YAR GIDAN YARBAWA

Pg21

by @zahrawriter12

.......babu wanda ya lura da halin da take ciki, dady ne ya basu umarnin tafiya,jafar har ya mike dady ya dakatar da shi, komawa yayi ya zauna,sai da dady ya tabbatar sun fita sannan ya sanar da jafar yadda auren ya kasance tare da bashi adireshin gidan su Zahran tunda shine wakilin Ab din .....

Sosai jafar ya yi mamaki dan kuwa shi ya san Abban Zahra shi yasa ya gane Zahra ce matar ogannasa,duk kuwa da cewa baifi so daya suka taba haduwa da Abban ba lokacin da aka dakatar da su zahran daga aiki,amma duk da haka ya yi kokari wajen gane fuskarsa a videon da dady ya nuna masa.

Tab akwai cakwakiya ya fada yana goge zufar da ta dan zubo masa,ey dole ya ce akwai cakwakiya mana dan yasan tabbas Zahra tasan waye mijinnata akwai ƙura,shi kansa ogannasa ya kasa karanto halin da zai shiga duk da cewa shi ba a gane abinda ke zuciyarsa akan fuskarsa, da wannan tunanin jafar ya koma gidansu.

Bayan kwana biyu Zahra ta warware daga gajiyar biki kamar yadda ta fada, tuni aka fara komawa yar gidan jiya.

Mama zaune a tsar gida taga Zahra ta fito daga daki sanye da hijab daga dukkan alamu dai fita take son yi,ke kuma ina zaki haka? Cewar mama,tura baki Zahra ta yi tana cewa mama fita zanyi abu zan siyo a kantin maman Sadik,"

Harara mama ta watsa mata sannan tace", babu inda zaki ai yanzu ba da ba ne da zaki dinga fita duk inda ranki yake so," cike da mamaki Zahra ta kalli maman ta ce", to mama meye marabar yanzun da baya? Marabar shine aure yanzu duk inda zaki sai da umarnin mijinki", kan bala,I wallahi kuwa aurennan bai dauru ba, yanzu mama kina nufin babu inda zan dinga zuwa sai mijin da ban sani ba ya ban umarni?

Haka maganar take ba kuma fada ta ba ce fadin Allah ne." Wani miyau Zahra ta hadiya ba tare da ta iya cewa komai ba saboda mama ce bata son ta yi shirmen da zata shiga fushin Allah,dan haka sai ta sassauta murya cikin marairaita ta ce", to Naji mama dan Allah ki barni na siyo daga wannan shike nan", me zaki siyo? Auduga zan siyo ", yaushe audugar taki ta kare ban sani ba? Tura bakin ta kuma yi idanunta har sun cika da kwalla ta ce", dan Allah Ni dai mama ki barni kayan sana a zan siyo na gaji da zama shiru babu taro ba sisi", oh ashe dai aikin Company yana da rana", maman ta fada tana dan harararta, sannan ta ce", na baki mintuna goma shima dole idan mijinki ya zo a fada masa", fita Zahra tayi tana ƙunƙuni da cewa duba fa mama kamar sanin mijin tayi kuma yace mata zai zo dinnan wai sai an fada masa", me kike fada Zahra? Da gudu ta karasa fita tana cewa babu komai mama.

Daga gida Zahra shagon maman Sadik ta nufa,maman Sadik na ganinta ta fara washe baki, tana cewa sannu Zahla kwana biyu ka ɓoye kamar baka a garin", zama Zahra ta yi kan benchin maman Sadik din tana dan yatsine fuska sannan ta ce", maman Sadik ina nan cikin gida ina huce gajiya,oh haka ya yi maman Sadik ta fada tana sallamar wani yaro.

Dan gyara zama ta yi tana cewa maman Sadik zuwa nayi ki bani aron fulawa da manja da maggi zan fara sa ar wainar fulawa saboda na dinga samun na batarwa", dan jim maman Sadik ta yi,tuni zuciyarta ta shiga tashin hankali dan kuwa tasan asara ce ta biyota har shagonta,dan tasan muddin ta bawa Zahra kayanta to wallahi shikenan sai a lahira.

Zahra ce ta katse mata tunani,ta ce", maman Sadik wai dan nace ki bani bashin kaya da na siyar na kawo miki kudinki shine kika dauke wuta kamar na miki wani mugunta?

Cikin dabarbarcewa maman Sadik ta ce,a'a Zahla kawai ina tunanin yadda abun ya zama yanzu kinga komi ya tashi jarin bashi da wani yawa Kum.... A dan tsawace Zahra ta katseta da cewa kinga maman Sadik bana son wani dogon jawabi kawai ki fito min a mutum kice ba zaki bani ba saboda bazan biyaki ba ko?

Girgiza kai maman Sadik ta yi tana dan dauke zufar da ta jikata a lokaci daya, wannan shine gaba kura baya siyaki dan tasan idan ta hana Zahra kayannan asarar da ta guda sai ta yi ta,dan haka Gara kawai ta bata cikin sauki idan tana da rabo sai ta biyata,dan haka ta bude baki ta ce ", mene kake so zan baka", dariya Zahra tayi tana dan dukan kafadar maman Sadik kana ta ce", yauwa maman Sadik Gara da kika yiwa kanki tunanin mafita me kyau dan hanani kayannan dai-dai yake da daina fitowarki shago tun da ai dole sai da kayan da zaki saida zaki fito ɗin,"karka damu Zahla nasan baka da wasa zaka biyani.

Tabe baki Zahra tayi ta ce daga baya kenan,daga haka maman Sadik ta haɗa mata fulawa kwano daya manja rabin kwalba magi gashiri duk tana hada mata ta mika mata tana cewa Ni kam Zahla ba dan ba da na baka sawala", dubanta Zahra tayi sannan ta ce tame kuma?

Yauwa dama cewa nayi tunda sana'a na farko ne da kayi komi kadan_kadan idan komi ya tafi dede se ka kala yawan fulawa", a fusace Zahra ta katseta ",kinga maman Sadik karfa kiga na sakar miki fuska ki dauka hali na canja to wlh ina nan a Zahra ta yar GIDAN YARBAWA wadda bata shiri dasu bata son hada inuwa dasu ko a lahira dan haka kisan cewa Kema baki wuce na gwada miki halinnawa ba dan haka ki sarara min tun kafin nasa kafar wando daya dake ehe",soriyo kayi hakuri abin bana zafi ba ne jeka Allah ye bada sa a", Amin ta fada tana yin gaba abinta....

Ajiyar zuciya maman Sadik ta sauke tare da goge gumin tashin hankalin da ya jiƙata,a fili ta murta kai jema'a wannan yaro ina ya samu wannan asiri nashi me karfi kowa yana shakka nashi dan garami dashi sai mugunta da ban solo,oh Zahla ka tafi gidan aule mu huta",

......tunda siyam ta shiga daki take kukan tashin hankali harma ta rasa abinda ya kamata ta fara yi,sai da taji numfashinta na neman daukewa Sannan ta lalubo wayar mamanta...

Tana ji an daga wayar ta kuma fashewa da kuka.cikin tashin hankali maman siyam ta shiga tambayarta abinda ya sameta,bata iya mata bayani ba sai da ta yi me isarta sannan ta rattaba mata abinda akayi mata ko ta ce", dady ya yi mata tunda ai ba zai ce be gane irin son da take yiwa Ab din ba...

Wata muguwar ashwariya maman siyam ta lailayo ta makawa dan uwannata har da Ammi da bata ji ba bata gani ba,karshe ma laifin kanta ya koma.

A matukar fusace maman siyam ta ce ", siyam kwantar da hankalinka in dai kana dani ba zakayi kuka ba,ina nan tafe da guzurin hargitsa rayuwar ko wane shegen yaro ne ya aura ,idan NAZO bazan taba barin gidannan ba har sai na tabbatar na wase rayuwarsi kuma an daura aurenka da den uwanka,maza kayi sulu daga yau babu kai babu kuka", daga haka maman siyam ta kashe wayarta tare da fara shirin tahowa kwatarwa siyam AB dan gidan labarabawa.

Duk abinda Zahra ke yi mama na kallonta cikin mamaki da tunanin abinda take shirin yi.

Aiko dai yar halak din bata bada kunya dan kuwa komai ta hada shi na fara suyar waina.

Zuba mata ido mama ta yi dan ganin a inda zata yi sana ar waje ko cikin gida,ga mamakinta sai gani ta yi Zahra ta zura hijab tare da sawa yaran gidansu su kai mata kujerar zama waje,ita da kanta ta kinkimi kullun wainar fulawarta da ta kindima shi kamar tana da tabbacin za a siye duka,hanyar waje ta yi tana cewa ba zan barku ku taba min kayan sana a ba 'ya'yan ƙazamai kawai,ku dai kai min kujerar zaman itama idan naga abinda be yi min ba sai na yiwa ɗa shegen duka", tana gab da fita cikin mitarta da take yiwa yaran YARBAWAN ta, mama ta kirata, tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba, mama bata kula da hakan ba ta fara mata magana, ta ce", Zahra a waje naga kike shirin yin suyar?

Ey mana mama idan banyi a wa je ba waye zai shigo gida siyan waina,aiko zan ci gaba da yi a cikin gida to sai na kafa kaina sosai",

Tafa hannu mama ta yi tana cewa yanzu Zahra da aurennaki zaki fita sana ar kofar gida wadda a da baki yi ba sai yanzu dan kawai ki janyo mana abin magana", tura ƙaramin bakinta ta yi kafin ta fara bubbuga kafafunta cikin shawaga ta ce", to Ni yanzu mama bani da damar yin abu sai ace aure miji shike nan maganar kenan tsakanina dake?

Mama zata yi magana ta yi saurin tare ta tana cewa dan Allah dan Annabi mama ki barni ko na yau ne idan na kafu aka sani sai na dawo cikin GIDAN," jin jina kai mama ta yi tana cewa kije tunda kin riga kin kwaba kayan da ba naki ba dan nasan wannan kayan ba naki ba ne arowa kika yi, Allah ya shirya mini ke darajar aurennan da alfarmar Annabi Muhammad s.a.w,Zahra ta ɗora sannan ta yi saurin fita dan kar maman ta canja shawara...

Kamar wasa sai ga Zahra na suyar waina,daga farko kin siya a kayi sai kawai ta fara alakoro kamar yadda ta saba sana'arta tun farko,ga wanda ba yerbawa ba kenan,sai kuma gashi an fara siya har ana layi.

Idan kazo siyan ta dari biyu in dai dari biyar ka bata to ko me za kayi bata da canji sai dai ta baka ta duka ko kuma kayi asarar canjin dan bazata bayarba,(Zahra ya da cuwa cuwa a haka zaki samu customer)

Da suka fahimci haka sai duk wanda zai siya ya samo canji ya kawo, to da haka aka samu lafiya.

Kawayenta nadiya da Hafsah suna daga gida aka kawo musu labarin Zahra na siyar da waina,aiko tafiya su kayi dan ganewa idanunsu...

Abba ma yana dawowa ya tarar an gama ana kwashe kaya,turus ya yi yana kallon Zahra ta ta fara rabewa jikin bango dan kuwa har ga Allah nata so Abba ya dawo ya sameta a wajen ba,kwafa Abba ya yi kawai ya shige GIDAN.

Sosai Abba ya yiwa mama fada dan acewarsa lefinta ne da ta bar Zahran wannan ai salon neman zagi ne,to in dai haka ne wallahi Gara na nemi alfarmar mijinnaki ki koma aiki tunda shi wannan kuna tare zai dinga ganin duk wani motsinki sakarar banza sakarar wofi saboda wannan sakarcin naki na aurar dake amma sai gashi babu abinda ya ragu sai karuwa ma da ya yi,wuce ki bani guri ko yanzu na doddokeki", da gudu Zahra ta wada daki tama matsar kwalla.

Kwanciya tayi cike da gajiyar da tabkwasarwa kanta, take kuma maganar Abba ta dawo mata,me kenan yake nufi?

Ba dai mijinnata a shima a Company yake aiki ba?

Tab idan kuwa haka ne zata so komawa aiki ko dan ta samu hanyar warware auren ta hanyar nunawa mijin halinta harma da sabbin da zata tsiro dan ya saketa salin alin ba wanda ya ji ya gani,dan haka gobe zata koma ko Abba bai tambayo mata ba,yo ai ita gaba ta Kaita can zata je ta nemo banzan mijin da aka daura ta yi maganin matsalarta ba tare da kowa yaji ba....

........washe gari ganin Zahra kawai su kayi ta shirya tsaf cikin shirin fita,zuwa ta yi ta kurkusa gaban Abba ta ce", Abba zan tafi aiki", sake da baki Abba yake kallonta kafin cikin dan fushi ya ce ", waike Zahra yaushe zaki yi hankali ne?.....yanzu daga fadar magana shine har kin aikata ko bari baki yi an tambaye mijinnaki ba..?

To Abba ba sai ka tambayesa daga baya ba ..hannu Abba ya kai zai mazgeta ta tashi ta fita da gudu daga nan ta samu hanyar tserewa Company......✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA* 😍