Pg 24
........suna zaune duka a falon mama ,mama ta shinfidawa Ab da jafar babbar sabuwar dardumarta,cikin mutunta juna suka gaisa daga nan Ab bai sake tankawa ba,kansa a kasa yau dai yayi yakanar hakura da taba waya,jafar ne ya sanar da Abba sakon dady na cewa suna son nan da sati Daya Zahra ta tare dan suma a satin zasu yi nasu bikin....
Jafar na cikin wannan bayanin Zahra ta rangado sallama a lokaci daya tana buɗe labulen falon,harara ta fara zabgawa jafar kafin cikin sauri ta ƙaraso gaban Abba ta zube tana cewa Wallahi Abba duk abinda ya fada maka sharri ne bari kaji abinda ya yi min dazu daga naje kai masa kara", wata zabura jafar ya yi yana son katse Zahran amma ina ko kallonsa ba ta kuma yi ba tun hararar da ta yi masa.
Shiko Ab dama ba cewar zai yi ba sai dai bai zaton abinda Zahran zata fada ba kenan,dan kamar daga sama yaji ta cigaba da cewa, Abba shima fa wannan ogan da kake gani sumi sumi to wallahi ba kanwar lasa ba ne dazu fa kamani yayi daga Allah ya aikoshi ya taimaka min kar na fado daga dogon benensu shike nan ya samu dama ya kama bakina ya dinga tsotsewa kamar ya samu alewa Kum.....wani mugun bugu mama ta kaiwa bakin Zahra dan haka babu shiri ta hadiye ragowar zancenta.
A hankali Abba ya mike ba tare da ya ce komai ba saboda tsananin kunyar da Zahra ta bashi,mama kam kusan da rarrafe ta bar falon dan har ta riga Abban barin falon,sai da Abban ya kama labule zai fita sannan ba tare da ya juyo ba ya ce", wallahi Zahra idan baki yiwa mijinki biyayya ba zan iya cewa babu Ni babu ke gashi nan wanda kikewa fitsarar shine mijinnaki kuma oganki", daga haka yasa kai ya fice da kunyar tabarar Zahra.
Jafar ma tashi ya yi sum sum ya bar wajen yana sosa keya fuskarsa cike da murmushin halin Zahra Wanda shi a yanzu nishadi kawai take sashi..
Zahra kuwa tun fitar Abba ta ƙame a zaune tana rarraba idon inda zata hango mijin da Abba yace gashinan a gabanta,da taga nata ga kowa ba sai Ab da yake zaune kamar babu shi a wajen sai wayar da tun dazun ya dauka ya shiga aiki da kuma kamshinsa da ya game dakin har waje gaba daya.
Ɗan matsawa ta yi gabansa tana leka fuskarsa dan ita kam har yanzu bata gama fahimtar abinda Abba ke nufi da ga mijinnaki a gabanki ba,dan Allah Oga AB ko ka ga wani a nan bayan Ni da kai? Shiru babu amsa,matsowa ta kuma yi tana kuma cewa dan Allah ka fada min abinda Abba yake nufi waye mijin kuma ogana? Bai bata amsa ba sai gani tayi ya mike tsaye tare da nufar kofar fita.
Da sauri ta bi bayansa dan ita kam so take a fidda ta daga duhu da rudanin da take neman shiga.
Har waje ta biyosa a nan ta jefawa jafar tambayar da ogansa ya kasa bata amsa saboda wulakanci da miskilanci,kai dan Kore dan Allah waye mijin da ake fada? Yana budewa AB din mota ya juya yana nuna mata Ab da ido,sai da ya rufe motar sannan ya ce da ita ga shi nan kin rako shi saboda kinga mijin nunawa sa a da baki taba zato ba,maza ki koma gida ki taka rawar murna da samun miji kamar ogana", daga haka ya bude motar ya shige yana kunshe dariya dan yasan ya kara haɗa bom a zuciyar Zahra da maganganunsa.
Aiko kafin su bar wajen Zahra ta kaiwa kasar wajen wata irin danka ta debo ta watsawa bayan motar tana jin kamar zata yi dan karamin hauka,Ni wannan mutumin zai mannawa hauka to wallahi ba zan zama.matarsa ba har abada da wannan mutumin ba Gara zahraddin din ba", da gudu ta koma cikin gidan tare da fasa kuka tana zubewa a tsakar gidan ta fara al'adar tata ta shure shuren kafafu, kan kace me YARBAWAN GIDAN sun fito kowa na son lallashinta ,sai dai kamar ma zugata suke yi dan duk abinda yazo hannunta wurga musu take yi...
Dama Abba tun baranbaramar da ta yi yana fitowa barin gidan yayi gaba daya,mama kuwa tana kallonta bata ce mata komai ba sai da taga abin yana kara ta azzara sannan ta ce"dan ma sakarci irin na Zahra da KURUCIYA me ye abin ƙi ga AB wasu suna can suna kukan nema ke kina nan kukan samu da tabara,wace macece zata ki Ab in ba mahaukaciya ba? To wlh idan baki tashi a wajennan ba sai na yi miki shegen duka kuma yanzu na kirasa nace ya zo ya daukeki ku tafi can ki karata su ma su ɗana mu ma dan huta na wasu kwanakin haka kawai yarinya kisawa ranki rashin ji da sakarcin banza.
Ganin taki saurarawa yasa mama dauko waya,Zahra na ganin haka ta gudu daki tana ci gaba da sheshsheka zuciyarta na cin mugun alwashin zama a gidan Ab din,wata zuciyar ta ce ke kam me ye na kuka? Shin kin manta da alwashin da kika daukawa akan duk mijin da aka aura miki,ai kawai ki kwantar da hankalinki ki tare su mama su huta na kwana biyu a cikon na uku su ganki baban AB din da kansa yasa ya sake ki kamar yadda yasa aka aura masa ke,da wannan tinanin ta dan ji nutsuwa tazo mata...
Suna ƙarasowa gida ko tsayawa jafar ya bude masa motar baiyi ba ya fito cikin nutsatstsan takunsa me haɗe da ɗan hanzari ya wuce zuwa main falon,maman siyam na zaune a falon tana ganinsa ta shiga washe baki wai ita a dole ga suruki,bai so tsayawa ba saboda ciwon da kansa yake dan yi,amma haka nan cike da jarumta ya dakata ya gaidata sama sama daga haka ya haura sama ba tare da ya saurari zantukan da take masa ba,da Harara ta bishi tana cewa yaro dani kake zancen sai ka dawo kana min kuka akan siyam wannan alkawarinane",
Kai tsaye bathroom ya fada ya sakarwa kansa shaya idanunsa a rufe,yana so ya ji zafin abinda ke faruwa dashi amma ta wani bangaren yana ganin babu amfanin hakan dan shi sam bai dauki Zahra wani abu ba bare har lamarinta ya damesa dan haka ya yakice damuwarta da duk abinda ya shafeta ya ake su gefe ya dauki abu me muhimmanci.
Yana fitowa ya kimtsa kansa cikin copy din jallabiya sai ƙamshinsa da ya zama wani abu na musamman a cikin gidan da ya bude ko ina da ina.
A hankali yake takowa hannunsa rike da dan karamin casbaha me shegen kyau yana ja, fuskarsa babu wani damuwa sai yanayinsa na kullum babu yabo babu fallasa.
Yauwa Abrahab karaso kaima Naji wane shiri kake yi na bikin? Cewar daddy da suke tattauwa da kanwarsa maman siyam wadda ta fuske kamar babu wani abu a ranta game da auren ɗan kaɗan ya dubi daddy bayan ƙarasowarsa cikin falon sannan a hankali ya bude baki ya ce", no daddy bana bukatar yin komai ku cigaba da shirinku Ni tafiya ce ma ta taso min a satin", maman siyam ta ce", kai haba yarona kai ko yaza ayi a kawo maka amarya baka nan", daddy ya ce", rabu dashi aunty ba zai fasa ba idan ya dawo ya sameta a gidan", ai shike nan har yanzu dai Ab kana nan da wannan tsayayyar maganar", fita yayi bai tanka ba,su kuma suka ci gaba da magana akan lefen da za akai gidansu Zahra.
Zahra na zaune a kofar dakin mama tana yar carafke da kananan duwatsu,taji Abba na sanar da ita cewa gobe za a kawo kayan lefen Zahra dan haka zai je ya sanar da kaka,to Masha Allah Allah ya kaimu goben ", ya tsine fuska Zahra ta yi sai kuma ta saki murmushi a fili ta ce", ashe dai zan zuba yammatanci me kyau idan na dawo ai ko tafiya da kayan ma bazan yi ba bare idan sun tashi koroni su koroni Ni kadai Gara na barsu a gida, dan nasan tsiyar da zan shuka musu baza ta bari su barni na fito da ko takalmi ba,sai ko ta kyalkyale da dariya ho ni Zahra YAR GIDAN YARBAWA ",
Fitowar Abba yasa ta gimtse dariyarta,ke kuma dariyar me kike sai kace sabon kamu? Abba ya tambaye ta yana kokarin sa takalmansa.babu komai Abba a dawo lafiya ka gaida min kakale,zata ji ya fada yana fita daga gidan.
Abba yana fita sai ga sallamar maman Sadik ,tsam Zahra ta yi bata amsa ba har sai da ta kuma yin wata, sannan ta amsa tana cewa waye ne? Maman Sadik ta shigo bakinta a washe tana cewa zahla ashe kana gida, zuwa nayi na duba kana lafiya kwana biyu banji ka ba", tashi Zahra ta yi tare da rike kugu tana kallon maman Sadik sama da kasa sannan ta ce", haba maman Sadik kina tunanin dan kin rigani kwana zaki rigani tashi ne? Na fa san abinda ya kawo ki",sosa keya maman Sadik ta yi sannan ta ce", ey wlh zahla dama ina so Naji ko ya batun wena fulawa", oh kudinki kika biyo kenan? Shiru maman Sadik tayi tana kallon Zahran cikin marairaita kamar zata yi kuka,dariya Zahra ta yi sannan ta ce", to na cinye bazan bayarba ke Ni fa wlh bazan iya ce miki ga inda kudin wainarnan suke ba,dan haka yadda nayi asara ke ma sai ki dauki na Annabi", daga haka ta suri buta ta yi bandaki tana cewa kuma mufukai masu labe ina sane daku,kuma baku ci bulus ba a cikin kwanakin da suka rage min saina yi waina da ku a gidan nan kafin na dawo mu dora daga inda muka tsaya",
Ai ko lola dake labe jikin labulenta tana kallon dramar Zahra da maman Sadik tana shan dariya tare da yiwa maman Sadik Allah ya kara tayi saurin komawa daki jiki na rawa, sun zamu kwana biyu sun dan huta yau kuma da kanta zata janyo musu masifa....
Maman Sadik na fita, maman daddy ta bi bayanta cikin sanda tana kallon hanyar banɗaki,
Zahra da fitowarta kenan ta hangota tana sandar fita, itama sai ta yi saurin aje butar tabi bayansu.
A soron ta tarar da maman daddy tana radawa maman Sadik hanyar da zata bi ta samu kudinta,tafa hannu Zahra tayi tana cewa ey lallai maman daddy baki so zaman lafiya da Zahra ba,bata saurari son kare kanta da take yi ba,ta koma ciki tana cewa tun yanzu ki ta nadi me dori dan da wuya idan banyi miki sanadin karaya ba.
Maman Sadik fita ta yi da sauri tana cewa me makon ka same Ni a gida sai ka tare Ni a nan maman daddy ? Tsautsayi ne wayyo zahla kayi hakuri,cewar maman daddy tana bin bayan Zahran,Zahra ko kallonta bata yi ba ta shige daki tana murmushin abinda ta tanadarwa YARBAWAN GIDAN kafin ta tafi dan a yanayinta tana buƙatar abinda zai sa ta nishadi.
Idon mama ta kwafa ta fita dan a yau take son koyawa maman daddy da lola hankali, bata son ta bari sai gobe saboda kayanta da za a kawo, dan a ranta ta shirya babu inda zata matsa bare suga babu idonta su yi mata sata,ita kuma maman Sadik dama tuni ta tanadi abinda zata yi mata( ah wannan shine a dake ka kuma a hanaka kuka).
Tana fita bata tsaya a ko ina ba sai wajen sale me wasa da macizai,tana zuwa ta gwargwada masa abinda take bukata,dariya sale ya yi ya ce", to yanzu Zahra ke idan na baki mataccen macijin za ki iya rikewa ne? Zan iya mana sale, abinda isa idan na samo na roba zasu yi saurin ganewa shi yasa nake son na gaske amma matacce", Tom shike nan yanzu kike bukata ko sai gobe,? Yanzu nake so sale", ta yi saurin bashi amsa", to ina zuwa ya fada yana shiga dakinsa,fitowa yayi hannunsa rike da ɗan akushi ya miƙa mata yana cewa da kin gama ki dawo min dashi dan ban cire komai nasa ba sabo ne yanzu na dawo daga farautarsa," yauwa salele godiya dubu malala gashin tunkiya," dariya yayi kawai tare da komawa cikin gida.
Ita ko Zahra hanya ta dauka ranta fes tana ji inama wannan basirar tazo mata lokacin da tana Company,da wlh AB zata sakawa in yaso taga karshen dakiya da miskilanci.......✍🏼
Mun shige su yau kuma Zahra ciwon zuciya zaki haifar mana ?dan abinda kike kokarin yi ya wuce ayi dori sai dai dashen zuciya🤣🤣
Wane tanadi a kayiwa maman daddy?
Har yanzu fa Zahra batasan wane yare ne mijinta ba🤣
Muje zuwa gidan Zahra nest pg ya zata kaya ne?
Ga dai siyam ga kuma mama🤣
Burin maman siyam zai cika kuwa?
Duk amsoshinku na nan tafe amma sai da kwarin gwiwar ku ta hanyar yi mana comments,
Dan Allah kar ku manta da yi min share ko dan mu samu ladan masu ciwon zuciya da hawan jini mu nishadantar dasu da labarin Zahra YAR GIDAN YARBAWA.
By FATEEMAH y ADAM
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*