YAR GIDAN YARBAWA

Page59

by @zahrawriter12

.......gaba ɗaya AB ya rikice lashe ko ina yake na jikinta yana jinsa kamar ba a duniya ba,ita kanta Zahra bata taɓa fita hayyacinta a karɓar saƙon ɗan kurmanta ba sai yau,yau ɗin ta kasance musu wata rana ta daban, ranar da dukkansu asirin dake binne cikin zuciyarsu yake bayyana kai tsaye ga junnasu.

Shiɗewa Zahra ta yi saboda jin yadda ab ya kafa kansa a ƙasanta yana mata wani irin sha me kamar yana shan madarar shanu, ƙanƙamesa ta yi jikinta na wani irin karkarwa hakoranta har haɗewa suke kamar me jin sanyi,rasa inda zata sa kanta yasa ta fashe da kuka tana kuma kanƙame kansa da har lokacin yake jikinta yana shanye duk wani ruwa dake fitowa daga jikinta.

Zahra so take ta gwada masa ƙauna kamar yadda ya gwada mata saboda ita bata taba zaton a rayuwa ana shan wannan guri ba domin a ganinta akwai ƙyama, hakan yasa itama ta nuna jarumta wajen kwatanta abinda ya yi mata da macijinsa wanda sai da ta yi da na sani dan kuwa ɗan kurmanta sume mata ya yi saboda tsananin shauƙi, sai daga baya ta fahimci dalilin suman nasa dan haka ta ci gaba da ƙoƙarin faranta masa da duk hanyar da tasan zaiji daɗi,daga nan ya samu abinda yake so ta hanyar zamansu guda a karo da dama.

Rungumeta ya yi tsam a jikinsa kamar wanda ake shirin ƙara ƙwace masa ita, ji yake babu wani abu da yake ƙauna a duniya idan aka cire mahaifansa sama da Zahra, bai san cewa zai tsinci kansa da irin wannan son a duniya ba sai da ya samu Zahra,duk da haka yana ganin kamar babu irin nasa ko kwatankwacinsa, dan nasa son na musammanne tare da a bar ƙaunarsa ta musamman,ɗaga ta yayi cak suka shige bathroom domin baya son su yi bacci da najasa a tare dasu,ko da suka fito shi yaja su sallah su kayi Isha da shafa'i,sun jima suna addu'a da godewa Allah abisa Ni'imar da ya yi musu,daga nan kwanciya suka kuma yi dan zahra a daddafe ta yi sallar, dan ita kanta sallah ab ji yayi da ana yiwa mutum to da yi mata zai yi,yadda ta shige jikinsa ta ƙudundune sai ka dauka babu mutum a gurin, a haka su kayi bacci me cike da wata irin nutsuwar zuciya,asuba ta gari zahrAB......

Washe gari ma babu inda suka fita sunyi fes abinsu,idan ka kalli AB ba ka ce shine wannan na jiyan ba,dan kuwa yayi shar dashi goshinsa sai kyallin amarci yake yi,ga Zahra agefensa tana ta zuba masa sangarta da taɓara kala kala,shi kuma yana biyeta yana da ɗa sakaltata, ko da wasa bai yi mata batun ɓatanta ba saboda baya son abinda zai sa ta a damuwa ko mai ƙanƙantarsa shi yasa ya bari ƴansanda su yi aikinsu kawai.sai da aka kira sallar zuhur sannan ya yi alwala dan zuwa Masallaci,kafin Zahra ta fito daga bathroom din ya yi saurin fita dan shi abin har mamaki yake basa kallon zahra ka ɗ

ai sashi a cikin feelings yake shi yasa idan ya yi alwala zai fita sallah yake takatsantsan da abinda zai warware masa alwala.

Zahra bayan ta yi sallah sai kuma ta fara neman wayarta saboda tana son yin waya da su mama,tunawa ta yi wayarta tana wajensu Durga dan haka sai ta dauki wayar ab da ya bari ta dannawa mama kira,mama na ɗagawa Zahra ta sa mata kukan taɓara, ita ko mama rarrashinta ta shiga yi tana mai hamdala ga Allah,da ɗaɗɗaya suka dinga gaisawa da kowa na gidan tun daga kan Abba kaka har zuwa kan yaya Habib da al'amin,daga nannne mama ta karba ta yi mata albishir din da take ta son yi mata akan gidan sa ab ya siya musu,Zahra har kukan farinciki ta yi ba kunya take cewa mama,"mama ina son yaya AB sosai kuma ku tayani sonshi dan Allah kinji manana",kashe wayar mama ta yi tana murmushin dramar Zahra.

Zahra kuwa tana ji mama ta kashe ta juya kiranta kan maman daddy,maman daddy najin Muryar Zahra ta fara rawa da juyi tana rera wata waƙarsu cike da farinciki,tsaida ita Zahra ta yi tana cewa,na gode maman daddy amma yanzu bar wannan murnar sai mun haɗu",to sikenan zahla meye kake da bukata nasan wannan kira naka yana da dalili?",

"Yauwa maman daddy so nake ki samo min cinnakar nan ta ɗakinki Allah yasa dai baki toshe wajen ba?"ɗan jim maman daddy ta yi kafin ta ce,"ey da na tose amma yanzu sun kuma fase wajen ko jiya sai da suka bawa daddy sizo biyu a bombom nasi"Masha Allah maman daddy maza ki samu wani abun da kika san baza su mutu ba har zuwa gobe ki kwaso min kamar guda dari biyu wani hukunci zanyi dasu saura kuma naji wannan bakin naki ya subce ya gayawa mamana" a'a zahla zanyi abinda kana so ba zan gayewa mamanka ba, yaushe ne kake so na kawo maka?" Ɗan jim Zahra ta yi kana ta ce,ki kawo min yanzu idan kin zo karki sake ki nuna wani abu kika kawo min ki nuna kin zo mana jaje kawai kinji" Tom sikenan zaka ji Ni nan ba da jimawa ba"ina jiranki zahra ta faɗa tana kashe wayar tare da tuntusrewa da dariya tana cewa, Wallahi siyam kin shiga tara ba uku ba dan ba zan taba tona miki asiri yanzu ba sai kin fara ɗan ɗana kuɗarki a hannun zahra yar gidan yarbawa fiye da yadda mamanki ta ɗandana".

Wani irin zullo ta ji cikinta yayi take ta ɗafe wajen, sai taji kamar motsi ake yi,shiru ta yi tana son tabbatarwa dan ba yau ta fara jin haka ba amma dai na yau yafi na kullum,"na shiga uku Ni Zahra me ye a cikina haka?" Ta yi wa kanta tambayar da babu me bata amsa a kusa,mikewa ta yi zata bar dakin sai taji cikin ya kuma walƙatawa dan haka ta koma ta zauna tare da dafe cikin dai-dai inda yake motsawar, zubawa wajen ido ta yi tana kallon yadda yake motsawa ta jikin fatar cikinta da ta ɗan dago wanda sai a yanzu ta kula da kunburin da cikin yayi,tashin hankali ne sosai ya bayyana akan fuskarta saboda ita har ga Allah abin tsoro ya bata kuma bata kawo komai ba sai ko wani abu ne ya shiga cikin yake mata motsi har ya kumbura,kuka ta sa tana ji kamar ta cire cikinta daga jikinta, kuka take sosai wanda ke fitowa tun daga ƙarƙashin zuciyarta.

Tun daga farkon shiga falon yake jin sautin kukanta,hakan yasa ya ƙara ɗaga ƙafa cikin zafin nama ya shiga ɗakin. samunta ya yi a zaune dirshan hannunta akan cikinta tana rusa kuka hawaye shaɓe_shaɓe a kan kyakkyawar fuskarta. a nutse ya zauna a kusa da ita tare da sa hannu ya fara share mata hawayen da suke gudun saukowa daga idanunta zuwa kan kuncinta, cikin kamewarsa da tsantsar kulawa a cikin deep voice ɗinsa ya ce, "me ya faru me yasa kike kuka Zahra hot?"hannunsa ta kama ta dora akan cikinta kafin cikin sheshshekar kuka! ta ce,"yaya AB shike nan zahranka mutuwa zata yi"ware madaidaitan idanunsa masu haske ya yi akanta cike da mamaki,kana ya ce, "zah Hot ba mutuwa zaki yi ba in sha Allah sai kinga tattaɓa kunnenki da jikokinsu, fada min meye matsala?" Ya faɗa yana janta jikinsa cikin nuna damuwarsa da kukan da take duk da Yana expect din kukan na sakalci ne. luf ta yi a jikinsa tana ƙara ƙarfin hawayenta, shi kuma bai dakatar da ita ba sai shafa bayanta da yake a hankali yana tarairayarta da kulawa har sai da ta gaji dan kanta ta buɗe baki ta ce,yaya dan kurmana wani wani abu ne yake shirin faruwa dani cikina ne yake kunbura sannan kuma.yana yin motsi sosai kamar wani abu ne me rai a cikinsa".

Tana kaiwa ƙarshen maganar ta kuma fashewa da kuka tare da jan hannunsa ta ɗora akan cikin tana ci gaba da cewa "yaya AB wallahi da gaske abune me rai a cikin ka saurara kaji kaima Zaka ji motsin.

Tunda Zahra take shirmenta bata taɓa sashi jin dariyar da ya kasa riƙeta ba sai yau,kai tsaye ya fara darawa abinda ya zama sabo a gurin Zahra bare kuma ga sauran mutane, sai hakan ya zama abin kallo a gareta dan bata san lokacin da ta saki baki da idanuwa da hanci tana kallon kyakkyawar fuskarsa me kyau da sheƙi ba,ganin yadda take kallonsa yasa ya dan tsaya sai kuma ya yi murmushi me fadi wanda ya kusan sumar da Zahra,hannu tasa a fuskarsa tana shafawa kamar wata makauniya kafin cikin muryarta me sanyi ta ce, "yaya AB kafin abinda ke cikina ya kasheni ka yi ta min dariyar nan ina kallo ina jin daɗi kaji"sumbatar lips ɗinta ya yi har yanzu fuskarsa cike take da wani irin fara a me haɗe da farincikin da yake bayyane tun daga can ƙarƙashin zuciya,kana cikin yanayin kamewarsa muryarsa kuma na bayyana ɗokinsa akan abinda yake son tabbatarwa ya ce,my Hot zahr ba wani abu ba ne so karki damu, yanzu zamu shuga lab na duba ki in sha Allah ba wata damuwa umm,"ka tabbatar?" zahra ta fada cike da yarinta, ɗage mata gira yayi yana shirin haɗe bakinsu dan nuna farin cikinsa ga kyautar da yake tunanin Allah ya basu wayarsa ta fara karkar ɗin babureshin,kallon wayar ya yi sai yaga Ammi ce dan haka dole ya ɗaga yana mai daidaita muryarsa.

Daga can ɓangaren Ammi kuwa bayan ab ya ɗaga wayar kai tsaye ta shiga sanar dashi cewa, idan Zahra ta tashi ga bakuwa daga gidansu ta yi"ok ab ya fada yana kallon Zahra da har ta miƙe zaune dan taji abinda ammi ta ce.zaki iya fita?"ya tambayeta yana kallon fuskar ta dake a narke, gyada kanta ta yi tare da cewa,ai kace babu matsala ko?" Shima gida mata kan ya yi, hakan yasa ta dan tura bakinta gaba cikin ƙunƙuni take cewa "shi mutum kullum sai ya yi ta bada amsa da baki sai kace wani kurma, Allah idan bakin mutum ya yi ciwo kar ma ace da ruwan Zahra ehe" daga haka ta fice daga dakin bayan ta zura wata kyakkyawar abayarta me kama da alkyabba, murmushi kawai ya yi yana mai lumshe idanunsa yana hango zahda da turtsetsen ciki tana tafiya da kyar ga kuma dramar da za a sha a gefe.

Zahra na saukowa ta samu an haɗawa maman daddy kayan daɗi a gabanta sai loma take zubawa tana zuba surutu,tana ganin Zahra ta yi ɗif tare da gyara zamanta ta nutsu kamar ba ita ce ke zuba surutu ba,kai tsaye Zahra wajen Ammi ta nufa ta rungumeta tana cewa "nayi kewar jikin Ammina me sona Allah ya barminku iyayena masu kaunata"shafa kanta ammi ta yi tana cewa.

"my doughter ai Ni ka ɗai nasan tashin hankalin da na shiga na kwana ɗaya da yini dayan nan da baki tare damu, shi yasa bazan iya yafewa wanda su kayi mana wannan cutar ba" in sha Allah Ammina wai ina aunty Amira ne?"Zahra ta fada tana ɗorawa da tambayar Amira,dariya ammi ta yi kana ta ce,"Amira na tare da yayanku al'amin"dariya zahra ta kyalkyale da ita ba tare da ta ce komai ba ta maida dubanta kan maman daddy, gaisawa sukayi cikin mutunci kamar ba zahran yarbawa ba, wani lokacin idan ta yi abin hankali sai kayi ta kallonta kana mamaki kamar ba ita ba,tashi ammi ta yi tana cewa "Ni bari na baku waje naga baƙuwar tamu ta kasa sakewa" maman daddy a ranta take cewa, "ai sai na sake a gabanka ban sake a gaban zahla ba dan si zahla baya wasa bos ne",zahra ce ta katsewa maman daddy zancan zucinta ta hanyar tafa mata hannunta a fuska tana cewa "heee maman daddy me ye ne kike bin ammina da ido sai kace ɗan takwalam?" Ɗan sosa kai maman daddy ta yi tana kame_kame kafin ta samu abin cewa Zahra ta miƙa mata hannunta ba tare da ta ce komai ba,dake maman daddy tasan abinda Zahra ke nufi yasa kai tsaye ta fito da yar battar dake boye a jikinta ta miƙa mata, kana cikin sassauta murya ta ce,"gasi nan guda dari uku ne suri guda na samo maka" kin kyauta ina nan tafe da tukuicinki,Ni zan koma sama dan akwai abinda nake yi dan haka ki kwashe kayan da ba ki cinye ba kintafi dasu kya bawa su daddy" daga haka Zahra ta haye sama tana cewa siyam yau zaki gane baki da wayo wannan takun farko ne kafin mu kai ga na biyu".

Maman daddy kuwa tuni ta kwashe kayan arziki ta zuba a ledarta ta fice daga gidan tana fatan gobe ma Zahra ta kuma sa ta wani aikin, dan aikin Zahra tun kafin ta shiga gidan daula ma arziki ne bare kuma yanzu da ta shiga gidan da babu ce kawai babu a cikinsa.

Bash dai har yanzu yana cikin halin ciwo,yayin da Durga yake cikin halin hauka, yo hauka mana daga ganin yarinya matar mutane sai ka haukace a kanta kai baka yadda ba so, saboda zauncewar da ya yi har bai san ya dauko wayar Zahra ya kunna ba, take ya shiga gallery dinta yana kallon hotunanta da su kayi da ab wasu kuma ita kadai, ai take ya kuma haukacewa da tunanin ta yadda zai samu zahra ko ta halin ƙaƙa ne.......✍🏼

To malam Durga idan da rabon shan bugu ai bari bata magani.....

Doka doka doka

Kun sani idan baku gyara ba akwai matsala gaskiya ya kamata ace muna kare mutuncin junannmu a matsayinmu na manya ba ƙananan yara ba.

Idan kin san ba karanta yar GIDAN YARBAWA ne ya kawo ki ba ki hakura ki fita kullum ina fada da babbar murya amma duk da haka kamar bana faɗa,daga yau idan na fahimci ba shine ya kawoki to kiyi hakuri zaki ji waje na gaji da yin alkunya.

Wannan PG din na sadaukar dashi ga masoyan yar gidan yarbawa, musamman wadanda basa gajiya da yi min comments dan karfafa min gwiwa ina godiya Allah ya bar kauna da zumunci har aljanna🙏

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*