ta fada tana kaucewa kallon zaki haɗu dani da mama ke antayo mata lodi lodi,juyawa su kayi suka tasa Zahra a gaba wadda suna fita waje ta ce", alanfur bazata shiga motarsu ba zata biyosu a okoda,juyin duniya taƙi binsu,saigashi ana kokuwar saka zahra a mota cizo ɗaidai tayiwa yansandan matan suka saketa suna faman zare idon jin zafin cizon da Zahra tayi musu. cikin masifa Zahra tace", wlh baku isa na shiga motarku ba tunda ba laifi nayi ba,ku rabu dani mu shiga nafe nida shaiduna mu biyoku,idan kuma kukace zakuyi fada dani to wallahi ba riba zaku ci ba,Ni an fada muku ina tsorone da zaku dinga tunanin gudawa zanyi eye? .

Dole suka hakura suka barta da sharadin su jera tare,dan sosai suka ji zafin cizon da tayi musu,itama bata yi musu ba ta shiga okada ita da su bola suka take musu baya.

Koda akaje polictation kowa ya bada shaida akan cewa lola bata bawa Zahra kudi ba dan haka Zahra batasan maganar kuɗin da lola take yi ba,nan take lola ta ce", ai ba kudi ba ne kayan kudine na sana'ar ta da ta dauka ta saida,nan ma Zahra tace waye shaidarta,,?lola ta ce yangida su kuma yan gida zahra bata ɗau kaya a gabansu ba,bayan haka koda ta dauka a gabansu ma bazasu iya bada shaida akan hakanba saboda tsoran kar gobe ta zuba musu attarugu a ido,dan sunsan cewa ko sun fada anyi mata hukunci dawowa zata yi kuma wallahi duk sai tayi maganinsu da salon muguntarta , wannan tunanin da sukayi yasa duk sukace basu gani ba babu ruwansu",

Dariya Zahra tayi tare da yiwa lola gwalo sannan ta radawa basu a kunne,kunyiwa kanku gyadar dogo Dan haka zaku zauna cikin Salama kuma zan daga muku kafa har na tsawon sati Daya babu wanda zan takurawa", aiko take basu ta shiga yake baki har ranta tana jin dadin abinda Zahra ta faɗa.

Take dpo ya kashe case din,Zahra Kuma tayi tsalle ta dire ta ce", sai anbi mata hakkinta akan sharrin sata da lola tayi mata dan haka a rufeta a cell kawai,aiko babu wani jan magana dpo da yake ta rawar jiki akan Zahra yace", to ai ko baki fada ba dama wannan ya zama dole,dan babu yadda za ayi muna gani ana cin zarafi da batawa 'yanmata kyawawa suna dan haka kar ki damu kije ki hutawarki kawai,ga wannan kiyi kuɗin okada kuma kiyi hakuri kinji,karbe dubun da dpo ya miko mata ta yi tana faman gatsine dogon hancinta tare da Farfara manyan idanunta da a take ta kuma susutar da dpo ya fada tafkin ƙauna me zafi.

Lola kuka tasa lokacin da aka tasa ƙeyarta zuwa cell,sai gashi ta bige da bawa Zahra hakuri,kiyi hakuri lola yaufa sai kin kwana a cell ko dan ki kiyaye gaba", daga haka taja zugarta suka fice daga ofishin dpo.

Suna fitowa harabar gurin suka ci karo da tawagar ABM,Wanda ko su kansu yan rakiyar da gaerd dinsa basu san dalilin zuwansu station dinba,abunda suka sani kawai shine dale akwai dalili dalilinne basu sani ba kuma ba su da karfin halin tambaya.

Sanye yake cikin wani farin boyel sassalka wanda zaka iya gano farar best din dake jikinshi kafarshi saye da bakin takalmi wanda yake wani irin ɗaukar ido,kanshi babu hula sai kwantacciyar sumarshi ta larabawa da take wani irin sheƙi,zagayeyyen sajenshi ya kuma bawa kyawunshi da kwarjinin shi damar fitowa sosai,babu wanda ya isa yayi masa kallo guda ya hakura ba tare da ya kuma yin wani ba,namiji ma bai gajiya da kallon ABM bare kuma mata.ga wani irin kamshinsa da ya cike hancin kowa dake harabar gun, kai har na ciki ma sun shako kamshin ABM,taku yake cike da zafin nama da karsashi wanda ke nuni da cewa shidin namijine wanda ya saba geming kakkarfar jikinshi.

Wani kallon banza Zahra ta watsa mishi tana jin wani irin zafinshi da tsanarshi a ranta,kowa ya kauce daga hanyar da ya doso dan girmamawa amma banda Zahra wadda ta canja salon tafiyarta da yanga ba tare da ta damu da tunkaro gurin da yake da ɗa yi ba.

Ke bazaki matsa ki bada hanya ba cewar daya daga cikin gerd dinshi fuskarshi babu annuri ko wasa,harara ta watsa mishi har da la'adar murguɗa baki,ji take da tana da hali wallahi sai ta bangajeshi ya kifa ta ka ya fasa hakoran da basa fitowa waje.

Ganin bata da niyar kaucewa yasa wani ƙaƙƙarfan gerd nufota da niyar ɗauketa da hannu ɗaya,sai dai ko taku uku baiyi ba yaji dakakkiyar Muryar ABM wadda ke gauraye da wani irin salo yana cewa,ba buƙata", wanda take gerd din ya koma baya,ita ko Zahra harara ta kuma watsawa gerd din kafin ta kalli gefenta da ABM yazo giftawa,saboda yadda tayi bake bake a hanyar yasa har sai da suka gogi juna hakan yasa Zahra yin tsalle ta koma gefe tana ambatan Ni bansan iskanci wannan ai wayon taba mutumne",babu wanda ya tanka mata ta Karachi ƙunkuninta taja zugarta su kayi gida.

A ranta kuwa ji take tana son sanin abinda ya kawo ABM polistatin ko Allah zaisa ta ci karo da abinda zaisa ta fara rama cin mutuncin da yayi mata.......

🤣🤣🤣🤣zahranmu ta mutunci yi komai ba komai ba kuruciya ce watarana ba zakiyi ba🤣

Fatima y Adam ✍🏽

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*