YAR GIDAN YARBAWA

Page43

by @zahrawriter12

.......cikin wani irin haki mama ta ce" kai siyam waye ya yi girkinnan? Girgiza kai siyam ta yi tana faman zaro harshe maganar ma ta gagara yinta," tashi mama ta yi tana goge hawayen azabar da suka fara saukowa kan kuncinta,fita ta yi tana kwala kiran baba talatu "Gaba daya hankalinsu Ammi da suke zaune a falo ya dawo kanta,ya yin da baba talatu ta ji kira tana daga keching ta fito da gudu zuwa kiran,cikin rawar jiki ta zube gaban mama tana cewa gani hajiya ".

Sai da mama ta yi wata sheshshekar azaba da radadi sannan ta ce", waye ya yi girkin dazu da ka kawo mana? Da sauri baba talatu ta ce", a'a bani nayi girki ba kuma ban San waye ya yi ba Ni dai kawai ance na kawo muku daki", ey lallai wato kaima talatu ka shiga sahun wadanda aka asirce ko? Ya subhana me ya faru Hajiya? Baba talatu ta tambaya cikin mamaki".

Ammi ta ce", mama me ya faru kike tambayar wanda ya yi girki ne? Cikin fasifa da azabar murdawar da cikinta ya fara yi ta ce", se ka fara gaya min wanda ya yi girkin se na fada me ya faru? "Ammi ta ce", ayyo to doughter ce ta yi ita da Amira", hannu mama ta ɗora aka ta zunduma ihu kafin ta ce", sike nan munyi mutuwa yaro yazo ze kasemu nida yarona", siyam ce ta fito daga dakin hannunta rike da kular abincin ta direta a gaban Ammi cikin rawar murya har yanzu ta kasa rike miyan bakinta ta ce "Ammi dan Allah ki ci abincin nan kiji idan bakwa yarda da halin Zahra to yau zaku yadda",Amira ta yi caraf ta ce", me kike nufi da halin Zahra? Zahra bata da wani mugun halin da za a kyamaceta kawai dai tana tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro kuma tana bi da marasa gaskiya ta hanyar da ta dace a horas dasu", ammi ce ta katseta ta hanyar daga mata hannu sannan ta sunkuya zata dauki spoon ta debi abincin ,da sauri Amira ta janye kular tana zabgawa siyam harara, bata saurari kowa ba ta mikawa baba talatu tana cewa baba talatu fita da abincin nan babu wanda zai ci bare ayi ɗa kwance uwa kwance dan ku kunci be zama dole ace muma sai munci ba Tom," lallai wannan yaro baka da mutunsi Ni kake fadawa maganar banza to wallahi ubannaka ze sigo sai na sa ya ci maka uwa", Kum....wata kara cikinta da yayi babu shiri ta rufe bakinta tare da juyawa da gudu har zaninta na hardeta sai da ta fadi sannan ta mike da gudu hannayenta rike da wajen zamanta....

"Zahra da tun ɗazun bata ce komai ba saboda har yanzu bata gama fita daga mood dinta na tafiyar AB ba,bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba harda sunkuyawa" hada ido da suka yi da Ammi yasa ta dan tura baki tare da waskewa tana kif_kifta ido irin na marasa gaskiya,Zahra abinda siyam ta fada gaskiya ne shin ke kika sa musu yaji a abinci?

"To me yasa baki zuba mana gaba daya ba eye?

Kuka Zahra ta fashe dashi lokaci daya ta firgice har da cewa dan an ga Yaya AB baya nan shine za ayi mata sharri",Ammi ta dafe kanta cike da damuwa idanunta akan Zahra dake ta burgima a kasa kamar wata yar baby,maida kallonta kan siyam ta yi tana cewa jeki siyam kuyi hakuri in sha Allah bazata sake ba", fuuu siyam ta juya fuskarta a kumbure" dan duk da haka Ammi ba burgeta ta yi ba dan bata ga wani action da ta nuna akan Zahra ba."

Sai da taga siyam din ta kule a dogon corridor din da zai maida ita dakinta sannan ta juya kan Zahra ta kamo hannunta tana cewa zo doughter yi hakuri idan banyi miki fada a gabansu ba cewa zasu yi na daure miki kugu kamar yadda suke gani,share hawayenki kinji doughter na", mikewa Zahra ta yi fuska kamas kamar ba ita ta gama danbarwar kuka ba."

Amira kuwa dariya ta sheke da ita har da rike ciki tana kwaikwayon maganar mama",dakuwa Ammi ta yi mata sannan ta gimtse dariyar, Zahra kuwa ranta fes suka cigaba da hirarsu Ammi tana wani lallabata kamar kwai.

Siyam kuwa tana shiga dakinta itama kai tsaye toilet ta fada tana tsinewa Zahra a ranta tsanarta na karuwa da burinta akan Zahran,dama itama dauriya take yi tun ɗazun dan kar Zahra da Amira su yi mata dariya,aiko tana hawa je kake ƙuuuuu karar gudawa part 2🤣..

Kwana biyu Zahra ta bar su siyam su huta saboda tana so ta lallaba Ammi da daddy su sa a Kaita gida ko dan taga mama sannan ta ci uwar maman daddy..

Ammi na sane idan AB ya yi waya da ita bata yi masa maganar Zahra bare kuma ta ce", zata bata su gaisa,duk da tana fahimtar wani lokacin saboda Zahran yake kira amma miskilanci ba zai bari ya tambayeta ba,ko tambayar lafiyarta zai yi sai dai yayi musu jam U da Amira ,dan haka itama sai ta yi biris da shi tana son ganin iya gudun ruwansa,"yayin da kuma ta gefe ta ke ci gaba da gyara diyarta ciki da bai kamar wadda zata canja mata halitta".

Yau Laraba wadda tayi dai_dai da kwana uku da tafiyar AB Zahra ta gama shirinta tsaf dan kuwa tasha alwashin yau ko me za ayi sai taje gida dan har ga Allah tana son ganin mama da kuma yarbawan gidansu,dan haka sama ta hau tayi kyakkyawan shiri kamar wata matar shugaban kasa saboda yadda jikinta yayi wani dumimi komai masha Allah fatarta luf kamar wadda ke kwana cikin ruwan madara, doguwar rigar Les din da ta saka ta kara fiddo ainahin surarta da ke karawa siyam bakin kishi akanta,cikin wani shegen taku take saukowa daga saman yayin da siyam da mama har da su Ammi suke zaune a falon gaba daya suka bita da kallo ga ƙamshinta da ya bude wajen kamar wadda ta yi barinsa ajikinta."

Zama ta yi kusa da Ammi tare da dora kanta a fadarta sannan cikin shagwaba ta ce",Ammi zanje gida inga mama"to Zahra kin sanar da mijinki ne??dago kanta ta yi tana kallon Ammin baki sake kana ta ce", to Ammi ta ina zan gaya masa? Dan Allah Ammi ki barni na je Allah ba zan ki dawowa ba na fasa guduwarfa tun rannan", au da guduwa zaki yi? To ashe kuwa babu ke babu fita kin tona kanki da kanki", Ammi ta fada tana zame kan Zahra daga kafadarta irin taya fushinnan"kasa Zahra ta zame ta ɗora kanta a cinyar Ammin sannan ta fara sheshshekar kukan da babu hawaye dan yau ta ce" bazata ɓata kwalliyarta da hawaye ba",oh ke ma Zahra da saurin kuka kike to kunga bari na kira babannawa in yaso sai ki tambayesa da kanki",

Ɗif Zahra ta yi tare da mikewa ta zauna gefen Ammin tana dan gyara gefen fsukarta da hawayen suka so zubowa suka fara bata wajen, sannan ta ce", to Ammi yi sauri ki kirasa kar lokaci ya kure", ikon Allah yau naga wata sabuwar taɓara mama da mamaki da haushin su ya gama cikata ta fada tana yiwa Zahra wani mugun kallo".

Dariya Amira ta yi tana cewa to mama kin san ita aikin KURUCIYA sai da uzuri,"dakuwa mama ta yiwa Amira tana cewa Wallahi Amira ka fita daga idona na rufe ka maida mamanka kamar kakan ka ko?siyam kuwa bakinta mut ya mutu sai ido da ta zubawa Zahra da Ammi dan so take taga yadda za ayi AB ya bar zahra fita," aiko ga mamakinta Kira daya ya daga kuma video call Ammi ta yi masa,"

Yana zaune daga gaban tap dinsa jikinsa sanye da wata tattausar riga me tsananin kyau fuskarsa babu yabo ba fallasa yana nan as usual cikin kamewar nan tasa,cikin taushin murya ya gaida Ammi da yake mata tambayar da ya saba kullum tun bayan tafiyarsa,"yauwa dama Zahra ce ke son zuwa gidansu shine nace sai dai ta tambayeka shi yasa nayi maka kiran katsaham", ta fada tana haska masa Zahra dake hakimce kamar wata sarauniya,karbar wayar Zahra ta yi sai kuma ta rasa abin cewa ," ammi ta ce", haba doughter ki gaidasa mana" tura baki ta yi kafin ta ce", ina kwana ya gajiya? Zubawa karamin bakinta da yake jin kewarsa ido yayi kafin ya dan daga labbansa a hankali ya ce", lafiya ya kk?? Harara ta dan sakar masa tare da kawar da kanta,sai yanzu take jin haushin banzatar da ita da ya yi har ma take nadamar amsar wayar,to amma tunda ita take nema yanzu dole ta yi hakuri ta samu biyan buƙatar ta kafin ta rama abinda ya yi mata", tashi Ammi ta yi ta bata waje Amira kuwa gyara zama ta yi saboda taga mutanennata suma basu da alamar tashi kuma hakan ya yi mata dai_dai dan haka ta gyara zama dan kallon show din da za ayi."

"Dan karyar da kai ta yi tare da danne haushinsa da take ji ta ce", dan Allah ka barni na je gida Allah ba zan zauna ba zan dawo", ta karasa maganar idanunta na cikowa da kwalla,numfashi ya dan fesar kafin ya dage girarsa guda da yi mata alamar me zata je yi? Kambu ta fada tana zaro manyan idanunta da suka sha gazal ta ce", wai ma Ni zaka tambaya me zanyi a gidanmu? To Ni kam ka barni na je ko na tafiyata wani wajen kuma babu wanda zai sa na dawo" ya ma za ayi Ni da gidanmu a ce me zanyi ??saboda kai kullum kana ganin Amminka da daddy shi yasa baka damu da damuwar ganin nawa ba,tana fada hawayen suka karasa saukowa zuciyarta cike da damuwar da bata san ta mece ba", josuwa zaizo ya kaiki idan kin gama sai yaje ya dauko ki shike nan?ya tambayeta cikin wata irin kasala da ganinta ya kuma haifar masa da ita yana kuma lumshe idanunsa da suka sauya daga ainahin kalarsu",

"Dan ihun da ta yi tare da yi masa kis ta jikin screen din wayar ya kuma konasa da tsayar da duk wani kuzarinsa, ita kuwa tuni ta kashe wayar ta mike tana rawa da juyi a gabansu siyam da suka kafeta da ido yawa tsoffin Mayu," tashi Amira ta yi tana taya ta da wakar auta mg boy da yake cewa(ina kewa ina kewar masoyiya ina kewa ina kewar Aminiya ",abokiyar shawara kece kin dara kin san in ba dake ba sai in hakura ,ki bani yar dama a sanda nai nema ki mini alfarma sanya ni a zuciya " ki kauda yan gulma irinki ke nema suna ta shan fama sun zaga ko ina)".

Baitukan da suka dinga maimaitawa kenan suna tikar rawa kamar wanda aka kunna musu mp," cikin wata irin fusata siyam ta bar falon kishi kamar ya kasheta mama kuwa kin tashi ta yi tana cewa yau sai naga karshen rashin kunyarku fitsararru haka kawai yaro kazo ka koyawa yaron gida rashin kunya." Zahra ta mikawa Amira hannu suka tafa sannan ta ce",aunty Amira dama kina sha'awar shagali ɗan ta yi ne kawai baki samu ba ko? Kwarai ma kuwa matar yaya ai Ni ina son irin wannan sabgar tana matukar kayatar dani da sanyani nishadi," a haka Ammi ta fito ta same su tana cewa Amira ki shirya ki raka Zahra inji yayanku", yeee zahra ta fada tana kankame Ammi saboda murna itama amiran da gudu ta koma daki ta shirya,alokacin tuni josuwa yazo yana waje yana jiransu,"cikin farin ciki suka fita dan Zahra tasan kasancewarta da Amira babu abinda zai rageta da shi wajen yin caskalenta da yarbawanta yadda ya kamata".

A kofar gidansu Zahra josuwa ya tsaya, kafin ya fito ya bude mata kofar tuni ta fincike murfin kofar ta fito,ko dan tsayawa ta jira Amira bata yi ba ta yi cikin gidansu da gudu tana kwala kiran mama,"girgiza kai Amira ta yi fuskarta cike da murmushi sannan ta bi bayan Zahra tana cewa josuwa ya je idan sun gama zata kirasa yazo ya dauke su ".

Kafin kace me gidan yarbawa ya kacame da murnar zuwan Zahra kamar basu ne suke fatin barinta gidan ba,dan fa da gaske sosai sunyi kewar Zahra ita kanta ta yi kewarsu da yawa(shi yasa masu iya magana suke cewa saboda turken wawa duk yadda kake tsama da mutum in dai kuna kwana ku tashi waje daya kuka zo kuka rabu sai kunji kewar juna)

Mama ce ta ture Zahra ta janyo Amira tana cewa ke kam Zahra yaushe zaki hankali??ashe tare kuke da bakuwa kika manta da ita a gefe? Dariya Zahra ta yi tare da cewa mama wallahi duk dadin ganinki ne ya cika Ni kanwar dan kurma ce fa"cikin rashin fahimta mama ta ce", waye kuma.dan kurma? Dan gatsine baki ta yi kafin ta ce, " yaya AB mana" harara mama ta watsa mata bata ce mata komai ba ta ja hannun Amira suka shige ciki,"

Ita fa mama a tunaninta Zahra ta fara hankali saboda ta ganta tsaf kamar matar shugaban kasa idan ba shirmen ta taɓa ba baka isa kace bata canja ba,shi yasa ta barta a baya bata taso ta gaba ba,ita ko Zahra na ganin haka ta yi wuf ta fita daga gidan tare da janyo maman iyoka ta yi mata rakiya zuwa gidan maman Sadik,"suna fitowa maman iyoka ta ce", ai maman Sadik yanzu yana shago baza ka same sa a gida ba", ban gane ba?Zahra ta fada tana rike kugu.

Maman iyoka ta ce", ah bake ne ka aiko masa da jari ba saboda kayansa da ka ara na shago? "Cikin rashin fahimta Zahra ta ce", kai maman iyoka maza yi min bayanin da zan fahimta dan wallahi bana fahimtar komai" maman iyoka ta gyara tsayuwarta kana ta ce", ai a ranar bayan kun gama waya da mamanka da maman Sadik ya zo ya risa mamanka sai ya biyasa kudin da ka yi masa asara, to a ranar ne da dare maman Sadik yazo yana yiwa mamanka godiya wai ka biyasa kudinsa har da kari saboda ka sika masa shagonsa da kaya ka kara masa jari so yana so ya mika masa godiya gareka sosai..dakatar da maman iyoka zahra ta yi ta hanyar cewa Tom na gane ai mantawa na yi kin san ni idan nayi alheri sam mantawa nake nayi dan hak koma gida gidan su nadiya zanje",

To maman iyoka ta fada cikin rawar jiki dan tasan yau tunda Zahra tazo to kuwa kakarsu ta yanke saka".

Zahra tsaye ta yi a gurin tana cizon yatsa gaba daya kanta ya kulle tabbas da tana da waya yanzu babu wanda ya dace ta kira sama da ab dan kuwa tasan wannan aikinsa ne", kwafa ta yi cike da takaicin ya biya ba tare da ta rama rashin mutumcin da tazo ta yiwa mamanta ba.

Ko da yake yanzu ma bata ɓaci ba maman Sadik baki isa kici bulus haka da yawa ba ina wallahi kin yi kadan,Ni ba damuwata alherin da aka yi miki ba damuwata shine ramuwa", daga haka ta dauki kafa sai shagon maman Sadik.

"Da sauri josuwa ya dannawa ogansa kira kamar yadda ya umacesa bayan yaga wucewar Zahra zuwa shagon maman Sadik.....✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*