YAR GIDAN YARBAWA

Page31

by @zahrawriter12

.......Binta da kallo suka shiga yi ganin tana ta fama da mayafi akan kokarinta na ganin ta yafa shi kafin ta fita,tana gab da fita ta juyo fuskarta ɗauke da murmushi ta ce", Ammi mun tafi Company sai mun dawo", wane irin Company kuma Zahra? Cewar daddy cikin mamaki,dan tura baki ta yi tare da cewa daddy dama fa Nima ina aiki a Company shi ne nace zanje shi kuma ya ce na ɗauko mayafi mu tafi, shi Abrahab ɗin? Inji Ammi tana mikewa da nufo zahran,ey mana yanzu ma suna waje suna jira na zamu tafi,Zahra ta fada tana bin Ammi da ta rike hannunta suka fita dan Ammin ta tabbatar da shirmen da Zahra ke mata...

Sai kuma me? Suna fita suka ga wayam babu ko daya daga cikin motocin AB din saima shatin tayoyin motocin da suka gani alamar dai sun fita,duban Zahra Ammi ta yi ta ce", to yana ina ko a waje suke jirannaki? Dube dube Zahra ta shiga yi kafin cikin son fashewa da kuka ta ce", wallahi Ammi shi ne ya ce na ɗauko mayafi kato mu tafi shine kuma ya gudu ya barni", sai a lokacin Ammi da daddy da ya biyo bayansu dan shima fitar zai yi suka gano wayo AB ya yiwa Zahra saboda gudun rugima,to amma dai ga dukkan alamu an gudu ba a tsira ba ne,dan kuwa , Zahra zubewa ta fara ƙoƙarin yi a gurin zata yi burgimar tata da ta saba,Ammi ce ta yi saurin kamata ta hanata kaiwa kasan,tana cewa yi hakuri baby AB bai kyauta ba kuma zai dawo ya sameni haka kawai dan me zai yi miki wayo ba Gara ya fada miki gaskiya ba,kuka Zahra ta fashe dashi tana buga kafa duk da tana jikin Ammin hakan bai hanata kukan tabarar da ta saba ba,dan wannan a zaune take duk Zahra zata yi kuka sai ta yi wannan shure shuren...

Daddy ma lallabata ya shiga yi kamar wata jaririya,daga nan ya ce", da Ammi su wuce ciki shima zai wuce office,to Allah ya kiyaye Ammi ta fada tana jan Zahra da har yanzu bata daina kukan ba,suna shiga falon ta kuma fashewa da kuka tana cewa Ammi kuma ya tafi tare da wannan mara lafiyan idan haka ne ita me yasa ta je bayan ma bata da lafiya,maman siyam da ta cika ta batse tun dazun da ta leka taga yadda Zahran ke yi su kuma sun wani shiririce wajen lalashinta ta ji kamar ta je ta shakesu gaba ɗaya.

A dan fusace ta ce ", ey ai shi siyam yar uwarsa ne ko kana da ikon raba hanta da jini ne?

Kallon Ammi Zahra ta yi cikin kebe baki ta ce ", Ammi kice ta daina maida Ni namiji kuma me yasa daddy da Amira su basa yin irin wannan Hausar naga suma YARBAWAN ne,kuma shima wannan yayannasu kurma ba ya yi amma ke sai ki ta damun mutane da kai kai", waro ido mama ta yi tana cewa kai yaro zan koya maka tarbiyya idan baka dashi fa", buya ta yi a bayan Ammi tana cewa kiyi hakuri Ni ba rashin kunya na miki ba kawai tambaya nayi", wani uban tsaki mama ta yi tana mai barin wajen dan idan ta cigaba da zama takaicin Zahra zai iya sumar da ita.

Amira kuwa babu abinda take sai kunshe dariya saboda yadda dramar Zahra da mama ta bata citta,zama Ammi ta yi tare da janyo Zahra jikinta tana cewa dan Allah ki bar kukannan dougter sai fa kanki ya yi ciwo,to me yasa ya tafi ya barni ta fada tana kuma kwabe fuska.

Sosai Ammi ta yi ta fama da rigimar Zahra kamar wata yar yaye, mama kuwa tana can tana kulla hanyar da zata bi ta gyarawa Zahra zama ta kuma raba ta da gidan cikin sauki,to amma a nazarin da ta yi dole sai ta hadiye takaicin Zahran a ranta sannan zata samu yadda take so,to amma ta yaya zata iya danne tsanar da take yi mata har ta iya janta a jiki dan cimma burinta? Wata zuciyar ta ce haka zaki daure in dai kina son biyan bukata, da wannan tunanin ta yi amfani ta mike ta fita aka ci gaba da rarrashin Zahra da ita duk da idan Zahra ta yi wani abun Ammi ta biye mata sai ta ji kamar zata kasa daurewa.

A haka har bacci ya dauke Zahra shine suka samu saukin yin wasu sabgigin,oh yaro sai segen rigima sai kace yaron goye mama ta fada da dakakkiyar fuska dan kar Ammi ta fassara maganar da wani abu,Ammin dai bata ce komai ba sai kama Zahra da ta yi ira da amira su ka kaita dakin Ammin suka kwantar tare da rufeta da blanket cikin lallabawa kamar wata kwai.

......samun kansa ya yi da tunanin halin da zahra zata shiga idan ta dawo taga ya tafi,shafa kwantacciyar sumarsa ya yi yana mai lumshe idanunsa shi kansa yana mamakin kansa saboda canjin yanayin da yake samu shi da sam damuwa ko tunani bai taba bayyana akan fuskarsa ba, duk tsananin zafi ko sanyin da yake ciki na zuciya ba zaka taba fahimta ba saboda kwarjininsa da nutsuwarsa da ke boye duk wata damuwarsa ko tsananin faruncikinsa,amma sai gashi a kwanakin haduwarsa da Zahra duk ko mai yana sauyawa daga gare shi ko me dalilin hakan ya yiwa kansa tambayar da bashi da amsarta,dan tabe baki ya yi yana mai murza goshinsa ko zai samu yanayinsa ya dawo dai dai...

A daddafe ya kai hudu ya tattara ya fito daga office din,cike da mamaki siyam take kallonsa bata iya cewa komai ba har ya fice cikin kamewarsa ba tare da ya kalli inda take ba,kambu wai tafiya zai yi ? Ko dai wani wajen zasu je? To idan wani gun zasu ai dole za taga jafar ya zo,barin wannan tunanin ta yi itama ta kwashe jakarta da wayoyinta ta bi bayansa dan komai ya faru akan idanunta idan ma gidan zashi su koma tare yadda suka fito tare ta yadda ko motar gerd ɗince ta kuma shiga.

Shima jafar kamar yadda siyam ta yi mamakin fitowar AB din shima haka ya yi, da sauri suka tashi shida josuwa da suke zaune waje daya suka nufosa cikin girmamawa haka ragowar gerd dinsa da suke baje a cikin Company suka yi hanzarin fara shirin fita duk da basu da tabbacin fitar zai yi,ganin ya nufi mota kai tsaye yasa duka suka fahimci tafiya ce,dan haka kowa ya yi shirin tafiyar josuwa ya yi saurin buɗe masa mota ya shiga jafar ya shiga gaba, ganin haka yasa siyam din saurin shiga motar da tazo a ciki nan aka yi comver suka bar cikin Companyn.

Dake suna gane maganar kurmancinsa ba tare da sun tambayesa ba suka dauki hanyar family mension dinsu.

A daddafe Zahra ta tashi ta yi sallar la'asar tare da wanka saboda zazzaɓi da ciwon kan da ya yi mata rigif,abinci ma dakyar Ammi ta lallabata ta ci kadan sannan ta ci ayabar da Ammi bare mata dan a yau daya ta fahimci zahran na son yaba sosai,zamewa ta yi ta kwanta ba tare da ta iya saka karamar rigar da Ammi tasa Amira dauko mata ba,Ammi bata takura mata ba dan sosai Zahra ta yi tasiri a zuciyarta jinta take kamar ita ta haife ta dan haka nan halin Zahra ke burgeta da sata cikin nishadi duk wahalar da ta bata yau amma bata ji haushi ko gundura ba sai ma lallabata da take ta kokarin yi cikin tausayawa da nuna kauna...Ammi na shirin kiran AB a waya sai kawai ta ji dirin motoncinsa , ta window ta leka ta tabbatar sune murmushi kawai ta yi ta dawo ta gyarawa Zahra rufarta, sannan ta fita daga dakin...

A bakin coridow suka hadu da mama zata duba Zahra a fadarta,Ammi ta ce, ai ina ga ta koma bacci amma dai duba ki gani daga haka Ammi ta bi dogon coridow inda zai maida ta main falon,da harara mama ta bi ta tana cewa duk zan yi maganinku bari dai na gama da wannan makirin suruki naku...

Zahra dake kwance tana jiyo Muryar mama dan mama da karfi ta yi magana atunaninta Zahra bacci take yi,kwafa Zahra ta yi duk da yadda take jin jikinta hakan bai hanata watsawa hanyar shigowa dakin harara ba tana cewa kafin kiyi maganina Ni zan fara yin naki maganin,juyawa ta yi ta dauki bawon a yanar da ta ci ta yi saurin jefawa a hanyar ta wajen kan tayils din bakin kofar,ta koma ta kwanta tana jiran sakamako,

Aiko ko bata fi sakan dari da jefawa ba ta ji tim tare da a zababban ihun mama saboda tsananin buguwar da ta yi a duwawunta,daidai Ab yana sako kai dakin saboda yana shigowa Ammi ta sanar da shi Zahra na dakinta bata da lafiya ya je ya dubata,duban mama da ke ta kwarara ihu hannunta da dafe da kugunta ya yi sannan ya kai dubansa kan Zahra da ke rufe da blanket kamar me bacci jin jina kai ya yi tare da tsallake maman ya shige dakin yana ci gaba da bin zahra da kallo.

Ammi da Amira har da siyam suka karaso da gudu ammi cikin tashin hankali dan atunaninta wani abu ne ya faru da Zahra tana zuwa ta tarar da mama janbare a ƙasa tana hawaye hannunta rike da kugu tana kiran kugunta ya karye,ajiyar zuciya Ammi ta yi kana ta fara temakon siyam da ke kokarin tayar da maman tsaye tana cewa garin yaya mam... Sai kuma ta hangi bawon ayaba daga can inda kafar maman take dauke bawon ta yi cikin mamaki ta ce, subhanalla me ya kawo bawon ayaba nan har kika taka?Ab na jin haka ya karasa jikin gadon tare da janye blanked daga saman kanta ya tsirawa fuskarta ido sai ga idanunta yana farfari alamar dai idanunta biyu.

Cikin fusata siyam ta ce" to wlh babu abinda zai kawo bawon ayaba nan sai dai idan waccan makirar ce ta kawo shi", Ammi ta ce", haba siyam yarinyar dake kwance babu lafiya me zaisa ta yi wannan aikin ko abinda kika ga ya faru jiya ai kinga ba laifinta ba ne sharrin jinnu ne,sakin baki siyam ta yi tana kallon mama kiri kiri ta goyi bayan karya yanzu kenan kowa ba ya ganin laifin Zahra a gidan nan ? Tab ashe kuwa da kwai ƙatuwar matsala dan shi kansa Ab din ta fuskanci baya son damuwar Zahra wani lallabata yake kuma ga alama baisan ma yana yin hakan ba,kwafa ta yi ta ci gaba da kokarin daga maman da har yanzu bakinta bai mutu ba dan kuwa ba karamar buguwa ta yi ba.

A hankali ya sunkuya saitin fuskarta har yana jin hucin numfashin zazzabinta,cikin kamammiyar Muryarsa fuskarsa a miskile ya ce", wato ke cuta ma bata hanaki yin mugunta ko? Tura baki ta yi tare da bude idanunta da suka nuna alamun rashin lafiya ta zabga masa harara cikin gunguni ta ce Ni ka rabu dani babu ruwana da kai sai hawaye shaaaa kamar an bude famfo,hade fuskar ya kuma yi,ya ce me yasa haka baki ga ita babbace ba,juya masa baya ta yi tana ci gaba da tsiyayar hawayenta ta ce", itama ai bata kama girmanta ba kuma kaima da kake wani tare mata ba mantawa nayi da guduwar da kayi ka barni ba har gashi bani da lafiya ta karasa maganar cikin kara sautin kukanta,uhm kawai ya ce ya fara kokarin kwasheta daga kan gadon, doke hannunsa ta shiga yi tana cewa ka rabu dani ina zaka kaini? Bai saurareta ba ya dagata cak sai gata a hannunsa daga ita sai dan karamin towel din jikinta,Ni ka rabu dani babu kaya a jikina sai kasa sun kalleni,hanyar fita ya nufa da ita take duk suka dare har mama da ke shinfide a kasa ta kasa motsi sai kururuwa, wayyo Allah Ammi kice ya sauke Ni,dalla ke kuma daina kalle min jiki ta fada tana kaiwa siyam hauri da kafa a daidai kan hancinta aiko take wani mugun zafi ya ratsa ƙwaƙwalwar siyam din kawai sai ta hawaye saboda tsananin zafi da takaicin sangartar da Zahra take zubawa a gidan a na daure mata kugu.

Fakar idon Ammi tayi musu gwalo sai kuma ta mele baki tana cewa kuma kallon min jiki da kika yi ban yafe ba wuta bal harma motar aga dan kurma da kika shiga wuta bal,daidai lokacin suka kule daga inda su Ammin suke....

Dakyar Mama ta yadda suka dagata tana ta tsinewa Zahra, wallahi wannan yaro bashi da kilki wannan jereba aka doko mana da mesofa eho da wannan sumbatun nata suka Kaita daki, yayin da siyam take fama da nata ciwon hancin da take ji kamar baya fuskarta.

Kai tsaye dakinsa ya wuce da ita, tana ganin haka ta fara ƙoƙarin kwacewa tana cewa barni naje dakina ba ka ce wannan hadaddiyar dakin tawa ce ba? Dan haka barni na tafi can bazan je naka ba kayi min irin abun jiya bayan nace babu ruwana da kai", bai saurareta ya direta saman gadon yana bin fararen cinyoyinta da kallon kasan ido.....✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*