YAR GIDAN YARBAWA

Page33

by @zahrawriter12

......kawar da fuskart ta yi saboda yadda kallonnasa yake wani mintsinin zuciyarta,tashi take kokarin yi ya yi saurin janyota ta dawo dabar saman cinyarsa,bakinta ta bude za ta yi magana ya yi saurin dora hannunsa akannasa bakin ya yi mata alamar zipin yana mai tsareta da mahukuntan idanunsa wanda take suka sa ta yin wani laushi ga kuma yunwa da rashin kwarin jikin dake tare da ita,haka nan ta yi shurun tana ɗan kallonsa saboda abincin da taga yana budewa cikin nutsuwa da rashin son hayaniya fuskarshinnan babu yabo ba fallasa, farar taliya ya zuba da miyar kifi wanda kusan gaba daya miyar zallar tsokar kifince babu abinda take bugawa sai ƙamshi alamar dake nuna cewa ya samu kula na musamman.

Bai bata damar magana ba ya nuna mata abincin da ido alamar ta fara ci,yadda ya yi din yasa ta kasa cewa komai,cikin sanyin da bata san tana da shi ba ta fara cin abincin,dan satar kallon sa ta yi taga kamar baya kallonta dan haka cikin sanda ta zame daga kan cinyarsa ta gyara zama dan kuwa abincin ya mata dadi ga kuma kayan dadi da ba a saba ci a house ba,sosai ta ci abincin ta kora da lemo,shika lemon sai da ta daga shi ta juya ta yi masa kallon tsaf sannan ta daga ta yi masa kyakkyawan sha, tana gamawa ta leka fuskarsa da idanunsa ke alumshe kai kace bacci yake yi,dan ita ma ta dauka bacci yake duk da yadda take ji kamar alamun idanunsa a jikinnata,lekawar da zata kuma yi sai karaf idanunsu suka haɗe ya bude idanun sosai dan ta tabbatar ba bacci yake yi ba.

Kawai sai ta wayance da rike ciki tana dan yatsine fuska,yanzu ma bai iya bude bakinsa ba dan da alama yau Zahra ta kuresa ya yi maganar da bai taba yin me yawanta ba a rayuwarsa shi yasa yake jinsa kamar mara lafiya,gane me yake nufi da kallonnasa da ta yi sai kawai ta bude baki cikin marairaice murya ta ce", cikina ne bashi da lafiya ka bani maganin da zan yi bahaya basir ke damuna,"cikin kamewa ya mike ya fita, cikin sauri tabi bayansa,Zahra tana kallonsa ya danna wani abu dan karami ta bude,wasu magunguna ya dauko ya zaro iya wanda zata sha sannan ya juyo,tana ganin haka ta yi sauri ta kawar da kanta daga kallon wajen,mika mata ya yi daga haka ya taba ta gefanta ya fice daga dakin,binsa ta yi da kallo kafin ta tabe baki tana cewa yau dai kurmancin ya dawo mutum ko gajiya da nuni da ido ba ya yi.

Sai da ta tabbatar ya fita daga ɓangaren gaba daya sannan ta koma dakinnasa ta bude drowar ta kuma dibar maganin da yawa ta fice ta koma dakinta.

Kwanciyarta ta yi kamar gaske duk da aranta tana jin kamar bazata iya kwana ita daya a cikin dakin ba.

.... ko da ya dawo bai ganta ba bai damu ba dan yasan tana dakinta,kwanciya ya samu ya yi bayan yayi duk abinda ya saba na kwanciyar bacci.

Sosai yau yake jin kansa kamar ya rabe saboda hayaniyar da ya sha, shi yasa saida yasha magani sannan ya haye gadon ya shige blanket,lumshe idanunsa ya yi yana addu'a....

Har bacci ya fara kwasarta kadan kadan saboda tsoron yinsa da take,farkawa ta yi a firgice tana kiran sunan mama da Mami, da bin bango ta ta bar dakin ta fito falo nan dinma duhu ko dan dem ligt din babu hakan yasa ta kuma firgicewa dan kuwa ji take kamar zata shiɗe saboda tsoro da ace a gidansu ne bazata ji wannan tsoron ba to amma nan sabon waje ne a girinta kuma bata saba kwana a irin wannan babban gida ba.

A can ƙasa bangaren mama da siyama kuwa har yanzu suna tare dan siyama kasa komawa dakinta ta yi,sai da suka tabbatar da nisan dare sannan suka fara tattauna abinda ke ci musu zuciya.

Mama ce ta dan muskuta zamanta tana dan runtse idanunta saboda zafin da ya ziyarci kwakwalwarta ta ce", siyama wannan yaron abin soro ne anya kuwa baisan abinda muke shirya masa ba? Duba gaba daya ya hanamu lafiyar da zamu sake mu aiwatar da kudurinmu akansa da Ab din duka,anya kuwa sima baya asiri? Girgiza kai siyama ta yi zuciyarta cike da tsanar Zahra akan aure mata Ab da ta yi ta ce", mama Zahra bata san komi ba kawai lissafine kamar tana da wani baiwa na sanin wanda bai kaunarta ko yake da wani shiri kanta tunda kinga ai mu kadai take yiwa ko fa Amira bata taba yi wa kallon rashin mutunci ba sai mu kadai,"jinjina kai mama ta yi tare da cewa shi yasa nace maka ko dai yana da asili me shima? Ey to tunda yaron hausa Fulani ne hakan zai iya faruwa,mama Ni kawai mu yi abinda ya kamata tun kafin taci galaba akanmu dan idan muka tsaya wasa wata rana zamu wayi gari mu ta Koremu a maimakon mu mu Koreta,mama ta ce kayi gaskiya yaro na miko min Bag dina tun yanzu zamu tsala komi.

Mika mata jakar siyama ta yi, tana karba ta bude ta dauko wani kullin magani a bakar leda kana ta kalli siyam fuskarta ɗauke da murmushi tana cewa siyama da wannan zamu fara,dole zan karfafa jikina zuwa gobe dan aikinmu ya tafi daidai,mama me za ayi da wannan ɗin? Siyama ta tambaya tana juya maganin a hannunta,mama ta ce kai dai ka tabbata ka boyesa zuwa gobe zan sanar da kai me ye da akwai,amma da fari mu fara sashi yin girki dan shine babban hanyar samun nasararmu ta wannan hanyar zamu fara rusa kaunar dake sakaninsa da surukai nasa,dariya siyama ta yi tare da dan rungume mama kana ta ce, Allah ya bar min ke mamana karbi magani kisha ina so ki ji sauki da wuri dan mu hadu mu yi yakin neman biyan bukata tare",karbar maganin mama ta yi tana cewa tashi ka kwanta kar gobe ka kasa tashi.

Can cikin baccinsa ya dinga jiyo dan karamin sautin kukan Zahra,tsam ya yi da ransa tare da bude idanunsa yana sauraren ta inda yake jin motsin,zuro kafafunsa ya yi ya sauka saboda fahimtar daga inda sautin kukan nata yake fitowa, a hankali ya bude kofar ya fita, daidai lokacin da Zahra ta kawo wajen bedroom din da lalube tana yi tana kuka can kasa tare da kiran kaka.

Karo ta ci dashi take ta bude baki zata fasa kara ya yi saurin rikota tare da sa hannunsa saman labbanta ya rufe bakin yana zura kansa ta gefan wuyanta kafin cikin kamammiyar Muryarsa ya ce", calm down ya fada mai hura mata iskar bakinsa a kokarinsa na dawo da ita hayyacinta.

Ganin taki dawowa daidai yasa ya cigaba da hura mata iskar bakinsa a kunne yayin da yake shafa bayanta da hannunsa, sai a lokacin ya ji jikinta ya daina rawar da yake yi a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya tana kara cusa fuskarta a jikinsa, sai da ya tabbatar ta dawo daidai sannan ya jata suka shige dakin, da ido ya nuna mata da yi mata alamar ta hau takwanta,a hankali ta haye gadon tana dan satar kallonsa shima kallonnata yake hannunsa sarke a kirjinsa.

Sai da ta kwanta sannan taga shima ya koma ya kwanta zumbur ta tashi duk da cewa akwai yar tazara a tsakaninsu amma saboda tsoron abinda ya yi mata dazu yasa ta kuma daukar fulullukan da suke jere reras ta shiga jerasu a tsakaninsu,yana kallonta amma ko tak bai ce ba, ta gama ta kwanta sama da kasa wato tasa kafafunta tawajen fuskarsa ita kuma tasa fuskarta ta wajen ƙafarsa,ajiyar zuciya ta sauke saboda hankalinta da ya kwanta ko wane tsoro ya barta ta dawo zahranta ta ainihi yar gidan yarbawa, jan blanket din ta yi ta rufa ta fara baccinta hankali kwance.

Bai damu da abinda ta yin ba shima dake baccinne akansa take ya daukesa.

Abin dariya lokacin da kiran sallah ya farkar dashi yana bude idanunsa ya ci karo da Zahra kanannade a jikinsa kamar zata koma cikinsa ,ta hasken dum light ya hango yadda duk ta yi watsi da filayen ko wanne ya kama gabansa a kasa, ware idon ya yi sosai cike da mamakin yadda hakan ta faru sai kuma ya ɗan saki karamin numfashi tare da zareta daga jikinsa a hankali ya gyara mata gashinta da ya baje a fuskarta..

Yana fitowa ya sameta zaune akan gadon ta kunna hasken dakin tana bin duka fulullukan da suka tarwatse a kasa da kallo fuskarnan a kumbure kamar an hura balo kiris take jira ta fashe...dan kallonta ya yi har zai yi magana sai kuma fasa ya nufi kofa zai fita ,saukar sautin zazzaƙar muryarta a kunnensa ne yasa shi dan dakatawa amma bai jiyo ba,cikin son fashewa da kukan tabara ta ce", dan Allah ya akayi na dawo nan? Me yasa ka cire min makarin da nayi mana? Kuma dan Allah ka fada min ko kayi min wani Abu? Juyowa ya yi ya watsa mata kallonnan nasa kana ya fice ba tare da ta samu amsar tambayarta ko guda ba,hawaye ne suka sauko mata tasa hannu ta share tana gungunin shurunsa a gareta..

Ko da ta yi sallar dakinta ta koma ta fada bathroom ta fesa wanka ta kuma ci adonta kamar yadda ta fara sabawa da hakan yau kuma wata doguwar riga me shegen kyau ta saka wadda ta kama ta daga sama ta fidda ainahin kyawun surarta ta diya mace,ta hade gashinta a tsakiya tayi rolling da tattausan mayafin rigar wanda yabi gewayayyiyar fuskarta ya lafe, sai ta fito tamkar ita ce balarabiyar dan ba karamin kyau ta yi ba.

Maganin da ta diba jiya ta dauka ta soke a jikinta,kafin a hankali cikin sanda ta fito daga dakin,sai da ta fita daga falon gaba daya ta ganta a corridor da zata bi ta sauka kasa sannan taja numfashi tana cewa yanzu da zai ganni da ya hanani fita," sauka ta yi kasan tana leke leke saboda jin ko ina tsit,dan lokacin bai fi Shida da rabi ba.

A bangaren siyama ita ma da wuri ta tashi ta shirya ta shiga kiching gurin su baba talatu wai zata taya su aikin breakfast,duk da mamakin da ya rufesu amma haka suka bata waje ta kama wani abun daban tana yi tana dan jansu da hira tun suna biye mata a dari dari har suka saki jikinsu da ita,hatta da gyaran wajen tare su kayi shi.

Sannan suka jere komai a kan dinning kamar konda yaushe, bangarensu suka koma ita kuma siyama ta tafi dakin mama cikin dan hanzari, tana shiga ta ce", mama yi sauri ki bani maganin farrakun na zuba musu dan na kagu na ga anyi wa yarinyar nan korar kare shegiya yar matsiyat...kafin ta kai karshen maganarta mama ta mika mata maganin tana cewa bar wannan maganar sauri kaje kayi aikinka ka zuba shi a duka abincin amma idan baka bi ka idarsa ba kuma ka zuba fiye da yadda ake bukata to fa duka zasu iya dacewa, dan haka sai ka kula de kyau.fita ta yi daga dakin,cikin sauri ,ya yin. Da wani bangare na zuciyarta ya tafi kan sabon tsari akan aikin maganin na biyu,in dai har idan na zuba musu da yawa zasu mutu to kuwa tabbas zan zuba musu idan yaso sai na yi dabarar da Ab ba zai ci ba shike nan na kawar da gaba daya matsalata.

Wannan shawarar ba karamin karɓuwa ta yi a zuciyar siyama ba dan haka cikin kwarin gwiwar da ta samu a lokacin ta isa dinning room ɗin .. daidai nan Zahra ta karaso bayan ta gama dube dubenta kasancewar takalmin da ta saka me taushi ne wanda baya fitar da sautin taku yasa ta karaso cikin falon sosai ba tare da siyama ta kula da ita ba.

A hankali siyama ta bude maganin tare da bude murya kadan ta ce,Ammi daddy Zahra Amira ina so su mutu ina so su mutu ina so su mutu ta maimaita so uku kamar yadda mama ta umarceta sannan ta bude abincin duka da yake wajen ta zuba maganin sosai har sai da maganin ya kare ta juya ta rufe tana wani makirin murmushi, ji take kamar ta samu abinda take so ta gama tana kyautata zaton ma har su gama breakfast din AB bai fito ba daga haka kuma zata yi dabarar da ba zai ci ko mai dake gurin ba,Zahra kuwa ko bata ci a lokacin ba zata yi dabarar da dole sai taci.....✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*