Page41
.......da sauri ta kama rigar idanunta na cika da kwalla kafin cikin rawar murya ta ce", Ni kam banso mutum ya dinga kalle min jiki haka nan",
Ko? Ya fada yana karasa zame rigar idanunsa a jikinnata da yayi matukar daukar hankalinsa,hannu tasa ta rufe kirjinta saboda yadda ya kafe wajen da ido hawaye kuwa tuni suka shiga zarya a kyakkyawar fuskarta takaicinta yau namiji yana kalle mata dukiyar jikinta da babu wanda ya taba gani ko shi yau da yayi bajakolinsa da ita bai gansu ido da ido kamar yadda yayi mata yanzu ba,da sauri ta manne kirjinta da nasa a nufinta na kare dukiyarta daga mayen kallon da AB yake musu.
.wani irin numfashi yaja saboda yadda tudun kirjinta ya tokaresa,shi dai bai taba ganin dukiyar mace ba amma tsari da suffar na Zahra ya tabbatar masa da cewa nata na Musammanne ko acikin mata sai an dage kafin a sami kalar nata,ita ko Zahra gaba daya jinta take kamar ba aduniya ba saboda yadda tsigar jikinta ke mukewa.
Nock din kofar da aka yi ya dakatar da Ab daga mayen kallon da yake bin Zahra dashi loko da sako kallon da bai taba tunanin zai iya yiwa wata diya mace a duniya ba.
Dakyar ya iya hade miyan bakinsa, yana maida kallonsa kan kofar, Zahra kuwa cikin farin cikin ta kubuta ta yi sama da rigarta tare da kokarin sauka daga jikinsa,fahimtar da yayi mata yasa ya riketa ya hanata damar saukar da take son yi.kafin a cikin kamewarsa ya ce", waye? Amira dake tsaye hannunsat rike da kulolin farfesun Zahra ta ce", yaya nice Ammi ce ta ce na kawowa Zahra farfesunta", uhm kawai ya ce", wannan shine amsarta dake sun san halin kayansu sai ta bude kofar ta shigo ,ganinsu a yadda suke yasa ta kawar da kanta ta isa can dinning room dinsu ta aje kulolin sannan ta juya sai da tazo fita sannan ta ce ", yauwa aunty zahra Ammi ta ce", lallai ki cinye su duka, daga haka ta yi saurin ficewa fuskarta dauke da murmushi da kuma mamakin yayannata da ya kanainaye zahra bashi da alamar barinta.
Amira na fita Zahra ta yunkura tana cewa ai dai kam yanzu za a barni naje naci dadina ko? Ta fada tana barin jikinnasa da a yanzu bai hanata ba,
Sosai Zahra ta yi kara i da farfesunta dan ko ta yi bata yiwa ɗan kurmannata ba,tas ta cinye kamar yadda Ammi ta bata Umarni, tana gamawa ta shige dakinta ta yi brosh ta daura alwala ta magriba saboda lokacin da ta shigo an kira sallah dan har Ab ma ya sauka tana kallo ya kulle kofar dan kar ta fita.
Zura hijab ta yi tana mitar an kulleta sai kace wata prizner,bata tashi a wajen ba sai da ta yi Isha ta haɗa da shafa i,tukuna ta mike ta je ta yi wanka ta fito ta yi shirin bacci,har ta kwanta sai kuma ta fara ta'adi nanin ta yadda zata yi bacci ita kadai to amma ta gwammace ta yi kwanan ita kadai akan ta kai kanta gurin dan kurma.
Sai da ya gama duk abinda yake na al'ada har nafifilunsa sai da ya yi, a lokacin wajen daya saura,fita yayi kai tsaye ya shige dakinta bayan ya bude da safaya mukulli, sosai take bacci ta cikin kwanciyar hankali dan haka cikin nutsuwa ya dauke ta ya fita da ita daga dakin,har ya kwantar da ita shima ta kwanta a kusa da ita tare da shigar da ita ji kinsa bata farka ba,hasalima rungumesa ta kuma yi da kyau tana cusa fuskarta cikin kirjinsa kamar wata yar mage,rufesu ya yi da tattausan blanket yayi musu addu'a daga nan shima yabi layinta,asuba ta gari zahrAB...
Bude ido kawai Zahra ta yi ta ganta a dakin AB a lokacin shi ya fice sallah asuba,tunzura baki ta yi kafin cikin ƙunƙuni ta ce", wai shi wannan gani yake har hanji? ko ta yaya ya bude dakin ya dauko Ni ma oho,haka nan mutum ya maida Ni kamar wata yar tsana duk minti duk sakan ya kinkimeni ko nauyi bai ji haba,duba jikinta ta shiga yi tana cewa Allah yasa bai kuma samin wannan katon macijinnasa ba yo dan ma mugunta ya za ayi ace wannan katon abun shi za a sawa mutum cikin jikinsa,mikewa tayi tana takawa dan ta tabbatar ko ya mata wani abu,jinta lafiya yasa ta ce Allah ya taimakeka yau da kowa yasan halinka acikin gidannan ehe,daga haka ta shige toilet ta yi alwala tazo ta yi raka tanil fijr bayan ta idar da Sallah ta yi zaman karatu dan shima ab din baya shigowa sai wajen shida saura....
Kafin ya shigo ta gudu dakinta tayi kwanciyarta,shima da ya dawo bai ganta ba bai damu ba,dan aiyuka sun dan cushe masa dole ya nutsu ya maida hankali.
Karfe bakwai ya samu kiran jafar akan tafiyar da ta taso musu ta sati Daya,kuma a ranar,Ab bai taba damuwa da duk wata tafiya da zata taso masa ba sai ta wannan rana.
Ba dan yaso ba ya fita dan kammala aiyukansa na ranar,dan haka Zahra koda ta tashi tuni ya fice,bata damu ba saboda ganin kofa a bude dan haka cikin farinciki ta yi ficewarta kasan.
Yau daga ita sai Ammi da Amira suka yi breakfast, daddy shima da wuri ya fita saboda mittin da yake dashi,su kuma su mama jikin siyam da ta kwana da zazzaɓi ne ya hanasu fitowa.Ammi ce ta ce", Amira ku gama ki raka doughter ta duba siyam", ayya Ammi bata da lafiya shi ne? Zahra ta tambaya fuskarta cike da nuna alhini,Amira ta ce", ey damuwar abinda ba zata taba samu ba tasa a ranta da mugun kishin da bashi da hujja bare makama", harara Ammi ta watsawa Amira tana cewa Amira ki fita idona wallahi bana son rashin kunya kinji ko", Zahra kuwa dan tabe bakinta ta yi sannan ta ce", to ammi haka zasu zauna basu ci komai ba ai mara lafiya bai kamata ya dinga zama da yunwa ba,bari na fito Amira ta taya Ni mu danyi mata ko fatan dankali da wake ne nasan zata ji fadinsa", ammi ta ce a'a Zahra ke da baki jin dadi ya da yin girki ki hakura su baba talatu zasu yi duk abinda ya dace", kalar tausayi Zahra tayi kafin cikin shagwaba ta ce", dan Allah Ammi Nifa duk kalar girkin da kika koya min nake son na fara gwadawa dan Allah ki barni", jinjina kai ammi ta yi tare da cewa shike nan kuje ku fito sai ku shiga kiching ɗin,yauwa Ammi na me sona", dariya su kayi gana dayansu sannan suka ci gaba da karyawa.
Suna gamawa, suka nufi dakin Amira,koda suka shiga tana jin alamun su ta yi saurin rufe idonta ita a dole bacci take,dan muddin ta sake ta kalli Zahra to komai zai iya kuma rikice mata mama kuwa dama tana dakinta,dan haka basu jima ba suka fito.
Zahra ce ta kalli Amira ta ce", aunty Amira bari zuwa anjima kayi mata girkin tunda yanzu bacci take yi,ey haka ne mu bari ma kawai sai muyi har lunch gana daya ko? Cewar Amira tana duban Zahra,haka za ayi,Amira ta kuma cewa amma dai ba wani abu kika shirya ba ko? Girgiza kai Zahra ta yi ta ce", a'a Ni kam me kika gani? Dariya Amira ta yi tare da cewa ai nasan hali ne da haka suka fito falon suka samu Ammi tana kallon tashar BBC...
Karfe daya da rabi su Zahra suka kammala girkinsu da duk ya cika gidan da azababben ƙamshi,Amira ce ta fita ta fara jera nasu a kan dinning yayin da Zahra ta shiga zubawa siyam da mama a kula fuskarta ɗauke da murmushin mugunta,dan wancan na dinning da aka kai daban yake da wanda take zuba musu.
Daidai lokacin AB ya dawo a gajiye saboda karfe hudu jirginsu zai tashi zuwa kasar Russia.
Amira ya samu tana jera abincin da lemuka a dinning din,Barka da zuwa ta yi masa sannan ta gaisa da jafar da ganinsa yasa ta fasa komawa keching ɗin.
Har ya fara takawa zai haye saman sai kuma ya ɗan juya kadan fuskar nan tana a yadda take kullum babu fara a ko digo ya ce", we're is she? Dan diri diri ta tsaya sai kuma tunawa da waye yake tambayar yasa ta yi saurin nuna masa keching,fasa hawa saman ya yi ya koma hanyar keching ɗin cikin takunsa me dan sauti wanda yake nuna jarumtarsa a fili.
Kallon Amira Jafar ya yi cikin kasa da murya ya ce", waye haka Oga ke tambaya da kulawa? Yar gidan yarbawa mana Amira ta bashi amsa tana dariyar ƙasa ƙasa dan kar ya jiyo su,zaro ido jafar ya yi kafin ya saki wata shegiyar dariya yana cewa shike nan wallahi Oga ya gama fadawa da yar rigimarsa amma wannan salon soyayyar tasu ya bani nishadi,Amira ta ce kai yaya Jafar ta ya ka san haka? Jan kujera ya yi ya zauna yana cewa kawo tukuici na baki kisha, langabe kai Amira ta yi tana cewa kai yaya Jafar nice fa,wani kallo ya sakar mata kafin ya ce, ai wannan auren ba hadin daddy ba ne kawai har da na zuciyoyin da suka fada SOYAYYA ta wani irin salon da su kansu basu san soyayyar suke ba.
Nan fa Jafar ya shiga bawa Amira tun daga farkon haduwar AB da Zahra da irin rikicin da suka sha da ita..
"Zahra ta shagala wajen zuba abincin su siyam fiskarta cike da fara ar me guntar da ta shirya musu "ji ta yi an rungumeta ta baya tare da zura wuyansa a kafadarta yana kallon abinda take yi da lumsassun idanunsa da suka dan shige ciki saboda rashin samun sukuni."bata tsorata ba saboda tuni ƙamshinsa ya sanar da ita ko waye"dan haka taci gaba da abinda take yi."
Numfashinsa ya sakar mata kafin cikin nutsuwa ya ce me kike yi anan? Idon matambayi ta fada kanta tsaye kuma hankali kwance",ummm ajiye kizo muyi bankwana tafiya ta taso min yau din nan" dan kar Katar da kanta ta yi a ranta tana cewa lallai ma Ni zaka yiwa wayo??,
Dabara ce ta fado mata dan haka sai ta dan marairaice fuska tare da cewa to bari na zuba maka faten kaci kafin ka tafi kuma Nima ina so dan yunwa nake ji," jin jina mata kai kawai yayi dan haka cikin sauri ta zuba masa a wani dan plet me shegen kyau da mugun rike zafi kamar kula,bashi ta yi ta ce rike muje to,kallonta ya yi sannan ya kalli abincin, tura baki ta yi tare da cewa to idan ba zaka rike ba kayi tafiyarka dama lemu zan dauka mana, "amma ai akwai a sama ko? Ni kam na nan nake so" bai ce komai ba ya karba abincin yana kallo ta yi gaba ba tare da ta dauki lemon da ta ce zata dauka ba, bin bayanta ya yi yana son yin mamakin kansa da ganin lefin Zahra amma zuciyarsa ta ki aminta da hakan sai ma kwarara masa gwiwa da tayi na tuna masa da rayuwar ma aiki da iyalansa "dan haka yaji a ransa bai aikata kuskure ba saima sunna da ya aikata".
Kiran baba talatu Zahra ta yi ta ce" maza ta dauki abincin ta kaiwa su siyam da mama,da rawar jiki baba talatu ta amsa tare da bin umarnin Zahra."
"Gaba daya suka zubawa AB dake fitowa daga keching dauke da plet ido,Zahra dake bayansa ta wurga musu harara," da sauri Jafar ya sunkuyar da kansa yana danne dariyar da ta ke cinsa Amira kam tashi ta yi ta yi dakinta da gudu dan tabbas ta cigaba da zama zata iya jawowa kanta don kuwa dariyarta bazata matsu ba".
Shi ko "AB tamkar ma bai san da mutane a falon ba hankalinsa kwance kuma cikin kamewarsa ya haye sama Zahra na biye dashi a ranta kuwa dariya take yi dan tasan yau duk kurmancinsa sai ya magantu saboda azabar yajin dake cikin abincin harma da gishirin da ta juye kusan rabin gwangwani aciki".
Suna hawa ta karba ta ce ka fara ci kafin kayi wanka ko? Bai bata amsa ba amma dai ya zauna a kujerarsa" ajiye flet din ta yi a saman tables Centre sannan ta kallesa idanunta na yin kifi kif kamar zata yi kuka ta ce" bismilla" duk da yayi mamakinta a ransa amma hakan baisa ya raya wani abu a ransa ba,dan haka cikin nutsuwa ya debi abincin da spoon din da tasa masa.
Sai kuma taji kamar ta hanasa" amma kafin ta yi yunkurin yin hakan tuni ya kai kyakkyawar loma guda bakinsa,abinka da abu me ruwa ruwa kuma yayi hucewar da mutum zai iya ci ba tare da zafi ya damesa ba,dan haka yana zubawa a bakinsa tafiya ya yi, take kuma bakinsa da harshensa suka dauki wani irin azabar yaji dama gashi AB yana da matsala da yaji."
Wani irin luuu idanunsa su kayi wanda hakan yayi matukar bawa Zahra tsoro abinka da matsalar mara magana take ta ga wani irin gumi na tsiyaya tun daga kafar sumar kansa har zuwa wuyansa ".wayyo yaya AB na shiga uku da sauri ta bude lemo ta kafa masa a baki amma babu wani abu da yayi yanayinsa kawai zaka kalla kasan yana cikin azaba, "kuka ta fashe dashi tare da rungumesa tsam tana rasa yadda zata yi dashi dan gaba daya ya fita daga hayyacinsa" .
Bakinta ta dora akannasa ta shiga tsotse harshensa tana jin yadda zafin yajin ya gauraye nata harshen gaba daya........✍🏼
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*