AISHATUL HUMAIRA (Labarin Indo)

005

by @queenie

Sai da ta tabbatar da tafiyar inna tana ta zuba allah ya isa sannan ta fito da robar, abin mamaki gaba daya ta cinye naman saura tsoka daya data rage, mikawa iyalle tayi sannan ta fice daga gidan tana wakarta.Dandali ta tafi a can taga tarin yammata da samari, wata kawar habi amarya ce da batasan halin indo ba ta matso kusa da ita tare da shako wuyanta, "ke uban waye yace ki karbi kudin ajo. Kuma kice bazakiyi a yau ba sai gobe, kallon ta tayi sororo tana mata dariya, yayin da dsukacin mutanen wajen ke cewa ki saketa, tsaki taja tana fadin aikin banza ni har wannan zanji tsoro, yarinya yar ficika da ita sai iskancin,bata karasa va taji wani shahararren mari akan kuncinta, wanda ya dauke mata gani na wani. Lokaci.Indo ce ta kalleta tace ubanki ne mana shegiya mai siffar aljanu kawai, kuma wallahi bazan bayar da kudin ajon ba, ke kuma habi kisan yadda zakiyi dasu, kinsan hali na ko to na cinye bazan badaba, habi ce ta durkusa a kasa tana rokon indo akan ta taimaka ta bata kudin amma ina fafur ta hana.Kabiru ta hango take ta tino da abinda ya faru a gida, karasawa tayi tana masa kallon sai naci ubanka, cike da fishi tace"kai kabiru wato baka da mutunci ko kai ga gagararre, to tsugunna anan ko kuma wallahi yanzu na shemar da kai, ba yanda ya iya dole haka ya tsugguna yana jiran hukuncinsa, dan ya tabbatar inna taje gidan su indo,"dan allah indo kiyi hakuri, tsaki taja tace kai dallah rufemin baki shashasha kawai maza ci gaba da tsugunno.Ke kuma maai suffar Aljanu me kike cewa, kodan dik ba wannan ba idan kina da karfi, zoki kwata, daga haka ta juya, domin jinta take kamar zata iya dukan mutum 30 dan fishin da take ciki, kamar abin arziki ta je gida, bokiti ta dsuka ta tafi rafin dan marka, debo ruwa ta farayi tana zubawa a gida, sai da ta cika ko'ina sannan ta koma rafin, wani dan kulli naga ta fito dashi daga jikin skirt dinta da daita da buje dik daya, cikin dan lokaci ta watsa shi dika.Tashi tayi maimakon ta tafi gida sai ta nufi bayan gidan su habi, shukar masara ce a wajen ta fara fitowa, cikin dan lokaci ta gama cireta tsabb, sannan tabi gonakin dake kauyen dik ta ciccire shukokin harda ta gidansu ma kuwa, maimakon ta tafi gida ta kwanta dan 11 ai ta riga datayi, aa sai tai hanyar gidan su dije, dakin yayan dije ta shiga wanda yayi mata rashin mutunci dazu lawan, ganin yana sharar bacci ne yasa ta janyo wani kyalle ta rufe masa baki, wata bulalace da bansan a inda ta samota ba ne ta fito da ita, lokaci kankane ta fara sharba masa, ihu yake amma bakajin komai sai guri, sai wasu uban hawaye dake zuba a idanunsa, wani kullin kuma naga ta fito da shi, debowa tayi ta watsa masa a ido, sannan tai sadaf sadaf ta fice daga gidan ba wanda ya jita.Safiyar yau bata tashi da wuri ba, tana tashi makewayi ta shiga, ruwa ta diba a baho tana shiga ta watsa ta fito, bukkarta ta koma ta dauki kayanta da dik sunyi ja ta saka, sanan ta zauna ta janyo kayan kwalliyarta, kallon mudubi tayi yayin data dakko wata uwar hoda ta fara shafawa a take fuskarta ta rine ta koma jawur kamar me, kwalli ta saka hade da jagira, kallon kanta tayi a mudubi tace "oh ashe nima dai kyakkyawace, fara ce tarr ko duhu batayi ba, ga wani uban gashi tuli guda a kanta, da farko na dauka na doki ne sai daga baya nai tinanin gashin fulani, siririn hanci ne da ita sai dan karamin baki, kallo daya ya ishi ka gane cewa eaa lalle wannan jinin fulani ce.Bakin kwallin ta dauka ta shafa a bakinta, sannan ta fito ta tarar da iyalle, bani abinci na, abinda ta furta kenan, iyalle ce tace "ke kika debo ruwa jiya indo, aa tace sai kuma tace anya iyalle ba aljanun bishiyar nan bane, zama tayi ta cinye tass ta sha ruwa, allonta t adauka tace 'iyalle na tafi makaranta daga nan ta fice.Tafiya take tin fitowarta take jin ana maganar rafin dan marka ya baci amma ita kam ko a jikinta, dariya takeyi tana tafiya, tana zuwa makaranta gaban malamin taje ta tsugunna ta gaisheshi"malam iliya dan me karfi ina kwana da lafiya ya amsa yaci gaba da karatu, tashi tayi ta nemi wajen zama.