Pg 8
..........dariya ta bawa Zahra dan haka ta dan murmusa tana cewa iyoka ƙaraso mana ya kika tsaya? Oh Zahla yaro me kirki kana shan iska ne? Ey haɗe da jiranki ba", Zahra ta bata amsa tana satar kallon dakinsu,cikin son ɓoye tsoranta ta ce", oh Zahla me kuma nayi yau Allah yasa de lafiya ne? kwantar da hankali iyoka babu abinda ya faru kawai tambayarki zanyi dan Allah ", to ina jin ka,iyoka ta fada tana dan matsawa kusa da Zahran,sai da Zahra ta tabbatar da cewa mama bazata fito yanzu ba sannan ta yi kasa da murya cikin raɗa ta ce", ina zan samu karara ko wani abu makamancin sa? Zaro ido iyoka ta yi tana cewa Zahla me zaka yi da kalala yana sa jiki ciwo da kaikayi fa zaka shiga damuwa idan ka taba kalala", na sani iyoka taimako na zaki yi idan kin san inda zan samu ki samo min Ni kuma na miki alkawarin dena yi miki abinda nake muku in sha Allah", kai haba dai Zahla ka tabbata ka yi alkawali? Ey nayi Zahra ta fada cikin sauri, Tom shike nan gobe idan na fita zan shiga ta wajen gonar zawaje za a samu a ta can," haba iyoka kizo muje yanzu mana ai gobe nake so nayi amfani dashi kinga kuma da wuri nake fita," Tom bari na aje kaya sai na fito muje", Tom ki yi sauri bana so Abba ya dawo bana nan", to bari na fito yanzu,iyoka ta fada tana shigewa dakinta.
Ajiyar zuciya Zahra ta sauke sannan ta nufi dakinsu cikin natsuwa dan tasan yau din tuni ta kame zuciyar mama dan haka bazata sha wahalar barinta ta fita ba.
Dan Allah mama zanje gidansu nadiya yanzu zan dawo", dagowa mama tayi daga kan hisnul Muslim din da take karantawa ta ce," haba Zahra sai gab da magriba zaki fita bayan kin san abbanki yana hanya", maraice fuska ta yi tana cewa Allah mama BAZAN dade ba idan ma ya dawo sai kice aikana kika yi, au fadan kike so ya dawo kaina ke nan tunda kinsa ai ya hanani aikanki da wannan lokaci, shuru Zahra tayi kafin ta juya dan barin dakin cikin sanyin jiki da karaya gwanin tausayi,aiko shirinnata ya yi dan kuwa kafin ta kai ga fita mama ta kirata cikin sanyin murya,juyowa Zahran ta yi tana amsawa a sanyaye,me zaki yi a gidansu nadiya? Mama littafin da muke karatun jarrabawa zan karbo saboda mun kusa komawa gashi ban karanta komai ba,kije amma kar ki dade har Abbanki ya dawo, kar ki damu mama zan dawo da wuri" daga haka ta fita suka haɗe da iyoka.
..........Amira ce ta fara dawowa daga school tayi murna sosai da ganin siyam,duk da cewa ita siyam ba wani sosai take da sakewa ba so ba wani shakuwa ne tsakaninsu da Amiran ba,ina broth AB abinda ta ke ta tambayar amira kenan,dariya Amira ta yi tana cewa kema kinsan ba zaki samu yaya AB a daidai wannan lokacin ba,so sai kin jira zuwa anjima idan baki da saurin bacci,numfashi ta danja kafin ta ce shike nan ba wani abun damuwa bane tunda aiki zan fara a kusa dashi me bi ma mu dinga tafiya tare", dariya maganar ta bawa Amira dan hanka ta dan dara sannan ta ce", lallai siyam kin manta w yaya AB amma mebi idan kuka hadu zaki tuna waye shi,dan harararta siyam din ta yi tare da cewa kefa Amira tuni na fahimci bakya bayan son da nakewa yaya AB ", zaro ido amira ta yi tana cewa haka kika fahimta? Siyam ta fada cikin dan tunzura,a'a siyam kar ki min gurguwar fahimta kawai dai Ni yar babu ruwana duk inda ta kwana sha ce amma ba wai bana sonki da yaya AB ba ne", umh ta fada tana ci gaba da latsa wayarta,ganin haka yasa itama Amiran ta kama kanta ta shiga Tata sabgar.
......…...suna fita suka tari nafef tare da gaya misa inda zasu,basu yi wata tafiya me yawa ba suka ƙaraso inda zasu gangara ya kaisu gonar,biyansa kudinsa Zahra tayi sannan suka wuce.
Sai da suka dan sha wahala kafin suka sameshi, sai kuma wajen cira anan ake yinta,cogewa Zahra ta yi ta ce da iyoka ta ciro mata,cikin tsoro iyoka ta kalleta tare da marairaice fuska tana cewa haba Zahla kai ka ce kayi alkawarin dena yin komi a kaina", harara Zahra ta zabga mata tare da murguɗa baki ta ce", ey ai cewa nayi idan kin samo min zan daga miki kafa dan haka kicika aikinki idan ba haka ba wlh zan diba kuma na zuba miki shi a ruwan wanka kinga kin gudu baki tsira ba kenan",
Aiko cikin wani irin rawar jiki iyoka ta yi kan karara har ma ta manta idan ta taɓa zai iya mata kaikayi saboda gani take Gara kaikayin karara akan muguntar zahra,tana dab da tabawa Zahra ta dakatar da ita da mika mata ledar da ta zaro a jikinta,tana cewa", karbi dai ba dan halinki ba kisa ledar ki debo, iyoka har da rissinawa tana fadin na gode yaron kirki", dariya Zahra ta yi har da sunkuyawa,wai iyoka a ina kika samo wannan yaron kirkin? To wlh Gara ma ki sani wannan yaron kirkin da kike fada min zai iya jawo miki matsala dan na tabbatar a RANKI zagina kike wai Ni zaki yaudara ko? Da sauri iyoka ta girgiza kai tana mai fara tsigar karara dan bata son maganar tayi tsawon da zata sha wahala a wajen Zahra.
Cikin sauri ta gama tsinka saboda a zalzalar Zahra akan tayi sauri kar abbanta ya dawo,hanya suka dauka suka koma gida zuciyar Zahra fes ta samu hanyar ramuwar gayya.
Lokacin da suka ƙaraso gidan Zahra ta kalli iyoka ta ce", ki tafi dashi ki boye min da safe zan karba,sannan ki bari na fara shiga da wasu yan mintinan sai ki shigo", Tom Zahra karka damu ta fada cikin gurbatacciyar Hausarta,ba tare da Zahran ta kuma tanka mata ba ta yi saurin shiga gidan cikin dan fargabar ko abban ya dawo.
Dubanta mama ta yi cikin dan fada tana cewa Zahra me yasa bakya jin magana ne? Yanzu da Abbanki ya shigo me kike so na ce masa? Dan sosa keyarta ta yi irin na rashin gaskiyar nan sannan cikin marairaita ta ce", kiyi hakuri mama littafin ne muka yi ta nema dakyar aka ganshi,ta karasa fada tana fiddo littafin da ta tsaya gidansu nadiya ta karba dan tasan dole mama zata nemi ganin littafin,aiko abinda ta sani ne dan mama cewa ta yi muga littafin", cikin sauri ta mika mata tana dan tura baki halin nata na sabo", wuce kije kiyi sallah mama ta fada tana zabga mata harara,kamar jira take ta ta fita da gudu kamar ance a kamata za a bugeta.......
.............yana tashi kai tsaye gida suka wuce.
Sai da jafar ya shigar masa da wayoyinsa da su laptom tare da sauran wasu takardun ,sannan ya fito,shi kuwa kai tsaye wucewa yayi ba tare da ya tsaya kallon mutanen dake zaune a falon ba bare har ya tantance fuskokinsu,suma su dadin hannu kawai ya daga musu ya wucewarsa,bai barwa hancinansu komai ba sai mayataccen kamshinsa.
da wani Irin mayataccen kallo siyam ta bishi wadda ke zaune zaman jiran shigowarsa,wani irin miyau ta hadiya me kauri tare da lumshe idanunta a dai_dai lokacin da taga kulewar sassaitan takunsa me cike da nutsuwar da ke tafe da gajiyar da yayi.
Babu shiri Amira ta mike ta bar falon saboda dariyar dake neman kufce mata,tana shiga dakinta ta saki abarta tayita son ranta,umm in dai yaya AB ne zaki sha haushi kina ga ko su dady hannu kawai ya daga musu ba tare da ya kalli kowa ba bare kuma ke da ba zai iya tantance kamanninki ba.
Dad me ya ce da siyam ta wuce take ta huta shima AB din gajiya ce tasa ya kasa tsayawa su gaisa,jiki a sanyaye ta bar falon tana jin kunar son yaya AB din kamar zai kone komai na zuciyarta.
Sabanin jiya yau da ya gama shirin bacci yayi sallolinsa, sai bai kwanta ba ya aiki ya shiga yi a computer,bashi ya samu runtsawa ba sai wajen wajen uku na dare.
.....Zahra kuwa ji take kamar ta janyo safiya saboda tsabar yadda ta kagu taje ta aiwatar da muguntar da ta shiryawa AB........
Haba zahranmu ya da haka me kike nufi ne😄
Team AB where are you?
Kuzo ku ceci yaya AB dinku Kar Zahra tai haukatasa🤣
Nayi nan mu hadu a sashen comments
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*