YAR GIDAN YARBAWA

Pg25

by @zahrawriter12

.....sai da ta shigo gidan sannan mama ta ankara da fitar da ta yi.

Ina kika je? Mama ta tambayeta fuskarta a hade", maman Sadik na kaiwa kudinta fa"Zahra ta fada tana boye hannunta dake rike akushin mataccen macijinta,kwafa mama ta yi ba tare da ta kula da abinda Zahra ke boyewa ba,tana juyawa Zahra ta yi wuf ta shige can cikin daki ta ɓoye akushin sannan ta fito ta fara taya mama aikin kayan masu kawo lefe.

Sai magriba suka gama taje ta yi wanka tare da dauro alwalar magriba,sai da suka yi sallah sannan mama ta saka mayafinta tana cewa Zahra ki kula da gidan zanje gidan kaka ba jimawa zanyi ba", to mama a dawo lafiya ki gaida kaka, daga haka mama ta fice tana mai kara yiwa Zahra kashedi akan kar ta dawo ta samu ba daidai ba.

Tana fita Zahra ta janyo fantekar da mama ta zuba kajin da suka gama soyawa tana cewa, mama aike ma kin san sai kin ga ba daidai ba,yo ya za ayi ina ji ina gani na bari a bawa wasu wannan uban kaji bayan mu bamu ci ba,dan haka wlh ragowata zasu ci.

Nan fa Zahra ta sa naman kaza a gaba ta yi masa cin koshi tana ci tana rera wakar ( ayye yara yaraye ayye gamu dandali zahra sai ki rausaya kinji lokacin ki ne,kaza kaza duniya kayan dadi Allah na gani ba zan bar kaza ba....)tana yi tana lumshe ido tana gyada kai,sai da taji kamar zata yi amai sannan ta diba na Hafsah da nadiya tana cewa yanzu da zan samu gishiri da na kara musu in yaso idan da me hawan jini sai ya karu", dan jim ta yi tana tunanin yadda za ayi ta kara gishiri akan kajin can kuma sai ta saki tsaki tana cewa to ko na kara ma ai su sun saba ci yanzu haka ma idan an basu almajirai zasu bawa bari kawai na kyalesu punishment dinsu sai naje gidan,ta fada tana dariya tare da yiwa kanta kirari,ho Ni zahra yar mama me sa yarbawa gudu da zawo,Zahra yar gidan kaka da yaya al'amin mai kuriciyar zamani,sai kuma ta mike da sauri ta gyara wajen sannan ta fita daga dakin.

Babu kowa a tsakar gidan hakan ya yi mata dadi, lekawa dakin maman daddy ta yi ta hangota sun baje ita da yaranta suna cin amala da naman kazar da mama ta sammusu, dariya ta yi tana cewa hakan yayi min daidai abun da zai bada citta.

Komawa daki ta yi ta dauko mataccen macijinta,cikin sanda tawo kofar dakin maman daddy ta tsaya, sai da taga maman daddy ta dauko naman ta fara rabawa yaran ta rage kato tana shirin kaiwa bakinta, saiko Zahra ta bude akushin ta watsa mata macijin,saitin kuwa ya yi daidai dan bai tsaya a ko ina ba sai fuskar maman daddy kamar kuma me rai sai gashi sulbinsa yasa ya sauko jikinta.

Zaro ido maman daddy ta yi, hannunta da yake saitin bakinta da nama tuni ya fara wata irin karkarwa shi bai sauka kasa ba shi baije bakin ba,a hankali ta fara kallo kasan cinyarta dan taga meye abun da ya wado mata,eho ta fada lokacin da ta yi arba da macijin kwance a kan cinyarta, ihu tasa tana kallon kamar yana tafiya a jikinta,gashi ta kasa mikewa ta yi ta kanta yaranta kuwa tuni suka watse suna ihun muciji.

Kankace me kowacce ta kulle kofarta,ita ko lola dama yanzu tun abinda ya faru da magriba ta yi take rufe kofarta,dan haka yanzu bata san me ke faruwa ba saboda kofarta a rufe take.

Maman daddy kuwa cikin kururuwa take fadin, shike nan maman daddy mutuwa yazo duniya ze beri be shirya ba,ya ilahil alamina ka kawo helpin gida ya lalace daga fetalwa se maciji ga masifar Zahla na yo daban na gobe daban, wayyo maman daddy ze mutu be yi kudi ba,'

Zahra da taga maman daddy ta shiga sumbatu gashi ta kasa mikewa, kawai sai ta yi sanda ta shige dakin ta dauki macijin tare da shammatarta ta kuma wurga mata shi aiko sai a cikin rigar shet dinta me katon wuya,wata irin yar dungure maman daddy ta yi sai ko ji kake kal alamun anyi targade a wani wajen,bata kula da gurdewar da ta yi ba ta kuma hantsilawa da ka sai gata a waje kafin ta mike tsaye tana ihu tana cire kayan jikinta tare da tsalle dan macijin ya fita,cewa take shike nan maman daddy ya mutu.

Masifa ya shigo gida Bala i kala kala,ga fetalwa ga Zahla ga kuma mashiji, wayyo Allah ye mana magani kar maman daddy ya mutu",Zahra me zata yi ba dariya ba, idanunta kuwa kamar me kuka saboda dariya,tana ganin haka ta dauki macijinta ko tsoro bata ji ta nufi window lola ta bar maman daddy da burgima dan har lokacin bata gama yarda macijin ya bar jikinta ba.

Lola na kwance ta saka filo ta toshe kunnenta dan tsira daga jin duk wani bala I da yake faruwa a cikin gidan, jikinta kuwa babu abinda yake sai rawa dan a tunaninta daren yakin bikin Zahra ne ya kuma dawowa,bata Ankara ba sai jin wani abu me sanyi da tsantsi ta yi ya fado a wajen ƙafarta,da sauri ta mike tana dube dube har bata sani ba ta dauko shi da hannunta.

Wata gigitacciyar kara ta yi tare da wancakalar dashi, kafin kace me gumi ya jiƙata kamar jiran kadan take sai ga fitsari, da gudu ta mike ta nufi kofa ta zare sakatar ta fito tana kururuwa,dariya Zahra tayi tana cewa ya dai lola ke da kika rufe daki kina ganin kin tsira ya da fitowa?

Ina lola bata san me Zahra take fada ba nuna kofar dakinta kawai take tana fadin help help,fadawa dakin Zahra da gudu ta dauko macijin tana cewa bari na temaka muku na fita dashi dan Ni nasha maganin saran maciji",

Thanks zahla yo kayi abin kilki,lola ta fada tana kallon jikinta da yake jike da fitsari,maman daddy kuwa sai da taga Zahra ta fita da macijin sannan rayuwarta ta fara dawowa daidai har ta fara jin radadin targaden da ta yi, tana zaune tana faman yarfe gumi ko motsi ta kasa yi,dawowar Zahra yasa suka maida hankalinsu kanta,sai kawai suka ganta dauke da akushi a hannunta dan sai da ta fita zauren sannan ta saka macijin a ciki ta dawo.

Da kallo suka bita ganin tazo tsakiyar tsakar gidan ta bude akushin,duka suka zabura har ragowar da suka fito saboda jin Zahra ta fita da macijin,ido waje suke kallon macijin da yake a mace,yemi ce ta yi karfin halin cewa zahla kaine ka iya kashe maciji?

Tashi tsaye ta yi tana kallonsu kafin ta kwashe da dariya har da rike ciki sannan ta nuna lola da maman daddy tana cewa ai dama mataccene kuma nice na kawo shi saboda ku", aiko kuka maman daddy ta saka tana yarfa hannunta da har ya fara kumbura,Zahra ta cigaba da cewa komai ma nice har aljanar da tazo muku ranar bikina duka nice, na gaya muku ne dan kusan cewa babu abinda Zahra bazata aikata muku ba in dai har baku canja hali ba, kuma wallahi ko na bar gidannan kar ku yi tunanin na barku dan duk abinda ku kayi sai na zo Nima nayi nawa ehe", daga haka ta kwashe akushinta ta yi daki tana juya musu baya cike da salon iskanci.

Babu wacce ta iya magana,saima komawa dakunansu da suka yi,dan kuwa yau sun kara sallamawa wannan bafulatanar dajin amma fa azuciyarsu Allah ya isa da tsinuwa suke ta zabgawa Zahra ko wacce tana tuna halin da ta shiga a waccan ranar.

Kan mama ta dawo ma tuni Zahra ta yi baccinta hankali kwance,mama bata duba barnar da Zahra ta yi mata ba dan a gajiye ta dawo itama, shi yasa wanka ta yi kawai ta kwanta dan Abba ma bai shigo ba yana waje.

Washe gari aka tashi da hada haɗar tarbar lefen Zahra,ga mamakin mama fitowa kawai ta yi taga su lola da su yemi sun gyara gida gaba daya sai kyalli yake,cikin mamaki mama ta yi musu sannu,bata tsananta mamaki ba dan tasan wannan aikin mutuniyarsu ne ko bata sa su ba zasu iya yi dan gujewa fitinar zahra.

Itama Zahra da taga abinda su kayi dariya kawai tayi ta wuce ta je tayi wanka,sai da ta shirya tsaf kamar abin arziki tasha kyau kamar ka saceta dan Zahran tamu ba daganan ba komai yaji Masha Allah.

Da kanta ta fita ta mayarwa da sale macijinsa har da bashi kyautar dari biyar,daga nan ta wuce ta dauko me gyaran targade.har dakin maman daddy suka shiga wadda ke kwance hannu ya tashi sosai sai nishi take gwanin tausayi,Zahra ce ta riketa tana ta ihu aka gyara mata targaden,yana gamawa ya fice bayan Zahra ta sallameshi, sosai maman daddy taji dadin hannun,dan lokaci daya ya daina yi mata azabar da ya kwana yana yi mata,Zahra ita ta yi mata komai ta gyara mata dakin tayiwa yaranta wanka sannan ta basu abin kari suka karya suka tafi makaranta.

Duk abinda Zahra take yi maman daddy binta kawai take da kallo cike da mamakinta,su kansu su lola abin ya basu mamaki da kuma burgesu,sai kawai suka ji duk abinda Zahran ta yi musu ya goge dan dama su kam suna son Zahra,dan suma shidane akan kyawawan halayenta kyauta tausayi da son ibada.

Karfe sha daya masu kawo kaya suka karaso a wasu jibga jibgan motoci kafin kace me unguwar yarbawa ta dauka,baran ma yadda aka ga ana ta shiga da akwatuna har saiti biyu wanda suke cike taf da kayan arziki.

Cikin kankanin lokaci bayan masu kawo lefe sun tafi gidansu Zahra ya cika da yan ganin kwaf,

Kuce min ina Zahra mana?

To Zahra dai na can kofar gida tsaye ita da kawayenta nadiya da Hafsah,su dai basu san me yasa Zahra ta tsaida su a nan ba,kuma basu tambaya ba dan gudun masifar Zahra,nadiya gajiya ta yi da tsayuwa hakan yasa ta dan tausasa murya ta ce", Zahra wai me muka tsaya yi a nan ne? Kafin Zahra ta bata amsa wata makociyarsu ta fito daga gidan tana cewa kai Masha Allah lefe sai sam barka Allah ya bawa yayanmu ya taku", to angode Zahra ta fada tana kara tare hanyar yadda baka isa wucewa ba dole sai ta matsa,matar me suna ladi ta ce", to dan matsa zan wuce", rike kugu Zahra ta yi sannan ta kawar da kanta tana cewa a'a fa ladi doka ce yau babu me fita daga gidannan ba tare da na cajeshi ba,dan yadda aka zubo min kayan yanmatacinnan da yawa nasan wata zata yi zaton ba za a gane ba ta yi mana dan hali shi yasa na yi wannan dabarar, dan yau ko kaka ce zata fita sai na caje ta ato,ta karasa fada tana kara kawar da fuskarta dan kar ma taji nauyin ladin.

Rike baki ladin ta yi cike da mamakin da Zahra ta kasheta dashi,har zata yi magana sai kuma ta tuna wacece Zahran ta wani bangaren kuma idan ta ki Zahran zata yi tunanin tayi satar ne,dan haka ta gyara tdayuwarta tana cewa Tom shike nan gani cajeni".

Kin nemi maslaha Zahra ta fada tana kallon su nadiya,me ye kuka tsaya kuna kallona kuzo mu cajeta,ke kuma ina fata kin gane dalilin tsayar daku da nayi anan? Ta fada tana kallon nadiya,a'a ke dai ki caje ta amma banda mu", cewar Hafsah tana matsawa gefe", ey ai dole kuce haka tunda ba kayanku ba ne,kuma wallahi duk wacce bata taya Ni ba sai nayi mata addu'a a sace kayan lefenta kala uku", ba ta kara sauraronsu ba ta fara ƙoƙarin caje ladi...

Da gudu Amina da ta zo fita taji ana wannan dramar ta koma cikin gidan ta sanar da mama abinda Zahra ke shirin yiwa ladi har ma da ita da ta tabbatar tana gamawa da ladin kanta zata dawo.

Da sauri mama ta mike tana salati da tafa hannuwa,oh Ni bilkisu Allah ya bani 'ya,ta fada tana zura hijab da takalmi.

Acan kofar gida kuwa Zahra tsaf taga lokacin da Amina ta fito ta koma da gudu,kuma tasan me ta koma yi dan haka sai kawai ta yiwa ladi murmushi tana cewa kai ladi wai kin dauka dagaske caje ki zanyi? Kin san fa yau dole sai da nishadi saboda muna cikin farin ciki", aiko ladi ta washe baki tana cewa aiko haka ne yar albarka to Allah ya bada zama lafiya yasa albarka kinji", Amin ladi ,Zahra ta fada tana bata hanya.

A fusa ce mama da komai ya faru akan idonta ta dubi Amina tana cewa Wallahi karki bari Zahra tasan abinda kika yi mata", daga haka mama ta koma gidan tana sakin tsaki da mitar halin gulma irin na mutane,saboda tana son yin gulma bata ma tsaya ta fahimci kan zancen ba.

Amina ki kiyaye haduwarku da Zahra ehe.

Kuyi hakuri naso mu tare a wannan PG din to amma rubutunne yazo da haka ,dan haka mu hade a nest pg.......✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*