Page48
Baba takatu na matsawa su daddy suka karaso wajen,duban Ammi daddy ya yi yana cewa,"har yanzu ba a gano matsalar ba"?girgiza kai Ammi tayi!tare da cewa, "ey to ina ga dai kamar doughter ta gano matsalar ku ku shiga daga ciki kawai saboda ita taƙi yadda mu shiga da ita tunda abune na mata" gyaɗa kai kawai daddy ya yi yabi bayan Ab da ko kallon inda suke bai kuma yi ba,sai dai yana kallon Zahra da ta wani rabe a gefe kamar bata san komai akan abinda ke faruwa ba, zuciyarta kuwa sai zullumi take kar ya ce ta koma,"tab aiko da wlh sai na daga masa hankali idan har yayi min buƙulun jibgar wannan dattijuwar banzar,ta faɗa ƙasa_kasa harda murguda ƙaramin bakinta kai kace hakan ta faru,dauke kanta ta yi daga kallonsa ta kaida kan maman siyam da take ta kokuwar susar jikinta kamar sabuwar kamu.
Ajiyar zuciya ta sauke bayan taga shigarsa main falon ba tare da ya kalli inda take ba, murmusawa ta yi tare da raɗawa Amira a kunne,"kai wallahi Amira ta wani ɓangaren muskilin namiji yayi, ko ba komai miji zai zama mai kau da kai daga dukkan wasu abubuwa da basu da muhimmanci" Amira ta ce, "ey daga cikinsu har da kula mata tunda gashi na cikin gidanma sun gagara samunsa" har zahra ta buɗe baki zata yi magana sai ga baba talatu rike da wata zabgegiyar itaciyar darbejiya, tana zuwa ta miƙawa zahra tana cewa, "gashi uwar dakina"karba Zahra ta yi fuskarta cike da damuwa, sannan ta ce,"yauwa baba talatu ina ragowar masu aikin suzo su tayaki ku riƙeta kunsan idan ana ruƙiya kuma sukaji duka ƙara haukacewa suke"Ammi ta ce,"wai doughter kina nufin dukan mama zaki yi"?ɗaga kai zahra ta yi har da share hawaye sannan ta ce,Ammi dole sai anyi musu haka idan ba haka ba zasu iya shafar kowa a gidannan tunda baza su taba tafiya ba dan mahaukatane sunfi ko wane irin aljanu wahalar fita.dan haka dole sai anyi duka amma fa ba ita ce zata ji dukan ba sune zasu ji,sai dai zaku ga alamun kamar ita ake duka tunda zasu yi ta maganganu kamar ita ce ke yi"jinjina kai Ammi kawai tayi tana mai dan ja baya tunda taji maganar zasu iya shafarsu.
Dai-dai lokacin baba talatu ta dawo tare da matasan masu aiki su hudu,dama suna daga can gefe suna kallon dramatic humen suna shan dariya, dan fa su kansu masu aikin mama da siyam sun addabesu, saboda ƴan wulaƙanci ne, sun raina masu aikin gidan ko yaushe cikin saka su aiki suke, kamar bayinsu, ga faɗa da hantara kamar su suka kawosu gidan.
Kama_kama su kayi suka rike mama,hannu da ƙafa,Zahra kuwa harda tattare hannun rigarta fuskarta babu alamun wasa,ta shiga karato wasu ayoyi daga cikin suratul jin, tana yi tare da zabgawa mama bulalar,aiko mama take ta yi wani irin ihu kai kace aljanunne na gaske ke ihun,Zahra na ganin haka ta koma karanta baƙara tana ci gaba da zabgawa mama bulalar.
Mama kuwa cikin ihu take tsinewa Zahra,"segen yaro mara tosayi wallahi ka sake yarona siyam ya dawo sai ka rena kanka,bakari kayi asala da ka rasa yaron masiyatan da zaka kawo mana masayin siliki sai wannan mugu yaro,zahla Allah ya sine maka rayuwa kaida zuriya naka mugu kwadayayye me kyawun ɗan masiji"
Kuka Zahra ta saka tare da ajiye bulalar bayan ta tabbatar mama ta daku iya adadin lefinta na yau,cikin kukan take cewa, "Allah sarki mama Ni kam duk abinda zaki faɗa ba zanji haushinki ba dan bayin kanki bane, Allah dai ya baki lafiya,baba talatu ku ɗauketa ku kaita ɗakinta har yanzu basu tafi ba, amma na tuna da wani turaren aljanu da mama take yi min lokacin aljanuna suna yawan tashi kuma shine yasa suka daina zuwa ko yaushe"cikin sauri Ammi ta ce, "yauwa ƴar albarka dan Allah maza nemo shi a samu a yi mata ko sa bar mana gida mu huta"
Da gumurzu su baba talatu suka shiga da mama dakinta aka rufeta dan kar ta fito,da mama taga dai da gaske kowa ya yadda aljanun take yi sai ta koma gaya musu abinda ya faru tana yi tana buga kofar dakin.
Cikin damuwa Zahra ta kalli Ammi da daddy da suke tsaye cirko_cirko, gaba ɗayansu kana kallonsu zaka san cewa a tsorace suke,ta ce, "Ammi kunji ko? Ai wannan kuna ji kunsan sharrin jinnu ne,idan ba haka ba ya za ayi kina zaune a watso miki ruwan doya da wasu tarkace sannan kice ba aljanu bane?ai daga jin wannan batu ma kunsan akwai lauje cikin naɗi"Zahra ta ƙarasa maganar tana ƙunshe dariyar yanayin su Ammi ɗin da take ta cinta a rai.daddy ne ya ce, "to maza jeki nemo maganin yanzu a yi mata kar wasu su ƙaru ba ayi maganin wasu ba" sosai yadda daddin ya yi ya bawa Zahra dariya dan haka sai kawai ta yi hanyar keching, tana shiga ta tuntsure da dariya,sai ga baba talatu ma tana yin tata, sai da suka yi me isarsu, sannan zahra ta ce, "yanzu baba talatu baki da wani ɗan hayaƙi haka me sa tari"? Ɗan jim baba talatu ta yi, kafin ta girgiza kai tana cewa gaskiya babu sai wani guda ɗaya amma shi turaren mayune dan haka yana da yaji sosai" jawo hannun baba talatun Zahra ta yi ta kaita bakin kofar fita hanyar dakunansu, sannan ta ce,"maza ɗauko indai kinsan baya kisa kuma ba zai yi mata muguwar cutarwa ba,"a'a ba zai mata komai ba sai dai zata sha azaba ta iya lokacin da take shaƙarsa" to ɗauko maza" Zahra ta fada tana juyawa,yauwa baba talatu dan Allah ko da kin dawo kin tarar ɗan kurma ya ɗaukeni ya maidani sama dan Allah ki yi kokari kiyi mata" jinjina kai baba talatun Tayi tare da saurin shigewa bangarensu.
A can ɓangaren su siyam kuwa,koda bash ya fita kai tsaye wajen Oga durga ya nufa, ya sanar dashi ko mai yayi daidai.miƙewa ya yi yana wani taku kamar irin samudawannan da suka sha suka koshi da burkutu,kai tsaye ya nufi ɗakin yana shiga ya maida kofar ya rufe tare da nufar siyam da sai yanzu bakinta ya buɗe take ta sambatu duk akan Zahra da ab,bai tsaya neman iso ba kamar wata akuya haka ya faɗa mata ya shiga aiki babu ji ba gani kamar wani engine,tun siyam na ganin abin na kare ne har dai ta fara sarewa ta hanyar neman taimako da magiya,shiko durga ko ajikinsa,sai da takai hatta da hannun siyam ta kasa daga shi saboda tsananin azaba da tsamin jiki,tunda siyam take yawon iskancinta bata taɓa cin karo da tantiri kamar durga ba, kuma ba a taba yi mata wulaƙancin da yayi mata yau ba,hawaye ne kawai suke wanke fuskarta a ranta tana ci gaba da tsinewa durga dan tun marin da ya faffalla mata bata kuma yin magana a fili ba,sai da yayi ya gaji da kansa sannan ya sauka daga kanta ya shige toilet ya watsa ruwa ya fitowarsa ya barta tana sauke numfashi da yi masa Allah ya isa.
Yana fita ya bawa femi umarnin taje ɗakin ta taya siyam gyara jikinta sannan su tafi ta gano masa gidansu siyam ɗin, dan yaji daɗin mu amala da ita sosai,haka kuwa a kayi femi da kanta ta temakawa siyam ta gasa jikinta ta maida kayanta, sannan ta sakota gaba suka fito,sai da suka fito sannan siyam ta samu bakin magana,duban femi ta yi ta ce,kije na gode da taimakonki" dan ita bata yi zaton durga ne ya turo femin ba,kafin femi ta yi magana durga ya baiyana a gabansu yana wani ƙarewa siyam kallon iskanci har da lashe lips, sannan ya ce,"baby kinyi min dan haka ga jakadiyata nan zata gano min mazauninki,idan kuma kika yi min gardama to ke da gidanku har abada,"daga haka ya yi gaba yabarta da binsa da kallo baki sake,ba dan taso ba ta wuce femi ta bi bayanta, sai a lokacin taga kawarta tazo tun ɗazu take nemanta da kiran wayarta amma bata samu ko ɗaya ba.
Bata tsaya yi mata wani bayani ba ta nuna mata su tafi gida kawai, sa tattauna a mota, dan bata jin zata iya barin maganar Zahra ta huce a ranta.ƙawarta ce take jan motar ita kuma tana gefe yayin da femi take baya tana sauraron hirar da suke tattaunawa akan Zahra da ab,ita siyam bata damu da durga ba tunda tasan bai isa yazo har gida yajata ba shi yasa ko maganarsa bata yi ba ta bari tukunna sai sun keɓe.
.....cikin sauri Ammi ta kama hannun Zahra tana cewa, doughter ina maganin yake"?Zahra ta ɗan karyar da kai sannan ta ce, Ammi kar ki damu na samo maganin yanzu haka na bawa baba talatu ta hada garwashi sai a sa mata"Amira ta ce,ai ba sai ta yi wahalar hada gaurashi ba ta kawo a kunna boner kawai"kafin su kuma yin wata magana Amira ta tafi dauko boner ,daidai lokacin baba talatu ta dawo hannunta ɗauke da maganin a bakar leda,Zahra na shirin karba sai hancinta ya shaƙo mata ƙamshin ɗan kurmanta dan haka sai kawai ta matsa tana maida fuskarta kalar tausayi.
Baba talatu na ganin haka ta yi saurin karɓar bonner ɗin da Amira ta ɗauko, ta nufi hanyar corridor dakinsu maman siyam,dukansu babu wanda ya motsa dan sosai Zahra ta saka musu tsoron kusantar mama a cikin wannan yanayin,sam Zahra bata so fitowarsa ba dan sosai taso zuwa dakin mama kodan tayi kallon sabuwar dramer,ihun mama ne ya katse mata tunaninta, Zahra dake jiran ƙiris tuni ta bi hanyar corridor tana cewa, "ayya baba talatu ai dama ba zaki iya da mutanennan ke ɗaya ba bari nazo na taimaka miki tunda nice nasan kan matsalar"daga haka bata ƙara ba ta faɗa ɗakin, inda ta tarar da mama ta zage tana ƙundumawa baba talatu zagi tana cewa, itama ai munafuka ce, kuma sai ta yi maganinta, tana ganin haka ra'ayi tayi saurin karɓar bonner ɗin ta kunna tare da zuba maganin me uban yawa, sannan ta dawo gaban maman ta janyeta da ƙarfi ta zaunar a saman gadonta, kafin mama ta yi wani yunkuri tuni zahra tasa igiyar da tayo guzurin abarta ta ɗaure hannunta da ƙafa a jikin gadon,sai da ta tabbatar ta ɗauru yadda bazata iya kwancewa ba,sannan ta saketa tana cewa baba talatu mu tafi idan mu kayi mata haka ba zata samu hanyar kashe turarenba",da gudu suka fita daga ɗakin saboda hayaƙin da ya turniƙe ɗakin ga wani yaji yaji me sa tsinkewar majina.
Dukansu a tsaye suka samesu, suna jiran tsammani fuskarsu har ɗan fadawa ta yi saboda yunwa da yau duk dinsu babu wanda ya ci komai a cikinsa,Ab ne kawai yake zaune saman kujerarsa ta gado ƙafarsa daya kan ɗaya hannunsa riƙe da waya yana magana a hankali da alama dai waya yake yi, fuskarnan tasa babu alamun Rahma.
Ɗauke kanta ta yi daka kallonsa tana ɗan tura baki tare da murguɗasa gefe, sannan ta ce, "ammi dan Allah ku kwantar da hankalinku in sha Allah tana faarkawa daggaa bacci komai ya wuce, yanzu muje muci abinci kunga duk yau babu wanda yaci abinci",ajiyar zuciya suka sauke a tare sannan Ammi ta ce,baba talatu kin yi lunch ne"?da sauri baba talatu ta amsa da cewa, "ai tun ɗazu uwar ɗakina ta kammala komai.
Duban Zahra daddy ya yi ya ce,Zahra ki daina wahalar da kanki wajen ganin sai kin yi mana girki,idan ma yin zaki yi kiyi iya mijinki ga keching nan a samanku pls"sunkuyar da kai Zahra ta yi kamar irin saliihan bayin nan tana cewa,"babu komai daddy ai ku din iyayena ne"Allah ya miki albarka" suka faɗa a tare shida Ammi,kafin su rankaya zuwa dinning room ɗin.
Har Zahra zata zauna Ammi ta dakatar da ita tana cewa,"a'a doughter tashi ki ɗibawa mijinki ku je can sashenku kuci kinji"Tom Ammi" Zahra ta faɗa ba tare da musu ba,dama komai nasa daban yake kamar yadda baba talatu ta koya mata a ɗazun dan haka ɗauka kawai ta yi amira ta biyota da wasu suka kai sama,sun fito kenan suka haɗe dashi a bakin upstairs ɗin ya hawo, dan haka dole zahra ta koma ta bar amira ta sauka,
Suna shiga falon zama yayi a wajen zamansa yana ƙoƙarin jawo tap ɗinsa,da sauri Zahra ta zauna a inda yake kokarin aje tap ɗin tana tura ƙaramin bakinta kafin cikin shagwaba ta ce,wai yaya AB me nayi maka sai wani sha min kunun kanwa kake yi? Ko dan na temakawa wancan me aljanun"?tsareta ya yi idanunsa masu haske da sheƙi ba tare da ya tanka mata ba,kawar da kanta ta yi tana cewa,to yaya AB bari na kawo maka abincinnan, "bana ci ya fada a hankali idanunsa a kanta yana Binta da kallon tuhuma,ƙif_kif ta yi da manyan idanunta sannan cikin sanyi da shagwaba ta ce, Allah ya Ab yau babu yaji kuma idan ma akwai ai ina shanye maka ko"? Ta faɗa tana leƙa fuskarsa da ya maida kan tap dinsa,wani takaici ne ya ishi Zahra dan haka sai kawai ta fasa masa kuka tana kai masa ƙananun duka a ƙirjinsa,babu shiri AB ya bar abinda yake kokarin yi, ya rungumeta ya shiga shafa gadon bayanta yana calming dinta kamar jaririya,a ransa yana cewa, yasan cewa za'arina,dan Zahra bazata bar fushinsa yaje ko ina ba,cikin kunnenta ya shiga raɗa mata sorry my headache hot zahr..........✍🏼
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*