Page57
Daga can wajen su Durga kuwa femi na ganin dan aiken ya shigo ta bar wajen tana gyara wukar Durga da ta sace ta ɓoye a ƙugunta,kai tsaye keching ta nufi komawa, sai dai tun kafin ta shiga ta fara ganin hayaƙi na fitowa ta kofar, har kofar ta fara kamawa da wuta. ihu ta sa tare da banke kofar ta buɗe sai gani su kayi wuta ta fara cin keching ɗin sosai tunda akwai gas a ciki,lokaci ɗaya hankalinsu ya tashi kowa ya fara ƙoƙarin ceton ransa,Durga kuwa zahra ya shiga bulayin nema a haukace, bash ne ya fara ƙoƙarin kashe wutar shida ragowar yaransu,sai dai kamar suna ƙara kunnata wani daga cikin yaranne ya buɗe Adebayo ya fito da shi daga cikin gidan a can gaba da gidan ya yasar dashi ya dawo suka ci gaba da ƙoƙarin kashe wutar. femi kuwa gaba daya hankalinta ya gama tashi domin yanzu sun tabbatar da cewa zahra ce ta kunna musu wutar ta gudu,dan haka cikin ƙaraji durga ya bawa kowa umarnin da a fita a karaɗe dajin a nemo masa Zahra duk inda ta shiga dan ya tabbata bata fita daga area ba.
Zahra kuwa gudu take ba na wasa ba ko waiwaye bata yi dan kar ma taga abinda zai daga mata hankali.
Sai dai kuma daga can ta ji muryar bash yana cewa "gata can mu bita" Zahra na waiwayawa ta gansu wajen su hudu suna binta aiko take ta ƙara ƙarfin gudunta tun tana yi a marmarce har ta fara haki ga yunwa da jiri na shirin yar da ita.
Ganin suna kokarin cimmata ƙarfinta kuma na ƙarewa yasa ta nemi wajen ɓuya daga cikin wasu dogayen ciyayi,ƙirjinta ta dafe tana maida numfashin wahala,muryoyinsu ta fara ji suna cewa "mu duba ko ina tana tsukin wajennan"hannu tasa ta toshe bakinta dan kar nishin da take yi ya jawo hankalinsu, dai-dai inda take bash ya tsaya yana basu umarnin duk wanda ya fara ganinta kawai ya kasheta da wuƙarsa,zaro ido Zahra ta yi tana jin kamar zata fashe da kuka.
Can kuma sai ta ji shiru,da alama dai sun bazama nemanta loko da saƙo na dajin,amma shi bash har yanzu yana a wajen da yake dan motsi kaɗan zai yi ya tarar da Zahra dake bayansa,can idanun Zahra suka hango mata wata ƙatuwar kunama ta ɗaga ƙarinta da alama neman na abinci take yi,cikin dabara Zahra ta dauki wani dogon ice dake kusa da ita sannan cikin sanɗa ta bar wajen tare da yiwa bash wata irin shammata ta hankaɗasa kan wannan kunamar da basu da tazara da yawa,cikin sa ar da Allah ya bata kuwa bai Waɗa akan komai ba sai kan ƙatuwar kunamar nan,da gudu Zahra ta bar wajen tana jiyo ƙarar da bash ya saki saboda harbin da kunamar ta shiga yi masa ajajjere,sai ga ragowar suna fitowa daga inda suka shige neman Zahra, cikin sauri suka ɗagasa daga wajen sai ko ga kunamar nan ƙatuwa har yanzu huci take tana neman daɗi,ai da sauri suka bar wajen tare da bash da tuni ya sume musu.
Shima Durga wani wajen ya nufa yana neman Zahra amma bata ba dalilinta, daga ƙarshe gidan kuma ya kama da wuta gaba dayansa,wanda ya zamar musu dole su bar wajen idan ba haka ba ƴan sanda zasu iya samunsu a wajen,basu yi tunanin ɗauke Adebayo ba suka bar wajen bayan dawowar su bash, Durga kuwa bai ma san inda hankalinsa yake ba saboda masifar bakincikin rashin Zahra wanda ya ji a ransa ba zai iya haƙura da ita ba dole ya tsira dan kawai ya nemo Zahra.
Suna barin wajen ƴan sanda suka ƙaraso, wanda dama suna kan hanyar zuwa dan bincikensu ya nuna musu cewa Zahra na sashen wajen. Sai dai suna zuwa suka tarar da gidan ya na ci da wuta kamar an sa masa fetur,nan suka shiga binciken da zasu yi har suka tabbatar da cewa babu kowa a gidan dan basu ga gawar kowa ba,sai Adebayo da suka tsinta yashe a ta bayan gidan wanda shi sam baya cikin hayyacinsa.
Kai tsaye asibiti suka wuce da Adebayo, yayin da commissioner ya sanar da daddy abinda ke faruwa da wutar da suka tarar na ci a gidan,duk yadda commissioner yaso fahimtar da daddy cewa basu sami kowa a gidan ba dan haka basu da tabbacin cewa Zahra tana cikin gidan amma ya kasa fahimta, dan kuwa ruɗewarsa sosai ta fito har ya kasa dannewa sai da Ammi dasu baba talatu suka fahimta dan haka bai tsaya zagaye zagaye ba ya sanar da su abinda commissioner ya sanar dashi,zubewa ammi ta yi a sume, da gudu baba talatu ta je ta ɗebo ruwa ta zuba mata,tana farkawa ta fashe da kuka me cin rai gwanin tausayi,sai alokacin daddy ya dawo hankalinsa ya fara lallashinta akan cewa zahra bata cikin gidan dan haka ta yi shiru kar ab ya ji abinda ke faruwa,Amira kuwa dama tana can gidansu Zahra tare da su nadiya da su al'amin.
Wani tsallan murna siyam dake laɓe tana jin komai ta yi, shike nan matsalarta ta zo ƙarshe, ashe duka suka ƙone duk wanda take tunanin zasu bata matsala sun ƙone, ashe shi yasa take ta kiran wayoyinsu bata samu ba?, yau murna har da shagali ranta fes ta shiga fesawa mama dan haka gaba daya suka dawo falon suna kukan munafunci da ganin ido,idan suka faki ido su yi gwalo.
A bangaren gidansu Zahra ma al'amin kin gaya musu abinda ke faruwa ya yi,ya dai sanar dasu cewa ƴan sanda suna daf da gano wajen da Zahra take dan haka su kwantar da hankalinsu in sha Allah zuwa gobe Zahra zata dawo,da wannan labarinne suka samu ƴar nutsuwar gabatar da wasu abubuwan.
Gaba ɗaya ƴan sanda sun zagaye asibitin da aka kai Adebayo,saboda kulawarsa tana karkashin hukuma,duk da cewa a bayanin da likita ya yi musu ya tabbatar musu da cewa Adebayo zai jima sosai a asibiti kuma duk da haka ba lallai ne a samu maganin matsalarsa ba dan a gwajin farko sun gano cewa mazantakarsa ba lallai ta tashi ta cigaba da aiki ba,kuma koda ta ci gaba da aikin ba zai samu kaso ɗaya cikin goman lafiyarsa ta baya ba,amma dai likitan ya basu tabbacin nan da kwana uku zasu iya magana da aden domin jin bayanan da suke son ji daga garesa.
Abrahab bai san duk abinda ke faruwa ba,yana samansa Jafar ne ke kula da shi saboda Daddy ya hana Ammi zama kusa da shi dan tana ƙara ɗaga masa hankali da damuwarta ne kawai,Jafar kansa ya sarawa jarumtar ogannasa duk da su a wajensu sun fi son ya fidda damuwarsa fili ko ya ɗan samu salama,amma tabbas aka kai wani lokaci ba a ga zahra ba suna iya ganin zuciyar ab ta buga ba tare da ya basu wata alama dazata nuna musu cewa tana kumbura ba,gaba ɗaya kalmominsa daga jiya zuwa yau basu wuce ashirin ba,baya cewa kuma baya bukatar a ce masa.
Sosai siyam ta fahimci cewa ba a son ab yasan halin da ake ciki dan haka ta fara shirya yadda zata sanar masa a yi ta kawai ta ƙare kowa ya huta, ai dole idan ya yi kukan mutuwar ya gama ya haƙura ya rungumi ƙaddara, dan haka take ta fakon idanun mutane tana so ta je lokacin da yake shi kaɗansa yadda babu wnada zai yi zargin ita ce ta faɗa masa.
.........Zahra kuwa sai da ta tabbatar da komawarsu sannan ta fito daga inda ta boye ta ci gaba da tafiya a hankali saboda jiri ga yunwa da ke sakadarta kamar ƴan hanjinta zasu fito.
Tsayawa ta yi ta ɗan huta sannan ta ci gaba da tafiya,duk da yadda take jin jiri da gajiya hakan bai hana ta sakin murmushi ba saboda hango titi da ta fara yi, hakan yasa ta daure ta kuma daga ƙafarta da ko takalmi babu jikinta kuwa daga ita sai doguwar rigar jikinta tun ta jiya.
Tana ganinta a titi ta yi hamdala kana ta fara ƙoƙarin tare a bin hawa,wani me nafef ne ya tsaya a gabanta yana kallonta cikin alamun tambaya amma dai baiyi ba tunda ya ji ta yi maganar hankali,"dan Allah malam ka Kaini mension Abrahab bakare"Abraham wanda na sani ko wani daban?"da sauri Zahra ta ce,"wanda ka sani me Company shinkafa da auduga me asibitin bakares hospital"an gama Hajiya gidan mutumin kirki zaki ce zan kaiki duk da ban san ke wace a gidan ba dan Ni ina mutunta duk wanda yasan wannan bawan Allah ko da bai haɗa jini dashi ba" shiga nafef din Zahra ta yi tana sauraren me nafef da yake gaya mata alherin ab a garesa ya ce, "wannan mashin din da kike gani wallahi shi ne ya siya min saboda wannan mutumin yanzu rayuwar farin ciki a ke a cikin gidana yarana duk suna zuwa makaranta daidai karfina saɓanin da da suke zaune a gida abincin da zasu ci ma yana gagararsu amma sai gashi komai ya zama labari duk a sanadin ABRAHAB" murmushi Zahra kawai take yi saboda yabon da ɗan kurmanta yake sha, dan yau duk surutu irin na Zahra ta haƙura dashi saboda cike take da kewa da shauƙin ganin ɗan kurmanta dan haka jinjinawa me nafef kai kawai take.
Sosai daddy da ammi har ma da masu aikin gidan suka ji daɗin fitowar AB sallar la'ar duk da dai kallo daya zaka yi masa kasancewa karfin hali da jarumta kawai yake nunawa,ko da ya dawo kasa hawa saman ya yi saboda jikinsa da yake kuma ɗaukar dumin zazzaɓi ga ciwon kai me tsanani wanda tashin farko Dr sonie ya tabbatar musu da cewa jininsa ne ya yi mugun hawa,shi yasa dinga yi masa allurar bacci daga safiyar zuwa yammacin nan, amma duk a banza dan ko rufe idanun da niyar bacci bai yi ba sai dai lumshesu kamar yadda yake aladarsa, daddy ne ya janye ammi zuwa daki yana mata kashedi akan ta daure kar Ab ya fahimci cewa suna ɓoye masa wani abu dan tasan halin danta da saurin fahimta,
Jafar kuwa fita ya yi ya kira Dr sonie dan idan AB din ya sani ba zai batsa ya kirasa ba,sai ya zama babu kowa a falon sai shi kaɗai sai kuma baba talatu dake can cikin keching tana aikace aikacenta cikin sanyin jiki.
Da sauri siyam dake fakon kowa ta yi wuf ta fito daga corridor na dakinsu tana sharar hawaye,tana zuwa ta zauna gefan Ab din tana cewa, "tsakani da Allah yaya AB ba kai da Zahra take matarka kuke zaman lafiya ba hatta Ni da ba jituwa muke ba naji zafin batanta,to sai kuma gashi dazu ƴan sanda sun sanar damu cewa an samu gidan da aka kai Zahra amma an samu gidan yana ci da wuta da alama dai duk wanda yake cikin gidan bai tsira ba kuma an tabbatar da cewa Zahra na cikin gidan wallahi naji mutuwar Zahra al.....inji ubanki ya ce miki na mutu?wato so kike na mutu ki aure min ɗan kurmana to wallahi macijin ɗan kurmana yafi karfinki sai gani sai hange kwartuwar banza kwartuwar wofi".
Zahra dake shigowa falon ta ta faɗa bayan ta gama sauraren maganganun siyam,Jafar dake waje shi da securitys din gidan su suka fara ganin Zahra dan Jafar tsayar da me nafef din ya yi saboda kawo Zahra gida abu ne da yake bukatar bincike ga wanda ya yi hakan,dan haka dole shima me nafef sai ya amsa tambayoyi,me nafef din bai razana ba dan kafar ya masa bayani sosai yadda zai fahimta to ita dama gaskiya ɗaya ce idan kana da ita baka da damuwa akan abinda kasan baka aikata ba.
Wani irin zaro ido siyam ta yi cike da firgici da tashin hankali tana kallon Zahra tamkar wadda take kallon fatalwa.
Cikin tsoro siyam ta nuna Zahra tana cewa, "dan Allah ki daina yi mana fatalwa ki koma ƙabarinki ki bar bawan Allah ya samu salama wannan wace irin masifa ce kin mutu din ma ba zaki barmu mu huta ba".
Kallon Ab siyam ɗin ta yi wanda ashe tuni ya fita hayyacinsa a zaune kawai yake tun maganarta ta kusan karshe akan cewa Zahra ta ƙone.
Da gudu Zahra ta ƙarasa inda ab yake idanunsa na kallon wuri ɗaya amma ga dukkan alamu baya duniyar mutane, shock ne ya shigesa mai matukar haɗarin gaske,jijjigasa Zahra ta yi sai kawai taga ya taho luuuu zai kifa,tarosa ta yi ta kwantar a kujerar,kana ta mike a fusace cikin wata irin zuciyar da bata san tana da ita ba da wani karfi da bata san tana dashi ba,ta fizgo siyam ta bata wani mari me mugun zafi hagu da dama kafin ta wurgata gefe sai da kanta ya bugu da Centre table sai gashi yana jini,nunata Zahra ta yi da yatsa cikin wani irin fusata ta ce, "wallahi siyama burinki ba zai taɓa cika ba,kuma ki tabbatar da cewa kin shiga uku tunda har na dawo gida domin zaman lafiya da kwanciyar hankali ya ƙare a wajen ki"komawa kan ba ta yi tana jijjigasa, dai-dai lokacin su daddy da Ammi suka fito nan su kayi turus ganin zahra ga kuma wani tashin hankali daban AB a kwance kamar matacce,to murna zasu yi ko bakinciki?ga Zahra ta dawo me ye dalilin shigar ab wannan hali?.
Kallon inda siyam take ta kuka ga jini na zuba a goshinta su kayi,me yake faruwa ne?
Shigowar Jafar da Dr sonie ne ya dakatar dasu daga neman ba asin da suke, da kuma rufuwar da suka yi akan ab hankali ta she...........✍🏼
[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*
💕
' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
***
*_____________________________________*