YAR GIDAN YARBAWA

Pg27

by @zahrawriter12

*SUBY COLLECTIONS &* *MORE....*

*Ina kuke? Nace ina kuke?*

*Ey *nace* *kowa ya zo* *kusa* *mata maza iyaye** *yayyaye da duk* *me son fita kunya,*

*Ina iyayen da suke shirin* *aurarwa?*

*Ina matan da suke shirin* *yin tariya?*

*Ina mijin da yake son* *burge matarsa?*

*Ina dan da yake son* *farantawa Mahaifiyarsa* *ko* *kanwarsa?*

*To duk ku matso nan dan* *kuwa sauki ya zo* *muku ta hanyar* *shahararriyar yar* **kasuwar nan SUBy* *COLLECTIONS & MORE* *tana saida kayan* *daki na kece raini* *kuma na fita* *kunya,ga kayan kiching* *na kere sa a duk* *abinda kuke bukata* *a har kar gida* *tana da shi,kuma masu* *son burge mazajenku ko* *masu son burge* *yanmatansu ta bangaren* *kayan sawa* *zaku iya samunta, tana* *hada lefe na kece raini* *da fita kunya, kun dai san* *in aka ce lefe to ana* *nufin komai da* *komai ko?*

*Haka a bangaren kayan* *yara nan ma ba* *abarta a baya ba kai na* *takaice muku labari dai* *takenta shine komai da* *ruwanka dan haka kawai* *ku taho ku* *tuntube mu dan faranta* *ranku,*

*A bangaren kayan yaji* *ma duk ba abarta baya* *ba, yajin daddawa yajin* *tafarnuwa farin yaji da* *kuma kayan kamshi* *masu *kankaro martabar* *mace wajen* *miji dan babu* *ke babu** *kunyar zuwan* *abokan miji cin* *abinci...ku dai ku* *nememu kawai mu kuma* *zamu fidda ku* *kunya*

*Zaku iya neman ta ta* *wannan lambar kamar* *haka*

**** ko* *****

*Muna nan muna jiranku* *mutanen* *amana.*

*Kar ku manta da sunan* *fa*

*SUBY COLLECTIONS &* *MORE........*

........Zahra fa ko irin ɓoye fuskar nan da ake yi bata yi ba,dan suna shiga motar ta ɗago kanta ta fara kalle kalle ,a zuyarta tana cewa bari na ga ta inda aka shiga kar naje na kasa dawowa gida.

Dan zungurinta Mami zainab ta yi tana cewa cikin yin kasa da murya, haba my love rufe fuskar mana ko wace amarya da kunya aka santa",tura ƙaramin pinkinsh lips dinta ta yi tana cewa Ni kam Mami ai ba auren kauna a kayi Mani ba",

Dan Allah ki rabu dani naga hanya kada idan sun koroni na kasa zuwa gida", Mami na jin haka ta ja bakinta ta zuge al'amarin diyartata kam sai du a i.

A haka suka karasa mention din nasu AB wanda yasa Zahra buɗe baki da ido da hanci tana kallon luxery House,Mami ce ta buge bakin tana cewa WLh Zahra idan baki nutsu ba zan tafi na barki ko shiga gidan bazan yi ba," yi hakuri Mami na daina idan kun tafi na fito na kalli aljannar duniya,anya kuwa Mami zan iya dawowa gida duba fa kiga irin wannan gida sai kace ba a duniya ba ",da sauri Mami ta rufe bakinta ganin sun tsaya a wata kyakkyawar haraba me tsananin kyau kamar ba wajen aje motoci ba.

Wata kyakkyawar mata ce wadda kallo daya za kayi mata kasan balarabiya ce,ta zo har gaban motar ta buɗe musu fuskarta ɗauke da ƙawataccen murmushi tana cewa oyoyo my dougter barkanku da zuwa sannunku da zuwa,ta fada tana rungume Zahra da ta ke ta kokarin danne halinta,dan bakinta fal yake da magana,uhmm wato dai shi wannan Ab din dama gadon kyau ya yi shi yasa yake shan ƙamshi kamar wani sarki,dan dai wannan da alama ko ba mamansa ba ce to jininsa dan suna kama matuka da gaske.

Janta da taji anyi mutane suna ta buɗa yasa ta dawo hayyacinta,wanka aka shiga yi mata da turare ta ko ina tun kafin su shiga cikin main falon,wasu al'adu da suke gabatarwa yasa Zahra da Mami da su nadiya da kaka da sune yan rakiyar amarya yasa suka tabbatar da cewa sun shigo ahlin larabawa.

Ashe su Zahra basu ga komai ba dan kuwa duk da cewa da mutane a falon sosai hakan bai hanasu ganin duniyar dake cikinsa ba,da kyar suka dinga dauriyar barin kauyancinsu a matsayinsu na dangin amarya,Zahra ma haka ta dinga dauriya har aka shiga da ita wajen Ammi,ashe matar da ta taro su kanwar Ammi ce.

Da sauri Ammi ta kama hannun Zahra ta rungumeta har da su sumbata ,daga nan aka shiga hidima kala kala,duk motsin da Zahra za tayi idon Mami na kanta wanda suke cike da gargadi dole yasa Zahra ta nutsu dan tana shakkar mamin saboda kaunar da take mata shi yasa take daga mata kafa.

Sosai a ka gabatar da shagulgula wanda suka kayatar da Zahra da danginta harma yasa bata yi wani abu da zai basu kunya ba,hakan ya musu dadi kuwa,lokacin da aka zo tafiya dasu ko kwalla Zahra ba ta yi ba sai dai ta nemi alfarmar nadiya da Hafsah su kwana gobe sai su tafi,har Mami zata yi fada sai Ammi ta dakatar da ita da cewa babu komai su zauna, dole suka hakura suka tafi da goma ta arzikin da aka hada musu.sai da Mami taga ta fito daga gidan lafiya ba tare da Zahra ta yi abinda zata basu kunya ba sannan ta saki ajiyar zuciya da fatan Allah yasa kar ta nuna hali ko na kwana biyu ne.

,,,tun daga nesa maman Sadik ta hango Sadik zaune a saman bench din bakin shagonta yana kuka ,aiko har cin tuntube take wajen kara sauri tana zuwa ta fara tambayarsa abinda ya faru a dan ruɗe dan a cikin kwana biyun nan dama duk hankalinta ba a kwance yake ba, kullum da tunanin ta inda zahra zata bullo mata take kwana take tashi.

Zama ta yi kusa dashi tana cewa Sadik meye ne kana kuka haka ina tambayanka babu amsa",cikin yanayin tasa Hausar ya sanar da ita abinda ya faru ko yace abinda Zahra ta yi mata.

Hannu kawai ta ɗora aka ta zunduma ihu kafin ta zube kasa a sume,da sauri mutane suka yo kanta a ka fara bata taimakon gaggawa, dakyar dai aka samu ta farfaɗo,sai dai yadda ta farfado din abun gwanin tausayi,dan ko magana ta kasa yi haka nan ta dinga yin wani abu kamar wata zararriya sunan zahra ne kawai ke iya fita daga bakinta.

Sadik ne ya iya sanar da mutane abinda ya faru, sai ga wadanda yaransu suka kai musu abin arziki suna cewa tabbas ko shakka babu wane ya shigo da kaza wance ta kawo kaza ta ce", Zahra ce ta raba musu sadaka ashe karya suke banna suka taya ta yi", daga karshe dai kama maman Sadik aka yi dakyar suka Kaita gida dan abun ya fara taba kwakwalwarta dan fa zahran ba karamar banna ta yi a shagon ba.

Sai da aka kaita gida ta fara kuka tana dambarwa da son fita wai zata je wajen maman Zahra bazata yarda ba sai zahla ya biyata,mijinta ne ya hanata ya ce", babu inda zaka idan kaje ka kuma jawo wani abu fa?

Zubewa kasa ta yi tana burgima da tumami tana cewa,oh baban sedik zahla ya shusheni zahla shegen yalo mugun yalo,oh Zahla ya kashe maman Sedik, maman Sedik bashi da komi bashi da jari. wayyo maman Sedik ya zama abin tosayi zahla baka da tosayi,"

Shima dai baban sadik din rabuwa da ita yayi dan yaga abinnata bana karewa ba ne,karshe dai sai kulleta ya yi a gidan sannan ya iya fita.

.......su Zahra amarya ana can ana rakashewa da kayan dadi ta bar maman Sadik da dan karamin hauka.

Duban nadiya ta yi tare da cewa, banzaye da ba kuna ta wani nokewa ba ai yanzu kun gane gata nayi muku da na roki a barku ku kwana,yanzu ba gashi kuna burushi da kaza ba", dariya Hafsah ta yi kana ta ce", wlh kuwa zahra kin kyauta tunda gashi muna dandalar arziki",

Nadiya tace," yo ai dan ma ba zama zata yi ba ai da dukan mu sai munyi arziki ko na kwana goma ne ", Zahra ta ce" ai yanzu zuciyata rawa take akan tunanin yadda zanyi na bar daular nan,nadiya ta ce ", to ga shawara in dai zaki dauka" fadi Naji idan ta dauka ce zan dauka idan bata dauka nace zaki sha mari kuma duk sai kin biya abinda kika ci ko da ta hanyar yin amai ne",zaro ido nadiya tayi tare da cewa haba Zahra kece fa kika sa aka barmu kuma yanzu kice sai nayi aman abinda naci",ey WLh sai kin yi cewar Zahra tana sude hannunta da ta gama cin farfesun ragon ruwa me shegen dadi,to na fasa baki shawarar, nadiya ta fada cikin karyar da kai, wallahi sai kin fada ko kuma yanzu a ji kanmu a gidannan ehe" wani miyau nadiya ta hadiya kafin ta ce", to dama cewa nayi me zai hana ki zamanki a nan din amma kuma ba a ma tsayin zaman aure ba,

Wani dan tsalle Zahra ta yi sannan ta bawa nadiya hannu suka tafa ta ce" shike nan wallahi haka za ayi idan yaso sai na sa ya sake ni saki uku, idan suka ce na tafi gida ni kuma zan kafe akan zaman idda zanyi. ai dama haka ake yi ko? Ta karasa maganar da alamar tambaya,girgiza kai Hafsah ta yi tace ai kuma saki daya ko biyu akewa zaman idda ba malam abu ya gaya mana ba, Zahra ta ce", ke dalla rabu dasu irin wannan masu kuɗin da kike gani ba wani ilmin addini ne ya ratsasu ba dan haka juya karatun zan yi yadda baza su gane ba,shewa suka sa ta samun mafita daga nan suka cigaba da Shagalinsu, hatta da kayan da suka bata masu aiki ne suka zo suka kwashe suka gyara, daga nan suka bi lafiyar lafiyayyan gadon da yaji shimfidu na alfarma,nan bacci me nutsuwa ya kwashesu dan haka sai muce asuba tagri ZAHRA n Ab....

Ko da asuba da suka yi sallah komawa bacci su kayi.

Kafin su tashi tuni an jere musu kayan kari a karamin dinning ɗin dake dakin ta can bangaren hagu.

Suna tashi wanka su kayi Zahra ta janyo akwatin da aka taho mata da kayanta dikkaku ta dauko masu kyau da tsada ta bawa nadiya da Hafsah ta ce su saka,kallonta suka tsaya yi da mamaki duk da cewa sun san wannan kadan daga halin Zahra ne, nadiya ta ce", amma Zahra bai kamata ki bamu aron kayanki a yanzu mu sa ba idan da muna saka kayan juna ai kinga yanzu kayanki manya ne masu tsada", Harara Zahra ta zabgawa nadiya kafin tace dallah Malama idan zaku sa ku sa ina ruwana da tsadarsu ai kin san Ni tsadar abu bai hanani yin kyautarsa dan haka Ni ba aro na baku ba kyauta na baku,idan kunje gida ma akwai kayan da mama zata baku", zasu yi magana ta yi saurin katsesu da cewa bana bukata in dai godiya ce ku rike kayarku kuje addu'a kawai nake bukata.dole suka maida yawu suka hadiye suna Mai yi mata fatan alheri.

Suna cikin karyawa Amira ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi, zama ta yi suka gaisa da su nadiya cikin mutunci, sannan ta jiya wajen Zahra tana cewa Barka da safiya amaryarmu,hadiye ragowar dankalin da tasa bakinta ta yi tana cewa yauwa kanwarmu dan nasan ba zai wuce haka ba duk da naga bakwa kama da wannan me kalar kasan yayannaki", dan bazan boye miki ba wallahi ya fi ki kyau,amma fa kar kice sonshi nake yi ato.murmushi kawai amira ta yi tana cewa ai dama nasan ya fini kyau,da sauri nadiya da Hafsah suka fara jan Amira da hira dan dauke mata hankali daga kan Zahra da ta fara sakin layi tun kan aje ko ina,

Suna gamawa Amira ta ce ",to ku tashi muje su Ammi na jiranmu dama ita tace nazo na taho daku,Hafsah ta ce ", to amma mu gida zamu tafi ko? Ey za a sa yanzu a kaiku,dan kune ka dai bakin da kuka rage dan yan ƙatar tun asuba jirginsu ya tashi, mikewa Zahra ta yi tana cewa irin wannan faka_faka haka sai kace ana korarsu ko bari gari ya waye ba zasu yi ba", babu wanda ya tanka mata suka fita,dan su nadiya sun kagu su tafi tunda Zahra ta fara fidda hali.

Daddy Ammi maman siyama sai siyaman su suka tarar a falon,waje suka samu a kasa suka zauna, sannan suka fara gaishesu,cikin farin ciki daddy da Ammi suka amsa,siyam kuwa banda Harara babu abinda take bankawa Zahra duk da kashedin da mamanta ta yi mata akan kar ta dinga nunawa Zahra tsana a gaban mutanen gidan to amma ganin Zahra da ta yi matsayin matar Ab din yasa ta kasa jurewa.

Sai yanzu ta fahimci abinda jafar yake nufi da maganganunsa na ranar,wata irin tsana taji ta kara yiwa zahran yadda take ji ko kasheta zata iya yi ba tare da fargaba ba.

Ammi ce ta mikawa su nadiya wata jaka me shegen kyau tana cewa to yammatan amarya mun gode Allah ya kaimu naku auren ya baku mazaje na gari, maza kuje driver na waje yana jiranku,Amira kuje ki rakasu, Tom Ammi Amira ta fada tana kama hannunsu suka kike duka suna ta yiwa Ammi da daddy da ya basu kudi masu yawa godiya,da sauri Zahra ta mike tana cewa Nima zan raka ku, kafin ma Ammi ta yi magana tuni Zahra ta riga su yin gaba dole suka rabu da ita sai ma dariya Ammi ta yi", siyam kuwa wata uwar tsaki ta saki tana cewa yan kauye kawai,buge bakinta maman siyam din ta yi tana cewa,baka da kilki siyama,su dai Ammi basu ce komai ba sai jiran dawowar yar balaja un surukarsu da suke yi.

Motar da aka tafi kai su nadiya na fita wata hadaddiyar motar na sawo kai sai wata bayanta,jan hannun Zahra Amira ta yi tana cewa taho mu koma ga su yaya AB Nan sun dawo ", fincike hannunta ta yi tana cewa babu inda zani", ke baki san halin yaya AB ba ko Ni da nake kanwarsa baya son ganina haka nan a waje bare ke matarsa wallahi ni zaiyiwa fada.

Zahra ta ce me ya shafeni da fadan da zai yi miki ya dakeki ma Ni bata shafeni ba,Ni ce dai ya taba Ni wallahi sai nayi masa kwalen yarbawa a wannan damejin fuskar tasa.

Zaro ido Amira ta yi baki bude ta ce", kai Zahra ki iya bakinki ya da zaginmu haka yanzu fa Kema kin zama beyerabiya tunda kin auri BEYERABE, kuma surukar BEYERABE wata irin juyowa Zahra ta yi tana kallon Amira baki bude hanci bude.

.... daidai lokacin jafar ya budewa ab mota ya fito idanunsa sakaye cikin farin galashinsa dake kara bayyana asirin kyawunsa da kwarjininsa........✍🏼

Tofa Zahra sai ki nemi saki da hujja tunda kin auri kabilar da kika fi tsana 🤣🤣

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *YAR GIDAN YARBAWA*