YAR GIDAN YARBAWA

Page44

by @zahrawriter12

.......tun daga nesa Zahra ta hango maman Sadik tana ta hada_hada da jama a.shago ya cika dam da kaya" fuskarta kawai zaka kalla kasan tana cikin farin ciki,"jinjina kai Zahra ta yi tare da yin kwafa sannan ta karasa bakin shagon tana kuma kare masa kallo ciki da bai tare da tunanin abinda ya kamata ta yiwa maman Sadik din a matsayin jan kunne ".

Maman Sadik na ganin Zahra ta fito da gudu tare da barin duk abinda take yi ta kwanta gaban Zahra kamar zata taba kafafunta", cikin gurbatacciyar Hausarta ta shiga yiwa Zahra godiya hade da kirari kamar wata marokiya", hade fuska Zahra ta yi sannan ta ce", maman Sadik ta shi bana bukatar duk wannan daga gareki,kuma dama na aiko da sako ne kafin na zo dan ke kin san wace zahra bata barin bashin gaba kar ki ga na aiko miki da uban dukiya ki dauka na yafe miki zunubin da kika aikata wa mamana ".

"Hade hannuwa biyu maman Sadik ta yi ta fara bawa Zahra hakuri har da su kuka,dan Allah zahla ka yafe min nayi kuskure ba zan sake ba na yi rantsuwa da me sama kayi min rai kar ka kwace wannan kaya pls for d sake of Allah zahla".

Harara Zahra ta zabga mata tare da cewa mantawa kika yi da Allah shi yasa kika je kika ciwa mama mutunci ko??to wallahi kin debo ruw...... hello Madam josuwa ya katse mata maganarta yana miko mata wayar hannunsa," kin karbar wayar ta yi ta tsaya tana watsa masa kallon tambaya da mamaki duka a haɗe,kafin ta bude baki ta ce", me ya kawoka nan? Wai ma meye ya tsaida kai? ce maka nayi gaisuwa zanyi na fito ? Ko kuma ance maka makota na shiga da har zanyi zaman da zaka iya jirana?kai wlh ka kiyaye Ni daga kai har me katon kan uban gidan naka sai na hada ku nayi muku hukuncin da za ku kasa fidda kanku hana da wannan dan karennasa dan dama ina ciki da ku ba mantawa nayi da ku a cikin a gender ta ba".bata saurari abinda yake fada mata ba ta juya gun maman Sadik tana nunata da yatsa kana ta ce", ke kuma punishment dinki a nan shine kullum kika bude shago zaki bawa yara mutum talatin sadakar alewa yar sha biyar din nan har zuwa kwana goma" idan ba ki ba kuma kin san sauran zan sa wanda zasu sa miki ido wallahi idan na dawo aka sanar dani baki yi ba to tabbas za a maimaita ta baya. "dan haka sai ki zaba sadaka don dole ko kwashe kaya ki koma zazzaɓinki in kin ga dama saboda rashin tawakkali ki margaya bani da asara,yanzu fara miko min alewar leda biyu na fara yin ta yau kafin na bar gurin ".

Cikin sanyin jiki maman Sadik ta shiga shagon ta dauko alewar ta mika mata,idanunta sun fito kamar zata saki kuka, dan wannan punishment din na Zahra ba karamin sokarta ya yi ba,ji take yi kafin kwana goman kayan shagon sun kuma karewa kai wannan yaro akwai azaba.fincike alewar zahra ta yi kana ta juya gun sadik ta ce ya je ya taro mata yara yanzu za ayi sadaka".

Kafin kace me yara sun cika shagon maman babu abinda kake ji daga bakinsu sai sunan Zahra,yee aunty zahra ta dawo zata ci gaba da yi mana sadaka aunty zahra Allah ya biya miki bukatunki na aheri", Amin yaran kirki daga yau zan cigaba da yi muku sadaka kamar yadda na saba amma na bawa maman Sadik ta dinga raba muku dan haka kullum da safe kuzo zata baku kunji yan albarka",yeee aunty Zahranmu."

"Gana daya josuwa saboda mamaki ya ma manta da sakon da me gida yace ya kawowa Zahra ,kawai kallon yadda yara suka rufe Zahra suna murna da yi mata addu'a ya yi,a ransa ya ce", wato a wajen yara sarauniya ce a wajen manya kuma dodanniya".

Tunaninsa ne ya katse daidai lokacin da Zahra ta kira wani yaro me suna Abbas da suke matukar shiri tun tana gida kuma ko sadaka zata yi shine me siyo kosai wajen kakarsa ko alewa ya kawo su raba, yaron Maraya ne a wajen kakarsa iya yake". yaron yana da hankali da hazaka shi yasa Zahra take sonsa ta ke taimakonsu lokaci_lokaci kasancewarsa "Maraya shi yasa ya kuma farinjini a gurin Zahra, kama hannunsa ta yi tana cewa Abbas me ya same ka ne naga duk baka da walwala kamar baka da lafiya?hawaye ya share sannan ya ce", aunty zahra tunda kika tafi na daina zuwa makaranta iya kuma jarin kosanta ya kare an daina ciniki dama ke kike sawa a siye kosan to tunda kika tafi suka daina siya sai dai su siya na maman iyabo".kwalla ce ta cika idanun Zahra da kyar ta cije ta shafa kan yaron tare kana ta ce" ayya Abbas yanzu zaka raka Ni muje gidan ka daina kuka kaji yarona".

Zabura josuwa ya yi saboda tunawa da me gida da yayi yana daga wayar zuwa fuskarsa sai ko yaga ashe har yanzu yana kan layi kuma ga dukkan alamu ya saurara kuma yaga komai da yake faruwa tunda dama kiran video call ne, sorry Oga dama", katsesa AB ya yi tare da yi masa nuni da ya kashe wayar kuma ya matsa daga inda zahra take zasu yi magana.harara zahra tabi bayan josuwa da ita harda murguda baki daga haka taja hannun Abbas suka tafi gidansu zahran.

Josuwa kuwa umarnin me gidansa ya tafi cikawa."

Zahra na shiga dakin mama ta yi turus saboda ganin uban kaya shirge a gefe gaban mama kuma kudi ne wanda ko kiyasin nawa ne bazata iya yi ba,Amira kuwa ta saki jiki da mama sai hira suke suna dariya kamar wada suka dade da sanin juna,a sanyaye Zahra ta karasa kusa da mama hannunta rike da na Abbas idanunta kuwa har yanzu suna kan uban kayan abincin da suke tsube a wajen babu ce kawai babu daga cikin nau i na abinci hatta da maggi da gishiri katan katanne kamar dai za a bude sabon wajen provision.....kafin ta yi magana wani yaro ya yi sallama ya shigo yana kiran Abbas wai yazo in ji iyarsa".dubansa Zahra ta yi ta ce" je ka Abbas ina nan zuwa kaji ka gaida iya kafin na shigo ", da to yaron ya amsa sannan yabi bayan dan aiken".

Zama Zahra ta yi tana shirin yin magana Amira ta katseta da cewa yar albarka kin yi abinda yasa mama kuka,ai fitarki ta dauka jan magana kika tafi wajen maman Sadik sai kuma kawai gashi an fara shigo da abin arziki wai kece kika ce a shigo dashi,nace Ni kaina ban san da kayannan ba" gaskiya Zahra kin yi dabara ke yar albarka ce kwarai Allah ya barku tare da yayana", yau dai a karo na biyu bakin Zahra ya kuma mutuwa dan kuwa bakinta kasa motsawa yayi sai ido da ta dinga bin bakin mama da take ta sa mata albarka dashi.tsawon lokaci Zahra tana cikin dogon nazari da tunanin wanda yake wannan aikin yana cewa ita ce,yanzu kam ta tabbatar da cewa ba ab ba ne," to me zai sa ma ab ya cika shagon maman Sadik da kaya bayan bai santa ba?? ko da yaji suna maganar ai bai tambayi komai a kanta ba?? sannan wannan na gidansu da shine ai Amira ba zata nuna bata san da abin ba tunda dole ta hannunsu zai biyo,?bubbuga kanta ta shiga yi saboda tunanin da ya cushe kan,"

Ko abincin da mama ta shirya musu dakyar Zahra ta iya ci jikinta duka a sanyaye saboda yanzu ta fara tunanin lamarin ta bangaren aljanu,shi yasa duk ta kasa sakewa,"wajen karfe biyar sai ga iyar Abbas ta shigo har da kukanta tana yiwa Zahra fatan alheri da godiya akan kayan abinci da kudin makarantar Abbas har da jarinta da ya karye da Zahran ta aiko musu,aiko take Zahra ta kuma rudewa lallai wannan aikin na aljanune tunda babu wanda yasan alherin da take yi idan ta samu dama a anguwarsu bare har ya kai wani abu gidan to ballantana ma yau din nan ta yi maganar da Abbas idan ba aljanun ba waye yasan abinda Abbas ya fada mata yana faruwa dasu?

Ana cikin haka josuwa ya kira Amira akan ya karaso yana waje,tsoron da Zahra ta ji ne yasa ta tafiya amma da da kudirin kwana ta taho gidan,"

Suna fita kofar gida taga ana tayi mata godiya har da magidanta ai take kan Zahra ya gama shiga depression ta zama kamar wata zararra babu bakin magana sai ido da jinjina kai da take yi kamar yar kadangaruwa,"

Suna fara tafiya Zahra ta fashe da kuka, tambayar duniya Amira ta yi mata taki kulata, sai kawai ta rabu da ita din tayi tunanin ko kewar gida ce ta saka wannan damuwar" dadin da ɗawa kuma tasan halin Zahra kuka ba wuya yake mata ba", har suka je gida Zahra bata daina kukan ba.

Da gudu ta fita daga motar bata tsaya ko ina ba sai jikin mama ta kankameta tana ci gaba da ihun kuka har wani sunne kai take dan kar taje idanunta su ci karo da fatalwar da take binta,lokaci daya Zahra ta raba kita gidan da mutanen gidan da rashin gimarta ko daki ta ki shiga saboda tsoro gashi taki fadar abinda ke damunta duk sai ta saka su cikin damuwa,"

Har dare ana abu daya da Zahra,dakyar Ammi ta yi mata dabara suka shige dakin Amira ta tsaya a bakin bathroom ta ce", ta shiga ta yi wanka,kin shiga ta yi wai sai dai Amira ta rakata, "zaro ido Amira ta yi tare da cewa haba matar yaya AB wace Ni da wannan aikin,Ammi jeki kawai ina da me yin maganinta dan na fara kamo bakin zaren," Ammi na fita Amira ta dauki wayarta ta fara danna kira ta video call sai da ta kira wajen uku a na hudu ya daga".

Yana zaune a bakin gado hannunsa rike da cup din cuppy Yana sipping a hankali kamar baya so fuskarnan a kame kamar kullum,ko gaidasa Amira bata samu yi ba ta ce", yaya dan Allah ka yiwa Zahra magana tunda muka dawo daga gidansu ta hana kowa zaman lafiya sai kuka take tana zabura kamar aljanunta ne suka tashi".

Harara Zahra ta watsawa Amira idanunta face_face da hawaye , tana tsaye a bakin bathroom din jikinta daure da karamin towel din wanka,"Amira bata bi takan Zahra ba ta juya fuskar wayar kan Zahra, Ab da yake saurarensu amma ya yi kamar hankalinsa baya nan, wani dan ƙaramin kallo ya yiwa Zahra kafin ya juya ya aje cup din hannunsa ya dawo da hankalinsa kan zahra da itama kallonsa take cike da wani irin kewa da shaukin da bata san daga inda yake zuwa ba".

Me ya faru?ya tambayeta idanunsa a cikin nata idanun da take ta faman kifkifta su saboda kaifin nasa idanun acikinnata, memakon ta bashi amsa ai sai wani sabon hawayen suka fara zarya,"numfashi ya dan furzar kafin cikin nutsuwa ya ce", me zaki yi? Wanka zan yi kuma Ni tsoron toilet din nake ji", ta fada cikin wata karyayyar murya me cike da shagwaba" hucin bakinsa ya kuma fitarwa sannan yana a kamensa baza ka taba cewa kallonta da maganarta kai da komai nata ma ya na tsikarar jikinsa da zuciyarsa ba ya ce", ki je da wayar bath din ki ajiye ta zan tsaya ki har ki gama", jinjina kai zahra ta yi ba tare da tunaninta ya kawo mata ai fa zai iya ganinta ba."

"Yadda ya ce ta yi hakan ta yi amma sai da ta samu saitin inda zata dinga ganinsa sannan ta ajiye wayar, a hankali idanunta akan wayar wai dan kar ta juya ya kashe", ta zame towel din tare da shigewa cikin bath din." Sai da ta gama tsaf ta daura towel ta yi brosh, sannan ta je ta dauki wayar, habarta ya nuna mata,"da sauri ta juya ta kalli mirror sai kawa taga kumfar brosh a kasan bakinta sai a lokacin ta yi wani nazari dan haka tana wanke kumfar ta jiyo idanunta akansa ta ce", yaya AB amma dai ba kallo na kake yi ba duk wannan abin da nayi ko", daga mata kai kawai ya yi ba tare da ya iya tanka mata ba,dan a wannan lokacin koda shi me yawan magana ne to tabbas ya zama kurma dan gaba daya zahra ta gama kwance masa notikan kansa ta tsinka duk wata jijiya da jini da suke aiki a jikinsa".

Ya so kashe wayar amma tasa masa rigimar akan ba zai kashe ba sai ta gama shiryawa tunda Amira ta bar dakin, " haka bawan Allah ya tsaya ta gama komai akan idanunsa ta barsa da fidda numfashi kamar me ciwon asma,shifa bai taba sanin akwai wata mace da zata razana duniyar sirrinsa ba sai yanzu da yake ji Zahra ta gama gamawa dashi ta ko wanne fanni,babu abinda yake iya yi sai tsotsar lips dinsa da cije su kamar zai hudasu", zama ta yi bayan ta saka rigar baccinta da Amira ta dauko mata, sai kuma ta sa masa kukan tabara har da buga kafafu a kasa,"

Dafe goshinsa ya yi yana murzawa kamar zai cisgesa daga jikinsa, kafin cikin wata irin murya ya ce", meye damuwar ko kina so ki kisa ne Zahr? Cak ta tsaya da kukan tana duban yadda ya koma kamar bashi ba, sannan a hankali ta ce", yaya AB ka dawo ko kuma na gudu saboda aljanune suke bibiyar rayuwata,a hankali ta bashi labarin abinda ya faru yau din a gidansu,"

Duk da Ab ba ma abocin dariya ba ne amma yau kam Zahra tasa shi wani kayataccen murmushi me fadi da kyau,sakin baki Zahra tayi tana kallonsa," kafin kuma ta tura ƙaramin bakinta ta ce," amma kuka ya kamata ka tayani ba wai kayi dariyar da ba yinta kake yi ba ko?yaya AB Ashe haka dariya yake maka kyau ka ganka kuwa?ta kuma dora da fadar abinda yake ranta",

Ki daina damuwa dukkan abinda ya faru Ni nasa josuwa ya yi kuma nace a yi da sunanki shikenan," kamewa ta yi a zaune kafin cikin tabara ta ce", Allah ko yaya AB ka dau hakkina kuma sai na rama", Nima aljanun karyar zaki min ko ba haka ba? Ya fada cikin wata siga da tasa Zahra nutsuwa kamar ba ita ba,kashe wayar ya yi ya bar Zahra cikin mutuwar jiki".

Yana kashe kiran ya saka kiran Jafar ,yana dauka ya sanar dashi ya yi masa buking dirgi ko na karfe nawa ne", amma yallabai bamu gama abinda ya kawo mu ba," ka zauna ka karasa na gama me muhimmancin," daga haka ya kashe wayar ya mike ya fara shirin komawa nageria.....✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*