YAR GIDAN YARBAWA

Pg7

by @zahrawriter12

..........koda ya shiga luxery room dinsa kai tsaye toilet ya fada,tsaf ya yi sababben shirinnsa na bacci,komai cikin natsuwa yake yi tamkar wata mace yar kwalisa,komai nasa babu hayaniya,ash ɗin jallabiya ya saka tare da tsadaddun turarukanshi da idan ya gwamutsasu duk saninka da turare baka isa tantance wanne yasa ba, sai dai duk sanda ka shaƙi ƙamshinnasa ya tsaya maka a ka saboda tasirinsa.

Kai tsaye ya nufi kebabban gurin sallarsa da yake tsaf tamkar wani dan ƙaramin masallaci,ya tada kabbara,Masha Allah bai gusa daga gurin ba sai misalin biyu na dare,kwanciya yayi a gadonshi dake neman cinye rabin dakin duk da girman dakin kuwa,rantse idanunshi yayi tare da gabatar da addu'a kana ya fara kokarin bacci wanda babu dadewa ya dauke shi saboda dama baccin yake ji.

Lokacin da Zahra ta fito daga banɗaki tuni mutanen nata sun kammala aikinsu ko wacce ta kwashe kayanta ta gudu daki tana tsinewa Zahra a ranta,dariya tayi bayan ta karewa tsakar gidan kallo sannan kai tsaye ta wuce dakinsu cikin jin dadin rashin dawowar mama.shiryawa tayi sannan ta ci abinci tana yi tana ƙunƙuni dan duk abinda take ta tuna da ABM sai taji ranta ya ɓaci wanda har mamakin hakan take saboda ita sam bata kasance daya daga cikin mutane masu riko ba,dan duk abinda zaka yiwa Zahra to da zarar ta amayar dashi ta fesar maka shike nan ta manta sai idan ka kuma yi mata.

Tana cikin cin abincin mama tayi sallama ta shigo idanunta fes akan Zahra,mama sannu da zuwa yau kin dade da yawa", ey wlh na dan tsaya can tsohuwar anguwarmu nayi zumunci innar larai da larai suna gaida ki", dan murmushi tayi tana cewa ina amsawa mama.

Koda dare Zahra kasa bacci tayi tana ta sake saken hanyar da zata fara bi dan kuntatawa abm ko ta ce rama abinda yayi mata,kwafa tayi tare da juyawa dayan bangaren,Zahra", mama ta kira sunanta ba tare data jira amsawar Zahran ba ta cigaba da cewa dan Allah Zahra yaushe zaki girma ne? Dan Allah Zahra ki nutsu kullum fa girma kike yi yanzu kuma kuna komawa makaranta jarrabarwar karshe fa zaku zana ga yammatanci ya fara kama ki amma kullum abunki karuwa yake ba raguwa ba, kullum fa kika fita sai an kawo min kararki daga wanda zai ce kin barar masa da talle sai wanda zai ce kin watsa mishi kasa a kan kayan sana a, wata yarinya ma baki kika fasa mata", tura dan mitsitsin bakinta ta yi tana cewa to mama ba su suka fara tsokata ba dan me zasu ce min yar GIDAN YARBAWA tunda sun san bana so? Au Dan sun ce dake yar GIDAN YARBAWA da yar wane gidance? Ai yanzu ne kika zama cikakkiyar yar GIDAN YARBAWA tunda kina tare dasu har kina cin kaniyarsu yar mitsitsiyarki da ke amma suke tsoron ki saboda masifarki Zahra", shuru Zahra ta yi tana faman tura baki,mama kuwa bata gaza ba haka ta ci gaba da yi mata nasiha da nuna mata rayuwa cikin dabara duk da tasan cewa Zahran ba dauka zata yi ba amma dai tana fatan gaba su yi mata amfanin da zata yi alfahari da Zahran Tata.

..........washe gari da safe Zahra yi tayi kamar nasihar mama ta shiga kanta saboda har ta gama shirinta bata kula kowa ba,su kansu yarbawan mamaki suka dinga yi duk da haka basu samu natsuwa ba har sai da Zahran ta bar gidan.

Cikin nutsatstsan takunshi yake saukowa daga upstairs,ƙamshinsa kuwa tuni ya cike ko ina da ko ina tare da bin kofofin hancin masu gida da yan aiki,take kuwa kowa ya shaida fitowar sa,tuni yan aikin da suke kaikawo a main luxury falon suka fara kai gaisuwa kaina kasa cike da wani irin girmamawa,saboda babu wanda yake iya hada ido da abm,tnk yake fada kawai shima a saman labbansa tare da dan daga hannunshi,basu damu da hakan ba saboda sun saba sun san dabi unshi kuma su wannan ba komai ba ne a wajensu tunda ya kasance me kyautata musu da kare hakkunansu tun baya kasar.

Karasowa yayi inda suke Dukansu akan dinning kowa yana ƙoƙarin sakawa cikinsa wani abu dan dukansu fita zasu yi,gaisuwa yayi musu tare da zama yana dan kallon saman dinning ɗin ko zai ga abinda zai iya ci,fahimtar hakan yasa Ammi dinshi da kanta ta haɗa masa tea tare da chimps kadan sai sos da agada,tnk ya fada a hankali tare da fara ci.

bai wani ci da yawa ba ya dai dan sha tea din sosai ya fara ƙoƙarin mikewa yana goge bakinshi da tissue,dubansa dady yayi yana cewa son ya batun sakatariya ne? Shuru yayi bai tanka ba,dadyn bai damu ba ya ci gaba da cewa munyi magana da jafar(pa dinsa) ya ce har yanzu baka bashi damar kawo kowa ba ko? Wayoyinsa ya kwashe ba tare da ya tanka dinba, har dadyn ya fidda ran samun amsarsa sai kuma daga can yaji yana cewa am talk t u letter,daga haka ya mikawa jafar kayan hannunsa da shigowarsa kenan cikin dan hanzari yana gaida me gidannasa da kuma su dadyn, ficewa yayi fuskar nan a kimtse kai baka ce ya taba sanin wani abu murmushi ba bare kuma a kai ga dariya,da sauri jafar ya bi bayansa shima yana daidaita nutsuwarsa.

Suna fita tuni an fito da motar da zasu fita da ita sale direba yana tsaye yana jiran ubangidannasa,da sauri duka securitys dake ta wajen suka fara miko gaisuwa tare da yan aiki ta bangaren kula da tsaftace gidan,hannu kawai ya daga musu jafar yayi saurin buɗe masa mota ya shige yana bar musu mayen ƙamshinsa.

Kai tsaye Company shinkafa suka wuce,tunda suka shiga motar jafar ya fara amsa wayoyi wanda kuma sai shi din dole yake yin maganar yana gabatar da komai cikin natsuwa da kwarewa ta fannoni da dama.

Motocin abm na kawo kai, Zahra ma na kawo kai bakin bulding din ita da su hafsa,da sauri security suka bude ƙatuwar gate din suna salut nasa kamar wani soja.

Nadiya ce ta yi saurin riƙo hannun Zahra da ke kokarin cusa kai dan shiga ta hanyar da su abm zasu shige da motocinsu tana cewa dan Allah Zahra ki bari kar ki jawo mana kora daga Companyn nan me yasa ba zaki bari su wuce ba? Kuma ma ai mu ba nan ce hanyarmu ba tunda da ƙafa zamu shiga", sai da nadiya ta gama maganarta sannan ta kula da mugun kallon da Zahra ke watsa mata tamkar idanunta zasu fado, sosai fushinta ya baiyana dan duk sanda zata hadu da abm sai wannan fushin ya taso wanda ita da kanta take mamakin karuwarshi duk sakanni", kafin ta yi magana nadiya tayi saurin cewa Allah ya baki hakuri muje kar lokaci ya shige", ba dan taso ba sai dan wannan din yana daga cikin lagonta da kawayennata suka sani, wanda muddin kayi mata abu ka bata hakuri shike nan in dai baiyi tsananin da zata kasa hakurin ba.

Jan hannunta nadiyar tayi tana murmushi da cewa sorry my ZAHRA,dole Zahran ta hadiye abinda taso zazzage mata ta bisu suka shige tana maida kallon harararta kan securitys din jiya.....

...............a hankali matashiyar budurwar da bazata wuce shekara ashirin da bakwai ba take saukowa daga matakalar jirgin, jikinta sanye da riga da wando masu fadi kirar balansino,fuskarta sanye da sunglass ɓaki da ya kusa cinye rabin fuskarta,kallo daya zaka yi mata kasan ita din cikakkiyar beyerabiya ce kuma yar gayu me ji da kwalisa.

Kai tsaye motar da tazo daukarta ta nufa saboda ta gane drevan gidan kawunnata,bude mata kofa ta yi ta shige tana amsa gaisuwarsa a ɗage tana wani shan ƙamshi tamkar yar gidan shugaban ƙasa.

Kai tsaye gidan ya nufa da ita, koda suka zo sai da ya fito ya bude mata kofar tare da ɗaukar trolly dinta,tana tafe cikin gwalli yana biye da ita har cikin falon bayan sun bude, suna shiga ya aje mata kayanta ya juya ragowar ya barwa yan aikin cikin gidan.

Jan me aikinsu ce ta fito tana mata sannu da zuwa saboda dama an san da zuwanta,(siyam kenan ya ga yemi ƙarwar dady)kai tsaye dakin da aka gyara mata suka nufa dan ta kimtsa,itama tasan babu kowa gidan dan sunyi waya da Amira.

..........da wuri Zahra ta bar gurin aikin acewarta tunda aka yi mata dolen zuwa da wuri to wlh bazata bari a tashi ba,koda su nadiya suka so hanata sam ƙi tayi sai ma cewa da tayi ku kun san ba dan ina son cimma buri na ba da babu abinda zaisa naji tsoran makara dan kar a koreni,ta fada tana tunawa da abinda ya faru jiyan a ofishinsa,murguɗa bakinta tayi tare da fadin dan iska kawai", zato ido hafsa da ke da tsananin ji tayi tana cewa Zahra tafi gidan kawai sai Allah ya kaimu goben", ko baki fada ba dama munafuka ta fada tana fita fuuu daga wajen.

........yau dai tsaf da dawo ta samu gidan,duk da cewa basa nan duka kowacce ta nufi wajen neman kudinta kunsan yarbawa ba daga nan ba.

To amma tasan da wuya idan ba mama ce ta share gidan ba, da sallama abakinta ta shiga dakin nasu, mama ta samu akan sallaya ta idar da sallar la asar,mama sannu ta fada tana fita dan dauro alwala.

Tana idar da Sallah mama ta bata abinci tana ta lallabata ganin yau din babu wani abu da ta yi dan ko kararta yau babu wanda ya kawo,har da yi mata kiran yayanta suka sha hirarsu, dan haka har wajen biyar suna tare da mama tana taya ta ayyuka da girki,mama cewa take Zahra ALLAH yasa ki dore da haka Allah ya muku albarka ya baku ingantacciyar rayuwa ", Amin mama ta fada ranta fal farinciki itama tana ji a ranta dama ta dore din kodan farincikin iyayenta,to amma ita da kanta bata so ta canja a yanzu har sai ta dauki fansar cin mutuncin da abm ya yi mata,daga nan sai ta shiryu kawai ta koma salaha ba sawa ba fitarwa,ko kwana ɗaya take yi a sati bata tankawa kowa ba ai ta rage....

Iyoka ce ta fara dawowa gidan cikin karadi da wake wakensu marasa kan gado,ganin Zahra da ta yi a kofar dakinta yasa taja wani dogon burki tana hadiye miyau tare da ragowar wakarta......

Fatima y Adam ✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*