YAR GIDAN YARBAWA

Pg 13

by @zahrawriter12

.........Ade kuwa kai tsaye yan sanda suka mikawa shi kamar yadda oga AB ya basu umarni daga bakin pa Ja'afar.

An shigar da lefinsa kamar yadda suka ji a bakin Zahra daga nan aka kulleshi.

Wayarsa suka karba a kayi kiran matarsa lola,wadda ta shigo wajen hankali tashe tana zuba ihun rashin tawakkali.

......lokacin da Zahra taji labarin dariya ta yi tare da cewa a karon farko dai kayi abinda ya faranta min amma fa duk da haka ba wai na yafe maka ba ne,a to dan shi kansa wannan dan kanzaginnaka ba kyaleshi zanyi ba ehe.

Sam Zahra bata yi kokarin zuwa polistation ba tunda ba a kirata ba kuma bata fada a gida ba,dan tana jin fargaba da halin da mama zata shiga ga kuma kaka da bakinta ba shiru yake yi ba.....

Ga mamakin Zahra babu wanda ya neme ta, hasali ma ko sunanta bai fito acikin wadda ta yi dalilin kulle Ade ba.

Dan tuni a kayi Shari a kuma ya amsa lefinsa dan haka yanzu yana can gidan kaso.

Sosai Zahra taji dadin wannan lamari dan sam bata so maganar ta fita.

A ranta ta dinga ji kamar Ab ya kyauta mata kamar zata iya yafe masa, sai dai kuma ta rasa dalilin zuciyarta nayi masa irin wannan mummunan rikon wanda kuma sam ita hakan ba halinta ba ne.

Dan tabe karamin pink lips dinta tayi tare da yamutse fuska irin bata son tuna shi da duk abinda ya dangance shi,dadinta ma gobe zamu koma makaranta ba zan kuma ganinka ba."

Abbanta dake alwala daga hanyar fita waje kamar yasan abinda take sakawa ya dubeta bayan ya zubda ruwan dake bakinsa ya ce", ke Zahra tunda jarrabawa zaku fara duk ranar da baku da ita zaki je aiki dan kinga ba zamu yi saurin sakin aikin ba dan yana temako sosai wannan yaro dai Allah ya saka masa da alkhairi,"

Take Zahra ta kuma hade fuska tare da tunzura karamin bakinta sannan ta ce", haba Abba dan hutun da zan yi shine baka so? A'a Zahra Ni fa kina gama jarrabawa aure zan miki dan haka dole mu hada karfi da karfe mu tara na kayan daki", aure kuma Abba?

Zahra ta tambayi Abban fuskarta na fidda alamun mamaki",

Ey aure mana ai kin isa,ko dan wannan shegen jan maganar taki ai nayi miki aure na huta",

Kuka Zahra tasa har da shura kafafu, Abba saura kwana biyar fa na shiga shekara ta sha bakwai Ni yar karamata dani zaka min aure wlh Ni BAZAN yi aure ba.

.....Tunda ba aure zaki yi ba sai ki zauna gadin yan mata da samarin duniya",

Cewar mama dake fitowa daga banɗaki tana shirin daura alwalar magriba,

Kuka Zahra ta kuma rushewa dashi har dasu burgima .

Mama ta ce", yau Ni naga 'ya yanzu ina ji ba sallsh zaki ba? Ko shi ba acikin girman yake ba? Kaji min ja irar yarinya kawai.

Abba dake shirin fita sallah bayan ya gama daura alwalarsa ya ce ", maman Zahra rabu da ita wlh da zarar ta samu miji aurar da ita zanyi idan karatunne tayi a can idan mijin yana da ra ayi, Gara ma tun wuri ki fara sauraren samarin da kike kora da dutsuna."

Ɗif Zahra ta tsaya da kuka da shure_shuren da ta ke yi dan har ga Allah batan cewa Abba yasan abinda take yi wa samarinta ba,dan ko jiya sai da tasa yaran anguwa suka raka wani saurayi da jifa dan kawai ya zo ya ce yana sonta..

Ni daina kallo na an gaya miki mu sakaran iyayene da zaki dinga yin abu ba tare da mun sani ba," daga haka ta yi shigewarta daki ta bar Zahra sake da baki.

Tagumi ta zuba tana tunanin maganar Abba wai aure zai yi mata,wata zuciyar ce ta ce da ita ke haba Zahra sai kace wata mara kai, ai shi aure sai da miji ake yinsa,ko shima baki ji me ya ce ba,ki fara sauraren samarin da kike kora da dutsuna,kinga kenan dole sai kin tsayar da mijin sannan za a yi miki auren,ajiyar zuciya ta saki tare da sakin murmushin da ya karawa fuskarta kyau har kumatunta na lotsawa....

.........sosai siyam ta karfafa kanta wajen tunkarar aikinta dan kawai son ta burge AB ko da na yini daya ne.

Sai dai ga dukkan alamu iskarce take ci gaba da wahalar da me kayan kara,dan tun zuwanta Companyn har yanzu uffan bai taba hada ta da Ab ba kai shi kansa pa Ja'afar ba wani kulata yake ba sai abinda ya zama dole, ko baki yayi da wani lokacin sai dai kawai taga sun zo zasu shige ba tare da sun bari ta yi musu iso ba,dan tuni yasan da zuwansu ta wajen jafar,shi yasa take matukar jin haushin jafar kamar me.

Ta bangaren josuwa ne ma take dan samun wasu bayanan da suka danganci AB din Dan shima josuwan mayan kudi ne amma duk da haka bai taba sakin jiki da ita ba dan suna son ogansu sosai duk da halinsa na Shariya da nuna bai san a nayi ba.

.......shi ko uban tafiyar ma ya manta da sharafin kowa a gabansa, dan tafiya ce a gabansu wadda zai iya kaiwa tsawon wata guda bai dawo ba.

.......su Zahra yan makaranta duk da abun Zahra akwai kokari da mai da hankali a kan karatu,dan haka ita ko jin jarrawar bata yi dan kanta akwai dauka.

Yau saura jarrabawa biyu su gama kuma basu da interval,dan haka cike take da jin haushi,duk da cewa tana zuwa Company amma ba za a sashi a lissafi ba dan tana zuwa take guduwa gidan kaka abinta.

.......AB kuwa tuni jirginsa ya lula zuwa kasar Poland tare da jafar dan halartar taron bude sabon Companyn hadin gwiwa da zasu yi da wasu turawa....

Tafe suke su uku abinsu dan Zahra bata yadda da kowace kawa ba bayan kawayenta na amana Hafsah da nadiya, ayi fada ayi dadi.

Tun daga nesa suka hangowa wata Black prado(se hakuri ba sunan motoci na sani ba 🤣)da gudu tazo ta wuce su, sai kuma suka ga ta dawo a hankali har zuwa inda suke tsaye suna jiran abin hawa,tsayawa ya yi tare da zuge glass din motar kasa ya zuro kansa ta waje yana cewa yan mata sannunku fa",

Kallon Zahra su kayi dukansu dan sun san basu isa yin magana ba in dai har ba ita ta gadama ko kuma ta fuskanci daya daga cikinsu ake yiwa maganar ba ita ba,kawar da kansu su kayi saboda yadda suka ga tayi kicin_kicin kamar taga kashi, shi ko saurayin BEYERABE daya ga sunki kulashi sai kawai ya fito daga motar ya karaso gabansu saitin Zahra ya tsaya hannayensa cikin aljihu yayi irin tsayuwar gayunnan duk dan ya burge Zahra ga kuma mota da yasan cewa tana tafiya da imanin yanmatan zamani.

Cikin saita murya yana mai jujjuya key din motarsa ya ce", hi baby kyar kekkewa ko zaki bani address don ina sonki zan iya aurenki yar diyar Fulani", sakin baki Zahra tayi tana kallonsa, kafin cikin mamakinsa da ya cikata ta ce", kai anya ko kai ba aku ba ne ka koma mutum? Ko da ike ba mamaki tunda kai din bayerabene ", to dan Allah malam kayi hakuri tun muna mu biyu uzurin da zan yi maka ma dan kawai baka san ko Ni wace ba shi yasa,Ni da duk yarbawan anguwarmu babu wanda ko da wasa ya taba cewa yana sona saboda sun san kwanan zancen amma kai daga zuwa har ka fara batun aure, to bakinka ya sari danyan kashi danni nafi karfin auren bayerabe koda kuwa zama yayi a cikinsu dan haka kara gaba malam",

Dariya yayi ba tare da nuna wani jin haushi ba, sannan ya ce", wallahi ina sonki kuma zan aureki,Ni bayerabene amma mama nace bayerabiya babana bahaushe ne kinga kenan zamu iya aure?

Zaro ido ta yi tare da cewa Ni Allah ya kiyaye wai duk baka ji abinda na fada maka ba ne? Ai ba dan Abba ya hanani ba da yanzu an lotsa motarka da ruwan duwatsu tare da wannan katon kannaka,"

To baby me yasa baki son auren bayerabe?

Ina ruwanka? kaji irin halin naku ko,a gulmawiya kawai,"ta fada tare da figar hannun nadiya da hafsa da suka kasa yin ko tari dan idan suka yi ma fadan kansu zai dawo.

Yana tsaye suka samu okada suka shige, shima da sauri ya koma motarsa ya tayar tare da bin bayansu.

Sam Zahra bata lura da binsu da yake ba,amma su nadiya sun kura kawai sunyi shuru ne dan tsaf zata canja musu hanyar zuwa gida gashi su kuma duka yunwar makaranta data jarrabawa suke ji....

Yana ganin gidansu ya shige ya tafi zuciyarsa cike da farincikin yaga matar aure,dan duk kurarin Zahra babu wanda ya dauka, hasali ma ya barshi a matsayin KURUCIYA..

Zahraddin elyakub shine cikakken sunansa, kamar yadda ya fada mahaifiyarsa ce beyerabiya mahaifinsa kuma bahaushe,suna da arziki me yawa,dawowarsa daga karatu bai fi shekara daya ba,yanzu haka yana aiki da gidan jaridar bayalsa,a kan hanyar dawowarsa daga aiki ya ga Zahra YAR GIDAN YARBAWA, a take ba tare da zuciyarsa ta yi shawara dashi ba ya kamu da matsanancin so......

Koda zahraddin yaje gida bai tsaya wata kunbiya_kunbiya ba ya sanar da Abbansa ya yi mata dan haka yana so aje a nema masa aurenta,sosai Abban nasa yayi murna ya karbi address din gidansu Zahra,ya ce", in sha Allah a cikin satinnan zan samu kawunka sai muje", marairaice fuska zahraddin ya yi tare da cewa dan Allah Abba kuyi sauri kar kuje ace an bada ita ko tana da wani wallahi ba zan iya dauka ba ina sonta da yawa", dariya ummansa ta yi tana cewa kai walle yaron zamani basu da kunya zahraddin kamar ba kai ba", tashi yayi cikin dan jin kunya ya bar gurin yana mai jaddadawa Abbansa akan suje da wuri...

Gaba daya Zahra ta manta da batun wani zahraddin tunda Indai samari ne tayi irinsu sau babu adadi, dan Zahran tamu akwai farin jini,

Cikin hukuncin Allah yau Zahra suke kammala jarrawarsu wanda yayi dai_dai da haduwarsu da zahraddin kwana biyu kenan,

Cikin farin ciki suka fito daga makaranta gaba daya, duk fuskar dalibai da ka duba zaka ga tsantsar farinci, ko wacce ta bata hijab dinta da koren fenti tare da fuskokinsu, wasu hijaban ma duk sun cire sun daure shi a kugunsu duk saboda farinciki.

Su Zahra ne suka tsare kan Babban titin da yake tsakani da makakanransu budurinsu suke ba tare da tunanin motoci suna bukatar wucewa ba,daga karshe ma kulle hanyar sukayi sai dai idan ka taho ka canja hanya kana mai jan Allah ya isa...

A hankali ya shaƙi iskar kasarsa wadda yake matukar jin dadinta tamkar wata ta musamman,da sauri jafar ya bude masa motar da josuwa ya zo da ita ba tare da ya taho da sauran gerd din ba wamda gakan umarni ne daga oga AB......✍🏼

Ab ka koma inda ka fito dan walle baka da hanya Zahranmu na yin selenburuti din candy🤣

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*