AISHATUL HUMAIRA (Labarin Indo)

004

by @queenie

Indo tin sanda ta fito daga gida har akai sallar laasar amma bata koma ba tana nan tana gantali da su habi, gaba daya kudinne da aka samo indo tace ita za'a bawa, dole sunaji suna gani suka bar mata akan gobe da sassafe za a fara rabon kayan ajo, al'adar kauyen kenan.
Tafiya takeda dan karanta tanayi tana wakarta ta karkara, Kabiru ne ya hango ta a take ya fara yankare hakora, tin daga nesa ta hangosa tassn me yake nufi, karasa wa tayi tana tsalle tana dariya tace "aa kabiru sannunka wannnan kajinfa, mika mata yayi yace" dama na inna ne zanje na saida mata su a kasuwa, karba tayi ta duba sai da ta samu katuwar ciki sannan ta karbe ta tace "to maza jeka na karbi wannan, dole yanaji yana gani indo ta karbe kazar ba damar yayi magana ta dankara masa wulakanci, shikuma gashi yana son indo bazai iya hana ta ba.
Kofar gidan su salame ta tsaya, sai kuma ta shiga ba wanda tayiwa magana ta tafi neman wuka, sai da tasha fama sannan ta samo wukan, tare da danne kazar ta yankata,dik wannan dramer a gaban uwar salame da salame domin su yanzu tsoron indo sukeji, sun kaita kara amma mai gari ya tashi kafa da targade, idan ba sa'a ba aljanun indo ne suka ligudesa, salame ce ke magana kasa², juyowa tayi tana kallon salame, sai kuma taga tayi tsitt.Tana gama yankawa ta bar musu wukar anan ta tafi abinta, gida ta shiga tana wakar samun nasara, iyalle ce ita kadai tana jan carbi, muryar indo ce ta katse ta, da take fadin ina Kawu garba ne iyalle, amsa ta bata da "ya tafi birni sai gobe zai dawo, bata kara magana ba sai madafa ta shige, ruwan zafin dake tukunya ta juyo ta zauna ta fige kazarta, sai kuma ta zabura ta mike, iyalle ki karasa min wannan aikin ki dafa min ita, ki tabbata taji daddawa yanzun nan zan dawo da gudu ta fice daga gidan.
Iyalle ce ta bita da addua'ar samun shiriya, domin ita abin ma damunta yake, ta rasa yadda zatayi da indo, kwata kwata bata biyo mai halin nata ba, amma zan san yadda zanyi, mikewa tayi ta fara kokarin aikin dan ta riga da tasan halin indo ba mutunci gareta ba, yanzu sai taja za mata asara.
Fitarta da tayi tinawa da tayi da gidan su dije da yake sunje karbar kudin ajo, taga suna dafa taliya da manja, gidan ta shiga tana haki tana kallonsu, cikin bacin rai ta fara fadin na rantse m
da allah dik wanda ya cinye taliyar nan bai bani ba wallahi wallahi yau sai na muku bakin aiki, yayan dije ne ya fito daga daki yana fadin ke"oh wai taliya to mun cinye kiyi dik abinda zakayi, cike da fada tace kai "katon banza badakai nake ba, duka ya kai mata ta goce ta nufi randar dake karkashin bishiya, wani katon icce ta daga ta sauke musu a lokacin suka tarwatse, wannan karar ce yayi sanadiyyar fitowar dije daga daki dauke da kwanon taliya.
Indo ce ta kalle tace "wato tsabar mugunta da ga taliyar amma kika hanani ko, wartar kwanon tayi tana zama akan kujerar katako, ta fara zuba taliyar, yayan dije ne yayo kanta, ya sakar mata dundu, amma ko a jikinta, ci gaba tayi da cin taliyarta, sai da ta gama sannan ta dago tace ka tabbata sai na rama. Ke kuma dije "wallahi sai na ci mutuncin ki da kin rage taliyar amma shi ne kika barni nazo ina hayaniya, maza samomin ruwa nasha, dije ta rasa ya zatayi sai can ta nemo wani a kofi ta bata tana sha ta mike tabar gidan. 
Ganin ta cika cikinta ne yasata yin hanyar gida domin zuwa ta cinye sauran kazar da iyalle ta dafa mata, tin daga kofar gida ta ke jiyo hayaniya, hakan ya tabbatar mata da muryar innar kabiru data kwacewa kaza, hakan yasata kama katanga tabi ta wajen rumbu, iyalle na can tana bata baki ta zagayo ta juye kazarta a roba ta mai da tukunyar, fakar idanunsu tai ta shige bukkarta.Iyalle da kyar ta bata baki akan a bata kazarta, tana dakko tukunyar kazar taji ba kaza ba alamunta, inna ce ke banbami akan a fito mata da kazarta, indo na daki tana jinsu.