YAR GIDAN YARBAWA

PG 9

by @zahrawriter12

............saboda tsabar zakuwa yau ko komawa baccin safe bata yi ba,wanka ta fara yi bayan ta yiwa mama sharar daki ta gyara dakin tsaf,Abbanta kansa sai da ya dubeta ya ce", Zahran Abba yau sammakon na miye haka? Dariya tayi cikin basarwa ta ce", Abba yau babu bacci a idona gashi kuma zan fita Company da wuri saboda ansa mana dokar makara", jinjina kai yayi kawai yana ci gaba da jan tasbinsa.

Ko da ta fito tsakar gida bata kula kowa ba,ta fara tattare wajen cikin kankanin lokaci ta share gidan fes kamar bashi ba.

Duk wacce ta fito taga Zahra tana shara sai kiga ta fara yan soshe_soshe tare da muzururai dan kar Zahran ta ce zata yi magana,ganin bata kula su ba yasa suka fara kokarin ficewa harkokinsu,iyoka kuwa yau hankalinta kwance tasan bata da wata damuwa tunda Zahra ta zama kawarta,ko da ta fito gaisawa su kayi da zahran baki washe yawa gonar auduga.

Adebayo ne ya fito daga dakin matarsa lola yana faman hura hanci da raba idanun inda zai hango Zahran saboda jiyo muryarta da yayi,dama so yake kawai yaga Zahran dan tunda abinnan ya faru basu hadu ba, kullum kaucewa haduwa da ita yake saboda yasan tijarar Zahra tsaf zata fallasashi a gaban lola babu ruwanta,to yau dinma kasa jurewa yayi dan kuwa yana matukar son Zahra yaron yayi sosai ko ina yaji gashi dai yaro be gama hankali ba kuma ba a gama mishi halitta ba amma se shegen kyau kai yaron yayi kyawu,abinda kullum yake fada a ransa kenan yana fatan ya samu hanyar ko tabata ne ko zai samu saukin abinda yake ji akanta.

Cikin washe haƙora ya ce", Zahla Good morning ka tashi lafiya? Harara Zahra ta watsa masa kafin cikin ƙunkuni ta ce", shegu yan kauye kullum cikin ɓatawa mutum suna suke daga bata suna sai maida ka namiji," ba tare da ta kula shi ba ta cigaba da ka kawonta cikin sauri dan tayi ta gama ta wuce duk da tasan cewa yau zata iya zuwa a farkon zuwa.

Binta yayi da kallon maita har dasu lashe lebe wanda hakan ya faru akan idanun Zahra ,cak ta tsaya daga kokarin shiga dakinsu da take yi saboda zuwan wani tunani ranta,juyowa ta yi da murmushi akan kyakkyawar fuskarta har kumatunta na lobawa,cikin Muryar da bata taba yi musu magana da ita ba ta ce", ayya Ade Ashe Dani kake ai ban kula ba saboda yau din na tashi ina sauri ina fatan ka tashi lfy? Dake ba hankali ko tsayawa wani tunani akan canjin Zahran lokaci daya baiyi ba ya wani washe manyan hakoransa idanunsa kamar zasu fado saboda tsabar kureta da kallo ya ce", ey Zahla dakai nake dama ina ta so na baka hakuri akan abinda lola yayi maka so sorry kaji", tsinanne Zahra ta fada can ƙasan makoshinta,kafin ta kuma sakin murmushi ta ce", babu komai tuni komai ya wuce,har tayi kamar zata shige dakin sai dai ta fasa ta juya inda yake ta kalleshi sannan ta kalli ko ina duk wasu sun fice wasu kuma suna dakunansu kamar su iyoka da ke dakin tun dazu tana dakawa Zahra kararanta.

Cikin sakin fuska Zahra ta ce", ba fita zaka yi ba? Da sauri ya amsa ey da fita zanyi ko kana da wani abu ne? Dan tabe baki Zahra ta yi tare da cewa yanzu kai Ade a haka zanso ka kullum kana tsamin dauda ko wanka nifa ban taba gani kayi ba tun da NAZO gidannan", sosa keya ya shiga yi cikin dan borin kunya sannan ya ce ", ina yi wani lokaci amma idan kana so zan dinga yi", a'a wlh sai dai kayi yanzu ina kallo kafin na fita bari ma kaga da kaina zan kai maka ruwan wankan", karasa maganar kasa_kasa tana dan kallon kofar dakinsu.

Bata jira cewarsa ba ta dauko bokitin lola dake kofar dakinta ta zuba ruwa, sannan ta dubesa ta ce, to kaje mana ka yi shirin wankan kafin ka fito na kai maka ruwan", cikin rawar jiki kamar wani raƙumi da akala haka ya fada dakinsu zuciyarsa kamar gonar auduga yana cewa yo addu'a na ya amsu Zahla ya kulani yau dakwai shan Shagali lokacin da ya shiga daki har rawa yayi kasancewar lola tuni ta fice sana Ar ta dan yanzu ta kuma yin sammako akan baya saboda abinda Zahra ta yi mata.

Zahra na ganin shigarsa dakin tayi saurin fadawa dakin iyoka wadda ta kammala daka karara a turmin karfe hannayenta duk ta nadesu da Safar leda,yauwa iyoka ke dai Allah ya miki albarka daga yau kin zama kawata babu ke babu shan wahala bani kiga zan fara ta kan me rabo yanzu,dan wlh sai nayi maganin Ade hege Mayan mata," cikin washe bakin farinciki iyoka ta mika mata bayan ta kulle mata a leda tana cewa shike na gode Zahra in sha Allah as from to day we are friends,Kar ki damu Zahra ta fada tana ficewa daga dakin.

Dai_dai lokacin Ade ya fito da soso da sabulu sai zani rataye a wuyansa,cikin sauri Zahra ta ce", oh sorry bari na kai maka, daga haka ta sunkuci boket din ta kai masa bandakin.

Fitowa ta yi da murmushi akan fuskarta tana cewa kayi wanka idan na dawo daga aiki zamu yi magana kaji my love", ai tamkar Ade zai zare saboda jin dadin wannan kalma ta Zahra dan haka baisan ma sanda ya fada banɗakin ba dan kawai yayi mugun wankan da Zahra zata yaba tasan cewa shima fa yana da kyawunnan rashin wanka ne kawai.

Yana shigewa Zahra ta kyalkyale da dariya iyoka na taya ta, matsawa ta yi kusa da iyoka ta ce", kiyi min video da wayarki dan nasan farkon wasan sai yafi bada show,tafawa su kayi a tare,daidai lokacin mama ta kwalo mata kira, Zahra wai kin fasa fita ne me kike yi ne haka har yanzu? Gani nan mama na gama cikina ne ya dan murda shine na shiga bandaki", hijab dinta kawai ta zura ta yiwa mama sallama tunda dama ta gama komai ta tsaya daukar magana.

Su kansu su hafsa sunyi mamakin rashin jiranta da basu yi ba sai ita ce ma ta dan jirasu tana yi tana mitar su yi sauri kar su makara sosai abin ya basu mamaki dake aminai na amana duka sun san halin kawarsu dan haka take suka sa alamar tambaya akan Zahran", basu dai ce mata komai ba suka dau hanya, yau dan fadan da suka saba duk zahra bata kula anyi ba,hasalima shuru tayi tana tunanin hanyar da zata bi dan sawa AB kararan, wannan dalilinne ya kuma saka zuxiyarsu cikin zargin cewa lallai zahran da wani abu da take shiryawa....

................yau ko karin bai saurara ba saboda sauri yake yana da bakin da zai gana dasu,dan haka yana saukowa jafar ya karbe kayan hannunshi, shi kuma ya ɗan karasa kusa da Ammi ya bata pic a kumatu tare da gaida ta amsawa ta yi tana mai shafa sumarshi ta asalin Larabawa ta sa mishi albarka,Dad dinma dan rungume shi yana mishi Barka da safiya duk da cewa sun hade da asuba,yaya AB barka da safiya Amira ta fada cikin nuna irin girman da yake dashi a wajensu,cikin karamin sauti ya amsa tare da dan shafa kanta zai juya kenan ya kuma jin wata gaisuwar da muryar da ba zai iya tantance ta waye ba,amsawa yayi da daga hannu tare da sautin tnk din da ya fito daga saman labbansa,kai tsaye ya fice jafar na biye da shi kamar jela.

Yana gab da fita dady ya daga murya yana cewa siyam ce take gaidaka yar uwarka, ya kamata idan ka samu lokaci ka tsaya ku gaisa saboda ita nake so kasa as a sectary ", daidai yana ficewa daga falon cikin karamin sautinsa da idan ba karantar yanayinsa na magana ka yi ba to tabbas ba zaka gane abinda ya fada ba, ya ce letter", dad dinne kawai ya gane tunda shine yake jiran amsar tasa, letter letter dai ko da yaushe idan aka yi masa magana letter, in dai har ba shi ya bukaci tattaunawa da kai ba,dad ya shiga mita bayan fitar AB ɗin.

Ita ko siyam da kallon kauna da sha'awa ta bi AB, itama ko Ab me aurenta ba in dai zai yadda sukasanxe tare to bata da damuwa akan auren tunda tasan ko bai aurenta in dai suka zama daya zata iya samun baby daga gareshi, wannan tunanin da ta yi yasa ta lumshe idanunta tana emagin ace suna tare da AB...dad ne ya katse tunaninta da cewa karki damu siyam AB sai an bishi a hankali san ba a yi masa garaje ko kuma kutse yana da murdaddan ra ayi da babu me sashi abinda be niya ba dole sai ta lallami dan haka kar ki damu zamu zauna dashi", jinjina kai tayi cikin da gamsuwa dan tasan ko da yanayin AB yana da biyayya matuka da kuma so da yakewa iyayennasa,dan haka zata kwantar da hankalinta abi komai a sannu.....

....... security s ma abokan fadanta yau bata kulasu ba salin alin ta wuce babu harara babu gunguni, kai tsaye bangarensu suka nufa,ga mamakinsu Hafsah sai kawai suka ga yau din Zahra tasa hannu ta fara aiki a maimakon zaman taya su hira da take yi,duk kallonta suka tsaya suna yi ko wacce ta kasa boye mamakinta.

Wani uban tsaki Zahra taja tana watsa musu harara bakinta cike da masifar da ta adana ta ce", ku nifa bana son gulma da munafunci duk kun wani bi kun dame Ni da kallo sai kace wadda baku taɓa gani ba,da wannan abun da kuke ai Gara ku fadi abinda ke ranku yan renin hankali kawai,"ta karasa fada da murguɗa ƙaramin bakinta,Hafsah ce ta ce", ai kema kin san akwai abinda yake ran namu shi yasa kika kasa shuru dan ke duk randa aka ga kin zama salaha to akwai abinda ke ranki kamar dai yau din da kika a ri halin da ba naki ba," zazzaro manyan idanunta ta yi cike da son yin masifa sai dai kuma ta wani bangaren tana tausar zuciyarta saboda a ankare take da lokacin zuwan AB idan kuma ta biye musu to tabbas zaizo ya wuce ba tare da ta cimma kudurinta ba,dan haka sai kawai ta hadiyi yawun masifarta ta maida shi cikinta ta tsaya musu a iya hararar da tamkar zata fado da bakar kwayar idonta.

Tsaki tayi ta bar gurin tana cewa idan ku Mayu ne sai kuci kanku", da kallo suka bita suna kara tabbatar da cewa zame musu ta yi dan ta samu damar aiwatar da abinda ta shirya duk da cewa basu san ko me ye ba.

.....ajiyar zuciya ta sauke har da su murmushi lokacin da taga motocinsw masu lafiya da koshi sun fara fakawa a inda suka saba tsayawa......hannunta ta kuma boyewa da yake saye cikin safar hannu ta leda wadda take har guda uku uku dan bawa kanta kariya daga samun nata rabon kaikayin....

.........tun yana wanka ya fara jin wani tsuttsut,tun yana yi da nishadi har ya fara kai hannu dan sosawa,wata irin zabura Ade yayi daga tsugunon da yayi tare da sheka ruwan duka ajikinsa waiko zasu bashi nutsuwa daga mugun kaikayin da ya fara neman zautasa.......🤣

Dan Allah yar gidan yarbawa ki rufa mana asiri kar ki sawa AB karara🤣

Idan ba haka ba kuwa Ni nayi nan🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️

Ya kuka Zahra a bayan kanta.......

Ina jiran ruwan comments kar ku share Ni dan Allah in dai kuna son typing a kan lokaci...✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*