BAUTAR ZUCI

010

by @queenwaleedah51




Yau aka sallamo ummi daga asibiti ya kama yau litinin yau ce ranar da za'a karb'i kud'in auren falmata, falmata dik wannan abin da ake bata sani ba, domin bata magana da kowa bare ta samu labari.

Umma na zaune sai tace"bara kiga na tashi na lek'a ummi saboda na san yanayin jikin nata ya yake, tashinta hakan yasa wata baquwarta shigowa ta fasa fitar.

Khalil ne zaune a bakin layinsu, abonkinsa munir ne ya k'araso bayan ya bashi hannu sun gaisa.

"ya dai mutumina naga dik kayi wani la'asar, d'ago da kansa yayi ya kalli munir wanda yake masa magana.

Sosa girar sa yayi ya sauke numfashi ya fuskanci munir.

" Bazaka gane ba munnir, yau kwana nawa da birthday Amir, wallahi tin ranar ban saka falmata a ido na ba.

" ai lefinka ne da zaka d' aga hannu ka daketa, dama kasan irin wannan matan ai ba kalar duka bane, kalar lallab'awa ne da tarairaya.

"munir wallahi son da falmata take min nasan so ne na zahiri, na rasa ya akayi ta kasa zuwa inda nake, sam zuciyarta ba zatayi mana shamaki ba, sai dai ko wani babban abu, kai falmata ko da rashin lafiya take sai tazo ta ganni, tabbas akwai wani abu.

" Sai kaje gidan su ka duba, munnir ya fad'a yana zaro wayarsa yana dannawa.

Shiru khalil yayi yana nazarin yadda zaiyi yaga falmata a yau.

Ameera ce ta k'araso bakin layin nasu, kallon khalil tayi wanda yake cakud'a sumar kansa. 

"besty ka tashi ko, tin d'azu na gama gyara maka room d'in, amma wannan jakar ta wacece kenan. 

D'ago da jakar tayi, jakar falmata ce ta makaranta, har da kaya kala 1 a ciki. 

" meerah please ki mai da jakar inda take, zanyi miki bayani jeki daga nan ki rufe room d'in kizo. 

Bata ce da shi komai taje tayi abinda ya umarce ta sannan ta dawo.

__----___

Ba laifi ummi jikin nata da sauki domin yanzu ma tana zaune tana cin abinci.

Sallamar ummar falmata ce yasa ta d'ago kai tana kallon ta da murmushi a fuskarta.

"eyee a'a lallai su ummi jiki yayi sauji, har da cin abinci, murmushi ummi tayi tana cigaba da cin abincinta.

Waje umma ta samu ta zauna suka fara gaisawa da maman ummi.

Falmata kuwa kamar jira take umma ta fita, a sad'ad'e ta fito daga d'aki da hijabinta a hannu.

Almajirinsu wanda yau ya shigo yi musu aikace aikace ne y ganta, ko kallonsa batayi ba ta sa k'afa ta huce ta bar gidan.

Tafiya take tana hard'ewa, ko ina ta samu cilla k'afarta takeyi domin yau burinta kawai taga khalil ko zataji sanyi a ranta.

Daidai kofar Shagon sa anan ta tsaya, idanun ta kwalla ce ta taru, ba komai idanunta suka gane mata sai khalil rungume da ameerah, wani irin numfashi ta sauke ta ke a wajen ta sulale ta fad'i k'asa.

A zaune taje, wanda hakan yaja hankalin khalil, sakin ameerah yayi yace"kije gida zanzo anjima.

Wani irin kallo tabi falmata da shi sai kuma ta dubeta taja tsaki. Khalil ta kalla tana masa kallon up and down.

"amma ka bani mamaki besty, yanzu akan wannan kucakaar kake wannan rawar jikin, ashe gaskiyar amir mana da yace kana sonta kawai boyewa kake, ita kuma da yake allah bai dasa mata zuciya a jikinta ba, har da wani biyosa, banza ye kawai.

Hucewarta tayi fuuu ta bar wajen.

Khalil ne ya k'arasa ya mikar da ita tsaye, shagon sa ya shigar da ita, hannunta ya kama yana murzawa, hawayen da suka zubo mata ne ya share mata.

"khalil why, kasan irin son da nake maka kuwa, khalil ina sonka, amma ka kasa fahimta, kullin nazo sai na ganka da wata, na kasa had'a soyayyarka da ta kowa, na kasa wallahi.

" Falmata dole ki ganni da mata, saboda ni namiji ne, kuma ki sani idan har naga wata to tabbas ne idan tayi mini na bita, ni badan ke kadai akayi ni ba, ni anyi ne dan maata hud'u.

D'ago jajayen idanunta tayi tana kallon bakinsa.

" Me yasa kwana biyu baki zo ba? Ya cillo mata tambayar.

" An hanani, an gane ina zuwa wajenka, kuma baba ya saka mini dokar fita, ko makaranta an hanani zuwa, yanzu ma ba kowa a gidan na taso na taho nan, so nake ma na koma da wuri kar umma ta koma gidan.

" Yanzu a haka zaki tafi ki barni kenan falmata, nayi kewarki fa sosai.

" To khalil me zan maka kuma, ta tambaya. 

"Bakomai shikenan lalubawa yayi k'asna filo, wata waya ya mik'o mata itel.

" karb'i ma dinga magana da ke kinji, ki boyeta zan na kiranki, zan saka miki kati mai yawa mu rinka text message, sannan kuma zan ci gaba da bibiyar lamarin naji ko.

Murmushi tayi sai kuma naga ta rungumesa.

" Ina sonka khalil, banajin akwai wanda ya isa ya rabani da kai, domin soyayyar da nake maka ta dabance, jinta nake tana ratsa gabobin jikina.

Sakin sa tayi ta fito daga d'akin tana faman sauri ta k'arasa gida.