YAR GIDAN YARBAWA

Page52

by @zahrawriter12

A hankali ammi da ta sako kai falon ta dinga ja da baya hannunta a saman bakinta ta rufesa,bata bari AB ya ganta ba har ta koma inda ta fito, dan tasan ta bari suka hada ido da AB ba karamin kunyar juna zasu dinga ji ba,"kai lamarin Zahra sai ita",ta faɗa tana sakin numfashi bayan ta ganta a ƙaramin falonta.

A hankali AB ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya dan cikin nutsuwa ya kalle falon ya tabbatar babu kowa sai siyam da ta yi mutuwar tsaye,kasa shiru siyam ta yi, cikin tsananin zafin Zahra da yake karuwa a ranta ta ce,"wai ke wannan wace irin tambaɗewa ce haka?? A gaban mutane a cikin main falo kike mana karuwanci saboda tsabar iskanci"Zahra bata kulata ba sai ma hannunta da ta fara turawa a jikin AB tana cewa,"yaya AB bari na gani Allah yasa dai bai fashe ba dan wannan kumburar da ya yi idan bai samu abinci ba tsaf zai iya fashewa"zubawa karamin bakinta ido ya yi kafin ya ɗan motsa daniyar janyeta su bar wajen dan yasan zata iya aikata abinda ta faɗa.motsawar da zaiyi kuwa sai hakan ya bawa hannunta damar shigewa jikinsa,cikin dauriya da son kuntatawa siyam ta rike macijin kafin cikin shagwaba ta ce,"shi ke nan yaya AB na fasa gani a nan saboda naga idon mujiya yayi zuru ana son ganin bati wannan macijin kuwa babu wanda yake da zarrar ganinsa ko daga nesa sai zahra yar GIDAN YARBAWA matar Abraham abadan abadan dan haka sai a maida mugun yawu banzar bata samu ba sai a koma ɗakin aro ta leƙo ta koma"Zahra ta faɗa tana ciro hannunta daga jikinsa.siyam tamkar wata sakara haka ta tsaya tana kallon zahra cike da mamakin yaushe yarinyar ta zama ƴar iska ta karo wulaƙanci irin haka??a sakarci da taɓarar zahra siyam bata taba tunanin zata iya wannan iskanci ba ashe iskancinnata ba iya iyashegen tsokana da rashin barin takwana kawai ya tsaya ba, lallai dole sai ta yi da gaske akan shirinsu na ɓatar da zahra, idan ba haka ba tun da zahra ta dauki wannan salon tabbas zata iya wayar gari da ciwon zuciya.

Tunaninta ne ya dawo lokacin da ta tsinkayi Muryar Zahra cikin sakalci tana cewa,"my Snake ka goyani mu tafi sama yau a can zamu yi dinner dan nayi maka girki masu daɗi wanda sai kunnenka ya tsinke idan kaci saboda daɗi"kafin ab ya yi wani motsi tuni Zahra ta ɗafe bayansa shi ko Ab ba tare da wani jinkiri ko jinkunyar idanun siyam da ke kansu kamar zata haɗiyessu ba yasa hannu ya gyarata sannan ya wuce ba tare da salon takunsa ya sauya ba,a nutse Zahra ta juya ta yiwa siyam gwalo da yi mata alamar wakar ta gani ta gani kwalelenta.

Daɓas siyam ta zauna a wajen hannunta akanta ji take yi kamar ta rusa ihu ko ta ji sanyi a ranta,dariya ta ji daga bayanta,cikin sauri ta waiga sai taga Amira ce take sheƙa dariya kamar mahaukaciya sabon kamu amma saboda iya shegantaka da zama da maɗauki kanwa sai ta fuske ta ɗora waya a kunnenta ta yi kamar dalilin wayarne yasa ta dariyar,dariya ta kuma kwashewa da ita tana cewa, ai na gaya miki ƙawata maganin shege karan maguzawa, idan juranki sawa ma aurata ido to kuwa tabbas wata rana zaki tashi da hawanjini me shanye barin jiki dan kin san mutuniyartawa ba dai kwashewa ba" kasa magana siyam ta yi sai barin falon da ta yi a fusace kamar kububuwa,tana barin falon Amira ta kuma sheƙewa da dariya har da zubewa idanunta har da hawaye dan kuwa duk abinda ya faru akan idonta ya faru sosai zahra ta burgeta ta kuma bata dariya kamar cikinta zaiyi ciwo,cikin dariya take cewa "wallahi irin su zahra a cikin gida rahma ne wayyo cikina".

A can bangaren Zahra kuwa suna shiga falon ya yi kokarin sauketa amma sai ta maƙale kafaɗa akan ita bazata sauka ba sai sunje dakinsa,suna shiga dakin da kanta ta zame daga bayannasa, kamota ya yi gabansa suna fuskantar juna idanunsa a kanta hannunsa a ta bayanta yana kunce igiyar kimononta, a hankali ya ce,Zahr me yasa kike son sani yawan bagana bakiji ko?"wani kallo ta yi masa tana ja da baya yayin da ta barsa da rigar kimononta a hannu,juya masa baya ta yi tana yafiya jikinta na wani irin juyi kamar tarwada, sai da ta je bakin mirror sannan ta juyo tana fuskantarsa idanunta da fuskarta a narke ta ce,yaushe kayi maganar? kaida duk abinda za ayi sai dai ka dinga bin mutane da lulu eyes ɗinka kana wani lumshe idanu kamar wanda ya shekara cikin duhu yaga haske, sannan kace na sa ka magana ko a ina kayi maganar?".

Biyota ya yi jikin madubin ya shige jikinta tare da ɗora hannunsa akan ƙorjinta kafin cikin wata irin murya me ɗumi ya ce,"me kyau kin yi kyau matuƙa komai kina masa kyau"ya faɗa yana cusa hannunsa cikin ƙaramar rigarta da ko br bata samu damar sawa ba,ɗora nata hannun ta yi saman nasa cikin marairaicewa ta ce,yaya AB ba kayi wanka ba baka ci abinci ba duka dai kana bukatar....ɗora lips dinsa da ya yi akan nata shi ya hanata damar ƙarasa abinda take son faɗa,cikin ƙanƙanin lokaci ɗan kurmannata ya birkice mata dan dama a ƙule yake da ita tun safe take tsokale masa ido yanzu kuwa da ya samu ta shiga hannu baya tunanin da abinda zai dakatar dashi,ɗaukarta ya yi cak suka shige bathroom bayan ya cire duka abinda ke jikinsu,yau dai Zahra dole ta shiga jakuzin da ta ke tsoro,a nan Ab ya kafa musu tarihin da mantasa abu ne me wuya,ya yin da bangaren zahra itama ta yi kokari sosai wajen gwada duk wani abu da ta koya dan farantawa dan kurmannata,yau kam ɗan macijinta yasha murza da tsotsa dan tamkar sweet haka ta maida macijinta,yadda suka tsotse junansu babu ƙyama sai zallar shauƙin juna yasa suka kuma dasa wata irin shaƙuwa da kauna a zukatan junansu...

Koda suka fito daga bathroom din, sangarta ta dinga zubawa iri da kala, shi kuma kamar bashi ba sai wani riritata yake, abinci ma a lalace a ka cisa dan da baki suke ciyar da junansu, tana zuba taɓara son ranta,daga nan brosh su ka kuma yi suka bi lafiyayyan gadonsa ba tare da sun nemi inda kayan bacci suke ba,a haka suka kwanta zahra na manne a jikinsa kamar zata koma Cikinsa,shi kuma a hankali cikin lallaɓa yake shafa bayanta da hannusa guda guda kuma yana a ta wuyanta yana shafosa zuwa kan ƙirjinta da yake matuƙar tsole masa ido da ɗaukar hankalinsa,a haka wani lafiyayyan bacci me cike da shauƙi ya suresu,asuba ta gari .....

...........

Washe gari da ƙyar mama ta iya tsayawa ta karya,jikinta har rawa yake wajen saurin ta fita ta yi rawar da aka sa ta,mama saboda tsoro ko siyam ta kasa fadawa abinda ya faru,Amira kuwa gaba daya yau a hankalce take dan tana so taga ta inda zata sha kallo kamar yadda zahra ta faɗa mata.

Zahra da kanta ta yi musu breakfast suka karya ba tare da sun sauko kasa ba,yanzun ma a gantale suka gama shirinsu ab na biyewa tabararta da sakalcinta,Masha Allah babu abinda suke dubawa sai ƙamshi ga wani irin kyau na musamman me fitar da annuri da su kayi kana kallonsu zaka tabbatar da cewa sun samu nutsuwar zuciya.

A hankali yake sauka kasan Zahra na gefensa kamar cingom, babu kowa a falon sai ƴar hayaniya da suka jiyo daga can compound,fuskewa Zahra ta yi kamar bata san me ke faruwa ba ta kallesa a mairairaice ta ce,"dan Allah ka barni na fita kaga dai kayan dake jikina manyane kuma fa har gyale kasa na saka",ta ƙarasa maganar tana ƙwalƙwal da ido kamar zata yi kuka,ɗan numfashi ya fesar ba tare da ya ce komai ba ya yi gaba, da sauri tabi bayansa dan tasan me shurunnnasa yake nufi.

A can waje kuwa mama ce ta tara ƴan kallo dan babu wanda ya Ankara sai ganin mama akayi tana zagaye gida tana rawar disco har da tafi da waka,da farko ma'aikatan gidan sun ɗauka nishaɗi ne kawai irin na yarabawa masu son rawa,sai da abu yayi abu suka ga fa ashe abun na gaske ne,take kowa ya ajiye abinda yake yi ya taho kallo,Ammi da daddy ne suka fara fitowa saboda josuwa da yaje ya sanar dasu,daga nan sai ga Amira sai kuma ga baba talatu da ragowar ƴan aikin, daddy ne yayi ƙoƙarin janyeta yana mata magana akan ta bar wannan abinda take yi zubda mutuncinta yake yi tunda kowa kallonta yake yi,wani banzan kallo mama ta yiwa daddy kafin ta fincike hannunta tana ci gaba rawarta harda yin ƙasa_ƙasa kamar tana tukyin tuwo.

Tun daga nesa Zahra ta fara tuntsura dariya, wlh ko ab duk miskilancinsa sai da lamarin mama yaso basa dariya kawai dai fuskewa yayi kamar yadda ya saba boye yanayinsa,"yaya AB yau kuma aljanun mama masu disko ne kai wallahi wannan lamari a kwai citta".

Tana fadin haka ya zuba mata ido cike da tuhuma,tura baki ta yi cikin ƙunƙuni ta ce,to Ni kam babu ruwana ato,aljanunta ne suke cikin nishaɗi kawai"wannan jawabinnata shi ya kuma tabbatarwa da ab cewa da sa hannunta,a hankali ya zura hannunsa ya kama kunnenta ya ɗan murɗa kaɗan,ƙara tasa tare da ƙankamesa tana sakin kukan taɓara, hankalin su Ammi ne ya dawo kansu dan basu san sun fito ba sai ƴan tsegumi irin su siyam da Amira,Ammi ta ce,"lafiya me kayi mata?"sakinsa Zahra ta yi ta koma wajen ammi tana cewa, "Ammi kunne zai cire min" a wane dalilin?"bai bada amsar tambayarba sai gaidasu da ya yi ya wuce inda motocinsu suke,da dan karfi Zahra ta ce,"yaya AB ka tsaya ka kalla mana ko kuma na yi maka video na ajiye maka?"

Wata uwar ashar siyam ta lailayowa Zahra tana jin kamar ta je ta yi mata shegen duka,Zahra bata kulata ba sai ma maida hankalinta kan Amira ta yi,suna haɗa ido kuwa suka sa dariya har da tafawa, kallon da ammi ta yi musu yasa suka nutsu suna ƴan kame kamen rashin gaskiya,

Daga can kuwa mama ta yi wajen zagaye na biyar, kafafunta tuni suka fara rawar gaske saboda gajiya,amma saboda tsoron abinda zai faru da ita haka ta ci gaba da juya jiki tana yi tana faduwa, waka kuwa ta yi kusan kala goma ta kama waccen ta saki ta kama wancan ta bari,har dasu salawaitu salo wakar dan Ibro, daga nan ta koma me dawayya, ta saki ta kama gwanja,siyam da taga abin na neman komawa hauka da gudu ta karasa wajen maman ta yi mata rikon tsauri tana cewa, wallahi mama ba zaki ci gaba da yin wannan haukar taki ba"bangajeta mama ta yi tana cewa "kai sasasa sakeni ko na si ubanka, kai dan baka san komi ba si yasa kake son hanani ka jawo min sabon bala'i.

Kuka siyam tasa dan a tunaninta mama haukacewa ta yi.

daidai lokacin aka buɗe katon gate ɗin gidan da ya kusan cinye rabin anguwar,motar Company ce ta shigo,dan dalilin da yasa securitys suka bude gidan ba tare da tambaya ko dogon bincike ba kenan,motar na tsayawa mutanen ciki suka shiga fitowa,wa Zahra zata gani kaf ƴan gidamsu ne har da kaka da kawayenta su nadiya.

Wani ihun murna Zahra ta yi tare da kankame kaka kamar zasu faɗi, sai kuma tasa kuka tana sakin kaka ta koma kan su nadiya daga nan kuma ta dinga bin yarbawan gidansu tana rungumesu,Zahra saboda farinciki tuni ta manta da yar tsamar dake tsakaninta da yarbawan gidansu ta manta da kyamarsu da take yi ta manta da halinsu da take ƙi.

Zubewar da maman siyam ta yi a wajen rigijif shi ya maida hankalin kowa kanta, da sauri siyam ta karasa gabanta tana ihu,mama kuwa numfashinta dakyar yake fita saboda tsananin gajiya,masu aiki siyam ta sa suka dauki mama suka shiga ciki da ita.

Zahra kuwa rankayawa su kayi ita da baƙinta da suka zama ƴan ƙauyen ƙarfi da ya ji......✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*