YAR GIDAN YARBAWA

Page 51

by @zahrawriter12

....... numfashi siyam ta furzar sai yanzu ta fahimci inda suka dosa,duban Adebayo ta yi sannan ta ce, "ina fata idan kuka saceta kasheta zaku yi ta rabu da duniyar gaba ɗaya domin bana bukatar ganinta a cikin duniyar"?

Duban juna Adebayo da bash su kayi, sannan suka sheƙe da dariya,bash ne ya bata amsa da cewa,ke kuwa kin san waye Durga??ai ina ga ko aikin da ya yi Miki jiya ya isa ki fahimci abinda zai iya da wanda ba zai iya ba,shi fa Durga duk wani aikin sheɗanci baya gagararsa,duk inda ake harƙallar tantiranci yana wajen,dan haka ki daina kokonto akan tsarin da yayi na sace Zahra, shi zai tsara mana komai dan haka ke dai kawai ki bamu bayanan gidan da duk wata hanya da kika san ana shiga gidan"girgiza kai siyam ta yi, sannan ta ce,ba zai yiwu ku sace Zahra a cikin gidannan ba, dan kuwa akwai tsaro me ƙarfi a gidan,kawai abinda zamu yi shine ku ba ni lokaci daga yau zuwa koda yaushe duk ranar da zahra ta fita ni kuma zan kira ku, ku dai kawai ku kasance cikin shiri",daga haka ta mike tare da kama hannun suzan suka bar wajen.

Zahra suna cikin buga game da Amira, wayarta ta yi ƙara, duban wayar ta yi tare da zubawa nomber ido dan bata san nomber ba,Amira ce ta leƙa wayar tana cewa,ki daga mana ko baki san me kiran ba....ai wannan nomber yaya ce dama baki da ita? Da gaske? Zahra ta fada tana saurin danna ok,tashi Amira ta yi tana cewa "ina zuwa amma dan Allah Zahra ki nutsu ki yiwa yayana hira me dadi kalamai masu sanyi,idan kin gama ki kirani dan na ga ya mata na saki a groups din matan aure wanda zaki karu da hanyoyin zaman aure" daidai nan ta fice daga ɗakin, zahra kuma ta kara wayar a kunnenta,cikin shagwaba ta ce,"yaya AB"ya kamata wannan sunan ya fita daga bakinki"to ya Ab wane suna zan fada ABRAHAB kake so na ce gatsa_gatsa"? Lumshe idanunsa ya yi yana kuma kwantar da bayansa jikin makarin kujerar yayin da yake jin wani irin sanyi na ratsa ɓargonsa saboda yanayin da Zahra ta yi amfani dashi wajen kiran sunansa na ainihi,bai iya cewa komai ba sai juya kiran da yayi zuwa video call.

Kallonta da ya kuma yi shi ya kuma haifar masa da wata irin mutuwar jiki, iska ya furzar daga bakinsa ya kasa cewa komai, ita ko Zahra tura baki ta yi tare da ɗan watsa masa harararta me kyau,"zaki kasheni"ya faɗa can ƙasan maƙoshinsa dan da Zahra bata kallon bakinsa to da bazata fahimci abinda ya ce ba,keɓe baki ta yi tare da nuna kanta, jinjina mata kai ya yi yana mai ɗora hannunsa saman kansa ya shiga cakuɗa sumar da take akwance luf,ji yayi Zahra ta fashe da dariya har da rike ciki,a hankali ya bude idanunsa da suke a lunshe yana kallon yadda take dariya gwanin sha awa wanda hakan yasa komai nasa ya kuma kwancewa duk da yadda yake kokarin boyewa kuwa,"meye ne?"ya tambayeta fuskarsa a kame dan gudun reni, dan yasan halin abarsa duk ya sake ta fahimci halin da yake ciki ya shiga tara Zahra shima ba barinsa ta yi ba, cikin dariya take nuna masa jikinsa,kafin ta danne bakinta dakyar don son rage dariyar ta ce,yaya AB kalli macijinka kagani, wallahi nema yake ya fasa wandonka ya fito sai kace wanda aka hurasa kamar wani balo"ɗif ya kashe wayar domin me faruwa ta faru, abinda yake gudu kenan Zahra ta ga makwancinsa,samun kansa yayi da sakin ƙaramin murmushin gefen baki al'amarin Zahra sai du'a'i Allah yasa kar ta haifa masa me irin halinta dan tabbas sai kansa ya dauki caji fiye da cajin da yake ɗauka yanzu akanta.

Zahra kuwa dariya ta ci gaba da yi har da su kwanciya,sai kuma zumbur ta mike kamar an tsikareta da allura,hijab ɗin Amira ta dauka ta saka tana cewa yau ina cikin gidan nan mama take can tana bacci cikin salama tab ai walle har yanzu ban gama baku punishment ba,dan ma ɗayar jakar bata nan kuma ita ma ba ƙyaleta nayi ba itama sai ta ɗibi kashinta a hannu" ficewa ta yi daga ɗakin, Allah ya taimaketa bata samu kowa a falon ba da alama Amira ma ta yi wani wajen daban.

Can bayan ɗakunansu mama ta nufa ta tsaya daga bakin window,sai da ta leƙa ta tabbatar mama bacci take cikin kwanciyar hankali sannan ta yi murmushi tana cewa, "zaki bayani ne da Zahra kike magana mugaye masu kashe mutane"juyawa ta yi bayanta ta duba taga babu wanda yayo ta hanyar dama ba wajen wucewar mutane ba ne tunda wajen ya kasance bayan dakunan masu gidan,kallon wajen Zahra ta dinga yi a nutse,can ta hango irin tsutsarnan me gashi da ƙayoyi a jikinta,cikin korayen ciyawar wajen.

Da sauri ta karasa wajen tasa tsinke ta dauketa,da gudu ta kuma komawa bakin window dakin mama,a hankali ta shiga zuge window kaɗan ta yadda hannunta zai shiga,tana zugewa ta yi saurin jefawa mama wannan tsutsar wanda ta jefa ta cikin Sa'a ta sauka akan kafar mama.

Cikin bacci mama ta dinga jin abu na tafiya yana sukarta a kafa dan haka ta yi saurin buɗe idonta,tare da kai kallonta daidai inda take jin tafiyar,aiko idanunta ne suka yi mugun gani dan bata tsaya tantance meye ba saboda a bacci ta tashi, duk da cewa rana ta fara yi dan Lokacin sha biyu da rabi ta yi na rana,"wayyo Allah me ye ne yake shirin faruwa da maman siyam? jereba ya yi yawa dega wannan se wancan masifa iri de kala, Allah ka siga sakanin mutum da aljanin da yake son lalase rayuwan maman siyam",

Zahra me zata yi ba dariya ba, durkushewa ta yi a wajen sai da ta yi ke isarta sannan ta dago ta leƙa maman siyam da take ta juyi a gadon ta kasa tashi gashi duk inda ta juya sai taga tsutsar nan ta koma wajen,hakan yasa Zahra ta shiga taɓa window tana dan bubbugasa, a zabure maman siyam ta juya idanu a waje take kallon window da babu kowa gashi tana tsoran leƙawa,da sauri Zahra ta bar jikin window ta dawo cikin gidan, kofar dakin maman siyam ta tsaya bayan ta rufeta ta waje, dai-dai lokacin maman siyam ta sauko daga gadon dan fita daga ɗakin tana tsinewa bokanta dan a cewarta duk shine ya jawo mata wannan masifar,jin kofar a rufe yasa ta kuma taurewa, durkushewa ta yi a bakin kofar tana cewa, sorry na tuba karebu Dani haka ka bari naji da masifar yaro mara mutunsi a beging you kome kana so zan yi maka",

Zahra na jin haka ta yi saurin gyara maƙogaranta, sannan cikin siririyar murya ta ce,"maman siyam kince duk abinda muke so zaki mana ko?"wata yar dungure maman siyam ta yi sai gata a kofar bathroom jikinta kuwa banda kyarma da babu abinda yake yi dan bata taba tunanin zata taba jin muryar aljanu ba a rayuwarta,tsawa zahra ta daka mata yanzu cikin ƙatuwar murya tana cewa,dole ki yi mana duk abinda muka saka ki idan ba haka ba zaku gane kurenku gaba daya ke da yar taki,dan munga alamar cewa baki daddara da abinda ya faru dake jiya ba",

Cikin rawar baki maman siyam ta ce,"na dedera wallahi na dedera dama zahla ya ce, serri naku ne bana mutum ba,yo gasi Allah ya nuna min"rufe mana baki ki saurari abinda muke so dake".

Da sauri maman siyam ta dora hannunta kan bakinta jikinta na rawa kamar ana kaɗa mazari fitsari kuwa ƙiris ya rage ya zuba,kamar Zahra ta sani ta kuma cewa,"idan kika sake kika yi mana fitsari a kan yaranmu sai mun hanaki fitsari har abada"cikin rikicewa maman siyam tasa hannunta ta dafe mararta tana cewa, "sikenan sikenan maman siyam ya ranse baze yi fisari ba"yauwa da dai yafi Miki"sharaɗinmu kuwa shine lallai idan kina so mu rabu dake sai dai kullum idan kika tashi zaki zagaye gidannan kina mana rawa, kullum sai kin zagaye gidannan har zuwa karshensa kuma kina tafe kina mana rawa da waka,kuma rawa sosai idan bata yi mana ba zaki ga abinda zai faru", daga haka Zahra ta lallaɓa ta bar wajen tana dariyar mugunta har ta fara hango mama tana rawa a gaban masu aiki da gerd da securitys.

Karo suka ci da Amira,Amira ta ce,"lafiya dai tun ɗazu nake nemanki har upstairs naje ban ganki ba"ɗan yatsina fuska Zahra ta yi sai kuma ta sheƙe da dariya har da hawaye,Amira ta ce,dan Allah matar yaya bani nasha kin san bana son irin wannan baurin na wuce Ni"dafa kafadarta zahra ta yi!sannan ta ce,"ki yi hakuri yau ko gobe zaki fara shan dariya a gidannan ke dai kawai ki zuba ido kiga ikon Allah"dole amira ta haƙura dan tasan tunda bata gaya mata ba bazata gaya matan ba sai dai ta gani da idonta kamar yadda zahran ta faɗa.

Jan hannunta ta yi tana cewa, "to muje lecture zanyi Miki dan na fison duk wannan sakarcin naki ya zama me amfani wajen dan uwana ehe, dan bana son ko wace mace ta shiga tsakanin wannan amintacciyar soyayyar"daidai suna zama a bakin gadon Amiran,tana ci gaba da cewa sai na fitsararwa da yaya ab zahransa ta yadda zata kuma haukatasa da salon ƙiriniyarta me hadi da salon soyayya me haukata jiki da ruhi gami da tunanin abocin kauna,"dariya Zahra ta yi kawai dan ita kam bata fahimci ko harafi daya daga batun amiran ba,saindai tasawa ranta tsayawa da duk hankalinta domin ɗaukar darasin da zata koya mata,tunda fara jin batun za wata zata shiga tsakaninta da yaya AB in dai bata koya salon da amira ke magana a kai ba(ita Amira bata san cewa tuni ƙauna ta fara sarrafa tunanin Zahra a shimfiɗar ab ba,to amma komai yana bukatar wayewa).

Mama kuwa da rarrafe ta shiga bathroom a tsorace ta yi fitsarin da ya cika mata mara,tana fitowa ta zube tana jan numfashi a ranta kuwa ji take kome ye zata iya yi musu in dai zasu bar rayuwarta ta zauna lafiya,dan haka ta shirya fara dancin a safiyar washe gari ba tare da tunanin komai ba.

Zahra da Amira basu tashi ba sai da Amira ta tabbatar ta budewa Zahra ƙwaƙwalwarta ta fahimci abinda take nufi.

Daga nan falo suka koma, sai a lokacin suka haɗu da Ammi, sosai ammi ta nuna damuwarta akan Zahra, abinci suka ci suka ɗan taɓa hira, Zahra dai kamar ko da yaushe rabin hirarta shirme ce, amma duk da haka,ammi da Amira na ƙoƙari wajen ganin sun buɗa mata tunaninta a matsayinsu na wayayyu da suka yi zaman ƙasashe da cuɗanya da mutane da kala_kala...

Sai da suka yi sallah la' asar sannan Zahra ta haye upstairs,kai tsaye keching din da bata taɓa amfani dashi ba ta shiga, kokarinta yau ta yiwa AB girki na musamman kamar yadda amira ta kwaɗaita mata.cikin kankanin lokaci Zahra ta tashi samannan da kamshin haɗaɗɗun delicious din da take haɗawa ɗan kurmanta.

Tana gamawa ta shiga wanka, sai da ta fara tsaftace bakinta ta hanyar yin lafiyayyan brosh,(bari na koya muku yadda ake yin brosh dan wasunmu da yawa brosh ɗin kawai suke yi ba tare da sun san abubuwan da ya kamata su wanke a cikin bakinsu ba,yar uwa idan kika tashi kika matsa makilin ɗinki a jikin brosh ɗinki, sai ki zuba ruwa kaɗan akai daga nan zaki saka shi cikin bakinki ko nace kan harshenki,zaki fara da cuɗa harshenki tun daga farko har zuwa wajen makogaranki sai kinji kamar zaki yi amai sannan ki juyasa saman handarki domin wannan wajen matattarar datti ne ,shima sai kin cuɗa yadda kika ji da kanki kin gamsu babu wani sauran datti a wajen,sai ki sauko kan hakoranki wannan dama kin san yaya za koyi wajen tsaftacesu,ƙasan harshenki jikin fatar lebenki ta ciki da ramin hakoranki,da duk wani loko da kika sani acikin bakinki,daga nan sai ki kuskure bakinki da ruwa sosai ,sai ki matsa mouse freshener idan baki dashi sai ki bari sai kin fito ki ɗauki cingon me kamshi ko kanumfari kisa a bakinki).

Jama a ku hango min Zahra cikin baƙar bets mara hannu da jan bomshot da ya fidda ainahin shep da ake kira shep, Masha Allah Zahra mu fa ba dai iya ado ba duk da cewa bata tashi gidan masu dashi ba amma dai kam tsafta da iya ado ba sai ance komai ba, lips ɗinnan sheki kawai jajawur da shi sai ɗan zagayen baƙi a saman lips ɗinta na sama yau kuma an canja salo ba a sa a ƙasan ba,sai hakan ya bada ma ana ta yi masifar kyau kamar ka saceta ka gudu,wata kimono ja da ratsin baƙi ta ɗauka ta saka tare da ɗaure madaurin ta baya,bakar hula ta saka bayan ta cusa uban gashinta ta ciki.

Ƙamshi kuwa ai ina ga har ƴan ƙasa sai da suka jiyosa, sallah magriba ta fara yi, sannan ta zauna ta fara murajiar ta ta alƙur ani,har sai da akayi sallah isha sannan ta Salllame ta yi Isha ta ɗora da shafa i,ta jima tana addu o inta kafin ta shafa ta miƙe, ta kuma shafa humrarta, sannan ta fita daga ɗakin takalmin da ta saka yana bada ɗan sauti kaɗan.

Kamar yadda ya saba idan daf da magriba ya dawo sai ya tsaya ya yi sallah har Isha kafin su shigo gidan shida Jafar da daddy,yana shigowa da ita ya fara arba tana saukowa daga upstairs cikin ɗan takunta da yake bada wani sauti me daɗi,juyawa ya yi ya karɓa kayan da suke hannun Jafar, mika masa jafar ya yi tare da yi masa sai dafe ya fita yana ɗan sosa ƙeya fuskarsa ɗauke da murmushin burgesa da soyayyar ogannasa ke yi,Zahra na ƙarasowa ta shige jikinsa tana cewa, "yaya AB muga micijinka ko ya sace naga ɗazu yayi kamar zai fashe"ta faɗa tana ɗora hannunta daidai saitin inda inda macijin AB ya ke....😂......✍🏼

Haba Zahra yaushe zaki daina bamu kunya ne haka??😂

To Allah yasa dai babu idan kowa a falon wata kila mu biye miki😄

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*