Page46
.......tare da dora bakinta kan nasa sai da ta yi masa kyakkyawan tsotsa sannan ta sakesa ta yi hanyar fita da gudu, cikin zafin nama ya janyo ta yana cewa, "zahr a haka zaki fita"? Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta kuma rungumesa tana bashi hot kisses a duk wata gaba ta fuskarsa!" a haka ya janyo abayarta da ta cire ya saka mata dan yasan fita kasa take shirin yi,yana saka mata ta sake shi ta fita da gudu tana kwalawa Ammi da Amira kira su zo suga sabuwar waya me karshen kudi da kyau yaya dan kurmanta ya siyo mata".
Ammi ce ta tareta tana cewa, "dan Allah doughter na rokeki ki daina yawan gudunnan saboda nan gaba zai iya zama matsala", ai ina Zahra bata saurari abinda Ammin take cewa ba ta rungumeta tana nuna mata ending iPhone da ya AB ya siyo mata,"kai masha Allah doughter dan kurma ya kyauta da wannan babbar tsaraba da ya bamu" hayaniyar da su siyam suka ji yasa su fitowa suna raba idon ta inda zasu ga Zahra na kukan tashin hankali na gaske, dan a kullum burinsu kenan wannan kukan shagwabar wata rana ya koma kukan azaba da radadin masifa a gareta,sai kuma duk su kayi turus!, ganin sun kuma rungume juna da Amira suna murna,Amira ce ta karbi wayar daga hannun ammi,tana cewa "matar yaya ke ce fa ta biyu a rike wayar nan a Nijeriya dan yaya AB ne na farko ke kuma ta biyu".
Zuru siyam ta yi tana kallon wayar da gaba daya burinta akan son riketa ne, kai hasalima son mallakar ab harda na neman son ya sai mata wayar, ashe ba ita ce zata rike ba makiyiyarta ce zata rike,hannun mama kawai ta kama suka juya suka bar falon dan bakinciki ba zai barsu su ci gaba da kallon wayar da me wayar ba.
Daddy ma sosai yayi farinciki yasa albarka daga nan fa suka wuce dakin Amira, suna zama Zahra ta ce, "ki tura min wannan wakar da kika rera rannan kamar kewa ko"? "Dariya Amira ta yi! tare da cewa kina son wakar ne"? "Sosai ma kuwa ki tura min wasu masu dadi dan Allah" "karki damu" cewar Amira tana buɗe wayar ashe ma har an sa sim da uban Kati da data kamar wayar yarkasuwa, suna kunna wayar kira ya shigo kamar jira ake yi, mamana suka ga anyi save da nomber da aka kira," mama ce" Amira ta fada tana danna ok dan amsa kiran.
Cikin rawar jiki Zahra ta karba wayar,tana cewa, "mamana kece"? daga can bangaren mama dake rike da wayarta me ɗan karen kyau da Ab ya aiko musu ita da Abba ta ce,"na'am Zahra ke dai Allah ya yi Miki albarka,ashe har da waya a cikin kayan nan,sai ɗazu kawai muna duba kayan muna muku addu'a ke da mijinki muka gansu guda biyu iri daya,dan Allah zahra ki yi mana godiya wajen mijinki da iyayensa mutanen kirkine sosai,tabbas mun bada ke a hannun da ya dace kuma in sha Allah ba zamu yi danasani ba,ke kuma ki nutsu da wannan sakarcinnaki ki yiwa mijinki biyayya da iyayensa ki guji duk abinda zai bata masa rai".
"Tom mama ai Nima ya siya min wayar baki ganta ba me kyau ita ce karshen waya,mama kuma ai ina gudun bacin ransa tunda ina jin maganarsa, amma fa yau na fara jin maganar tasa mama"murmushi mama tayi tana tuna ranar da Zahra zata yi hankali,miƙawa Abba wayar mama ta yi!,shima ya yiwa Zahra nasiha me haɗe da gargaɗi akan sakarcinta,shima dai ta amsa masa da irin amsar da ta bawa maman,da wannan su kayi sallama cikin farin ciki".
Basu san lokaci yaja ba suna kan waya,dan ko duba lokacin basayi.
A can bangaren AB kuwa,ya gama duk abinda yake,har aiki ya taba a tap dinsa, yana yi yana duba a gogo tare da duban kofa lokaci lokaci,amma shiru babu Zahra babu alamarta har kusan ƙarfe ɗaya saura,rufe tap dinsa ya yi ya miƙe ya fita daga falon zuwa ƙasa dan dubawa ko tana nan,ganin bata falon yasa shi nufar ɗakin amira.
Suna zaune a saman gadon Amiran,Amira ta loda mata waƙoƙin Hausa na zamani masu daɗi suna ji suna gyada kai!,ji take kamar ita ce ke rera waƙar,batare da zato ko tsammani ba yaji anyi sama da ita,wayar hannun amira ya karba ya juya sabe da ita a kafaɗarsa,"ayya yaya ɗan kurma ka bari mu ƙarasa yanzu fa zamu gama na taho"bai tanka mata ba kuma bai yi mata abinda take so ba,dan haka ta tura bakinta tana ƙunƙuni ƙasa_ƙasa.
Shi da kansa ya yi mata shirin bacci tana ta faman yi masa ƙiriniya amma har lokacin bai tanka mata ba,ita kuma so take sai ya magantu, dan haka ta ci gaba da ture duk rigar da ya ɗauko mata tana cewa ba ita take so ba,riga ta shida ya ɗauko ta karɓa ta kalleta sannan ta taɓe baki tana cewa,"ni bana son wannan ta yi min tsirara da yawa",bai ce komai ba sai tattareta yayi daga ita har towel ɗinta ya ɗauketa sai cikin dakinsa, duk bige_bigen da take yi na son ya sauketa bai kulata ba sai da ya danganeta da gadonsa tare da fizge towel ɗin ya yi cilli dashi gefe ɗaya,sai a lokacin ya buɗe bakinsa ya yi magana cikin kamewarsa,ya ce,"am tried da wannan jan rannaki baby"za ta yi magana ya rufe bakin da nasa da haka kuma karatun ya canja da wata sassanyar SOYAYYA me gudana cikin jiki da ruhin ma a bota shauƙin juna,asuba ta gari zahrAB.
Yau gana daya gidan basu tashi da wuri ba,dan haka babu wanda ya fito cin abincin safe sai misalin sha daya saura,kasancewar weekend ne ab da daddy duka suna gida.
A hankali AB ya matso jikin Zahra dake tsaye bakin mirror tana ta daukar selfe da sabuwar wayarta sai iyayi ake yi na farin shiga,sanye take cikin wata ja da shudin atamfa me kyau da tsada ɗinkin stretgouwn wanda ya yi cif_cif a jikanta ya fidda surarta me jan hankali sai tayi wani dumimi gwanin sha awa fuskarta babu komai sai bakin kwalli da ta zana a idanunta tare da kewaye karamin lips ɗinta da baƙin gazar ta dan goga lipstick a tsakiyar lips din,wayyo kar kuga irin kyan da Zahra ta yi,(yar uwa gwadawa me gida irin wannan kwalliyar kiga yadda zai dinga binki da kallon kauna,dan su maza ba kasafai suka cika son wannan kwalliyar haukan ba,mafi yawansu sun fison ganin real face wife dinsu,kuma duk son da mijinki yake da shiga daya kar ki sake ki biye masa da wannan shigar kullum, dan watarana a waje zai gano wadda ta yi shigar da bai saba gani a gida ba,yar uwa dinga sauya salo a komai naki na zaman takewar aureki zaki ce na fada miki, gwada wannan kafin muje nest ).
Dora kansa ya yi a kafaɗarta yana wani lumshe idanunsa da shigar dasu ciki saboda tsananin kyawun da zazzafarsa ta yi, dai_dai lokacin Zahra ta ɗaga camara ta ƙyasa musu pic, waw duk da ab ba ma'bocin irin wannan shirmen ba ne amma haka ya biyewa Zahra tana ta yi musu hoto har da video,aiko sosai abin ya bada ma ana,dan kuwa dakyar mutuniyar taku ta kwaci kanta gun sarkinta,kadan ta tura bakin tana kallon yadda ya lashe duka kwalliyar bakin da ta yi,harara ta dan jefa masa tana juyawa dan gyara kwalliyarta,kwantar da kansa ya kuma yi a bayanta tare da zagaya hannunsa ya dora a saman cikinta yana shafawa kafin a hankali cikin wani irin sauti me kashe jiki ya ce,"Zahr ki daina yi wa kowa wannan hararar taki so naga Jafar ma kina yawan bashi sako ta hanyarta so pls kar ki kuma"juyowa ta yi hannunta rike da lipstick da take kuma sawa bayan ta zizara gazar din,ta ce, "yaya AB me yasa? Bai bata amsa ba sai karbar lipstick ɗin dake hannunta ya yi ya ajiyesa sannan yaja hannunta suka fita...
Ƙamshinsu ne ya sanar da mutanen falon zuwansu,har yanzu hannunsa na cikinnata sai dai fuskarnan tasa a tamke kamar ko da yaushe kamar ba shine ya gama lalube ƴar mutane ba,ga mamakin Zahra sai kawai taga siyam na sakar mata murmushi mama kuwa har da gyara musu wajen zamansu.
Koda suka ƙaraso Zahra gun Ammi ta nufa ta rungumeta tare da gaisheta cikin ƙauna, daddy ma gaidasa ta yi ya amsa yana dafa kanta cikin sa mata albarka saboda yana jin daɗin yadda Zahra ta kawo farinciki da walwala cikin iyalansa,dan duk ƙin Ab da son a gane walwalarsa da faruncikinsa sai da ta bayyana, fuskarsa kawai zaka kalla kasan yana cikin nutsuwa,hannu suka sha ita da Amira fuskarsu dauke da murmushin da ke nuna shaƙuwar da su kayi da juna,ko kallo su siyam basu isheta ba duk kuwa da yadda suke ta kallonta suna yake,da sauri siyam ta janyo flet tana cewa, "kowa ya tsaya yau Ni zan yi saven ɗinku na hutar da sis amira"dukansu babu wanda ya kawo wani abu a ransa game da hakan, sai ma daɗin yadda suka sauya mu'amalarsu da su daddy da Ammi suka yi.
Zahra kuwa binsu kawai take da kallo tana son fahimtar wani abu,dan ita kam sam bata ji ta yadda da wannan sauyin nasu na lokaci guda ba,ji ta yi zuciyarta na kuma shiga cikin zargi dan haka ta miƙe tana cewa, "ina so na ɗauko ruwa a keching"bata tsaya sauraren abinda zasu ce ba ta wuce,Ammi na cewa ta tsaya amira ta dauko mata amma sai ta ce ta bari tunda ta riga ta miƙe, da hararar ƙasan ido siyam ta bita tana mai yin ƙwafa da sakin murmushin mugunta duk a lokaci ɗaya.
Shima Ab kallon da ba kowa ya fahimta ba ya bita dashi yana ji a ransa kamar da wani abu daban."
....Zahra tana shiga keching ɗin ta fara ƴan dube_dube ko zata ga wata alama akan abinda take zargi,sai dai babu wani abu da tagani,cikin sarewa ta juya zata fita sai taji kamar Muryar baba talatu tana kiranta a tsorace,da sauri ta juya tana kallon baba talatu ta window keching ɗin a raɓe,da alama dai bata son shigowa keching ɗin gaba ɗaya,da sauri ta fita zuwa wajen baba talatu tana cewa,"lafiya me kike yi a nan"?cikin rawar baki baba talatu da zufa ta jikata ta ce,"matar uban gidana maza kije duk yadda zakiyi kiyi ki tabbatar da cewa babu wanda ya ci abincin nan"ai da gudu Zahra ta juya ba tare da ta tsaya tambaya ko jin dalilin baba talatu ba,
Dai_dai lokacin suka fara ƙoƙarin cin abincin, Zahra bata ce ga abinda ya hanasu fara ci tun fitarta ba,kawai ganinta su kayi tana wuri_wuri da tunanin ta yadda zata hanasu ci,gaba ɗaya sai hankalinsu ya dawo kanta,tana ganin haka sai kawai tayi amfani da wannan damar ta saki jiki luuu ta tafi zata faɗi zuciyarta cike da tsoro da shahada dan tasan da wuya idan bata karya ƙashin bayanta ba,
Jinta cikin irgaman kuma wadataccen ƙirjin ɗan kurmanta yasa ta sakin boyayyiyar ajiyar zuciya,cikin tashin hankali suka fara taɓa fuskarta suna kiran sunanta hankali a matuƙar tashe,cikin sanɗa baba talatu ta fito daga keching ta kwashe duka kayan abincin da suke a kan dinning ta fita dasu tana sakin ajiyar zuciya tare da godiya ga Allah da ya shigo da Zahra dan da ba dan haka ba shike nan sai dai wani labarin,siyam kuwa suka hankalinsu tuni ya koma kan Zahra shi yasa har baba talatu ta kwashe kayan basu kula da ita ba,"
Ɗaukar Zahra ya yi yana cewa su ammi su kwantar da hankalinsu zai dubata baya tunanin wani abu ne babba,duk da shi ɗinma boye damuwarsa kawai yake yi.
Dukansu babu wanda ya kula da abincin bare su gane cewa an kwashe,watsawa su kayi daga falon da tunanin Zahra ciki ne da ita tabangaren Ammi kenan shi yasa da suka shiga ɗakin daddy ta gaya masa abinda take zargi saboda yadda taga ya damu sosai,aiko sosai taga samun nutsuwarsa da wannan labari nata Duk da cewa basu tabbatar ba.
Zubawa teburin cin abincin ido su kayi zuciyarsu na cikin wasi_wasi akan lamarin Zahra,mama ce ta dubi siyam ta ce,"siyam anya ko wannan fitunannen yaro zahla ba aljeni ba ne??dafe kai siyam ta yi cike da baƙin ciki da takaici ta ce, "mama zahla shegiyar yarinya ce me wayo,shi yasa nace Miki mu hakura da wannan sabgar mu canja salo amma kika dage saboda kin fi yadda dasu a kaina".
To wai shin tayaya ne tasan shirinmu bayan sai da muka bi duk wata hanya da zata toshe hakan??
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*