Page45
.......cikin bacci Zahra ta dinga shako ƙamshin da tasan duk duniya mutum guda ne wanda ta taɓa jinsa a tare dashi," juyi ta yi dan ci gaba da baccinta tana dan turo baki sannan cikin Muryar bacci ta ce", shi mutum ba dawowa ya yi ba amma ya yi ta yiwa mutane gizo,"
Murmushi me sanyi ne ya subcewa Ab dake tsaye jikin mirror yana fesa turaren sa me sanyi na bacci". Shaƙar kamshin ta kuma yi sai kawai ta shiga bude idanunta a hankali tana kallon ko ina na dakin da yake babu haske sosai sai bata kula da Ab din ba,zuro kafafunta ta yi dan mikewa ta bar dakin dama ba baccinne ya kawota dakin ba zuwa ta yi kawai ta fesa turarukansa "amma" sai ta samu kanta da hayewa saman gadonsa bata ma san bacci ya kwasheta ba."murza idanunta ta yi tana cewa Allah yasa Amira bata rufe dakinta ba da taga ban koma b.... innalillahi wa innahu sulaimana wa innahu bismillahi... ..ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba Allah ka yafe min Ni Zahra daga yin shigar aljanu shike nan kuma sai su fara bibiyata." Zahra ta fada cikin neman maboya lokacin da ta yi arba da Ab dake sanye da karamin towel Yana gyara tattausar sumar kansa ta asalin Larabawa."
"Duk abinda take yi kuma take fada yana jinta "amma bai ko kalli inda take ba har sai da ya gama abinda yake sannan ya juyo ya fara takunsa a hankali idanunsa a kanta duk da ba wani ganinta yake sosai ba," ganin ya nufota yasa Zahra ɗora hannu aka cikin hawayen da ba wahalar zuba ne dasu a wajenta ba ta fara cewa" dan Allah aljanin larabawa ka yi hakuri wlh ba zan kara tsorata su maman daddy da sunanku ba,"idan kuma kai ɗan uwan ɗan kurma ne to dan Allah inci alfarmarsa kar ka bari na mutu dan ance duk wanda ya taba ganin aljani ido da ido to mutuwa zai yi "dan Allah ka yi hakuri na cika burikana, daga ciki ina so idan ɗan kurma ya dawo na fada masa nayi kewarsa idan yaso sai ku tafi dani duniyartaku dan nasan can zaku kaini saboda abinda nayi na burge mutanenku amma Ni ba dan haka nayi ba wlh....ta tsaya tare da hadiyar miyan da tunda ta fara maganar bata hadiya ba saboda tsabar tashin hankali, dan ita fa da gaske aljani me kama da ab take dauka ne a gabanta". colm doun" ya fada cikin taushin murya,aiko take Zahra ta kuma rikicewa tana cewa lahh wlh har maganarsu ma iri daya Allah ka fidda zahra daga cikin wannan Bala i na mutanen boye,Ni wlh turarensa kawai nazo dauka amma ba shigowa nayi da niya ba yanzu haka ma kuka sani baccin"dafe kai AB ya yi tare da shafa sumar kansa yana rasa yadda zai yi da rigimar Zahra,shi da ya dawo saboda samun nutsuwar rayuwarsa amma sai ga abinda ya fara cin karo dashi."
"Jarumta ya yi ya nufeta gadan gadan duk yadda take masa magiya tana mannewa da karshen gadon da ta kai "idanunta a rufe amma hakan baisa ya dakata daga Binta har saman gadon ba,"tana ihun kuka da karanta ƙul'a'uzai tana tofa masa ya riketa kam a jikinsa kafin cikin wani irin shauƙi me haɗe da kewa doki kauna soyayya", ya haɗe bakinsa da nata ya shiga bata wata irin sumbata da tunda ta fara shan zakin bakin ɗan kurmanta bata taba jin zaki da gardi irin ta yau ba,"cikin zafin naman dake cike da wata irin kewar da bai taba sanin da a kwai irinta a duniya ba yake bin fuskarta da duk wani abu dake jikinta da sumbatarsa me tsayawa a rai da zuciyar Zahra," Zahra kuwa yadda ya kidime yake neman kidimata yasa ta fara gasgata shi din ne ba aljani ba,to amma ta ina ya dawo?yaushe kuma? Shi da yace sati Daya zasu yi me yasa ya dawo yau? Me ya dawo dashi cikin daren nan?bata da amsa domin Ab bai bata damar yin tambayoyinta a sarari ba saboda yadda ya kanainaye komai nata kamar zai maida ta cikinsa", jin matsar ta yi yawa yasa ta dan saki karar da ta kuma sashi cikin wani hali domin ita Zahra komai nata zuwa yake yi da wani irin salon tafiya da hankali ,duk da cewa ba wai ta yi ne dan jan hankalinnasa ba".
"A hankali ya dan sassauta rikon da ya yi mata kafin cikin kamewarsa da idan kana wajen baza ka dauka shi yake neman cinye Zahra ba,ya ce", me yasa kika cika tsoro ne? Harara a duhu ta yi masa kafin cikin gunguni ta ce", to ba kaine ba waye yasan zaka dawo gidan a wannan lokacin? sorry ya fada yana sumbatar dan karamin bakinta da ya kuma yin jajawur saboda shan da yasha wajen Ab.
"Umm umm "naki din", ta fada tana makale kafada da kuma tunzura baki kamar zata yi kuka,"hancinta yaja yana dan sakin numfashinsa akan fuskarta,kawar da kanta ta yi tana cewa Nifa har yanzu ban yadda kai ba aljani ba ne ba"lumshe idanunsa ya yi yana fatan rikicin Zahra ya tsaya iya KURUCIYA kuma iya kanta kar abun ya masa yawa,"maganarta ce ta katseshi daga faman sunsunar fuskarta zuwa wuyanta da yake yi,turesa ta yi tana cewa dole fa sai naga ƙafarka idan babu kofato to sai na yadda kaine ɗan kurmana".numfashi ya dan fesar kana ya mikar da dogayen ƙafafunsa masu zara_zaran yatsu farare tas kamar ba a taka kasa da su", kafin yayi magana ta mike ta kunna fitila me haske tare da dawowa kusa da kafafunnasa tana kare musu kallo kamar wadda take kirga yatsun",a hankali tasa hannu ta taɓa kafar ganin bata canja ba sai tasa dariya tare da fadawa jikinsa ta rungumesa tana cewa yaya AB i miss You i miss your lips and shurunka da kallonka". Sai kuma ta kebe baki har da guntun kwalla ta cigaba da cewa komai ka tafi dashi sai ƙamshinka kawai ka barmin,"ta fada tana dan kaiwa kirjinsa da ba kaya duka, rike hannunta ya yi yana yi mata kallon da yake bin duk wata gaba dake jikinta,bai iya furta komai ba sai hade bakinsu waje daya da yayi tare da cire karamar rigar dake jikinta ,ya shiga wassafa mata komai a aikacensa ba tare da ya wahalar da bakinsa da ko ya fada ma bazata fahimta ba, wannan sirrin Zahra yar gidan yarbawa ne", asuba ta gari zahrAB".
"Mutanen gidan dai sai wayar gari su kayi da Ab cikin gidan,babu wanda yayi masa tambayar ya akayi dan tuni suka je gano dan haka kowa ya fuske abinsa abinka da yan boko wayayyu",Ammi ce dai da bata ga Zahra ba ta tambayesa ko me yasa bata sauko ba? "Nothing" kawai ya ce", da ammi ya cigaba da karyawarsa cikin nutsuwa kamar ba wani abu da yake tunani,nan ko shima tunanin dalilin rashin saukowartata yake,tunda shi dai yasan da kansa ya mata wanka ya shiryata tana faman yi masa tabara kamar wata yar yaye," kaya kawai ta tafi sakawa shi kuma ya sauko kasan dan haka baya ce ga abinda ya hanata saukowa ba."
"Yaya AB" yaya AB"yaya AB ", kamar daga sama yaji siririyar Muryarta da kamar ana busa sarewa tana kwala masa kira daga can sama cikin taɓara da salon da bata san tana yinsa ba", gaba daya suka juya suna kallonta Ammi har hankalinta ya fara tashi da tunanin ko wani abu ne ya sameta", daddy ne ya ce", zahra me ya ke faruwa ne?tura bakinta ta yi tana kallon AB cikin yar harara me sanyi".
Ammi ta kuma cewa doughter me ya sameki?
"Ammi yaya AB ne fa alkawari mu kayi dashi tun kafin ya tafi kasar waje akan idan zan sauko zai dinga goyani idan ba haka ba zan fada muku abinda yake m.....su kansu basu san yaushe ne? Ya a kayi ba ya tashi? kawai dai sun gansa a can sama wajen Zahra bakinsa a kannata yana sumbatar dole da wata kunyar ai Gara wata🤣.
Turesa ta yi tana cewa idan ba kayi min goyon ba zan fada musu", dagowa ya yi ya zuba mata idanu na wani lokaci,kafin kuma ya ja hannunta a hankali suka koma cikin falon," suna shiga yaja ya tsaya sannan a hankali cikin nasiha da kamewa ya ce", zahr abinda yake tsakaninmu sirrine ba a fadawa kowa dan haka ko ke zan miki a makwancinmu karki kara kwatanta fadawa su Ammi ko amira ko wani da ban".
Au dama ba kawaye ne kawai ba a fadawa ba? Ta tambayesa cike da KURUCIYA ,"gyada mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba," shigewa jikinsa ta yi tana cewa to yaya AB ranka ya ɓaci ne? Hancinta ya sumbata a hankali yana cewa sosai kuwa yaso ɓaci amma tunda baki fada ba shike nan",dariyarta ta yi me kyau tana cewa to ba zan kuma ba tunda ranka yana ɓaci bana so ka daina bani zaƙin bakinka me daɗi", lumshe idanunsa ya yi yana jin wani irin yanayi na shauƙi da kauna mara algus wadda aka ginata ta wani salo me taba rai da zuciya," muje ba sai ka goyani ba tunda idan ka goyani Ammi zata gani da daddy,amma dai idan siyam da amira suka gani ai ba komai ko? Jinjina mata kai ya yi idanunsa na bin ko ina nata da kallon kai tsaye", jan hannunsa ta yi suka fita tana masa hirar da kusan rabinta shirme ce,"
"Yau kam siyam suman zaune ta yi dan duk abinda ya faru tana wajen,numfashi ma dakyar take fiddasa kamar wata me ciwon numfashi",
"Ko da ya zo fita sai da taso masa rigima akan sai ta bisa dakyar ya lallabata ta koma," Jafar da Amira kuwa babu abinda suke sai dariya tare da tu ajjibin wannan lamari na Oga AB,duk da cewa idan suka fita sosai yake komawa ab dinsa amma a gaban zahra kam dakyar yake iya control din kansa".
........wata irin durgowa Adebayo ya yi daga katangar magarkamar da aka kaisa,"kafin ya fara waige_waige domin samun hanyar ficewa daga cikin dajin,"wata siririyar hanya ya bi yana gudu don kuwa idan ya tsaya zasu iya kamasa,sai da ya yi nisa sosai sannan ya tsaya yana hutawa tare da maida numfashi, sosai yaci wahala kafin ya samu ya gudo daga magarkamar tare da taimakon wani kasurgumin kiler kuma ba haushe me suna durga".
"Durga ya bawa Adebayo address din inda zai je ya jirasa dan shi fitowarsa me lasisi ce ba wai guduwa zai yi ba,"shi yasa ya fara yiwa Adebayo hanyar guduwa ",dan ba dan ya tsaya temakon Adebayon ba da tuni ya dade da fita ".
"Kai tsaye Adebayo ya samu mota ya bada address din inda za a kaisa,"ba tare da yayi tunanin komawa ga iyalansa ba,domin basu ne a gabansa ba fansa ce a gabansa dan haka zai je ya jira durga da zai fito gobe domin ya taimaka masa da karfinsa ya dau fansar abinda Zahra ta yi masa."
"Mashin yana saukesa a kofar gidan da yake a kulle kamar ma ba mutane a ciki "ya shiga kwankwasawa dan shima ba dan durga ya bashi tabbaci akan cewa da yaransa a gidan ba to da juyawa zai yi," sai da ya jima yana bugu kafin yaji wata murya kamar ta mace tana tambayar waye?,kai tsaye ya fada mata sunansa dan umarnin da durga ya bashi kenan,aiko ga mamakinsa bude kofar tayi tare da figosa ta maida kofar ta rufe,"nuni ta yi masa da ya biyo bayanta," binta ya dinga yi har zuwa cikin matsakaicin falon da ke cike da hayakin wiwi da barasa da duk wani nau in kayan maye."
"Bash dake zaune a kan kujera yana zukar shisha tare da wiwi a tare cikin ƙwarewa da iya salon iskanci ya dago jajayen idanunsa ya kalli Adebayo sannan ya maida kallonsa kan femi dake tsaye tana jiran umarninsa" dan idan durga baya nan to bash shine Oga a wajen," nuni ya yi mata da ta kaisa daki ya huta kafin gobe Oga ya karaso".
Tofa Adebayo da bash da femi sun hade waje daya me kuke tunani?? Muje zuwa mahaukaci ya hau doki......
"Yau ma Ab bai kai dare ba dan a masallacin gida su kayi sallah da daddy."sai da suka yi Isha sannan suka dawo, lokacin Zahra tana sama, ta sa wasu kananan kaya sai lankwashe lankwashe take a gaban mirror tana gwada yadda ake tafiya da dogon takalmin da tasa". Gurdewa ta yi da takalmin tana shirin yin kasa ab da shigowarsa kenan ya tallafota jikinsa yana cewa zahr me yasa bakya ji wannan takalmin ai yadda ke zaiyi? Mikewa ta yi tana cewa a'a yaya AB ba zai yadda Ni ba,to yanzu me yayi miki? Ya tambayeta yana mika mata kwalin dake hannunsa", karba ta yi tana cewa yaya AB me ka siyo min na manta ma baka bani tsarabata ba", tsaraba ta wuce ta micijin da na baki",ya fada a hankali kamar bashi ya fada ba,tura baki ta yi ba tare da ta ce komai ba ta shiga bude kwalin da ya bata."
"Wata irin karar murna Zahra ta yi tare da kai masa rungumar da ta kusa tsaida numfashinsa.....✍🏼
A tunaninku me sarki ya bawa sarauniyarsa?
Me zai faru idan Adebayo da bash suka san cewa abu daya suke shirin farmaka?
Me shurun siyam da mama ke nufi anya babu wata a kasa?
To mu dai Zahra Allah ya fiddaki tsakiyar makiya
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*