YAR GIDAN YARBAWA

Pg20

by @zahrawriter12

.........duk kuka da ihun da maman tunde take yi,babu wanda ya iya zuwa inda take dan suma tsoron karnukan suke yi.

Wata yar dungure da maman tunde ta yi sai da Zahra ta kusa faduwa saboda dariya, saboda yadda fuskarta ta yi futu_futu tamkar ta fito daga filin yaki, kokarin tashi take yi amma ina gwiwarta ta rike gashi karen suna dab da ita,lokacin da take samun damar tashi tuni har karnukan sun ƙaraso inda take duk yadda ta kai ga kokarin guduwa hakan bata samu ba sai da su kayi mata mummunan cizo a cinyarta tana ihu tana dambarwa ta mike da wani irin gudu ta Wada wani gida dake kusa da su,tana shiga ta rufe kofar tare da zubewa a jikin kofar tana rusa kukan azaba jini kuwa duk ya bata mata jiki tambar anyi yankan rago..

Yarfe hannu Zahra ta yi tare da yiwa maman Sadik nuni da karnukanta akan taje ta dauko su su tafi.da rawar jiki ta janyo kannukan ta yi musu magana suka nutsu dan kar su razana me nafef din da sauran mutanen hanya,suma Zahra shiga nasu su kayi a lokaci daya suna barin anguwar...

Daidai suna fita daga layin Abban zahraddin din da bai san me ke faruwa ba saboda hankalinsa yana kan dansa da yake ta faman rarrashi akan kar ya tafi ya bar gidan kamar yadda ya fada, ya fito saboda labari da me gadi ya je ya bashi a kurarren lokaci,dan shi ma me gadin kin zuwa ya fada yayi saboda kar ace sai ya fita ya taimaketa dan wlh ba zai iya ba haka kawai a jawo masa lalura akan abinda baiji ba bai gani ba..

Har aka dauketa aka yi asibiti da ita bata daina ihu ba,wanda ya cika gaba daya anguwar ,yadda ta damu mutane da ihun yasa ko tausaya mata wasu basu yi ba,dake sun san me ya faru ma da yawa cewa suke Allah shi kara alhakin bawan Allah uban Zahra ne ya fara kamata...

Lokacin da suka ƙaraso gida maman Sadik ce kawai ta sauka da karnukanta su kuma su Zahra suka wuce gidansu nadiya duk da cewa ba wai nisa ne tsakaninsu ba,amma saboda tsaro sai kawai suka wuce a nafef din..

..........tunda dady ya koma gida yake tunanin hanyar da zaibi dan sanar da baudaddan yaronnasa wannan batun auren,sosai ya damu da neman mafita duk da yasan cewa AB ba zai watsa masa kasa a ido ba,to amma yana fargabar yadda zai mu alamalanci yarinyar tunda ba sonta yake ba,kai shi fa yasan AB in dai ba hukuncin Allah ba babu abinda zaisa ya fada soyayya harma ya tsaya bata lokacinsa akan matar,to bare kuma wadda ko saninta bai taba yi ba, shi yasa ta wani bangaren sam baya nadamar abinda yayi dan kuwa yasan in dai ba haka yayiwa AB ba to lallai zaiyi ta zama babu aurene.....

Ko Ammi kasa gaya mata yayi har sai da ita da kanta ta fahimci damuwar da yake ciki sannan ya yi mata bayanin abinda ya faru kai daga karshe ma nuna mata videon ya yi wanda hakan yasa itama ta tausayawa Abba ta kuma amince da gamsuwa da abinda dadyn ya yi,dan har ga Allah ji ta yi ta samu nutsuwa da auren akan na siyam da tuni ta gano take takenta,bata son auren siyam ko dan mahaifiyarta dan sarai tayiwa maman siyam din farin sani alan wasu da yawa na halaiyarta,dan haka yanzu ranta fes za kuma ta ci gaba da addu'a akan Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, wannan yasa ta shiga kwantarwa da mijinta hankali da bashi kwarin gwiwa wanda hakan yayi matukar tasiri a gareshi...

........

Yallabai yarinyar nan fa da gaske take ta aje aikinnan", ko tari AB da ke ta dangwalar tap dinsa baiyi ba bare jafar yasa ran cewarsa,to dake an saba da hali sai kawai.ya share ya bar maganar dan tunda yaga ogannasa yayi haka to yasan abinda hakan ke nufi,dan haka sai kawai ya kwashe Abinda zai kwashe dan lokacin fitarsu ya yi.

Sai da AB ya gama abinda ya fara sannan ya mike tare da rufe tap din ,glass dinsa da yake kara kawata fuskarsa da idanunsa masu rudar da mutum da sashi jin shakkarsa ya saka,kafin cikin dan takunshi me nutsuwa wanda ke hade da hanzari irin na mazaje ya fita daga office din tuni jafar ya bishi da dan sauri,dan tuni har ya fice duk da cewa baka taba gane saurinshi a haka sai idan kuna tafiya tare dan akwai matukar nutsuwa cikin tafiyarsa haka kuma akwai hanzari irin na jajurtattun maza.

Siyam na ganin sun fita itama ta bi bayansu dan yau kam baza ta tafi ita kadai ba,saboda tsabar rashin mutunci irin na AB yana kallonta kullum a bakin titi tana jiran Kabu Kabu amma bai tana cewa tazo su tafi ba a matsayinsu na wanda zasu shiga gida daya,shi yasa yau tasawa ranta tafiya tare dashi ai tana ganin dole idan ta nema ya barta ta shiga motar tunda dai da kunya yaki daukarta,,, Allah ya taimaketa tana fitowa basu riga sun wuce ba AB din ya dan tsaya amsa waya,tana zuwa yana shiga motar dan haka cikin sauri ta ce dan Allah broth AB mu tafi tare mana Nima fa gidan zanje",yadda ta yi maganar cikin dan shagwaba sai abin yayi wani iri ,dan haka sai da jafar ya dan murmusa. shiko uban gayyar ko kallo bata ishesa ba kai babu wata alama da ta nuna yasan da mutum a gurin,daga karshe ma dagowa ya yi yana yiwa su jafar din kallon mamakin rashin tafiyar da basu yi ba,aiko kamar ya yi musu allura josuwa ya figi motar a tsiyace, sai tashin kurarsu kawai kake gani.

Cikin sanyin jiki da kunya siyam ta bar wajen tana tsinewa AB a ranta, dan kuwa yau dinne ta kuma tabbatar da rashin mutuncinsa...

Anyi biki lafiya angama amarya zahra tuni ta ware ta shiga sabgarta kai baka ce auren dole a kayi mata ba,dan tuni ta gama shirya makomar auren a ranta,sai da kowa ya watse sannan abbanta ya kirata yayi mata bayani cikin nutsuwa dan yana so ta kwantar da hankalinta da auren,ai Zahra Naji ance ba yanzu za akaitaba ta kuma sakankancewa tun kafin a Kaita zata lalata auren dan haka bata nemi sanin kowaye mijin ba,shima Abba bai gaya mata ba dan yasan ba tun yanzu ba basa jituwa da ogannata,shi kansa idan ya tuna hakan yana jinjinawa kudirar Allah...

Yarbawa kuwa tuni murna ta koma ciki jin ance Zahra ba yanzu zata tare ba,dan har ga Allah sunso Zahra ta tafi gidan mijinta ko sa dan sarara da samun rangwame akan halin da take sakasu..

Dukansu suna zaune kan kujerun kewayayyan dinning ɗin da zai iya cin kimanin mutum goma.

Yau din ma dai sunyi sa ar kasancewa tare da AB da yake zaune ta bangaren hagun dady yana cin abincinsa cikin nutsuwa da ke nuna tsantsan kwanciyar hankalin da yake ciki.

Takaita cin abincin dady ya yi saboda kar damarsa ta wuce, dan yasan Ab yana gamawa zai mike ya bar gurin wata kila kuma shida kara ganinsa sai safiyar gobe idan muna da rai,dan haka ya dan muskuta akan kujerarsa tare da yin gyaran murya.

ABRAHAB idan ka gama cin abincin ina son ka saurareni dan ina son yin magana da kai", yadda dadyn yayi ne ya tabbatarwa da Ab cewa maganar me muhimmanci ce dan haka ya dan gyada kansa ba tare da ya ce wani abu ba.

Daga shi sai Ammi suka zauna a karamin falon dady dake ta cikin bangaren dinning ɗin,su siyam kuwa har yanzu suna bisa food babu alamun za a koshi anga banza.

Gyaran murya dady ya kuma yi tare da zubawa ab ido na wasu yan sakanni kafin cikin nutsuwa ya fara da cewa ", AB ba dogon magana zan jaka da ita ba dan ba sonta kake yi ba shi yasa na fi so nayi maka ita a takaice dan kafahimceni yadda Yakamata," ba tare da ya jira cewar ab din ba ya kwashe duk abinda ya faru a wajen daurin auren da kuma hukuncin da ya zartar.

Shiru yayi yana kallon fuskar AB din ko zai fahimci wani abu akai,sai dai kuma babu abinda ya canja daga farkon maganar zuwa yanzun,fuskarsa na nan a yadda suka saba ganin sassaucinta idan yana gabansu.

Ajiyar zuciya dady ya dan ja sannan ya ce", AB baka ce komai ba kuma kasan kai nake sauraro kuma dole ka bani amsa dan ba zan sauwake maka magana a yau ba kamar yadda na saba yi maka dan wannan maganar tasha banban da sauran saboda muhimmancinta.

Jinjina kai yayi kafin cikin karamar sauti ya ce", Allah yasa haka yafi alkhairi", Amin dady ya fada yana maida bayansa jikin makarin kujerar da yake kai hankalinsa na karasa kwanciya.

Ammi kuwa zuba masa ido ta yi lokacin da yake barin falon,bata dauke idonta akansa ba har sai da ta daina ganinsa, sannan ta dawo da dubanta gun dady tana cewa, wannan yaro Allah ya yaye masa wannan halin, duba fa yana da abin cewa amma ya gwammace ya yi shuru akan ya bude bakin",

Murmushin manya dady ya yi yana cewa daidai kenan domin yawan magana a wasu lokutan bashi da wani amfani ko a yanzu ma hakan yayi amfani a gareshi da mu baki daya saboda baiyi mana musu ba,kinga kuwa ai hakan yafi alheri", haka ne amma akwai cutuwa wani lokacin", dady ya ce", ba dai shiru irin nasu Abrahab ba shurunsa ba irin wanda zai bari a cutar dashi ba ne,yanzu ma dan yasan babu cutarwa a abinda muka yi masa ne,amma da dole ko baiyi magana ba akwai hanyar horaswa da bada gamsasshiyar amsa da yake da ita", haka ne to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi", cewar Ammi,da Amin dady ya amsa daga nan suka fara tattaunawa akan yadda za su fara nasu shirin bikin.

........

Washe gari da safe tuni lokacin Ab ya fice daga gidan, anan dady ya tara mutanen gidan har da masu aiki da securitys dinsa duka.ya sanar da su maganar auren amma bai gaya musu asalin yadda auren yakasance ba,take kowa ya shiga fatan alheri da sa albarka..

Siyam kuwa har yanzu bata sani ba saboda itama sammakon fitar ta yi daga gidan...

A yinin wannan ranar Zahra yini tayi a gida ita da mama babu inda ta leka ba kuma wai dan saboda auren da aka daura mata ba ne kawai dai ra'ayi tayi,tunda bata san cewa za a hana ta fitar ba kamar yadda ta saba..

Yau AB bai zauna dinner ba,dan haka dady ya kira josuwa da jafar tare da siyam suma ya sanar musu da abinda ke faruwa, take siyam ta dauke wuta tamkar bata numfashi saboda tsananin shock da ta shiga.......✍🏼✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA* .....😍