Page40
........gumin da Zahra ke yi ne ya farkar dashi lokaci ya dan duba yaga har anyi sallar la asar istigfar ya yi kafin ya fara zareta daga kanannadewar da ta yi ajikinsa babu wani sarari da ta bari inda bata yi kane kane ba,kamar dai yadda ta yi a zuciyarsa.
Yana barin dakin ta bude idonta dan tun cireta daga jikinsa da yayi ta farka,maida idanun ta yi tana aje numfashi kafin itama ta yunkura a hankali ta mike dan sosai ta ji ta garau babu wani sauran zazzaɓi sai dan ciwon da take ji kaɗan kaɗan daga kasanta,tana shiga bathroom ɗin ta yi tunanin shiga ruwan zafi saboda lokacin da ya yi mata ɗazun taji dadi sosai shi yasa a yanzu take tunanin kara yi amma bata san ya zata yi ba dan haka kawai sai ta yi brosh ta daura alwala ta fito,wata blue din doguwar riga me taushi ta saka rigar ta yi mata kyau sosai sabida yadda ta bi lafiyayyan dirarrran jikinta da ya kuma murjewa ta yi wani dumimi da ita gwanin sha awa.rigar ta kwanta luf kamar tasan ta samu irin jikin da ya dace da ita.
Sallah ta fara gabatarwa tana mai neman afuwar Ubangiji saboda makarar da su kayi,fitowa tayi daga dakin bayan ta bula uban humras da turarukanta masu tsada da ƙamshi masu sanyi dan itama tuni ta bi layin Ab da ba a gane kalar kamshin turaren da yake amfani dashi,a hankali take takawa tana dan yatsine fuskarta da take ta wani glowing,karo tayo da kirjinsa a daidai kofar shigowa dakinnata dafe gishinta ta yi tana sauko da hawayen da dama kiris take jira ta samu wanda zata saukewa su,hannunsa yasa a samannata da yake kan goshinta kafin a nutsensa ya shiga murza mata goshin yana kallon cikin idanunta da ta hana shi kalla tun hadewar tasu, jin yadda kallonsa ke ratsata yasa ta dan buga kafa tare da tura bakinta cikin gunguni ta ce", Ni kam banso ta fada tana ture hannunsa daga kannata tana kokarin bin gefansa ta wuce cikin kasalallan takunta,binta ya yi da kallo kafin ya dan ja numfashi sannan a hankali yabi bayanta yana kama hannunta da yaga inda take kokarin fita,tasan me yake shirin yi sai kawai ta kebe baki zata sa kuka alama ya yi mata akan ta yi shiru make kafada ta yi tana kallon kofar fita falon dan murza goshinsa ya yi a ransa yana cewa yau kuma ko ina bakin tsiwar da baya mutuwa oho ga alama dai itama yau ta zama yar kurma kamar dan kurmannata....
Nuni ya yi mata da ta tafi aiko bata san lokacin da wani dan kyakkyawan murmushi ya kufce mata ba duk da yadda tasha alwashin AB ba zai kuma ganin sakin fuskarta ba bare ya kuma kawo mata farmaki,tuna hakan da ta yi yasa tayi saurin gimtse fuskarta har da tukyicin harara, nuna kansa ya yi alamar dashi take? Girgiza kanta ta yi tana mai saurin barin wajen amma tunkafin takai kofar ta durkushe tana sakin hawayen azabar da taji ta ratsata,yasan hakan zata faru shi yasa ya barta yaga gudun ruwanta.
Durkusawa ya yi a gabanta yana cewa ki hakura da zuwa falon yanzu amira zata kawo miki abinci", um,umm ta fada tana kara make kafadarta,to me kike so a yi? Bata yi magana ba sai jikinsa da ta shige tana cewa ka ɗaukeni ka kaini bazan iya tafiya ba,idan ba haka ba sai na gayawa Ammi abinda kayi min ", tallafarta ya yi hannunsa saman fuskarta bai yi magana ba amma yasan tsaf zata aikata hakan ,ko ba haka ba ma da ta yi masa wannan darunnata ya gwammace ya kaita har kasan idan ya so ya fuske abinsa.
Daukarta ya yi cak kamar wata yar baby ya dora bisa kafadunsa kafin ya fita daga falon cikin kamewarsa fuskarnan kamar bashi ya gama bannawa Zahra ba.
Ammi da Amira ne kawai a dinning room ga dukkan alama sun dan jima da dawowa dan ga alamar jimawar nan a tare da su dan fa Ammi da tasan abinda fitarsu ke nufi har tayiwa Zahra roman kifi da na kaza,Amiran ta kalla ta ce,fara kira mana siyam da mama su fito mu yi lunch idan yaso sai ki kaiwa doughter wannan nasan yau ba lallai ta sauko ba," tashi Amira ta yi ta kira su bata tsaya mamaki ko damuwar yanayin da ta gansu aciki ba ta sanar dasu sakon Ammi ta yi ficewarta ba tare da ta tsaya jin ta bakinsu ba.
Duban siyam mama ta yi tana cewa siyam tashi kaje dole kayi abinda nasa ka idan har kana son cika buri ehem", haka nan siyam ta daure ta tashi ta fita maman ma binta ta yi domin sunyi shawara akan dole sai sun sauya daga kiyayyar da suka fara nunawa Zahra sannan zasu samu karɓuwa da yarda wajen mutanen gidan da shi kansa uban gayyar da tuni suka fahimci yayi zurfi a kololuwar SO.
Daidai sun fito tsakiyar falon basu karasa dinning room din ba idanunsu su kayi mummunan gani ganin da yasa siyam jin wani mummunan jiri na kwasarta har sai da ta kai zaune bisa kujerar dake kusa da ita tana mai runtse idanunta zuciyarta na wani irin duka kamar zata yi amanta.
A hankali AB ya dire Zahra daga bakin upstairs din yana hamdalar ganin Ammi a dinning room ɗin da bai san tuni ta gansu ba,ita ko Amira har wani dawowa falon ta yi saboda kawai taga show din siyam,aiko ta gani ɗin dan har yanzu bata iya bude idanunta ba kuma hannunta yana kan kirjinta tana fidda numfashi da wuya.
AB bai kula dasu ba dan kaf hankalinsa yana a kanta dan so yake yaga ta karasa dinning din lafiya ba tare da ta fama jikinnata, ita ko Zahra ta gansu amma bata nuna ta gansun ba dan yanzu ba ta su take yi ba.
Oh my doughter oyoyo Ammi ta fada tana buɗe mata hannunta bayan ta mike tsaye, yau dai Zahra ta kasa yin gudu kamar yadda ta saba dole sai a hankali ta lallaba ta shige jikin Ammi tana sauke mata hawayen shagwaba,AB kuwa fatansa a rabu lafiya kar Zahra ta yi masa abinda ta yi masa a gun Abba da mama.share mata hawaye tana cewa haba Zahra meye na kukan ba gamu mun dawo ba,tura baki ta yi tana kallon gefen da Ab ya zauna ya fuske abinsa kamar bashi ya gama lallabata ba yanzu, yana jin idanunta akansa ya dake yana ta addu'ar Allah ya rufe bakinta daga bashi kunyar gaban ammi da wannan sakarcinnata.
Ammi kamar tasan shirin Zahra sai kawai ta yi saurin zaunar da ita tana cewa yi shiru doughter bari kiga abinda na shirya miki ina dawowa, janyo kulolin da ta zuba farfesun ta yi tana cewa ai zaki ci ko my love? Gyada kai ta yi tana share ragowar hawayenta.
Da rarrashi mama ta ciyo kan siyam ta tashi suka karasa dinning room ɗin,sai dai fuskarnan tata kamar biri ya sha kunu,zama su kayi mama na yaken dole har da tambayar Zahra me ya sameta take ta yatsine fuska,Ammi ta ce", kawai shagwabarta ce wai dan mun fita mun barta a gida shine take ta bata rai haka,oho cewar mama tana kai lomar sakwara bakinta,ita ko siyam gaba daya idanunta da zuciyarta suna kan AB da taga iya yau kawai amma ya kara wani haske da kwarjini sai kawai ta ji ita fa bazata taba iya hakura da shi ba ko da so daya ne sai ta tabbata ta cika burinta akansa,Zahra da ke cin farfesunta hankali kwance ta dan dago sai ko idanunta suka sauka kan siyam da take yiwa AB kallon mayu,juyawa ta yi ta kalli AB din da shi kuma nasa hankalin kaf yana kanta amma fa ba kowa zai fahimci irin yanayin kallon da yake mata ba,tabe baki ta yi tana ƙunƙuni a ranta ta ce", to ko dai anyi gadon maita ne irin wannan kallo haka ai sai mutum ya kware,ture farfesun ta yi daga gabanta sannan ta marairaice fuska ta ce", Ammi dan Allah ki kira min mama a waya kinji",bari idan kunje sama mijinki zai kira miki ita kiyi hakuri,tura baki Zahra ta yi tana ƙunkuni akan ita bazata koma sama ba,"to Ammi ai dama anan kika tafi kika barni Ni gaskiya dakin Amira zan koma dan har yanzu wannan micijin yana nan kuma mugunta zai min dan dazu ma daga ha......cak ta ji Ab ya daga ta sama tare da barun wajen gaba daya..
Dan ya gwammace yaji kunyar dagata da jin kunyar abinda Zahra zata fada,harba kafafu ta dinga yi tana dan turasa tare da cewa Ammi kingansa ko kice ya rabu dani Ni a dakin Amira zan kwana idan na bisa macijin jikinsa......hade bakinsa da yayi da nata ya hanata karasa abinda taso fada a haka ya haye saman da ita,ya yin da ammi ta yi murmushi kawai tare da cewa Amira ki gama ki kai mata farfesunta dan so nake ta cinyesa duka, to Ammi Amira ta fada tana kallon siyam da ta tsayar da itanunta a waje. Daya suna tsiyayar kwallar da bata san ma tana fitowa ba....
........
A bangaren maman Sadik kuwa tun ranar da abin ya faru take fama da jinyar zuciyarta dan sosai take jin bazata iya tawakkali da rashin jarinta ba,sai yau ne kawai ta samu ta ji sauki har ta fito zuwa gidan su Zahra.
Tana shiga ta samu mama tana girki sai kaiwa da kawowa take ragowar yarbawan da suka rage a gidan basu fita ba suma kowa na gabatar da nata uzurin, kallon maman Sadik mama ta ci gaba da yi bayan sun gaisa ta ce", lafiya dai ko? Dan da ace Zahra na gida to ba zan tambayeki lafiya ba nasan karar ta ce yanzu kuwa bata nan baki shiru kwana goman nan kamar bansha gwagwarmaya ba",
Kuka maman Sadik ta fashe dashi tana cewa yo ai ko da zahla baya nan ya bar baya da kura dan bai tafi ba sai da ya tabbatar da ya talauce maman Sedik ,ban gane ba me kike nufi?mama ta tambayeta cike da mamaki.
Take maman Sadik ta zaiyane mata abinda ya faru ranar tas bata da ɗa ba bata rage ba,dan tasan sauran idan har ta fadi abinda Zahra bata yi ba,rike baki mama ta tana salati dan duk ita bata sani ba.
A can bangaren AB da Zahra kuwa suna hawa sama ta kwace daga jikinsa tana cewa Nifa ba zan shiga ba ina falo haka kawai na bika ka je ka kuma samin macijinka,zama ya yi a kujerarsa tare da ɗaukar wayarsa ya fara tabata kamar yana taba kwai,a hankali ta matso kusa da shi ta zauna tana cewa to naji zan zauna a saman amma da sharadi,bai yi mata kallon kai tsaye ba amma yana kallonta ta gefen idonsa, jin bai tanka ba ta ci gaba da cewa sharadin kuwa shine babu kai babu Ni ba za ka kuma sa min wannan abun ba amma dai na yadda ka sammin zakin bakinka, sannan kuma kullum sai ka kira min mama wannan kuma daga yanzu za a fara.
Sannan kuma idan zan sauka kasa za ka dinga goyani har sai na warke daga cizon macijinka na karshe kuma zaka dinga min tausa idan zanyi bacci shike nan babu wahala sharadin, ai nasan ka yarda ko? Ta fada tana leken fuskarsa,wayar hannunsa taga ya miko mata wanda take ta shiga murna dan tasan ke nan ya yadda da duka sharadinta,ƙasa ƙasa ta ce," ehe dan wallahi ba zaka wahalar da Ni na kyale ka ba dole kaima ka dandana irin halin kuncin Zahra yar gidan yarbawa,wayar maman daddy ta kira dan mama har yanzu bata da waya kuma tasan yanzu Abba baya gida.kiran yana shiga ta daka tsalle dan har ta manta da ciwon da take ji barin wajen za ta yi yayi saurin janyota ta fada saman jikinsa har tana bige goshinta da kirjinsa raurau ta yi da ido tana gunguni daidai lokacin aka daga kiran da ta yi,ai tuni ta manta da mitar da take shirin yi cikin doki ta ce", maman daddy nice zahla maza hadani da mamana.
Maman daddy da suke tsaye Duka suna rarrashin maman Sadik da ta tubure sai an biyata asarar da Zahra ta yi mata,ta mikawa mama wayar tana cewa dan halek Zahla ne a kan layi,"da sauri mama ta karbi wayar tare da kanga ta a kunneta.
Mamana i missing You Zahra ta fada tana wani juyi a jikin AB dan ita gaba daya ma ta dauka akan gadonta take wayar,haba Zahra da ace maman Sadik bata shigo ba da Nima nace dake i miss You din duk da cewa bakina ya huta na kwana goma,saboda rawar jiki Zahra bata san ta saka wayar a hansfree ba a tunanin ta ai duk da maganar ji take kamar suna kusa da juna amma ita kadai take ji,dan haka hankali kwance ta ce", yanzu mama saboda wata maman Sadik zaki ce baki yi missing Dina ba?
E mana Zahra dole na fadi haka ashe ranar da za a kawoki gidanki sai da kika je kika kwashe kayan shagon maman Sadik kika rabawa yaran anguwa saboda rashin ji ko Zahra? Tura baki Zahra ta yi ta ce", to mama baki ga abinda ta yi min ba lefe na fa ta diba masu kyau da tsada saboda kawai na karbi kayanta nayi jari,a'a fa Zahra wannan ba kawai ba ne me yasa da kika gama siyar da wainar baki hada kudinta kin kai mata ba? Sacewa a kayi fa," rufe min baki sakaryar wofi to yanzu gata nan tazo ta daga min hankali sai na biyata.
Wani tashi zaune Zahra ta yi tana cewa kambala'i dan taga bana gidan lallai ma maman Sadik har yanzu baki gama sanin Zahra ba,to mama kice mata an cinye ba za a biya ba ta kaini wajen dpo ta gani idan ban maida ta a ciki ba tunda dama ai saurayina ne,kinga tazo gidan sauki.
Ji ta yi kawai ya zare wayar daga hannunta, kai dan Allah ban fa gama ba,wani kallo ya watsa mata tare da maida hankalinsa kan wayar, juyowa ta yi sosai ta raba kafafunta ta gefe da gefensa ya zamana suna fuskantar juna, ta ce", dan Allah ka barni na je gida na kashe wancan wutar Allah yau idan banyi maganin maman Sadik ba ba zan iya bacci ba,ko ya fada a hankali kuma can kasan maƙoshinsa idanunsa akan dan karamin lips dinta da suka kuma yin ja.
A can kuwa cikin rawar ji ki maman Sadik ta ce da mama kinga Ni ko har yanzu zahlanka be yi hankali ba,yana gidan aule yana fadin zaizo ya yi rigima,ohoooo bari na je gida ku shirya min dukiyana kafin kuji kira tunda mara kunya ya ce ", na kaisa wajen dpo,yanzu dpo babu ruwansa dasi tunda yayi aule hukunci za ayi masa babu dege kafa,fuuu ta juya ta fita tana zage zage dan gani take a yadda tasan auren Hausa basu bari matansu na fita to Zahra ba zata iya zuwa ba fada kawai ga yi dan ta tsoratata.mama dai bata iya cewa komai ba da kuwa tasan in dai Zahra ta samu dama to tabbatas zata fito tazo wajen maman Sadik din dan haka ba zata sawa kanta damuwa a banza ba.
.......kawar da fuskarta ta yi saboda kallon da yake mata jinsa take har can kololuwa ga tsigar jikinta da take wani mikewa,juyo da fuskarta ya yi ya hadeta da tasa,kafin cikin kamammiyar Muryarsa ya ce", me yasa kika kwashe mata kaya kuma baki son gaskiya? Dan zaro ido ta yi cike da mamaki ashe yaji komai,wani irin har ta yi idanunta da bata san tayi ba kuma bata san yadda ya nemi janye numfashin AB ba,tsura mata ido ya yi yana kallon farar kwayar idonta da har yanzu bata daina walainiya da ita ba,numfashinsa me dumi ya fesa mata a saman fuskarsa take kamshin banana mint din da yayi amfani dashi ya shige kofofin hancinta lumshe idanunta ta yi, kafin da sauri ta bude su saboda jin AB yana yin kasa da rigarta......✍🏼
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*