YAR GIDAN YARBAWA

Page61

by @zahrawriter12

Me nafef yana ajiye siyam ya ƙara gaba abinsa,ita kuwa tsayawa ta yi tana kallon dan ƙaramin gidan me ɗauke da ƙaramar ƙofa. kana kallon gidan kasan na marasa gaskiya ne dan hatta da network gidan baya dashi,cikin mutuwar jiki da raɗaɗin da take ji ajikinta kamar ƙaruwa yake yi ta nufi kofar tare da kwankwasawa,jim kaɗan taji Muryar Durga yana tambayarta waye?tsaki ta yi! tana cewa "wa kasan zaizo dan renin wayo?"murmushin mugunta ya saki yana buɗe kofar a ransa kuwa tausaya mata yake tunda ta riga ta shiga komarsa,matsawa ya yi gefe ta shiga gidan tana ƙare masa kallo, daki daya ne tak sai toilet, a dakin ma katifa ce guda daya sai wasu tarkacen bakko a gefe,rufe ƙofar ya yi ya bita yana kallon tafiyar da take yi wanda ya dauki hakan a matsayin renin hankali. kafin ya ce,"Ni zaki rainawa hankali zaki zo kina min wata tafiya ta yan shayi to ko me zaki zama wallahi sai na ɓaraki bani da wata damuwa haushin rashin Zahra zan wuce akanki"zaro ido ta yi cike da wata irin fargaba da tashin hankali har da dafe kirjinta,ta ce 'me kake nufi Durga?"abinda kika ji shi nake nufi".

Samun kanta ta yi ta tsugunawa a gabansa tare da ɗaga hannunta tana rokonsa. dan Allah Durga ka rufamin asiri wallahi idan kace zaka min wani abu yanzu to tabbas mutuwa zanyi saboda a halin yanzu ma ji na nake kamar gawa,kuma na tabbata aikin waccen tsinannniyar yarinyar Zahra c.....kafin ta rufe bakinta Durga ya wanke ta da wasu lafiyayyun maruka hagu da dama har hudu da kafcecen hannunsa me kama da itace,sai da siyam ta wuntsila ta kifa ta yi wata ƴar dungure me haniniya bakinta kuwa tuni ya fashe ya kama jini.nunata Durga ya yi da yatsa yana wani irin huci me zafi wanda ke nuna ainahin zafin zuciyarsa ta rashin imani ya ce "kar ki kuma zagin Zahra idan kuma kika kuma wallahi sai na kasheki a nan na binne gawarki ta yadda ko doyinki babu wanda zai ji".

Kafin siyam ta gama dawowa daga zafin mari tare da mamakin kalaman Durga tuni ya kwasheta kamar wata tsumma ya watsa saman katifarsa tare da bin bayanta,kuka take tana rokonsa da magiya amma Durga babu wannan imanin a ransa haka ya danneta ya yi mata kaca_kaca,tun tana kuka har ya zamana muryarta ta dashe sai wasu hawaye na tsananin nadama ,tasan cewa da bata sawa ranta tsanar Zahra da burin kasheta ba da yanzu tana rayuwarta lafiya. tunda ta sanadin haka ne Durga ya shiga rayuwarta,sai yanzu ta fara Allah wadai da irin zuciyarta me kafiya da rashin tawakkali.

Sai da Durga ya tabbatar da cewa ya yi wa siyam aikin da yasan har ta mutu ba zata manta dashi ba, sannan ya rabu da ita a lokacin kuwa sumanta na wajen biyar ne,duk sanda ta suman kuma azabace ke farfaɗo da ita.a haka Durga ya kwasheta kamar gawa ya fita da ita can baya inda ya aje motarsa ya sakata ciki sannan shima ya shiga ya ja ya nufi gidansu da ita.

A can kuma ɓangaren ƴansanda tuni bash ya basu tabbacin inda za su sami femi, sannan ya sanar da su harda siyam a cikinsu,dan haka kai tsaye a daren su ka yiwa gidan tsinke.

Lokacin da commissioner yake sanar da daddy abinda ya kawosu ba ƙaramin shock ya shiga ba,a lokacin baba talatu tana gyara dinning sai ko ta yi tsulum ta sa baki tana cewa "ai nasan a rina wallahi yarinyar nan Zahra yar kirkice dan na tabbatar da cewa tasan harda siyam aka sace ta amma ta yi shiru bata tona mata asiri ba, bayan irin abubuwan da suka dinga shukawa tana rufa musu asiri ammma duk hakan bai zama ishara a garesu ba. nan dai ta kwashe duk abinda ke faruwa a gidan ta sanar dasu da yadda Zahra ta dinga karesu daga cin gubar da su mama suke zuba musu da horon da take musu ba tare da kowa ya sani ba,jinjina kai kawai Abba da ammi suke yi cike da ƙaunar Zahra da kuma mamakin yar uwarsa da take ƙoƙarin kasheshi.

Mama kuwa tana laɓe tana jin abinda ke faruwa ,saboda tsananin tashin hankalin asirinta ya tonu wanda bata taɓa zaton haka ba yasa ta sakin gudawa daga inda takez jikinta kuwa banda kyarma ba abinda yake yi,komawa ɗaki ta yi ba tare da ta damu da gudawar jikinta ba,ta shiga neman hanyar guduwa sai dai ina ta makara tunda gaba ɗaya gidan gewaye yake da ƴan sanda,tana fitowa kuwa suka yi ram da ita tana ihu tana komai suka cusata a mota.

Dai-dai lokacin Durga ya tsaya da motarsa a gefen mention din,ba tare da ya fito ba ya watso siyam daga cikin motar,aiko ƴan sanda suka bisa da mugun gudu suna harbin motarsa amma ina tuni Durga yayi musu shal, sai dai kuma yana fita Babban titin a ƙoƙarinsa na kauncewa harbin da ƴan sanda suke masa yasha gaban wata ƙatuwar tifa wanda lokaci ɗaya ta yi awan gaba dashi, take kansa ya rabe biyu ko shurawa bai yi ba ya ce ga garinku nan.

Ƴan sanda na ganin haka suka juya da kotarsu ba tare da ko wajen sun ƙarasa ba,siyam suka kwasa suka wuce da ita asibiti in da Adebayo yake itama suka barta anan a ƙarƙashin kulawar ƴan sanda,

Mama kuwa saida wata yar sanda ta daka mata tsawa sannan ta daina ihun da take yi,gashi duk ta cika su da warin gudawarta dan haka sai hantararta suke yi.

Daddy ne yasa kiran AB, yana dagawa ya ce,yazo kasa yana nemansa da shi da Zahra,lokavin Zahra na jikinsa tana ta sakalci iri iri shi kuma yana biyeta kamar wata ƙwai,hijab ya saka mata akan kayan baccin dake jikinta sannan yaja hannunta suka fito falon ƙasan,suna zuwa Ammi ta kamo Zahra tare da rungumeta tana sa mata albarka, Zahra da ab basu san me yake faruwa ba sai da daddy ya sanar dasu abinda ke faruwa,daga nan ya dora da sawa zahra albarka akan hadaruruwan da ta tsallake a gidan ba tare da su sun sani ba,sosai suka kuma ganin kimarta da mutumcinta, shi kansa ab ya jinjina mata da ganin jarumtarta darajarta da ƙaunarta sun kuma nunkuwa a zuciyarsa da rayuwarsa gaba daya.da wannan suka rufe babin su siyam wanda karshensu bai yi kyau ba, son zuciyarsu ya kaisu ya baro, sai dai mu ci gaba da addu'a akan neman tsari da sheɗan.

Suna komawa sama Zahra ta rungume ab tana cewa "yaya AB ku daina min godiya nice ya kamata na yi muku godiya saboda inganta rayuwata da ta iyayena da kuka yi dan haka babu abinda zan iya biyanka dashi sai dai addu'a Allah ya faranta maka fiye da yadda ka ke faranta min my hot" ta ƙare maganar da bashi kyakkyawar sumba a lips dinsa,tana ƙoƙarin cire bakinta shi kuma ya ce bai san zancen ba dan riƙe bakinta ya yi yana ci gaba da yin yadda yaso dashi,bata tsaya sanya ba wajen miƙa masa ragamar rayuwarta domin danshi a kayi ta komai nata nasa ne. sosai ta zage ta faranta masa wanda hakan ya kuma ƙara janyo mata ƙauna me tarin yawa wadda bata da iyaka a wajen Sarkinnata.

Washe gari Zahra ta ɗira masa rigima akan sai ya kaita taga sabon gidansu,babu yadda ya iya da rigimar Zahra dole haka ya kaita da kansa, kuma ya rakata har cikin falon suka gaisa da su mama wadda ta yi shar da ita kamar dama ta jima a gidan, daga nan Jafar da josuwa suka karaso suka wuce hospital.

Zahra ta dubi mama ta ce,ina Abba Ni ban fansa ba ko har fita?"Mami zainab ta ce,ya za ayi kiga yaya bayan ya samu gurbin aiki me matsayi a Companyn mijinki, wallahi Zahra ki godewa Allah saboda a wannan zamanin samun miji irin su ab ba karamin aiki ba ne,nasan dai zuwa yanzu kin fahimci illar tsananta tsana ko da kuma yiwa mutane kudin goro"

Jinjina kai Zahra ta yi kana ta ɗan tura baki sai kuma ta nutsu kamar gaske ta ce,mamina ai tuni na sauke wannan a ƙidar dan ko ba akan ahlin ab ba na koyi darasi akan yarbawan gidanmu saboda duk abinda nake musu basu taba nuna min tsana ba hasalima duk sanda nake bukatar taimako su nake nema mu kashe mu binne ba tare da kowa ya ji ba,na fahimci cewa a ko wane yare a ko wane ƙabila da jinsi a kwai mutane kala_kala masu hali kala kala na fahimci cewa ba a yankewa mutum hukunci da dabi un wasu daga cikin jinsinsu dan ko ina akwai na kirki akwai kuma akasin haka,tunda yanzu ai kinga mutanen da suka saceni a cikinsu akwai mabanbanta yaruka yarbawa uku ne a cikinsu shi kuma durga da bashir duk hausawa ne kinga kuwa ashe ba yare daya ne masu dabi mu Shedan ba,ga kuma yaya AB dina shima bayerabe ne amma ya banbanta da ko wane bayerabe domin shi ɗin na musammanne saboda zahrarsa ma ta musammance haka mafarin soyayyarsu ta musammance karshenta ma zai zama na musamman saboda tare zamu mutu in sha Allah"rike baki mama ta yi kafin ta ce ey lallai rashin kunyarki ma ta musammance"al Amin da Habib da suke shigowa suka hada baki wajen cewa autarmu da sakalcinta shima na musammanne tare da Babyn da zata haifa mana duka na musamman ne"dukansu dariya suka sa Mami zainab ta ce,to alhamdulillah tunda kin fahimci abinda kullum muke son fahimtar da ke"al'amin ya ce, Finally yau Zahra ƳAR GiDAN YARBAWA ta zama matar BEYERABE surukar BEYERABE kuma ƙawar YARBAWA",dariya aka kuma sawa a nan dai Zahra ta wuni cikin ƴan uwanta da iyayenta ana ta lelenta, kaka kuwa babu abinda bata shirya mata irin na masu ciki ba kowa son faranta mata yake.

Sai dare AB ya zo ya tafi da sarauniyarsa.

Bayan kwana biyu Ade ya dawo hayyacinsa har yana iya bude baki ya yi magana,dan haka Zahra da kanta ta kira lola ta sanar da ita komai tare da bata umarnin zuwa duba aden a can asibitin da suke,sosai lola ta yi kuka ta kuma yi tur da hali irin na Ade dama basu taɓa haihuwa da shi ba, dan haka ta shirya ta je har asibiti ta ce ya saketa taje ta auri wanda rayuwarsu zata yi daidai ba kwarto dan kidnapped irinsa ba,babu wani ja ya sake ta ɗan shi kansa yasa idan bai sake ta ba to tabbas ya cutar da ita tunda dai shi a halin yanzu ya gama tashi daga aiki.

Itama siyam an samu ta farfaɗo amma ta zama kamar wata mahaukaciya surutai kawai take wanda dole sai da aka danganata da gidan masu taɓin kai dan abinnata ci gaba ya dinga yi.

Mama da su bash tuni a ka mikasu kotu aka yankewa kowa hukunci dai-dai da laifin da ya aikata,mama tamkar zata yi hauka saboda kuka da kururuwa, duka yan uwanta sun tausaya mata amma babu yadda su ka iya son zuciyarta ne yaja mata.

Femi ma dai karshe kukan na dama ta yi saboda babu wani nata da yazo kotun bare ta sa ran za ayi mata kallon tausayi, a haka aka tasa keyarsu zuwa makomarsu ta duniya.

Bayan sati biyu da lafawar komai,Zahra ce ta shigo dakin AB inda fa samesa saman sallaya ya isar da sallar nafila yana addu'a hannunsa a sama,tsayawa ta yi da dan cikinta da ya fara bayyana tana kallon bakinsa dan son fahimtar abinda yake roka.

Ab bai san hawa ba bai san sauka ba sai jin ihu kukan Zahra da danbarwarta ya yi saman kansa,cikin sauri ya shafa addu'ar ya mike tare da nufarta,ya riƙeta yana tambayarta lafiya,amma ina so take kawai ya saketa ta cigaba da jijjiga jikinta kamar yadda ta saba wanda shi kuma hakan yake matuƙar tsoro......✍🏼

Muje PG na gaba kuma na karshe in sha Allah dan jin kukan me Zahra da ba ta rabo da sakalci take yi,

Jiya banga comments na pg 60 ba ko guda duk da ina cikin halin rashin lafiya na yi muku,to ga na yau nan shima dai a daddafen na gama.

[8/21, 9:14 PM] khalidunah@: *Typing*

💕

' **YAR GIDAN YARBAWA* 💕

*NA*

*FATIMA Y. ADAM*

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

***

*_____________________________________*