YAR GIDAN YARBAWA

Page 56

by @zahrawriter12

.......sai da ta bari ya zo daidai inda take yana ƙoƙarin taɓa ta ta yi wani irin juyi ta koma ɗaya ɓangaren kafin yayi tunani juyin da a ta yi na bacci ne ko na ido biyu ne tuni ta kaiwa gabansa wani mugun duka da ƙaton kofin silbar da aka kawo mata ruwa me shegen nauyi irin na da can,dafe wajen ya yi cikin azabar da ta shigesa, amma duk da haka dake jaraba na cinsa da tsautsayi kuma yasan babu wanda zai farka a wannan lokacin,dan haka bai karaya ba cikin karfin hali ya kuma yunƙurin kamata, nan ɗin ma bai samu sa'ar tabata ba,sai sa'ar kuma samun wani bugun a daidai macijinsa da yayi, inda a wannan karon zahra bata yi da wasa ba wajen zage karfinta wajen buga masa kofin ba,ihu yasa yana dafe wajen idanunsa har sun fito saboda azabar raɗaɗin da wajen ke masa.

Ganin haka yasa Zahra ta yunƙura ta miƙe tana kallon yadda yake taurza wajen,ɗagowa ya yi da niyar sake jarrabawa,ita kuka Zahra tuni ta kai masa duka a wajen da ƙafarta take ya sube a wajen yana matagugu,da wannan damar ta yi amfani ta shiga dukansa da kafafunta tana take shegen macijinnasa, tun Adebayo na ihu har ta kai ya koma numfarfashi kamar zai mutu dan shi kadai yasan irin yadda hukuncin Zahra ke shigarsa, Zahra bata barsa ba sai da ta tabbatar da cewa ta nakasta macijinsa koda zai samu lafiya tabbas zai jima kuma ba zai dawo daidai kamar da ba,miyau ta tattofa masa a fuskarsa sannan ta tsallakesa ra fice daga ɗakin da gudu tana fatan barin gidan kafin masu gidan su tashi.

A bangaren ab kuwa, tun yana dauriya da azababben ciwon kan da ya addabesa har alamu ya fara nunasa a fuska,Ammi da daddy suna kansa sun kasa barinsa duk yadda yake dauriya wajen nuna musu lafiya yake suje amma sun kasa,dan suma ko sun tafi ba za su iya runtsawa ba,kansa yana kan cinyar ammi,ganin yadda tashin hankalin ya musu yawa yasa ab miƙawa ya shiga bathroom ya dauro alwala ya fito,suna ganin ya tada sallah dole suma suka fita zuwa dakinsu dan miƙa kokensu ga Allah dan shi ne zai kawo musu mafita.

Sallah kawai yake iya yi dan ita ce yake ganewa a wannan lokacin,dan haka yinta kawai yake ba tare da yasan ya gaji ba, addu'a kawai da neman dauki yake nema wajen Ubangiji,daga ƙarshe ya dangana ga ɗaukar littafi me tsarki ya shiga karatu da yaƙinin ƙudurce bukatarsa a zuciyarsa.

A can ɓangarensu mama ma,tuni Abba ya bada sadaka almajirai suka shiga addu'a da karatu,yara kuwa sadaka aka dinga basu wanda su dama ko ba a basu ba tuni suka fara addu'ar Allah ya baiyana aunty Zahra me basu sadaka da kyautata musu cikin Aminci,ko da su Mami zainab da al'amin suka sauka babu wani shaukin murna da dokin ganin juna sai zaman jimami da addu'a dan gaba ɗaya suna zaune a falonne ba tare da wani yana shirin runtsawa ba,kaka ce ma ke iya kuka amma Dukansu zuciyarsu a ƙone take babu abinda take yi sai azabtuwa,hatta da yarbawan Zahra sun shiga damuwa me tsanani dan duk bidurin da suke da Zahra sun ɗaukesa wani abu na ɗaukar darasi da kawo gyaran da ta yi a cikin rayuwarsu suna son Zahra kodan aherinta da nishaɗin da take basu.

Haka wajen ƙawayenta abun yake suma zaune suke suna addu'a da jimami sun kasa runtsawa.sauran masoyan Zahra kuwa addu'a suke mata ta fatan kuɓuta daga duk wani sharri ya kuma dawo da ita gida lafiya.

Maman siyam dai baccinta take hankali kwance. yayin da siyam ta kasa bacci saboda tunanin sanin halin Zahra, tabbas idan basu yi saurin kasheta ba zata iya kuɓuta, dan a ɗan zaman da su kayi na watanni kusan shida ta gama sanin wacece Zahra a haka kamar wata sakarya amma tana da wayo da dabara wanda suka haɗe cikin sakalcinta shi yasa ba a ganin hakan, wannan tunani shi ya hanata runtsawa kamar yadda tunanin Zahra ya hana masoyanta runtsawa.(acikin fans din Zahra ma akwai wanda basu runtsa ba 😄).

Zahra na fitowa taga gari dundum gashi da alama a daji gidannnan yake,tsayawa ta yi daga bakin kofar cikin tunanin yadda za tayi, cikin yanayin son fashewa da kuka ta ce,"to ni ya zanyi? Kar naje na fita aljanu su kamani su cinye?"fasa fita ta yi ta juya ta koma cikin gidan, dan da ta fita a wannan lokacin cikin dajin Allah da bata san ko ina ba bata san ina zata nufa ba,Gara ta haƙura Allah ya kawo mata wata hanyar kuɓutar.

Tana komawa ɗakin ta samu Adebayo ya suma, ruwa ta ɗebo ta zuba masa tana cewa "ai wallahi ta shi za kayi kaci gaba da cin wahala tsinanne kwarto" zama ta yi daga can ƙarshen katifar tana kallonsa yana juyi da mata gugu kamar zai mutu, Zahra bata ji komai ba dan tasan ko mutuwa ya yi bata da hakkinsa tunda ƙwatar kanta ta yi.

A haka aka kira assalatu, Zahra ta miƙe ta ɗauro alwala ta yi raka'atanil fijr ta ɗora da Sallah asuba,bayan ta idar ta zauna ta yi laziminta tare da karatunta da ka a fili tunda bata ga alamar ko takarda a gidan ba bare littafi me tsarki.

Ana idar da Sallah Ammi da daddy suka nufi saman dan duba ab,shima Jafar da josuwa nan gidan suka nufo.

Akan sallaya suka samesa kwance ya yi matashin kai da hannayensa idanunsa a lumshe kamar me bacci,jin motsinsu bai sa ya motsa ba,ammi ce ta dafa kansa, aiko cikin sauri ta ɗauke hannunta saboda wani mugun zafi da ta ji,kallon daddy ta yi a ruɗe tana cewa "daddin amira ya kamata mu tafi hospital karmu daka ta babana har yanzu bai san ciwon kansa ba",waya daddy ya fara ƙoƙarin kira amma sai Muryar AB da ta zama wata iri ta katsesa da cewa,"no dad Kar ka kira kowa magani ko wani treatment ba zai min ba kawai ku yi addu'a shine mafita"daga haka ya rufe idanunsa kamar yadda suka zo suka samesa.cikin lallaɓawa ammi ta ce,"to amma da ka daure ka tashi ka sa wani abu a cikinka kaga fa rabonka da abinci tun breakfast din jiya" ba tare da ta saurari uzurinsa ba fita da kanta zuwa keching din Zahra ta haɗo masa tea me kauri ta dawo, dakyar suka lallabasa ya tashi zaune,kurɓa ɗaya biyu ya yi ya miƙa mata idanunsa akan tafkeken gadonsa wajen da Zahra ta fi kwanciya ya ce,"Ammi ba zan iya sa komai a ciki na ba saboda ban san halin da Zahra ke ciki ba ta ci ko bata ci ba Allah masani"ɗan jim ya yi kafin ya dawo da kallonsa kan Ammi da take hawayen tausayin ab da na zahra,ya ce "Ammi kaka ta yi wata magana da ta tsaya min sosai ta ce,wai zahra na da ciki" zabura ammi ta yi sai kuma ta fashe da kuka lallai wannan shi ake kira da ga koshi ga kwanan yunwa.

A wannan safiyar da masoyan Zahra suka tashi da tabbacin cewa Zahra fa ta bace tunda gashi har an kwana babu ita babu labarinta duk da yadda ƴan sanda suke tsaye a kan lamarin amma an kasa samun wata shaida guda da zata basu damar samun susfec a cikin lamarin.hakan ya kuma ɗagawa kowa hankali dama shi ab babu um ba umm sai idanun da zai daga ya kalleka ya mayar ya lumshe, yaki cin komai ya ƙi shan komai, ko ya yi niyyar sa wani abu a bakinsa da ya tuna Zahra fa babu tabbas din ta ci sai kawai ya haƙura,Amira dai al'amin shine me rarrashinta.

Su nadiya da Hafsah kuwa tuni suka tare gidan su Zahra bayan sun gama karaɗe anguwa da gidajen yan uwan da abokan arziki tare da al'amin da Habib da mami zainab,ƴan gidan yarbawa ma har yanzu shiga suke suna fita basu gazaba wajen neman Zahra.

Ƴan sanda kuwa sun samu wanda ya shaida musu motar da ya gani tun safiya a wajen,a yadda ya sanar da su yanayin motar,haka shima yaron da aka aika ya kira Zahra ya sanar dasu ita ce,sai dai kuma basu rike nomber motar ba,amma anyi nasara yaron ya ce, ya gane fuskar wanda ya aikasa gidan kaka kiran Zahra, to da wannan ne ƴan sanda suka samu ƙwarin gwiwar fuskantar lamarin sosai dan sun fara shinshino nasara.

Sai wajen karfe takwas sannan wasu suka fara farkawa cikin yaran Durga tare da mamakin nauyin baccinsu,lokacin da bash da Durga suka tashi kai tsaye ɗakin Zahra suka nufa dan lokaci daya tunaninsu ya basu cewa wannan bacci da su kayi ba na lafiya ba ne dole akwai abinda ke shirin faruwa ko ma ya riga ya faru.

Turus su kayi cike da mamaki suna kallon Adebayo da ya gama fita daga hayyacinsa wandonsa kuwa duk ya ɓaci da jini kamar wanda aka yanka rago,Zahra kuwa na daga can gefe raɓe tana zabga gyangyaɗi. wani uban ashar Durga ya yi tare da Haurin Adebayo da kafa yana cewa "dan ubanka tashi ka fada min abinda ya faru me kayi mata? Wato Ni zaka munafunta duk halaccin da nayi maka ko?" jin muryarsu yasa Zahra ta farka cikin kuka take sanar dashi abinda ya faru har da cewa ya mata alkawarin idan ta barsa ya yi zai buɗe mata kofa ta gudu,wani mugun duka Durga ya kaiwa Adebayo wanda take a nan ya sume saboda akan matsalarsa ya yi masa dukan maza. cikin kuka Zahra ta ce, $Ni ku bani wainar fulawa yunwa nake ji" da sauri Durga ya kalli femi ya ce, "maza je ki mata wainar fulawa yanzu ki kawo mata"a'a ni da kaina zan yi zahra ta fada cikin kuka me ƙarfi wanda duk ya ɗaga musu hankali, duk da cewa gurin daji ne to amma abinka da marasa gaskiya duk sai suke tsoro da ganin kamar kukanta zai iya tona musu asiri.

Kai tsaye Durga ya ce da femi ta raka Zahra keching ɗin ta yi abinda take so,jinjina kai femi ta yi ranta cike da ƙuna akan yadda durga yake neman zama sakarai akan Zahra,tashi Zahra ta yi ta bita, shi kuma Adebayo suka ɗaukesa suka watsasa a wani ɗaki daban suka kulle.

Suna shiga keching ɗin wayar femi ta fara tsuwa, da sauri ta fita ta wata ƙofa dake keching ɗin tana mai ɗaga wayar,Zahra na hangota tana kalle_kalle kafin ta fara magana da siyam da ita ce ta kirata.cikin sanɗa Zahra ta bi bayanta ta laɓe,tana tabbatar da cewa da siyam femi ke waya ta koma keching ɗin cikin sauri ta duba inda aka ce fulawa na nan ta ɗauke ta ɓoye sannan ta koma ta tsaya kamar tunda femin ta bar keching ɗin bata motsa ba. kallonta femi ta yi cikin mamakin tsayuwar da take yi ba ta fara yin abinda ta fito yi ba,ɗage mata gira Zahra ta yi sannan ta ce,"ina fulawar take na duba inda kika ce ban gani ba" da sauri femi ta duba wajen amma fulawa ta ce ɗaukeni in kin ganni, dan haka ta fita da sauri tana cewa "bari na sanar da Oga yasa a karɓo ko kuma ki haƙura" sam femi ta manta da cewa Zahra fa zata iya fecewa domin hankalinta yana kan umarnin da siyam ta bata akan ta san yadda ta yi ta kashe Zahra tare da yi mata alkawarin kuɗaɗe masu yawa wanda yawansu ne ya gigita femi har ta manta da tunaninta.

Femi na fita Zahra ta kunna gas ta dauki wata roba ta ɗora akai sai da ta kama sannan ta cilla ta daga can bakin kofar keching ɗin ta cikin gidan har zata fita sai kuma ta dawo ta kashe gas ɗin saboda ba burinta ta kashesu ba burinta kawai ta kuɓuta ta hanyar dauke musu hankali da wutar da ta kunna musu dan tana da tabbacin zasu Ankara da wuri tunda sun san tana keching ɗin,sannan ta fice ta wannan ƙaramar kofar tare da rufe ƙofar ta waje,cikin sa a ta ganta a ta wajen ƙofar fita daga gidan sai dai kuma akwai masu tsaron kofar, dan haka ta raɓe a jikin katangar tana tunanin yadda za ta yi ta fita.

Daga can kuwa femi tana sanar da Durga, shi kuma ya kira masu tsaron kofar mutum daya akan yazo ya siyo fulawa tunda dama shi ne me iya shiga cikin gari ya shigo musu da abinda suke buƙata. yana tashi shi kuma ɗayan ya ɗauki buta ya shiga banɗaki. hamdala Zahra ta yi ta fito da gudu tana zuwa ta zare kwaɗon jikin kofar da ba a riga an datse shi ba, a hankali ta buɗe ta fice daga gidan ta yanki daji ba tare da waiwayen baya ba.......✍🏼

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*