YAR GIDAN YARBAWA

Page6

by @zahrawriter12

Tuntuben da taci da mutum tare da fadawa jikinshi gaba daya yasa ta firgita ta buda baki zata fasa kara,amma sai hakan bata samu ba saboda jin tattausan hannunshi da ta yi a saman fatar bakinta ya rufe bakin da karfi, batare da yace komai ba ya dubi securitys din da sukayi ciki cirko cirko suna kallonsu tare da jan nishin gudun da Zahra ta saka su,alama yayi musu dasu je kawai zaiji da lamarin,juyawa su kayi suka bar gurin suna jin haushin Zahra da mamakinta.

Zahra kuwa babu abinda take sai kici kicin kwatar kanta saboda a halin yanzu riko ne akayi mata na mazaje dan haka ta kasa kwatar kanta.

Janta yayi ko nace dauka cak tamkar wata yar tsana ya fara taku da ita zuwa hawa na shida inda office dinsa yake.

Zahra kuwa zuciyarta tamkar zata buga haka take jinta saboda a halin yanzu ta gama gane ko wane ta hanyar kamshin turarensa da ta rasa dalilin haddaceshi,sai kuma yanayin takunsa da lallausar sumar kansa ta larabawa, so take tayi masa TSIWA ya sauketa amma ta kasa bude bakinta saboda tukukin da zuciyarta take yi mata akan tsanarsa da rabar jikinsa da tayi wanda hakan bai taɓa faruwa da ita ba.

Har ya shiga da ita office babu wanda suka hadu dashi saboda kowa ya shiga aiki ba lokacin zirga zirga ba ne,shi dama bai da sactariya yana kan binciken nema saboda tsantseninsa da kakale ba kowa yake iya zama dashi ba,diretan da yayi ne ya bata damar kallonsa tamkar zata hadiye shi babu ko tsoro saman fuskarta sai acan kasan zuciyarta wanda ta rasa na meye,yana jin yadda take watsa mashi kallon tsana amma bai ko kalleta ba saima wani abu da ya shiga yi daban, wannan Shariya ba karamin kara harzuƙa Zahra tayi ba , hakan yasa ta bude bakinta da take jin ya mata kadan wajen fadar abinda ke cikinsa ta ce", malam me ye hakan? Karfa kayi tunanin dan ina karkashinka zan zauna ka dinga takani,"sam Zahra ba haka take ba,wlh duk ka kuma tabani ranar sai nayi maka tijarar da zaka kunyata idanun staffs dinka, Ni ba yar iska bace rashin kamun kaina ba na iskanci ba ne,ta fada cike da tasowar tsohon mikin dake ranta.

A hankali ya dago kansa tare da watsa mata shanyayyun idanunsa masu kamar me shan maganin bacci,yadda ta furta kalmar yasa shi ɗan zuba mata idanunsa yana tuna ranar da abin ya faru da irin bakin cikin furucinsa da ya gani a idanunna tun a ranar,gashi yanzunma ya gani.

Kallon da yake matanne yasa ta kawar da kanta tana ci gaba da gunguni ƙasa_ƙasa bata san ya akayi kallonsa yayi tasiri a gare ta ba,har yasa ta kasa ci gaba da fadar abinda ke bakinta,waye dan iskan? Tambayar da ta fito daga bakin abm kenan ba tare da ya cire idanunsa akanta ba,ɗan ƙaramin bakinta ta murguɗa tare da gunguni,ɗal taji an buge labbanta hakan yasa ta kalleshi da sauri tana mamakin lokacinda ya karaso inda take ba tare da ta kula ba,ga kuma zafin dallin da yayi mata,sunkuyowa yayi daidai fuskarta har suna jin hucin numfashin juna kafin cikin muskilar muryarsa ya ce", daga yau kika kuma murguɗa min baki sai na cireshi inga da abinda zaki kuma rashin kunyar ,umm kuma daga yau babu makara kika kara kaiwa goma baki zo ba,ba korarki zanyi ba kawai dai zanyi miki abin 'yan iska da fatan kin gane karatun? Ki wuce ki koma wajen aikinki tun kafin a fara yi miki kallon 'yar iska kinga kenan reshe ya juya da mage", wata dariya Zahra taji na neman kufce mata amma sai ta yi kokarin dakewa dan karma ya dauka ta yafe dan yanzu take jin za a fara wasan dan wlh sai ta tsula masa tsiyataku kala_kala zai san yayi da Zahra yar gidan yarbawa,wai shi a dole sai yayi Hausa ana cewa rashe ya juye da mujiya shi kuma yana da mage aikin kawai zamu gamu wlh sai kazo kana bani hakuri mugu dan iska kawai",

Yana kallon yadda bakinta ke ta jujjuyawa tana hararar gefansa yasan sarai tsiwarta take yi a ciki wanda ba zata iya fitowa fili ta yi su ba,bai tanka mata ba har ta gama ta juya ta fice tare da buga masa kofar kamar ana yaki,tabe baki yayi ya koma ya ci gaba da aikinsa yana kokarin ya kice damuwar Zahra da ciwon kan da ta fara sa masa.

Lokacin da securitys din suka ga ta fito hankali kwance fuskarta babu alamar bacin rai ba karamin mamaki suka sha ba,ba su kuka shiga mamaki ba sai da suka ga ta shige babban room na kananun ma aikata wanda hakan ya basu tabbacin aikin dai za ta yi ba tare da doka ta yi aiki akanta ba,harara ta watsa musu saboda kallon da suke mata,da sauri suka dauke idanunsu akanta dan haka nan suka ji ta yi musu wani irin kwarjini.

Su hafsa ma sakin baki su kayi suna kallonta yayin da a wani bangaren farincikinsu ya ƙi boyuwa,tarbarta su kayi cikin farinciki ,ita dinma fuskarta da annuri dan tana son kawayennata kamar yadda suke matukar sonta,a tunaninsu aikinta zata karba amma sai suka ga sabanin haka dan kuwa Zahra guri ta samu ta shiga taya su hira ba tare da ta taɓa ko zare dake gurin ba,suna son yin magana suna tsoro,da kyar dai nadiya ta hadiyi miyau sannan ta ce", zahra wai ba aiki kika zo ba ne?shi nazo amma ba zanyi ba ko da magana? Ta fada tana wani tamke fuskarta kamar wata boss,nadiya tace", amma kinsan idan ba ki aiki ba tamkar babu ke a cikin ma aikata ko? Inji ubanwa ? Zahra ta fada tana zazzarowa nadiya manyan idanunta sannan ta ci gaba da cewa ai to naga sunana ya shiga jerin sunan ma'aikata an wuce gurin dan haka Ni ma aikaciya ce zanzo aiki kuma ba zan yi aiki ba amma zan karbi albashi ko zuwan da nayi ai shima wani abu ne ko? Dan kallon hafsa da take ta aikinta kamar bata san me suke yi ba ta yi tana cewa munafuka idan zaki fadi abinda yake RANKI ki huta Gara ki fada dan nasan karshen maganar kenan ", Zahra ta karashe maganar cikin zazzafar harara tamkar zata huce hushin me Company akanta.

Uhmm hafsa ta ce tare da cewa bani na kar zomom ba,ko ratayar ma ba wanda ya bani",

Haka suka ci gaba da aikinsu ba tare da sun kuma kula yar balaja un tasu ba.

Zahra kuwa tana zaune tana kallon kowa dai dai, jiran wanda ze tabota take kawai ta sauke masa hushin me Company.

A haka har lokacin tashinsu yayi kowa ya kimtsa tsaf ya dauki hanyar gida,

Koda suka zo fita daga bulding din sai da Zahra ta tsaya rike da kugu ta harere security dinnan tas har da su gatsine da tofar da yawu,amma ga mamakinta ko inda take tsaye sun kasa kalla ba wai dan basu ganta ba ne a'a sai dan wani dalili da su kadai suka barwa kansu sani.

Haka ta Karachi jan maganarta daga karshe taja zugarta suka bar wajen ranta be so ba akan bata samu wanda zata juyewa takaicinta ba.

Da sallama ta shiga gidan tare da yin ball da kwanonin da suka tare mata hanya,tsayawa tayi rike da kugu yatsa a baka tana karewa tafkeken tsakar gidannasu na yarabawa kallo,kafin cikin zazzaƙar muryarta me cike da sauti ta ce", wlh mutanen GIDAN nan ku fito ku share tsakar gidan nan ko yanzu kuga aikin Zahra yar gidank....

Kan ta gama rufe baki sai gasu sun fito da gudu har da me daura zani da me saka riga da alama dai suna tare da mazajensu amma wannan yar balaja un tasu ta zo tayar musu da hankali,wani irin watsatstsan kallo take binsu dashi dan tantance wanda basu fito ba,aiko zaraf idanunta ya sauka akan labulen dakin iyoka wadda itace ta rage bata fito ba,iyoka iyoka iyoka ta shiga kwala mata kira tamkar wata yar cikinta.

Kamar daga sama iyoka da tafi kowa tsoron Zahra tajiyo kiran da take mata,zare idonta tayi tana kokarin kwace jikinta daga na mijinta da yake ta kokarin biyawa kansa bukata,ganin yaki sakinta yasa ta tureshi da karfi tana cewa kai dayalla cikani haba tun dazu kana abu daya se kace maye karabu dani wancan shegen yaro na kira ina kin zuwa ze Turo wani bala in", ta karasa fada tana mai jan zanin gadonta ta rufe jikinta, a haka ta fice jikinta na rawa kar zahra ta kuma yi mata azabtar da ta yi musu shekaran jiya.

Tana dab da fitowa Zahra ta tace wlh idan baki fito ba zan kyastawa wannan dukulƙulallan labulen naki ashana dan dama na gaji da hanani hadiyar miyau da yake", tana rufe bakinta sai ga iyoka har da cin tuntube sabida yadda jikinta ya dau rawa da jin batun kone labule.

Kallon tsaf ta yiwa iyoka sannan ta tuntsure da dariya tana kallon yagalgalin zanin gadon da ta yayimo.

Saida ta gama dariyarta ba tare da sun tanka mata ba sannan ta fara nuna musu tarkacensu dake yashe a tsakar gidan tare da basu umarnin gyara shi kafin ta fito daga wanka.

Aiko duk kyuyarsu haka suka zarge suka fara gyara gidan, lokacin da zata shiga bandakin ma sai da tasa lola ta wanke shi tas sannan ta shiga tana dariyar mugunta ko ba komai dai ta huce hushin wancan mugun me suffar salihan,amma a ranta Allah Allah take su kammala kafin mama ta dawo dan tasan itama zata ci kanoyarta gun abbanta da mama.

_____________

Jere suke a saman tafkeken dining din da yayiwa dakin cin abincin kawanya,duk wanda ka kalla fuskarshi a washe saboda farincikin yau Abrahab bakari yana tare da su yana dinner Wanda da wuta ka tsinci hakan,tunda shi kullum cikin killace kanshi daga hayaniyar mutane yake,duk da cewa ko ya zauna din babu wani abu da zai nuna maka shedar yana gun in ka cire ƙamshinsa na musamman me nacin zama a duk inda ya bari.

Yanzunma haka ne ta kasance dan hatta da kannenshi basu da ikon yin wani kwakkwaran motsi wanda zai dami kunnenshi komai a nutse ake yin shi in dai yana waje domin shi kanshi nutsuwarne saboda tsabar kwarjini da cika wajen da yake ko baka sanshi ba ka tsaya a gabansa dole ka samu kanka da kamewa.

Stubon girl ya fada a saman labbansa tare da lumshe fararen idanunsa da ko da yaushe suke kusan a lumshen,ya tsine fuska yayi tare da dan mele tausasan labbanshi da suke kamar na baby yana jin damuwa akan tunata tsiwar Tata da yake yawan yi wanda hakan ke bata mishi rai tare da jin rashin kunyar yarinyar yayi yawa.

Sama_sama ya tsakura abincin ya zari tsue ya goge karamin bakinsa daga nan ya dan yiwa Amminsa side hug haka dady kannensa su kayi masa good night,ya haye saman yana mai bar musu mataccen kamshinsa.

Zahra yar balaja un yarbawa🤣🤣🤣

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*