Page34
......zuciyar Zahra babu abinda take sai bugu dan kuwa ta yi matukar razana da abinda siyama tayi,dama Allah zai hadata zama guri daya da masu zuciya irinta su siyama da mamanta?
Ita dai tasan babu alkhairi a zuciyarsu a kanta dan tun ranar da siyama ta sa mata bawon ayaba a Company ta gama sanin cewa tana iya nakastata dan bata kai ga tunanin zasu iya kasheta ba,ranar sam bata nuna ta ga siyama dinba kuma bata sawa ranta zata rama ba Allah ne ya dubeta ya hadata zama dasu cikin sauki take yin ramuwar gayya,to amma abinda ya kuma jefata cikin firgici shine wai harda su Ammi take son kashewa to su me su ka yi mata? Idan ita suna da hujjar kasheta dan ta yi ramuwar dasu basu san cewa ramuwar take yi ba su mutanen gidan ina ruwansu?
Ganin siyama tana fitowa daga dinning room ɗin yasa ta yi saurin boyewa,bata fito daga gurin ba har sai da taga siyama ta shige dogon coridow din da zai kaita dakunansu ita da mama,sai da ta tabbatar babu motsin kowa sannan ta yi saurin fitowa ta shige dinning room bata tsaya duba kayan breakfast din ba ta kwashe su gaba daya ta fita dasu zuwa kiching,bata tsaya sanya ba ta bude famfo na sink ta fara zubar da duk abinda yake da ruwa kamar su farfesun kafar sa da na kayan ciki sai ruwan shayinda ke cikin pulas, wanda ruwa ba zai tafi dashi ba kuwa leda ta samu ta juye kamar su doya da kwai chips da bread kai komai sai da Zahra ta fitar dashi daga kiching dinnan cikin wani irin zafin naman da bata san tana dashi ba.
Cikin tsananin sa a Zahra ta samu komai da akwai saura dan yau komai da yawa siyama tasa a kayi, dan ita bata da hakurin ci, anufinta idan suka gama sai ta fito ta dibi na kiching din ta kaiwa mama da Ab. shi yasa wanda ta kai dinning din ma a kididdige yake dan tana so suna diba ya kare yadda dole ita sai dai tazo ta dibi na kiching din.
Sai da zahra ta tabbatar ta zuba komai ta maida shi kamar yadda siyama ta ajiye sannan ta saki ajiyar zuciya,dan tsayawa ta yi cike da tunanin yadda za ayi ta zubawa siyama maganin sakin cikinnan dan kuwa ta tabbatar tunda har ta zuba maganin mutuwa to bazata fito cin abinci ba ita da mama,har taje bakin kofa sai kuma ta yi wani tunani wanda yasa ta dawowa ta bude dan ragowar da ta bari ta zuba maganin over doos yadda tasan ciki zai ruɗe,tana cewa na tabbatar yadda siyama take mayyar abinci to tabbas wannan kanta ta ajiyewa a tunaninta idan mun mutu sai ta shigo kiching ta yi fati da gadon mijin....sai kuma ta yi saurin kama bakinta tare da dan kaiwa bakin bugu tana cewa Zahra me ya kaiki wannan tabargazar waye kuma mijin? Sai kuma ta marairaice fuska kamar dai wani ne ya yi mata tambayar da kwabarta a kan hakan ba kanta ba,ta ce,na manta mijin wuccin gadi zance,yanzu naji magana ta kuma fadawa kanta tana barin kiching din.
Zama ta yi a falon ta kasa ta tsare.
Karfe takwas saura mutanen gidan suka fara fitowa, kowa da wuri ya ke karyawa a gidan saboda Dukansu masu fitar sassafene ammi da bata fita kuwa sabon zama dasu yasa ta koya, Amira ma ko da school ko babu ƙa'ida ne ta saba sai ta fito, shi dama uban gayyar bai cika zaman cin abinci tare dasu ba amma dai na safenan ya zamar musu kamar dole tunda kowa fita zai yi,kuma kamar shine wata damarsu ta haɗuwa a kullum a matsayin su family.
Duk wanda ya fito da Zahra yake cin karo a falon, amma basu cewa komai sai dai su gaisa daga haka suka nufi dinning room ɗin gaba daya Ammi sai tattalin Zahra take kamar zata maidata ciki, shi kansa daddy duk lokaci bayan lokaci yakan tambayar Zahra tana lafiya dai ko?
Zahra da kanta ta yi zaven dinsu Ammi da daddy har da Amira kana ita ma tayiwa kanta,basu yi mintuna biyar da fara karyawa ba,hancinsu ya fara sinsino musu azababben finannan ƙamshin AB da baya buya a guri,Dukansu sai da suka daga kai suka kallo hanyar da suka san tanan ya ke bullowa, da sauri Zahra ta kawar da fuskarta saboda cin karon da fitunannun idanunsa da basa kunyar kallonta a kanta.
Ɗan murguda mitsitsin bakinta da yake cike da chips tana masa wata irin tauna ta yi,cikin kasan makoshi ta ce", shi mutum sai masifar kallo kamar zai cinye mutum,daidai lokacin ya ke kaiwa zaune gefan kujerarta wadda ta zama kamar tashi saboda yawan zama akai harma babu wanda yake zama ko da baya kusa,cikin kamammiyar Muryarsa wadda ke fidda yanayin girmamawa da biyayya ya gaida iyayensa,Amira kuma ta shiga gaidasa,amsawa ya yi cikin kulawa,ganin haka yasa Zahra ta dan tura baki a ranta tana cewa nima yanzu sai na gaidasa kenan?
Dauriya ta yi ba tare da ta kalli inda barin damanta da yake zaune ba ta ce ", ina kwana an tashi lfy", shiru ta ji babu amsa hakan yasa ta dan juyo tana kallonsa har idanunta sun cika da ruwan takaicin dizgatan da yayi,sai taga shima itan yake kallo amma ta wata sigar da babu wanda zai gane sai ita da akewa kallon kuma take jinsa har can cikin kwakwalwar kanta.
Babu kyau dai nuna wariyar launin fata saboda ita yar uwarka ce shi yasa ka amsa mata Ni kuma tunda bare ce ka min shiru, tana maganar hawayen da take rikewa dan kar su Ammi su gani suka karasa gangarowa dan kuwa ta ji zafin abinda ya yi matan duk da su basu ma san me yake faruwa ba abincinsu kawai suke ci,ya Salam ya furta can ƙasan maƙoshinsa yana mai bin hawayenta da suke gudu akan kyakkyawar fuskarta da kallo,rasa abin cewa ya yi gashi kuma kamar yana so ya ce wani abun,dan haka kawai sai ya dan riko hannunta guda ya ɗora saman jikinsa yana mata wani kallon kasan ido wanda yasa taji wata muguwar kasala da sabuwar shagwabar da bata san ta inda ta bullo ba,sanyin hannunsa da taji akan fuskarta yasa ta dan aje numfashi bai dakata daga dauke hawayen ba har sai da ya sharesu tas sannan ya yi mata kallon kai tsaye tare da girgiza kai fuskasa har yanzu a kame sai dai a kwai sassaunci akan na kullum.
Zare hannunta dake cikin nasa ta yi tana kallon su Ammi da har sun kammala nasu break ɗin,ta ce", Ammi kinga har yanzu su siyama da mama basu fito ba ko naje na duba su ko jikinne ya tashi? Ba sai kinje ba ta ji dakakkiyar muryarsa ya fada kuma ya yi kamar bashi ya fadan ba,dan Hararar da yanzu take shakkar yi masa ta kaiwa bangaren da yake ba tare da ta ce komai ba,Ammi ta ce rabu dasu zasu fito in dai siyama ce idan ma basu fito ba ga Amira sai ta kai musu,ke kuma yi zaven din mijinki kinji yar albarka", jinjina kai Zahra ta yi tana janyo flet daidai saitin kunnensa ta ce", ka ci albarkacin Ammi,daga haka ta yi saven nasa ta tura masa tana mai ci gaba da cin nata da zuwansa ya dakatar da ita.
Tashi su Ammi su kayi gaba daya dan yiwa daddy rakiya har Amiran, daddy a dawo lafiya Zahra ta fada tana masa bay bay,yauwa my dougter ina fatan dawowa na sameku lafiya,in sha Allah daddy ta bashi amsa fuskarta da wani kayataccen murmushi.
Siyama dake labe tana jinsu ta yi dariya tana cewa ai sai dai ku hade a can shegu Mayu yau dai nayi maganin matsalata dan haka yanzu zan bude faifai na sabuwar rayuwa Ni da my love AB.
Lokacin da siyama ta fito tuni Zahra ta matsar da duk abinda yaci daga gabansa, kai idan ba agabanka ya yi break ɗin ba bazaka taba cewa ya ci wani abu ba,sai kuma tsarin Zahra ya kuma tasiri saboda kamewar AB din.
Cikin fara a siyama ta karasa kusa dasu tana cewa Zahra Barka da safiya fatan kin tashi lfy? Murmushi Zahra ta yi tare da cewa lafiya kalau aunty siyama ya jikin mama ina fata dai taji garau", sosai ma siyama ta fada idanunta akan kwanunkan da suka gama cin abinci tana jin tamkar ta taka rawa sosai fuskarta ta kasa ɓoye tsananin farincikin da take ciki,dakikancinta da son cikar burinta ya hana ta yin tunanin hukuma da bincike me zafi akan mutuwar mutum uku rigis wanda idan haka ta faru ko shi Ab din ba zai tsira daga tuhumar hukuma ba.
Gaida Ab din ta yi ba tare da ta saurari amsar ba, ta ce", Zahra naga kamar abincin nan sun kare bari na duba kiching ko da akwai saura", cikin sauri zahra ta mike tana cewa aa aunty siyam bari na dauko miki yau ai naga mutunci kike ji wata kila kin sauke makaman yakinki.
Dariya siyama ta yi tana zama a kujera hankalinta kwance ta ce", haka ne Zahra ai ke surukar mu ce dole mu biki,dariya kwai Zahra ta yi ta tafi kiching,ita ko siyama dake tasan duka abincin da ta bari a kiching din lafiyayye ne shi yasa bata hana Zahra ba.
Zahra na shiga ta dauki flet ta zuba mata ko mai daidai yadda ya kamata sannan ta kuma daukar wani ma ta zubawa mama tana cewa idan mu bamu mutu ba ku zaku yi yinin wahala sannan ta dauka ta fita tana dariyar dariyar da zata sha tun kafin aiki ya kammala.
Tana fitowa ta yi Turus ganin har yanzu AB din na zaune idanusa da hannunsa akan tap dinsa da yake dakilarta a nutse da alama wani aiki me muhimmanci yake yi a ciki,ita kuma siyama tana zaune inda ta barta ta yi wani mugun tagumi ta zubawa AB din ido kamar tsohuwar maiya babu abinda take yi sai murmushi wanda ita kai dai tasan ma anar abinta,hade fuska Zahra ta yi kafin ta karasa ta ajiye mata abincin cikin dangwararwa hakan yasa siyama ta dawo hankalinta saboda karar ajiye flet din da Zahra ta yi,waw my enlow thanks for d care," Zahra bata ce komai ba ta zauna tana dan murmusawa can kasan ranta kuwa haushun AB ne fal saboda ya zauna siyam tana kallonsa.
Na mama ta nuna mata ta ce ya kamata ki fara kaiwa mama nata tunda ya baro kula kar ya huce ko? Mikewa siyam ta yi tana cewa haka ne Zahra bari na kai mata na dawo", jinjina kai Zahra ta yi tana Binta da harara.
Shi ko AB bai ma san tana yi ba duk da cewa yaji a jikinsa siyama din kallonsa take yi amma sai ya daure yaki tashi saboda bai san barin Zahra a gurin daga karshe ta yi abinda zata bashi ciwon kai,dan ya tabbata wannan kirkin da ta yiwa siyama ba na Allah ba ne,duk da cewa ita siyaman ya yi mamakin yadda ta yiwa Zahra sai dai abinda yasa a ransa kawai cewa siyam ta fara tsoron halin Zahra ne shi yasa ta nemi zaman lafiya.
Bata jima ba sai gata ta dawo ta zauna.
Cikin walwala da farincikin da yake fitowa tun daga kasan zuciyarta ta fara kai lomar farfesun cowleg din bakinta tana yi tana haɗawa da chips tare da kurbar ruwan liptom hankali kwance tana yi tana lumshe ido tana emagen AB cikin idanunta da yadda zata kasance cikin shauki duk ranar da mafarkinta na hada jiki dashi ya tabbata ko da ba ta hanyar aure ba.
Da sauri ta bude idonta da suke a lumshen saboda jin wata karta da cikinta ya yi,ɗan dafe cikin ta yi tana yatsina fuska,lafawar da ya yi yasa ta ci gaba da cin abincin, can ta kuma jin ya murɗa da karfi tare da wani irin juyawa har da irin karar nan,daurewa ta ci gaba da yi sai dai ta ɗan tsaya da cin roman dan a tunaninta ko romanne ya fara murda mata ciki..
Jin abun yana yin gaba yasa ta yi saurin mikewa dan kaiwa bathroom ziyara, takun da zata yi sai ga wata tusa me karfi da amo kan sauti ta fito kusan guda uku a jere babu coma bare pullstop......✍🏼
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*