YAR GIDAN YARBAWA

Pg16

by @zahrawriter12

........Har tasa ƙafa zata shige sai kuma ta dakata tare da danyin nazarin da bai wuce sakan talatin ba.

Komawa ta yi da baya cikin sanda dan bata son kowa ya ganta bare a san tazo.

Fita ta yi daga gidan ta Wada gidan maman Sadik wata makociyarsu beyerabiya, gidansu yana da dan kyau ba laifi shi yasa mijinta ya saka musu karnuka har biyu duk dan saboda kar barayi su zo su kwashe dan abinda ya tara,(hu yarbawa nawawo😄)

Itama Zahra daga barandar gidan ta tsaya saboda jarabar karnukan ,dan saboda Zahra ne ma suka daina sakinsu.

Maman Sadik maman Sadik Zahra ta shiga kwallawa matar gidan kira.

Waye ne aka yake min kira kamar yaro nashi? Maman Sadik ta fada tana fitowa daga cikin gidan,ganin Zahra yasa ta danyi turus ,dan kaf YARBAWAN anguwar basu son hanya ta haɗa su da Zahra dan dole sai ta kirkiri muguntar da tayi musu ko yaransu.

Ƙaraso mana kika tsaya kamar nadakariya", cewar Zahra tana wani yatsine karamin bakinta da dogon hancinta da yake neman shigewa baka,lafiya de Zahla kake nemana? Wallahi dadina da ku gajen hakuri ko kuma nace tsoro to Ni ba wani abin ya kawo Ni ba,ina nufin ba tashin hankali ne ya kawoni ba," to ina jin ka,aikin banza baku da aiki sai maida mace namiji da baka,Zahra ta fada cikin ƙunkuni sannan ta ɗora da cewa dama so nake ki sako min wancan karnukan naki muje cikin gidanmu dasu,"

Zaro ido maman Sadik tayi tare da cewa Zahla kasan fadan wannan dogs basu da kyau suna cizo sosai fa", dalla Ni ba cewa nayi ki barsu su ciji wani ba ba shi yasa nace muje tare ba,kawai ina so a danyi gudun ceton raine amma ki bari sai na shiga na fito zan miki magana ki sake su, amma ki tsaya a gun da kinga alamun zasu kama wata sai ki musu magana ina fata kin gane? Ey na gane bari naje na fito da su", zahra ta ce", ba fa cewa nayi ki sake su yanzu ba, ki bari na shiga na fito nayi settings wasu abubuwan ko", to shike nan ina jiran ka",

Wucewa Zahra ta yi tana sakin murmushin mugunta,ji take a ranta inama zata ga Ab yanzu wallahi da sai tasa an sakar masa karnukannan taga karyar iskanci yana wani taku kamar baya son yi yana wani hade rai kamar ance masa wata zata so shi,to shi wannan ma uwar me za ayi da shi,duk wacce naga tana sonsa sai na bata shawara ta hakura fuska sai kace kullum kosai,ta fada a fili tana sakin tsaki.

Har yanzu babu abinda ya ragu daga hayaniyar har zuwa kan fadan da ake yi.

Zahra na shiga kamar an yi walkiya ji kake tsit, duk wacce ka kalli makogaranta zaka ga yadda yake kaiwa yana kawowa alamun cewa kakkauran miyau ake hadiya ba tare da an shirya ba.

Kallo daya Zahra ta yi musu ta dauke kanta, ba tare da ta ce musu komai ba,ta nufi kofar dakinsu ta rufo, sannan ta juya ta bi duka dakunansu ta rufe ta rike makullan hatta da banɗaki bata barshi ba,sai da ta rufe ya zamana babu wajen tsira sai waje.

Tsaye suke kamar wasu gumaka suna kallonta cike da mamaki sai dai sun kasa cewa komai.

Fitar da ta yi ita ce ta basu damar yin magana,lola ce ta ce", kai wannan jarababban yaro ya dawo ko mi zai yi da keys dinmu?.

Maman Jo ta ce", kai akwai wani abu da yaron nan ya shirya ,dan ganin Zahla ba akheri b.....kafin ta karasa abinda ke bakinta mahaukatan karnukan gidan maman Sadik sun shigo gidan da gudu suna wani irin haushi na fitar hankali,dan dama sun yi kwana biyu basu yi mugunta ba yau kuma abin nema ya samu, a haukace suke da neman agarar wani.

Kafin kace me yarbawa sun haukace da ihu da neman dauki,duk wacce ta nufi hanyar dakinta na ki na wata sai taji shi a garkame Zahra ta rufe.

Ihu kawai suke suna neman dauki amma babu wanda ya kawo temako saboda duk wanda yazo zai yi magana Zahra dake waje ita ke rufe masa baki da tuwon kasar da tayi tun fitowarta.

Da mutum ya bude baki sai dai yaji yana tauna kasa haka zakaga sum sum ya bar wajen yana faman furzar da ƙasa da neman ruwan kuskure baki.

Haka Zahra ta dinga dariya saboda abin ya kayatar da ita,bata ankara ba sai ganin lola ta yi ta fito da gudu daga ita sai daurin kirji ta dau hanya kamar wata zararra,can kuma sai ga maman Jo itama da gudu tana fadin help help my people ita kuma wani gida ta fada,da haka da haka suka dinga fitowa cikin kwarereta suna yin takansu,har suka fice duka.

Dake Zahra tayi kashedi wa maman Sadik shi yasa ta kasa ta tsare ta hana karnukan duk wata hanyar da suka bi dan samun cizon daya daga cikinsu,to Allah dai ya kiyaye babu wadda aka ciza amma fa sunsha wahala da gudun ceton rai ko wacce ka duba ta jike sharkaf da gumi.

Mama kuwa tunda ta ji ihun tayo hanyar waje dan ganin me ke faruwa,sai kuma taji kofa a garkame,tun daga haka tasan cewa aikin Zahra ne,to itama dake cikin jin haushinsu take sai kawai ta koma ta ware rediyo tayi kwanciyarta...

Sai da Zahra ta tabbatar sunji jiki sannan ta ce da maman Sadik ta maida karnukan sai wani lokacin idan ta nema.

Gida ta shiga ta budewa kowacce dakinta sannan ta fada nasu dakin , inda ta samu mama zaune tana sauraren rediyo,fadawa jikinta Zahra ta yi tana cewa i miss You mamana ", dan ture Zahran mama ta shiga yi tana cewa rabu dani a hakan ki kayi kewar tawa bayan kinje kin yi zamanki daga yin kwana uku",

Dan karamin bakinta ta tura kana ta ce", mama ai kune kuka sa na guje ku tunda zaku yi min auren dole", ta karasa maganar cikin hawayen da basa yi mata wuya.

A hankali mama tasa hannu tana share mata hawayen tare da da cewa haba zahraty baby meye ne a cikin tashin hankali naga fa yaron nan yana da kirki ga tarbiya ki yi hakuri kiyiwa mahaifinki biyayya nasan zaki ga sakamako me kyau",

Kuka ta fashe dashi tana cewa da gaske mama auren zaku yi min kenan?

Kuma da BEYERABE mutanen da kuka san cewa bana son zama dasu me yasa zaku yi min haka?

A'a Zahra mummunar fahimta kikayiwa yarbawa amma ba duka ne masu irin halayyar da kika tsana din ba,dan haka dan Allah ki sassautawa kanki wannan tsanar,tunda gashi nan ko yanzu kinga ishara, shi yasa ba a son ka tsananta so haka ƙiyayya komai ana so kayi tsaka tsaki saboda gudun abinda zai biyo baya,yanzu me gari ya waya gashi Ubangiji ya jarrabeki da abinda kika fi tsana din tun ina ganin lamarin naki KURUCIYA ce amma sai naga kullum abin gaba yake kina girma lamarinki na girmama",

Dakyar dai mama ta kalleshi Zahra ta yi shuru .

Ga mamakin Zahra mama bata ce mata komai akan abinda ya wakana a gidan ba,hakan yasa itama ta share.

Basu suka dawo gidan ba sai bayan sallah isha'i duk wacce ka kallah a tsume take sai dai babu halin yin magana,da farko sunyi tunanin dauko yansanda sai kuma take abinda ya faru akan lola ya dawo musu,hakan yasa suka fasa dan sun san kadan da aikin Zahra tasa reshe ya juya da mujiya,hakan yasa suka hakura suka dawo gidan kowacce tana faman dingisa ƙafa.

Dariya Zahra tasa tana rike ciki sai da ta yi me isar ta sannan ta dakata tare da cewa Wallahi kar wacce ta sake ta shiga daki ba tare da ta gyara gidannan zuwa banɗaki ba,dan baza ku sa mana cuta muna zaman mu lafiya ba ehe", ta fada tana rike kugu da karkada jiki har da fari da ido.

Cirko cirko su kayi suna kallon Zahra kafin maman Jo ta yi karfin halin cewa , gaskiya Zahla baka mana adalci kasa mu wannan gudu haka sannan kace sai muyi sara," sai kun yi din wallahi idan ba kuyi ba yanzu zanyi muku barkonon tsohowa babu wacce za ta yi bacci a gidanna....ai kafin Zahra ta kai karshe kowacce ta nemi abinyi daga me daukar tsintsiya se me kawar da kaya sai me dibar ruwan wankin banɗaki.dariya Zahra ta yi tana kallonsu har suka gama,ko da Abba ya dawo ta gaidasa ya shige daki bai fahimci komai ba dan haka bai yi mata magana ba.

Zahra bata tashi daga gurin ba har sai da ta tabbatar komai ya kimtsu yadda ya kamata sannan ta shige daki.

Haka nan suka shige dakunansu da tsamin jiki bakunansu fal Allah ya isa ga Zahra ....

Washe gari tsaf Zahra ta shirya zata wuce wajen aiki daga nan zata koma gidan kaka,babu wadda ta yiwa magana a cikinsu ,sai dai ta sawa ranta cewa zata dinga yi musu zuwan bazata idan basu yi hankali ba sai ta koya musu har su yi hankalin bin dokinta ko bata nan.

.........daidai lokacin da su Zahra ke sa kai cikin tafkeken Companyn ,a daidai lokacin motocin Ab suka sako kai.

Wata muguwar harara Zahra tabi bayan motocin dashi tana mai cije lips dinta ,ji take kamar ta kamo su ta yi ta duka har sai abinda take ji a kirjinta ya sauka,to amma ba hali,tafiya tayi tana cewa Wallahi yau sai nayi abinda zan samu sa'idar abinda su kayi min a wancan ranar BAZAN iya hakuri ba,ta fada tana ci gaba da harare motocin kamar idanunta zasu fado.

Dakyar ta hadiye komai ta wuce bangarensu.

Basu fi awa daya da shiga ba,suka ji wannan daddan kamshin da yawancin mutanen da suke mu amala dashi suka fara rike shi a hancinansu,kafin su yi wani yunkuri tuni ya shigo wajen shida mukarrabansa cikin takunnannasa me nuni da mazantakarsa tare da jarumta tsayayyan namiji miskili wanda mata ke wawarsa.

Tsaye yake a kan dogayen ƙafafunsa hannunsa saye cikin aljihun arniyar wandonsa da kallo daya za kayi mata kasan cewa taci kuɗi,lumsassun idanunsa farare tas sanye cikin siririn farin glass tas Wanda bai ɓoye farar kwayar idanunsa ba.

Bakajin motsin komai sai na fankokin da suke ta falfala gudu tamkar zasu fado,idan kuma kanutsu zaka iya jin sautin gungunin Zahra da take ta faman yi tun bayan gane wanda yazo wajen.

Kowa ya je ya mika gaisuwa ita ko tana a tsaye wajen aikinta ko motsi ba tayi ba,tana kallon wani gurin daban.

Jafar kuwa ji yake kamar ya je ya tankado ƙeyarta saboda bala in haushi,sai dai bai yi hakan ba,saboda yasan abinda Oga ya shirya mata a kan sauyin aikin da za ayi wa ma'aikata yanzu duk ta dalilinta......

Wani murmushin mugunta ya sakar mata lokacin da suka hada ido tana harararsa.

Cikin sautin muryarsa me dan kauri da amo ya yi musu godiya da fatan alkhairi,da ga haka ya tsuke baki tare da ja baya ,da ido ya umarci jafar da ya dora jawabin.

Gyaran murya jafar ya yi fuskarsa cike da murmushin mugunta ya fara fado sunan ma aikata tare da aikin ko wanne da yawa ci gaba suka samu, dan haka sai farinciki suke suna zubawa Ab addu'ar gamawa da duniya lafiya,hatta su nadiya sun samu cigaba.

Zahra na nan tsaye tana jiran ta ji nata matsayin.

Zuru ta yi tana kallon bakin jafar dake rattafo aikin da aka sauya mata wanda yasa ta ji wani hayakin bala'i na fitowa daga kofofin hancinta da kunnuwanta.

Ni zan yi wannan kaskantaccen aikin kan bala'i, wallahi AB ka taro mach dan nasan wannan duk shirinka ne mugu dan ta adda ta fada tana ficewa daga gun Dan bin bayan Ab da tuni ya haye lipt dan shiga office.....✍🏼

Wagga cin zarafi tayi yawa abb.

Zahra ya da haka ko tsoro bakki ji kina bin Oga office Kai tsaye,kina karamar staff.🤣

Wai shin aikin me ka bawa zahranmu ne?

Team Zahra come forward Ni dai nayi nan🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️🏃🏾‍♀️

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*