Pg11
.......matsowa ya cigaba da yi idanunsa akanta,yana kallon karfin halin dake tattare da ita har yanzu.
Murguɗa ƙaramin bakinta tayi tana mai kifkifta idanuta,shi kuma bai daina biyota ba har sai da ta dangane da bangon office din,juyawa tayi taga babu inda yayi saura da zata matsa hakan yasa ta dan kalleshi cikin son ɓoye tsoronta ta ce", wai me hakan kake yi? Nifa musulma ce kuma yar gidan tarbiya ba wai yar iska ba dan haka ka bani hanya na tafi", babu inda zaki sai kin ciremin abinda kika shafa min a jikina,ya fada yana matso da fuskarsa daf da tata,kafin Zahra tayi wani yunkuri tuni ya hade fatar jikinsa da tata ya cusa fuskarsa cikin wuyanta yana murzawa saboda bilhakki neman hanyar da zai samu sassauci kawai yake yi.
Sosai jikin Zahra ya dauki rawa dan kuwa wagga mutum da gaske yake tare zasu shanye kaikayinnan ga kuma iskancin da yake mata,to wai shi wannan anya kuwa Musulmi ne? tayiwa kanta tambayar da babu me bata amsa,yadda yake murza jikinsa a nata jikinne yasa ta dawowa hayyacinta lokaci daya ta fara jin kaikayin a saman wuyanta inda fatarta take a bude.
Bata san lokacin da ta fara mintsininsa ba saboda yadda yabi ya kanainayeta ko kwakkwaran motsi ta kasa,sai dai mintsinin ma ko ajikinsa bai rabu da ita ba sai da ya tabbatar ya samu nutsuwa daga kaikayin da ya addabi wasu bangaren jikinsa.
Yana sakinta ya taka cikin nutsuwarsa ya shige bathroom ba tare da ya kuma kallon inda take ba,kuka Zahra tasa tare da fadin Allah ya isa na ban yafe ba wuta balbal ta karasa fada tana mai barin office din,a ta gefe daya kuma tana jin kamar tayi ta tsalle saboda kaikayin da ya fara addabarta.
A yanzun ma taci sa a babu wanda ta hadu dashi har ta bar Company gaba daya tana tafe tana kuka tare da sosa duk inda ta ji yana mata kaikayi.
Lokacin da ta ƙaraso gida tuni ta yi kokarin saita kanta dan kar wani ya ganta ya yi mata dariya, Allah ya isa kuwa tayi wa AB tafi cikin kwando,tana shiga dakinsu ta wuce kai tsaye tare da fara kokarin cire rigarta da hijab dinta da duk ya cukukuye saboda maguzar data sha a hannun oga Ab.dubanta mama ta yi tana mai aje kayan da take ninkewa ta ce", ya dai zahra naga kamar kuka kikai? Ina Zahra babu amsa sai susa da ta cigaba da yi tare da ruwan hawayen da da suna karewa da yanzun nata sun kare tas,ganin yadda take susa yasa mama ta rafka salati tana cewa yanzu dama Zahra kece sanadin haukar da Ade ya dinga yi a cikin gidannan gwanin tausayi kamar zai cire fatar jikinsa ya huta?Ni dai mama ki sosa min dan Allah", naki na sosa mikin kaji min muguwar yarinya wai shin ma a ina kika samo karara dan nasan shi kadai ne zai iya wannan aikin? Shuru Zahra tayi babu amsa dan itama yanzu shirin fara taka tata rawar take yi,mugu kawai Ni da naje dan ganin rawar shokin da zai debo sai Ni na bige da diba Allah kuwa BAZAN bar mutumin nan ba", zantukan da Zahra take ta faman yi kenan cikin ƙunkuni da susar jiki.
Abun na Zahra kamar har da langwai da sangarta dan kuwa ihu ta dinga yi wa mama tare da sata aikin susa har da inda babu kaikayin,daga karshe dai man kadanya mama ta murza mata tana ci gaba da lailaya mata farar fatar jikinta da kamar ba a gidan marasa shi take rayuwa ba.
......Ade kuwa yana can daki yana jinyar kansa dan kuwa shi nasa yafi na kowa tunda shi sosai yayi wanka dashi,yayi rawar sa da baturiya abinsa dan haka ya fi kowa shan wahala, sai da ya fara samun nutsuwa sannan ya fara tunanin ta yadda akayi ya samu kaikayi daga shiga wanka,se yanzu hankali suka zo masa har ya fara tunanin yadda akayi Zahra ta kulashi, take komai da ya faru ya dawo masa cikin kansa,babu kokonto ya tabbatar wa da kansa Zahra ce sanadi,ihu Zahla ka dauko match walle ba zan barka ba yaro mara kirki, ya fada yana zabura daga kwancen da yake,lola dake kusa dashi ta tafa hannuwa cikin karadinta ta ce", Allah ya toneka Ade miye ne hadinka da wancan sinanne yaro? Zazzaro ido ya shiga yi dan baisan maganar ta fito fili ba cikin borin kunya ya maida fadan kan lola nan fa aka fara tashin hankali,tun suna yi a daki har suka fito waje.
A lokacin tuni Zahra baccin wahala ya dauketa dan haka sam bata san wainar da ake toyawa ba har suka yi Bala in su suka gama.
.........dake yau din ba a daidai yake ba bai ma bi ta hanyar main falo ba ta can asalin kofar da zata kaishi har upstairs dinsa ya bi dan haka babu wanda yasan ya dawo,jafar yana aje masa tarkacensa yayi masa goodnight ya fice,dan ko shi jafar din da yake tare da shi bai fuskanci komai a tare da ogannasa ba,saboda babu wani sauyi da ya bayyana a dukkan motsinsa da asalinsa ,ko a dazun ma baza ka iya fuskantar komai ba baya ga idanunsa da ba kowa ne yake iya kallon cikinsu ba.
Yana gab da shigewa room dinsa yaji an rungumeshi ta baya,kafin ya yi wani motsi yaji saukar Muryarta a kumnensa,haba broth AB saboda Kai fa na zo gidan nan amma tun zuwa na ka gagara bani lokaci ko na gaisawa ne pls ka saurareni ko sau daya ne na taya ka bacci yau kaji broth AB", jin shuru bai motsa ba kuma bai tanka mata ba yasa ta dago kanta ta maida kan kyakkyawar fuskarsa da lokaci daya ta koma wani irin da kalar da tasa ta sakinsa babu shiri har tana dan ja da baya,babu magana iya gargadin da ta gani a kan fuskarsa ma ka dai ya wadatar,rsmatsa ta ya yi ya wuce ba tare da taji kalma daya daga bakinsa ba,kanbu anya zan iya shawo kan wannan gayen kuwa? Kai anya ma kuwa yaya AB yana da lafiya?
Babu me bata amsa dan haka taja jikinta da ya yi sanyi kalau ta fita, amma ba wai dan tana ji ta karaya ba, kai ita yanzun ne ma take jin sonsa kamar zai kasheta dan haka sai inda karfinta ya kare da zarar ta hau matsayin sectary dinsa an wuce gun.
Kai tsaye bath ya shige ya sakarwa kansa shaya,ya jima sosai kafin ya fito jikinsa daure da karamin towel da bai gama zama jikinsa ba, cikin nutsuwarsa gama shirinsa,wajen sallarsa ta nufa, bai tashi a gun ba yauma sai wajen biyu saura daga nan ya haye saman tattausar gadonsa ya rufe jikinsa da gaba daya tare da lumshe idanunsa yana son kawar da duk wani tunanin abinda ya faru yau din musamman akan aljanar yarinyar nan da ko sunanta bai sani ba...
Washe gari da safe Zahra bata yi kokarin shirin fita ba, dan sam yau bata da niyar fita acewarta sai ta samo sabuwar hanyar ramuwar ta ga mugun ogansu,bata fito da wuri ba sai wajen sha daya, kai tsaye dakin iyoka ta nufa dan tasan ita bata fita da wuri,daga bakin kofar ta tsaya ta yi mata magana,sai ga iyoka ta fito rike da wayarta tana faman washe baki,Zahra bata ce komai ba ta karba wayar ta fara kallon tun daga lokacin da Ade ya fito daga bandaki yana ihu har zuwa tsalle da rawar asosa da ya yi,tun zahra na rike dariyarta har ta kai ga ta fara yinta har dasu dafe ciki,cikin dariya ta ce", iyoka ashe kema yar hannu ce wallahi ban taba yin kawance da yarbawa ba amma ke kam kin zama ta hannun damana na karya record a kanki,dan zamu je dake daga gani,irin wannan dauka me kyau haka", aiko take iyoka ta fara juyi da rawarsu ta YARBAWA tana wata waka saboda jin dadin Zahra ta yabe ta ta fita daga cikin masu zaman ukuba a gidan yarbawa.
Ganin Ade kawai su kayi akansu yana wani irin huci tamkar wani tsohon kumurci,cikin sauri Zahra taja da baya tana gimtse dariyarta saboda yanzu kallonsa ma kadai dariya yake bata saboda tuna rawar asosa dinsa,harara ya zabgawa iyoka kafin ya maida kallonsa kan Zahra ta nunata da yatsa cikin kwadayinta da tsanarta da suka mamayeshi ya ce", wallahi baka ci banza ba walle sai naci mutunci naka ba dai Ni kayiwa wannan sin mutunsi ba,to ka kiyaye hadewar mu na dauki alkawali", daga haka ya barsu a wajen ya fice zuciyarsa cike da kudirin daukar fansa,dan jim zahra ta yi kamar abinda ya fada din zai dameta sai kuma ta fuske tare da mikawa iyoka wayarta tana cewa bari na shirya nazo na raka ki ko bakya so? Da sauri iyoka ta ce", ina so mana Zahra yaron kirki ya zama abokina ", .......
..........mamma kinga abinda broth AB ya yi min dama har yanzu yana nan da wannan halin nasa? Sorry mana siyam me yasa baki da hakuri ne dole sai ka yi hakuri da dan uwanka sannan buri naka ya cika Nima buri nawa ya cika,ki basa a hankali Ni kuma zanje wajen me sasuba zai yi min aiki akansa dole ne ya dawo hannunka ka dinga juyasa son ranka kaji ka share hawayenka", a hankali siyam ta saki murmushi kamar Mamman nata na ganinta ta ce", yauwa mamma shi yasa mike sonki da yawa ina nan ina jira dama abinda nake so kice kenan kinsan aikin masasubi yana de kyau tunda ya yi akan fafa ", haka ne siyam in dai ina da numfashi baza kayi kukan rashin wani abu ba", na gode mamma ,daga haka ta kashe wayar tana mai samun nutsuwa akan ci gaba da yakin neman soyayyar AB.......
A can kuwa Mamman siyam tana sauke wayar daga kunnenta ta mike ba tare da ko mayafi ta dauka ba, ta fice daga gidan, zuciyarta tuni ta makance da neman cikar burinta,ko wata wane halin kuwa......
...........ina kuma zaki? mama ta fada tana kallon Zahra dake yafa dan mayafinta saman doguwar rigar da yayanta ya aiko mata,tura baki tayi to mama gidan kaka zanje,au saboda baki je aikin ba shine sai kin nemo abinda zaki fanshe fitar da baki ba", a'a wallahi mama dama ina son zuwa gidan kaka shi yasa banje aikin ba", shike nan sai kin dawo saura ki tsaya tsokana,an kusa dai komawa makaranta mu huta duka",
Ita dai Zahra bata ce komai ba ta fice tunda dai ta samu an barta.
Ade dake ta can karshen layi a labe Yana gadin fitowar Zahra yayi saurin daga waya ya kanga a kunnesa Yana cewa,samu maza ku fito kai da Babaye gata nan ta fito ku tabbatar babu wanda yaga fuskarku kai tsaye ku kai min ita can bayan gari, daga haka ya kashe wayar yana cewa yau zaka gane Ade ba sa an yi naka ba ne...
Kamar yadda ya Ade ya tsara musu haka suka yi sai da suka bari su Zahra su kayi nisa inda babu mutane sannan suka cimmasu....dubansu Zahra ta yi lokacin da suka tare hanyar da zasu shige ta ce", kai lafiya kuka tare mana hanya? Babu wanda ya tanka mata daga cikinsu saima gani tayi suna kokarin daukarta,aiko ta ce", kafa me naci banbaki ba,take suka mara mata baya cikin kure gudunsu......
Iyoka hannu ta ɗora aka tana ihun a kawo dauki amma babu wanda ya gifta ta wajen ma bare ya ji ta,ita ba abin ta bi bayansu ba,nan ta shiga kokarin tsaida duk abin hawan da yazo giftawa ta wajen..........✍🏼
Mamman siyam wane buri ne a RANKI shin na auren siyam da An ne ko kuma dai da wani abu daban???
Wai Ade me zaka yiwa zahranmu ta mutunci ne?
Team Zahra ku fito zanga zanga dan da alama wannan karan yar GIDAN YARBAWA ta debo abinda yafi karfinta🤣
Ko ma dai menene mu hade a nest pg,
Ku suburbudo min comments Ni kuma na suburbudo muku yar GIDAN YARBAWA ina godiya da SOYAYYA fans yar GIDAN YARBAWA 😍😍
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*